Halysaah Page 91 By Khaleesat Haydar
HALYSAAH PAGE 91…Nenne ta jawo handbag din Khaleesat bayan ta ajiye maficin da take yi ma Khaleesat din fiffita da shi ta bude jakar ta ciro wayar sannan ta fara tashinta tana cewa “Ga wayarki na ta ruri ki duba ko kira ne, kila ma Ahamad din ne” Khaleesat ta juya ma Nenne baya taki bude idonta kuma taki cewa komai don wani azababben ciwo kanta ke mata, Aunty Murja ce ta shigo dakin tace “Nenne ai da kin bar ta tayi baccin tunda bata jin dadi, kuma har da gajiyan hanya ma” Nenne tace “Ƙudajen nan naki ai ba bari za su yi tayi baccin cikin dadin rai ba, na tambayeki ko kiwon su kike kince A’a, banda ma ina korasu da mafici ai dakin bazai zaunu ba, ke dai kina da tsaftarki da sai ince kazanta ce ta kawo maki su, ina Parida ta zo ta duba ko kiran waya ne, tun daxu wayar ke ruri” Aunty Farida ce ta shigo dakin Nenne tayi maza ta mika mata wayar tace “Gashi yana ruri duba ko kira ne” Aunty Farida ta amshi wayar taga Jay ke kira, Aunty Farida tace “Jawwad ke kiranta” Nenne tace “Waye Jawwal, ko Ahamad din?” Aunty Farida tace “Eh shi ne” Da sauri Nenne tace “To ɗaga mana Parida, tun daxu fa yake ta kira, ki daga ki ce masa bata jin dadi tun da muka sauka Bauchi, yanxu haka a kwance take, kar ya ga an masa walakanci, maza ki ɗaga don Allah” Aunty Farida tayi murmushi ganin seriousness din Nenne, fita tayi daga dakin ta daga kiran, bayan kusan minti biyu ta dawo dakin tana kallon Aunty Murja tace “Wai gashi ki masa kwatancen nan din Aunty Murja” Aunty Murja ta amshi wayar, Nenne dai sai murmushi take har Aunty Murja ta gama yi masa kwatancen ta mika ma Aunty Farida wayar, bayan Aunty Farida ta katse wayar Nenne tace “To kun ga ai gwara haka, ai shi ma ɗan Bauchi ne, yaro me kirki ga hankali da nutsuwa” Aunty Murja ta mike tace “Allah sarki, Allah Ubangiji ya saka masa da alkhairi, to yanxu Nenne a dora tuwo ko kuma shinkafar za a sake maku naga yamma ya gabato” Nenne ta kalli Aunty Farida tace “Gwara ki hura iccen Parida tayi mana girkin ke kuma ki ji da yaranki kawai…” Nenne bata rufe baki ba sai ga yarinyar Aunty Murja me Cerebral palsy tana rarrafowa zata shigo dakin, Nenne tayi wani ihu tana yarfa mata mafici da sauri tana cewa “Tafi, tafi ki je can kofar gida, fitaa….” Aunty Farida ta ɓata rai tana kallon Nenne tace “Haba Nenne meye haka?” Nenne ta wani kalleta tace “Haɓa Nenne? Aljanu fa suka maida mata halittar ta haka tana dalalar da yawu, in bance ta fita ba me zance? Me zata shigo tayi cikinmu idan ba neman magana ba, ai laifin Murjan ne da take barin ta a sake, nace ta dinga daureta ko jikin bishiyar tsakar gidan nan nasu ne taki ji, ai ba a bari su shigo cikin mutane babu kyau haka, sa’ar su Islam ne fa amma ku dubeta kamar er shekara shidda in ba aljanu ba wa za su yi haka, su suka shafeta a ranan da aka haifeta” Ita dai Aunty Murja tayi shiru bata ce komai ba tana ɗan murmushi, Aunty Farida ta mike ta ɗaga yarinyar suka bar wajen, duk da ciwon kai da ya saka Khaleesat a gaba ga wani tashi da zuciyarta yake tun bayan da Nenne ta tilastata ta sha fura da Nonon da aka kawo masu daxu amma haka nan ta daure ta mike zaune tana ma Nenne wani kallo tace “To wai Nenne ita ba mutum bace kamar kowa? Wa ye yace maki aljanu ne suka shafeta? Tunda ba karatu kika yi ba ai baza ki san meye matsalar ta ba, ita da gidansu kuma ki dinga korarta bayan wajen Mamarta take son zuwa” Nenne tace “Ni bazan biye ki ba kiji da ciwon kan da ya saka ki gaba, mu zamaninmu yaushe za a bar irin wannan yarinya ta shigo cikin mutane, ai boye irinsu ake, ko a kai su wajen mai magani a bar su can, nono uwar zata bata da zata wani rarrafo ta biyo ta” Aunty Murja dake ta murmushi har sannan ta mike tace “Bari in hura abun girkin Nenne” Daga haka ta fita daga dakin, Khaleesat tace “Wallahi ki dena haka Nenne babu kyau, ita ma mutum ce kamar kowa kawai lalura Allah ya jarabceta da shi tun daga wajen haihuwa, yanxu duk an dena kalan wannan tunanin naku na mutanen da, kai ya waye, yara masu lalura haka jan su ake a jiki suna bukatar kulawa da soyayya ba tsangwama ba, Aunty Murjan ma ai bazata ji dadi yanda kike ma yarinyar ba” A fusace Nenne tace “Zamaninmu daban naku daban, mu dai mun san ‘yan ruwa ake haifowa haka ko kuma wa enda aljanu suka shafa tun a cikin uwarsu” Komawa Khaleesat tayi ta kwanta don bata da strength din ci gaba da magana ga tashi da zuciyarta ke yi…. Karfe biyar da minti arba’in Khaleesat ta mike zaune da kyar ta dalilin tashinta da Nenne ke yi babu kakkautawa gashi ta samu bacci ya dauketa, Nenne na mika mata wayar da sauri tace “Maza daga kiran, kilan shi ne ya iso” Khaleesat ta amshi wayar taga Housemate dinta ke kiranta, komawa tayi ta kwanta tayi picking call din yace “Halysaah” Da kyar tace “Uhm” Yace “Are you still sleeping?” A hankali tace “Na tashi” Yace “How are you feeling now?” Tace “Uhm” Yace “Ina Aunt dinki da tayi mana kwatance daxu?” Khaleesat ta mika ma Nenne wayar tace “Aunty Murja zai yi magana da” Da sauri Nenne ta mike ta fita daga dakin da wayar tana cewa “To bara a kai mata, suna can sun daura mana sanwa da Parida” Bayan minti goma yaron Kishiyar Aunty Murja ya dawo tare da su Jay bayan yaje ya taro su, daurewa Khaleesat tayi ta mike ta dau Hijab dinta ta saka don Nenne takura ta tayi wai gasu can kofar gida ta tashi taje, tana fita waje taga Ride me suna ride da suka zo da shi, tana tafiya a hankali ta karasa har kusa da motar, Jay ya sauke glass din motar yana zaune front seat yana kallonta, ta kallesa shi da Ajay sannan ta jingina jikin motar don har ta gaji ɗan tafiyar nan da tayi, ya bude motar ya sauka yana kallonta yace “Halysaah” Ta ɗaga idanuwanta ta kallesa, yace “Me yasa kike damun kanki haka?” Ɗan murmushi tayi tace “Nace maka kaina ke min ciwo, kuma na gaji” Yace “Amma ai da wuri ku ka iso Bauchi” Ita dai ta sauke idonta tayi shiru bata ce komai ba, yace “Kin ci abinci?” Gyada masa kai tayi duk da bata iya ta ci komai ba sai fura kadan daxu, yace “Ohk bari mu duba pharmacy so I can get you some drugs, ki koma ciki, idan mun dawo zan kira ki….” Ta gyada masa kai ta fara tafiya a hankali ta shiga gidansu Aunty Murja, Jay ya koma cikin motar yana kallon Ajay yace “She is not feeling fine, mu ɗan duba ko za mu samu pharmacy a nan in siya mata magani” Ajay dai bai ce masa komai ba ya tada motar ya fara reverse. Bayan minti arba’in suka dawo Jay ya sake kiranta ta fito, Shopping yayi mata na abubuwan da zata bukata irin pack din bottle water, drinks, costly cookies,, Sae gwangwanin powdered milk da Milo with sugar, da carton din Indomie, bread ma manya uku ya siya da Butter, a gefe kuma ga kwai, duk dai wani abu da zai sa ta zama comfortable a gidan duk da bai san kwanaki nawa zasu yi ba, sannan ya siya ne not for only her to use, ya kuma siya masu abinci a restaurant pack biyar da gasassun kaji, Ita dai Khaleesat na jingine jikin motar ta ma rasa abinda zata ce har yara suka gama shiga gidan da kayayyakin, ya mika mata ledan drugs din yace “You check the prescription idan kin ci abinci sai ki sha” Cikin sanyin murya tace “Thank you so much, Allah ya saka da alkhairi” Ya wani kalleta, ita ma dai kallonsa kawai take ɗan tsayuwar nan da tayi har ta gaji, yayi kasa da murya yace “Pls Halysaah in sha Allah komai zai wuce ki dena saka ma kanki damuwa, i am assuring you babu abinda ya isa ya maki don ya gama samun nasara kuma a kanki, ki kwantar da hankalin ki and trust my words” Ɗan murmushi kawai tayi bata ce komai ba, yace “Go get some rest, ki ce da Kaka in sha Allah za mu dawo gobe yanxu Magrib ya gabato shi yasa baza mu shiga mu gaisheta ba, from our place to here is almost 45 minutes ride” Khaleesat ta ɗan bude ido cikin sanyin murya tace “Da nisa ashe” Ya ɗan yi murmushi yace “May be mu zo around 11 in the morning gobe” Tace “To Allah ya kai mu” Yace “Ameen, in kin ji zaki Iya magana anjima ki kirani, bana son in kira kina bacci kaka ta tashe ki” Tana murmushi ta gyada masa kai sannan ta ɗaga masa hannu alamar Bye bye ta juya ta wuce cikin gidan, Jay ya shiga mota yana kallon Ajay yace “Common ya jiki baza ka iya yi mata ba alhalin idan ita ce sai ta maka ya jiki ko baza ka amsa ba” Ajay ya kallesa yace “Dama bata da lafiya ne?” Banza Jay yayi masa don shi ne ma ya hado mata maganin a Pharmacy shi kuma ya shiga yayi shopping wanda duk da Atm card din Ajay din suka yi duk siyayyar don shi ya mance nasa a gida amma yake masa tambayar rainin wayo yanxu….. Washegari karfe takwas da rabi Jay ya kira wayar Khaleesat, Nenne dake ta tambayar wanene bayan Aunty Farida ta sanar mata Jay ne tace “Ɗaga ki bani shi” Aunty Farida tace “Ki ce masa me, bari dai in daga tunda bacci take” A fusace Nenne tace “Ki bani nace, ke komai sai kin nuna iyawa” Aunty Farida ta kyabe baki tayi picking call din ta mika mata, Nenne ta doka sallama tace “Ina kwana Ahamad” Jay na jin muryarta ya gaisheta cikin ladabi, ta amsa tace “Wallahi in gaya maka jiya dai ba mu yi baccin kirki ba, jikin nata ba dadi, dama tana dadewa ita bata yi ciwo ba amma in ta tashi yi ba kyau, da ta sha magungunan kamar zazzabin ya sauka sai kuma ya dawo da karfinsa, dama jiya muna mota zuwa garin nan sau biyu tayi amai, to daren jiya ma tayi sau biyu, gashi taki cin komai har shayi an ƙada mata ta kasa sha” Jay dake ta sauraronta duk sai yaji a hankalinsa ya tashi, a hankali yace “Toh ina ga za a hada mata da allurai Kaka…” Nenne tace “Atoh, ni na rasa kan ciwon nata…” Yace “Yanxu za mu taho in sha Allah” Nenne tace “Toh Allah ya kawo ka lafiya Ahamad” Bayan Nenne taji shiru alamar ya katse wayar ta ajiye tana kallon Aunty Murja tace “Lafiyan Allah take da, daga sanda iyayen tsinannen yaron can Awdul suka turo barayin gwamnati da daddare wajen Ali shikenan ta birkice, ba komai ne ya ja mata wannan ciwo ba sai damuwa, ta saka ma ranta damuwar abun sosai ba kadan ba, ba dole ta damu ba tunda ita tasan ukuban da ta sha gidan Awdul don bai da kunya ya kuma dawowa yace ga zance ga magana, in sha Allahu karshensa ne ya zo, in ma yana da mugun nufi ne a kanta to ga dai ta a Bauchi bazai kuma taɓa sanin inda take ba” Aunty Murja ta sauke ajiyar zuciya tace “Abun kam babu dadi, Kuma Allah ya fi sa, babu abinda ya isa ya mata wanda Allah bai yi mata ba” Nenne tace “Maza ku tashi ku tsaftace tsakar gidan can, banda ke ma ai sai dai gidan nan ya ruɓe don na lura kishiyarki akwai aukin kazanta, yarinyar can taki kuma ki kulleta a daki ki saka kwado kar ta kunyata mu idan bakinmu sun iso….” Aunty Murja dai tayi murmushi ta tashi ta fita. Da fara’a Nenne ke welcoming din Jay da Ajay tana nuna masu shimfidar da ta masu na tabarma, shi dai Ajay kansa na kasa har ya zauna saman tabarman, Jay ma ya zauna sannan suka gaisheta, mafici take mika masu tace “Kamar za ayi ruwa daxu kuma sai garin ya washe” Jay yace “Inda muka fito anyi ruwan” Nenne tace “Kaji ikon Allah, nan kuwa sai iska, to ya gidan da iyayen ku?” Jay yace “Alhamdulillah, ya me jiki?” Nenne tana cire bargon jikin Khaleesat tace “Ga ta nan, daga wanka daxu lamari ya sake lalacewa” A fusace Khaleesat ta fixgo bargon daga hannunta ta kara rufe jikinta, shi dai Jay kallonta kawai yake haka ma Ajay, Nenne tace “Haka fa take idan bata da lafiya tayi ta nukurci kamar mu muka dora mata, tunda kina jin su ai daurewa zaki yi ki tashi ki gaishe su” Jay yayi murmushi yace “Kyaleta kawai Kaka” Nenne tace “To ai shikenan…” Mikewa tayi tace “Ina zuwa” Daga haka ta fita daga dakin, Jay yace “Halysaah” Ta ɗan juya ta kallesa amma bata ce komai ba, yace “Are you running temperature?” Shiru tayi, ya tashi ya tafi kusa da ita ya durkusa yana kallonta, shi dai Ajay ya ciro wayarsa yana dubawa, Jay ya kai hannu forehead dinta yaji jikinta da zafi, yace “Bari a maki allura you will feel better in sha Allah” A hankali tace “Ai ban gama shan maganin ba” Yace “Duka za a hada” Juya masa baya tayi tace “A’a ni bana son wani allura bayan ga drugs” Ajay ya wani kalleta, Jay yace “Amma alluran zai taimaka maki ai” Bata sake tanka sa ba sae ma daure fuska da tayi, ya mike ya koma ya zauna, sai ga Nenne da kofin shayi biyu ta ajiye masu Aunty Murja na biye da ita da katon bread da soyayyen kwai lafta lafta a plate, Ajay ya kalli Jay, tana ajiyewa tace “Gashi nan yanxun nan aka soya maku, shayin ma sai tiriri yake kun ga…” Ajay yace “Ni na tashi da azumi yau alhamis, sai dai Jawwad” Jay ya juya ya kallesa, Nenne tace “Ai kuwa yau alhamis nima ina yi saboda ba a garina nake ba shi yasa ban yi ba” Matsar da farantin kwan tayi gaban Jay da katon bredin da kopin shayi duk ta maida gabansa, Khaleesat bata san sanda dariya ya kusa taho mata ba duk da yanda take fama da kanta ganin how shock Jay was looking at Nenne, shi kansa Ajay kawai dakewa yayi, yayi keeping serious face a gefen Jay kar yayi dariya, Nenne tace “In kuma baka ci ba Allah ya sani bazan ji dadi ba, kuma jikina zai yi sanyi” Daga haka ta nemi waje ta zauna tana jiran ya fara shan shayin, Jay ya ciro handkerchief dinsa yana goge fuskarsa, Aunty Murja ta nemi waje ta zauna ta kara gaisawa da su da fara’a sannan tace “Wani unguwa ku ke a Bauchi?” Nenne tace “Nima dai na tambaya ranan amma bai gaya min…” Jay ya ɗan kalli Ajay, shi dai Ajay babu abinda yace, Jay ya sauke idonsa ya sanar masu daga inda suka fito a garin Bauchi, Nenne ta saki baki tana kallonsu can tace “Kun hada wata dangantaka da sarki ne?” Jay yace “Mahaifinmu ne” Wani salati Nenne ta saki saboda shock tana kallonsu tace “Sarkin ne mahaifinku?” Jay bai sake cewa komai ba, Nenne ta kira full sunan Mai martaba tace “Kuna nufin shi ya haife ku??” Aunty Murja tace “Haka fa kika ji suka ce Nenne, ni dama ina ta kallon wannan na kusa da shi naga yana kama da yaran gidan sosai, tunda zaki ga ana nuno mana su ta waya yanxu, su dai wa ennan ban taɓa ganinsu a waya ba” Tsabar yanda Nenne ta girgiza ta kasa cewa komai sai kallonsu Jay take kamar ranan ta fara ganinsu, can ta ambato sunan Baban Jay me rasuwa sai kuma ta fashe da kuka tace “A sannan ina garin nan Allah yayi masa rasuwa, duk muka gigice, garin nan ya dawo shiru kamar ba kowa tsabar tashin hankali, Sarki adali me jin tausayin al’uma, mun yi babban rashi wallahi, kaninsa dake kan kujeran yanxu ne ban wani san sa ba, amma yanxu ace zan samu hanya wallahi zan je har fadarsa mu gaisa in saka masa albarka in masa addu’a” Jay na murmushi yace “Sai mu kai ki Kaka, ai yana nan” Nenne tace “Da kuwa nayi farin ciki wallahi, sai Parida ta rakani mu je, ita wannan rubabbiyar me ciwo ta zauna a gida ba sai mun je da ita ba, ita kuma Murja tana da yarinya me shafar aljanu bata zuwa ko nan da can saboda yarinyar….” Ko rufe baki Nenne bata yi ba sai ga yarinyar Aunty Murja na kokarin shigowa dakin, Nenne tayi wani ihuu ta dau mafici ta fara korar ta daga inda take zaune tana cewa “Fitaa, tafi kofar gida, Murja ba nace ki saka kwado a dakin ba wannan wani irin fitina ne saboda yarinyar nan nake fargaban zuwa gidan nan wallahi” Ajay ya mike yana kallon yarinyar yace “Ta fita kuma Kaka?” Nenne tace “Ta fita mana ɗan nan, er ruwa ce fa” Jay was totally speechless yana kallon Nenne, Aunty Murja ta mike zata dau yarinyar ta bar wajen Ajay yace “A’a ki kyaleta” Sai ya karasa ya shigo da ita dakin ya zaunar da ita kusa da shi, ga shi Fes uwar ta shiryata har da su packing gashinta me uban yawa, Nenne dai sai zazzare ido take tana kallonsu don ita abun kunya ta dauka ai, Ajay ya kalli Aunty Murja yace “Ya sunanta” Aunty Murja tayi murmushi, Nenne tayi karaf tace “Sunansu daya da Khaleesah, ita ma Hauwa ce, dama kuma sunan uwar Murjan Khaleesah ta ci, kunsan uwarta kishiya ta ce kuma mun yi zaman mutunci, Murja na da shekara biyar uwar ta mutu rikonta ya dawo hannuna har na aurar da ita, Ali na ji da Murja kamar ni na haifeta, yanda na sha wahala Ali yayi karatu ita ma haka don sai da tayi poly kafin tayi aure, da iliminta haka da ku ke ganinta har turanci tana ji, bayan na mata aure haihuwar farko ɗan ya rasu bayan shekara hudu Allah ya bata wannan yarinya er ruwa” Calmly Jay yace “Kaka ba haka bane, ki dena kiranta da er ruwa, ita din mutum ce kamar kowa, a ƙasashen da aka ci gaba masu irin wannan lalura kulawa ta musamman ake basu, babu tsangwama babu kyara sai soyayya da ake nuna masu ana jan su jiki, wannan lalura tasu a likitance ita ake kira da Cerebral Palsy ba wai yan ruwa ba kamar yanda yawancin Hausawa ke kiransu wasu ma su ce ai aljani ne ya taɓa su, to duk ba haka bane, kusan lalura ce ta ƙwaƙwalwa wanda jariri ke samu tun yana cikin mahaifiyarsa ko kuma bayan an haifesa, kyara da tsangwamar masu irin wannan lalura da ake yi yana jefa iyayensu cikin damuwa, duk da yanxu kai ya waye hakan ya ragu ba kamar da ba, don haka Kaka don Allah wannan yarinya soyayya take bukata da kulawa ba tsangwama ba, haka Allah ya so ya ganta, mutanen dake kewaye da ita sai su ja ta jiki su nuna mata so da kulawa” Nenne ta sauke ajiyar zuciya tace “Ai shikenan, mu ce mana ake yan ruwa ne zamanin mu, amma tun da ba haka bane ko ta shigo na dena korarta sai dai Allah ya kiyaye mu kar ta mana barna mu shiga uku” Ajay yayi murmushi kawai ya kalli Aunty Murja da kanta ke kasa yace “In sha Allah za a duba mata Wheelchair that will improve her mobility, da abubuwa da suka kamata” Mami ce zaune tare da Mai martaba a parlonsa, bayan sun gaisa tace “Dama Allah ya taimake ka akan maganar Jawwad nace bari in sameka, bayan sun dawo ya kawo min maganar wata yarinya da yake so da aure, duk da nasan kun yi magana da shi kafin yayi da ni, to nayi masa fatan alkhairi, shi ne yanxu na same ka inji what is ur take on the matter” Mai martaba yace “Ai mun gama wannan maganar, har nayi ma wakilai na maganan tafiya wajen iyayen yarinyar, akan haka ake yanxu” Mami tayi shiru tana kallonsu, can ta gyara zama tace “Amma Ranka shi dade ban tari hanzarin ka ba, daga magana sai tura wakilai na zata ai sai anyi bincike me zurfi kafin tura wakilai” Mai martaba kallonta kawai yake don dama ta saba fada masa duk maganar da ya zo bakinta, can ya sauke ajiyar zuciya bayan kusan minti daya yace “Kina ganin zan tura zuwa gun iyayen yarinyar babu bincike Fulani?” Mami tace “To naga abun yayi gaggawa ne ranka ya dade….” Mai martaba yace “To haka muka shirya Fulani” Tace “To yanxu har an tsaida ranan zuwa Kanon kenan?” Mai martaba yace “Kwarai kuwa… Nayi wasu baƙi zan je in same su yanxu Fulani” Yana kai wa nan ya mike ta bi sa da kallo har ya fita daga parlon.*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah*Ur evidence via 07087865788
