Uncategorized

Macizai ne Page 11-20 Hausa Novel

 

Shuru Arɗo ya yi yana kallon Baffa na wasu lokuta kafin ya ce

“Shike nan Magaji, ba zan takura maka ba, amma ban yi tsammanin zaka tsorata da maganar Banju haka ba”

“Ba tsorata nayi da maganar Banju ba a lokacin da ya faɗi, amma a halin yanzu ina cikin zullumi na maganar Banju, dan idan baka manta ba ya ce zamu gani ko ba jima ko ba daɗe sannan kuma zai dawo daukar fansa a kaina da mutanen yankin nan, abunda yake faruwa a halin yanzu abun a duba ne, sannan bamu san wani martani sarkin fulanin yankin jimo zai maidowa mutanen da suka je ban hakuri garesu ba, ba kowa bane zai lamunci hakan, munyi aiken neman taimako anzo dan a taimaka mana amma kuma sai a mai da musu da kaya ace an kashesa! Innalillahi wa inna ilayhirrajiun!” Baffa ya faɗa fuskarsa dauke da zallar damuwar da yake ciki, Arɗo yaja ajiyar zuciya ya ce

“Ko ma miye ne idan suka dawo ma ji, yanzu dai ka je amma ka tabbatar bayan sallan isha’i ka halacci fadar mai unguwa”

“In sha Allahu zan zo” daga haka suka yi sallama, Baffa ba hanyar gida ya yi ba dan ba gidan zai koma ba illa cewa da ya yi su Hajja da Aziza su koma gida, ina Azima bata zo ba? Aziza ta ce

“Eh Baffa bata zo ba” girgiza kai kawai ya yi ba tare da ya yi magana ba, Hajja da Aziza suka dauki hanyar komawa gida, su na tafiya su na hira, Hajja ta ce

“Ohh Allah ni Jumala, ko me ya hana Azima zuwa? Ita kullum ta fi so ku ta zama a bakin zargi”

Download>>> Bakar Inuwa By Billy Abdull

“Ai ko basu zauna a bakin zargi ba, ba lallai bane yaranki su kasance mutane ne!” da sauri Hajja da Aziza suka juya su na kallon Mairo da Hadi wanda suka riƙe ƙugu sai kace zasu dake su, Hajja ta ce

“Mairo me kike nufi?”

“Oho miki kuma! Kin fi kowa sanin abunda nake nufi, yara ko ma dai nace iyayen yara! Ace kamar su Azima da Aziza a wannan yankin gote-gote dasu amma babu aure! Sannan suna tafiya jiki na lankwasa! Daga mai idon mage (wato Aziza kenan) sai mai ido ruwan ganye(Azima kenan) taya kuwa zasu zama mutane, ga shegen kyau! Duk da lokacin da muka yi yan matanci dake duk yankin nan babu mai kyawunki sannan babu jarumi sama da Magaji, ba wai hakan yana nufin zaku haifi yara masu kama da mutanen wani duniya daban bane ehe! Ko ki so ko karki so Azima da Aziza dai ba mutane bane!”

Idon Hajja ne ya kawo ruwa ta ma kasa magana, da kyar ta ce

“Mairo idan ke kike aurar wa sai ki zo ki aurar dasu, sannan kuma idan kina canza halitta ki zo ki canza musu” caraf Hadi ta cab’e zancan da cewa

“Wa ye bai sani ba, ba mamaki duk wannan kisan da ake yi a yankin nan Azima da Aziza suke yi, kuma da saninki ke kike daure musu…..”

“YAAAA ISAAAAAAAA!!!” Aziza ta faɗa da kakkausar murya, ganin yadda fuskar Mahaifiyarta ya jiƙu da ruwan hawaye, gaban mahaifiyarta ta tsaya yayinda idonta suka kara rinewa zuwa fari-fari ,yatsarta manuniya ta ɗaga tana nuna Mairo da Hadi cikin gargaɗi ta ce

“Zan iya jure komai! Zan iya shanye komai! Amma kar na ga hawaye a idon MAHAIFIYATA SANYIN IDANIYATA! ku fita tsabgarmu! Mu mutane ne, maganar da kika fada yanzu kuma Inna Hadi ki bar shi a iya nan kawai kar yaje gaba!” Aziza na gama fadi ta kamo hannun Hajja suka bar su Mairo da Hadi jiki na rawa, Hadi ta ce

“Mai….Mai…Mairoo….ban….gaya…miki….da…da..da cewa ba mutane…bane…wollah inaji ko rantsuwa nayi ba zan yi kaffara ba…kalli ki ga lokaci daya yadda idonta ya canza…anya ma ni kuwa ba su bane…..” saurin dakatar da ita Mairo ta yi ta ce

“Hadi ki bar maganar nan a nan dan ban shiryawa mutuwa ba, zo mu tafi” Mairo ta fizgi hannun Hadi.

      @@@@@@

Sun ɗan yi tafiya Hajja ta tsaya, Aziza tasa hannu tana sharewa Hajja hawaye tare da fadin

“Kiyi hakuri Hajja, dan kuka mai ja wa uwa jifa ko Hajja!?” Aziza ta faɗa tana fashewa da kuka, Hajja ta ce

“A’a Aziza, har ga Allah ni har zuciyata ban taba zargin yarana ba, na san ni dai mutane na haifa”

“To me yasa kike kuka Hajja?”

Karanta Littafin>>> Yar Harka Page 11-20 Hot Romantic Hausa Novel

   “Saboda dukkan uwa ta gari ba zata so a dinga sokin yaranta ba! Har raina nake jin zafi” Hajja ta fada tana mai kamo hannun Aziza, wani tausayin mahaifiyarsu ne ya ɗarsu a zuciyar Aziza, duk yadda take tausayawa kanta da yar uwarta tafi tausayin Hajja, ranar da zata gane cewa su din ba mutane bane MACIZAI NE ranar da zata san duk kisan da ake yi Azima ke yi, shin ya dace ta ci gaba da boyewa Hajja cewa su ba mutane bane? Ko dai ta fito ta gayawa Hajja da Baffa gaskiya? Kai amma kuwa gunduwa-gunduwa za ayi dasu, sannan Azima ta ce ko da ta faɗi ba shi zai hanata cika burinta ba! Girgiza kai Aziza ta yi ta sake rungume Hajja tana kuka, Hajja zata yi magana suka ji nishi na tashi ta gefensu wanda yake ciyawa ne kore shar a wajan, saurin maida hankalinsu suka yi, Aziza ta ce

“Hajja kamar fa nishi nake ji?”

“E nima naji Aziza, kamar ta nan yake fitowa zo mu duba mu gani” suka yanki gefen ciyawar, wani yaro suka gani kwance fuskarsa ta koma blue bakinsa sai fitar da farin kumfa yake yi tare da jini, salati Hajja ta saka, da sauri Aziza ta dagosa tana kallonsa tare da jinjigasa, gefen wuyarsa ta kalla ta ga saran maciji, wanda bata raba dayan biyun *AZIMA* ce, girgiza kai ta hau yi cikin tashin hankali, ta buɗe baki, Hajja ta ce

“Aziza me ya faru da shi?”

“Hajja maciji ne ya saresa, bari na gwada yi masa magani” kasancewar lokuta da dama Aziza na gwada wa Hajja kamar tana magani wanda Hajja ke danganta hakan da nasaban Baffa, bata jira Hajja ta yi magana ba ta hura iska a bakinta ta rufe ido gam na wasu daqiqu sannan ta buɗe, yayinda idon ya koma fari sol, hannu tasa a bakinta ta dibo farin yawu ta gogawa yaron a wuyarsa dai-dai shatin saran, sannan ta koma kallonsa, duk fuskarsa ta yi blue, tana saka masa ya hau gurnani yana murkususu sannan ya koma ya yi ɗifff! Hajja ce ta daga hannunsa ta ga ya koma, da sauri ta janye Aziza ta ce

“Aziza zo mu bar nan wajan”

   Kallon Hajja Aziza ta yi cikin damuwa ta ce

“Hajja taya zamu barsa bayan yana buqatar taimako,ki bari na taimaka masa Hajja kar ya mutu”

“Ai ya riga da ya mutu Aziza! Ki zo muje kar ace kece kika masa wani abun” 

Suman tsaye Aziza tayi tun sadda Hajja tace ai ya riga da ya mutu, kallon yaron kawai take yi, hannu Hajja tasa ta ja Aziza da sauri suka bar wajan basu tsaya ko ina ba sai gida, suna shiga gida Aziza ta shige bukkansu bata ga Azima ba, duk yadda akayi tana rafin jimulo, hannu tasa ta goge hawayenta tare da daukar mayafinta, Hajja ta juyo zata bata ruwa ta ga ta fice a gidan da sauri Hajja ta bi bayanta tana fadin

“Aziza! Ke Aziza!? Azi…” Hajja bata karasa ba sakamakon dakatar da ita da Aziza ta yi, ta rufe mata ido ta hura mata iska, haka kawai Hajja ta tsinci kanta da komawa gida, Aziza kuma hanya ta yanka ta yi rafin jimulo, a yadda take tafiya zaka gane cewa ba mutum ba ce, haqiqa yau Azima ta kai ta karshe! Me wannan karamin yaron ya mata da zata kashesa!.

Tana isa rafin ta kwala kiran sunan Azima.

“AZIMAAAAA!” sulalowa Azima ta yi hannunta dauke da mangoro fuskarta wasai, ganin fuskar Aziza ya sakata sakin baki dan bata taba ganin fuskarta a haka ba

“MACIJIYA AZIZA LAFIYA!” Azima ta fada cikin halin ko in kula.

“AZIMA ME YARON DA KIKA KASHE YA MIKI!?” 

kyalkyalewa da dariya ta yi ta ce

“Sabida ya cancanci ya mutun ne, saboda ya ganoni, kuma yace sai ya faɗa kin ga kuwa dole na kashe sa tunda….” dauketa da mari Aziza ta yi, tana dagowa ta sake kai mata wani marin, ran Azima ya tunbatsa nan ta riƙiɗe ta koma macijiya,in da ita ma Aziza yau ta rikiɗe ta zama macijiya fara sol, nan dambe ya kaceme.

Dambe suke yi sosai a tsakaninsu ba ji ba gani, yayinda Azima ta yanki Aziza a gefen wuya,nan ta koma mutun ta faɗi kasa, ita ma Azimar rabi mutum rabi Macijiya ta zama tana kallon Aziza ranta a haɗe idonta ya kara rinewa zuwa blue, a hankali Aziza ta miƙe tsaye tasa hannu ta karkaɗe jikinta ta juya baya,ta sa hannu a gefen wuyanta inda yake zubar da jini ta lumshe ido, kamar ƙiftawar ido da bismillah ta shafe wajan, sannan ta daga hannunta sama ta haɗa wani guguwa mai karfin gaske ta turawa Azima, Azima bata ankara ba taji anyi sama-sama da ita, sai da taje can sama kafin ta faɗo timm! Da kasa nan ta koma mutum, a hankali Aziza ta juyo tana kallonta yau fuskarta babu fara’a, haqiqa dan faɗa su na faɗa amma basu taba dambe ba, bar su a cacan baki.

    Saurin tashi Azima ta yi ta sake komawa macijiya ta yi hajijiya ta tada ƙura ta yi kan Aziza, da sauri Aziza ita ma ta sake zama macijiya suka haɗe aka hau dambe, da jelarta na maciji ta nannaɗe wuyar Azima ta shaƙeta sosai, murkususu Azima ta hau yi tana son kwacewa daga hannun Aziza amma ta kasa, inda karfinta ya fara karewa dan duk muguntarta bata kai Aziza karfin dafi ba.

    Nan numfashinta ya fara yin sama inda a karshen jikinta ya sub’ale ta koma mutum sumammiya, ganin haka yasa Aziza sakinta ta wullata kusa da rafin ita ma ta koma mutum sannan tasa hannu ta dibo ruwa ta watsa mata a fuska, wani wawan ajiyar zuciya Azima ta sauke alaman ta sha wuya, da tari ta farka tana yunkurin tashi ta ce

“Duk abun da zakiyi Aziza kema kin sani ba zaki iya kasheni ba!”

   Karanta Littafin>>> Gidan Uncle Page 10 Hausa Novel

    

   Kafadarta Aziza ta kama hawaye cike a idonta ta ce

“Nima bana fatar kasheki! Har na bar duniya bana fata na kashe ko da tururuwa! Azima kisan ya yi yawa! Azima me kikeson zama ne! Ga shi yau kin sani na aikata abunda bana son aikatawa wanda ban ma taba aikatawa ba! meyasa Azima! Me yasa! Me yasa!” Aziza ta karasa tana sakin kuka mai cike da ruɗani.

    Zufa Azima ta goge tana ture hannun Aziza daga kafadarta ta ce

“Kullum ba zan gaji da faɗin cewa da ni ce da karfin gubarki da na shafe jama’ar yankin nan an wuce wajan! Duk wanda nake kashewa sun tab’oni ne! Bana mantuwa bana yafiya!”

    A fusace Aziza ta sa hannu ta dago Azima tsaye tare da fadin

“Da anyi magana za ki ce ba ki mantuwa ba ki yafiya! Ni a iya sanina ban ga abun da aka miki ba kike wannan kisar! Shin zaki iya gayamin laifi daya tak ƙwaƙƙwara wanda aka miki kike kisa? Mutum ko da ya miki kallon bai miki ba shikenan ya cancanci kisa!? Kina fakewa da cewa dan kar a tona mana asiri da cewa mu ba mutane bane macizai ne, a da ina yarda amma a kwana biyun nan na daina yarda dake! A da kin san da cewa ke macijiya ce amma ba kya kisa kamar na kwanan nan me yasa Azima!? Me yasa!?”

     Idonta ne ya sake rikiɗewa zuwa blue sosai, fatar jikinta har na caccanza kala ta ce

“Fansa! Fansa! Fansa! Fansa nake ɗauka Aziza!”

    “To fansar me Azima gaya min?”

“Abun da mutanen yankin nan suka min shekarun baya”

Da mugun mamaki Aziza take kallon Azima dan ba ta taba furta wannan kalman ba sai yau, ta ce

“Shekarun baya fa kika ce!? Duka-duka yaushe aka haifeki da zaki dinga lissafin shekarun baya?” 

Murmushin mugunta Azima ta yi ta ce.

“Koma yaushe aka haifeni! Ba damuwarki ba ce! Amma ina so ki sani ki kara sani! Sai na kashe BAFFA! sai na kashe ARƊO! sai na kashe TSOHON SARKIN FULANI KWANA! da kuma wanda suka sauka a bayansa! sai na kashe MAI UNGUWA! kee sai na shafe dukkan mutanen yankin nan! Sannan na shiga birni cikin inda yake da jama’a da yawa na tarwatsasu! Zan bar wannan alƙaryan!” 

Gabanta Aziza ta tsaya ta ce

       “NI KUMA AZIZA MAGAJI ARƊO! ZANYI YAƘI DAKE NA DAKATAR DAKE! ZAN TAIMAKI MUTANEN YANKIN NAN KO DA KUWA ZASU GANE CEWA NI MACIJIYA CE SU KASHENI! ZAN TSAYA A GABAN BAFFA NA KARESA BA KI ISA KIYI MASA KOMAI BA!”.

Murmushi Azima tayi ta ce

     “Idan kin isa ki dakatar dani Aziza! Na fi ki mugunta! Kin fini karfin dafi! Muje zuwa Allah ya ba wa mai rabo sa’a!” Aziza ta yi murmushi ta ce

“Amin!” nan Azima da Aziza suka rabe ko wacce tayi hanyarta daban.

      🍃🍃🍃🍃

Hankali tashe Maga Isar da sakon sarkin fulanin yankin jimo ya faɗo fadar sarki Haruna ya ce

“Allah ya taimakeka! Mummunar labari! Mai cike da tashin hankali, hakika yau munyi asara! Munyi babbar rashi!” daga nan kuma ya fashe da kuka! Nan hankalin jama’ar wajan ya tashi yayinda Sarki Haruna ya miƙe tsaye ya ce

“Maga Isar da sako, me ya faru!?” 

    “Haqiqa mun shiga ruɗu da ruɗani! Munyi sallama lafiya-lafiya da jarman macizai, amma yanzu haka sako ne daga yankin kwana a kan cewa an kashe jarman macizai! Yanzu haka gasu can sun dawo da kayansa da dokinsa! rigarsa duk jini!”  ba iyakar sarkin fulanin jimo ba harta jama’ar da suke zaune a wajan sai da suka miƙe tsaye.

   Waziri ne ya yi karfin halin faɗin

“Ce dasu su karaso su mana cikakken bayani dan bamu fahimci maganarka ba Maga Isar da Sako!” da sauri Maga Isar da Sako ya tashi yaje ya ce dasu su karaso, jiki a sanyaye babu kwari suka karaso suka zube a gaban sarkin fulanin yankin jimo, daga kallon da ake musu yasa suka sha jinin jikinsu, da kyar garkuwan fulanin yankin kwana ya ce

“Allah ya taimaki Sarki Haruna, da fari kafin muce komai zamu fara da ban hakuri da neman afuwa da gafarar duk wani wanda yake wannan yanki a kan rashin jarman macizai! Haqiqa munji kunya! Mun yarda munji kunya! Amma ba laifinmu bane, mai afkuwa ce ta afku, amadadin Sarkin fulanin yankin kwana da Arɗo, da mai unguwar yankin kwana wato Ori, dani Garkuwan fulanin yankin kwana da Magaji Bawa da duk jama’ar da suke yankin kwana muna mai neman yafiyarku a kan abunda ya faru na rashin jarman Macizai! Haqiqa ya cika jarumi kuma ya amsa sunansa, ba zamu manta da halaccin wannan yanki ba har izuwa karshen rayuwarmu! Mun gode da yunkurin taimakonmu! Haqiqa mu abun tausayi ne, kuyi hakuri ku yafe mana! Bai kai ga aiwatar da aikinsa ba muka iske gawarsa da saran maciji, ba zamu iya kawo muku tashin hankali goma da ashirin bane, shi yasa muka sallacesa muka binnesa muka yi masa sutura, zaku iya zuwa ganinsa tare damu gobe idan Allah ya kaimu sai muje ku ga ƙabarinsa!” Garkuwan fulani ya karasa maganar a sanyaye yana mai duƙar da kai.

Download>>> Walijam Hausa Novel Complete Document

    Tabbas jama’ar yankin jimo sunji mutuwar jarman macizai har can kasar zuciyarsu yayinda suka ji tsanar yankin kwana duk da hakika sun tausaya musu matuƙa, amma zafin mutuwar jarman macizai ya hanasu ce uffan wasu Garkuwan fulanin yankin kwana, ba a wani musu tarba mai kyau ba dan kuwa su na cikin ƙunci da jimanin mutuwar jarman macizai, inda suka sa da washe gari  da safe zasu yi asubanci su tafi yankin kwana.

        @@@@@

*YANKIN KWANA.*

Ko da su Aziza da Azima suka koma gida ba su shiga hidimar juna ba, harta abinci da Hajja ta haɗa musu ga mamakinta sai gani ta yi sun raba kwano, sosai abun ya damu Hajja ta yi musu tambayar duniya me ya hadasu, Aziza ce dai ta iya cewa babu komai fa Hajja, amma Azima kam ko kallon Hajja bata yi ba.

@@@@@@

    Bayan anyi sallar isha’i dukkansu suka hallara a fadar mai unguwa, kowa da kalar shawarar da yake badawa, shi dai Baffa duk sauraronsu yake yi ya gaza cewa kanzil, inda a karshe Arɗo ya ce

“Magaji in ce dai lafiya ko? Na ga kowa na ta magana amma kai baka ce komai ba” ajiyar zuciya Baffa ya sauke ya ce

“Hankalina yana can wajansu Garkuwan fulani, ko ya Haruna zai dauki lamarin? Abun fa sai wanda ya ɗaure” Ardo ya ce

“Tabbas haka ne Magaji, to ya zamu yi? Mu ma ba yin kanmu bane, Allah yasa su fahimce mu” aka amsa da amin, tsohon sarkin fulani ya ce

“Yanzu abun duba a nan shine taya zamu shawo kan wannan matsalar? Abun kara yawa yake yi fa? Jarman macizai da safe! Yaro dazu! Ba zamu zauna mu naɗe hannu a kirji mu zuba ido a shafe mu ba, mai zai hana mu aika da kokon barar mu neman taimako yankin tudu?” wani zabura Baffa ya yi yana girgiza kai ya ce

“A’a Baffa Mandi, kar mu kara wannan kuskuren! Munyi kuskure na farko an rasa jarman macizai, yanzu kuma sai mu sake aikata wani ta hanyar yin aike yankin tudu! Mu nemi taimakon IRO MAGANIN MACIZAI? Duk shawaran da za ayi a sauran yankuna amma banda yanki biyu, ban da yankin tudu ko yankin ja’i, kar mu taro wani yaƙin ba tare da mun dakatar da wani ba, kun san tsananin gabar da ke tsakanin yankin tudu da yankin ja’i da yankinmu, har kwanan gobe ana samun kisan kai a tsakanin yankin nan da yankin ja’i, har kwanan gobe yankin tudu su na riƙe da abunda ya faru sun kasa mantawa kiris suke jira su fasa abunda yake zuciyarsu, dan Allah ku fahimceni!”

    Shuru wajan ya dauka kowa da abunda yake tunani,

Sai zuwa can anjima Mai Unguwa Ori ya ce

“To shikenan, za ayi ƙuri’a duk bangaren da ya fi rinjaye shi za a zaba, idan bangaren kar aje neman taimako yankin tudu ko yankin ja’i sunfi yawa to ba za aje ba,idan kuma bangaren wa inda suka ce aje sunfi yawa to za a je” shi dai Baffa shuru ne ya yi yana hango musu gagarumar balbalin gobarar yaƙin da zai tashi amma sun kasa ganewa.

Da washe gari asubanci yankin jimo suka yi, takwas na safe su na yankin kwana,a maƙabarta jikin ƙabarin Jarman macizai, kuka sosai sarki Haruna yake yi shi da jama’ar yankinsa wa inda suka zo, an sha musu mutuwa amma farat ɗaya na Jarman macizai wanda yake jarumi a yankinsu ya gigita tunaninsu, haka suka ƙarashi koke-kokensu suka gama dan ba dawowa zai yi ba, haka jamar’ar kwana suka taru ƙwansu da ƙwarƙwatansu suka sake yiwa yankin jimo ta’aziyya tare da ban hakuri, daga fuskarsu kawai zaka kalla ka gane su na cikin mugun damuwa da tashin hankali, babu yadda yankin jimo suka iya dole suka hakura tunda dai Jarman Macizai ba dawowa zaiyi ba ya tafi kenan, sai dai fatan Allah ya yafe masa.

       @@@@@

Bayan kwana biyu an gama ƙuri’u, inda aka samu sab’anin ra’ayi, jama’ar da suka fi rinjaye shine wa inda suka ce aje yankin ja’i neman taimako kar aje yankin tudu a fara zuwa yankin ja’i, dan ba za a zauna da matsala ba tare da an bukaci taimakon Allah da wa inda zasu shawo kan matsalar ba, shi dai Baffa shuru ya yi bai ce kanzil ba, haka aka sa mai rubuta wasika ya rubuta aka yiwa yankin ja’i aike da shi.

      🍃🍃🍃🍃🍃

     Sarkin fulanin yankin ja’i na zaune Maga Isar da Sakon yankin ya zo ya zube a gabansa yana fadin

“Allah ya taimakeka! Hakika a yau nasara tamu ce” wazirin fulani ya ce

“Maga Isar da Sako meke tafe da kai ne?” murmushi Maga Isar da sako ya yi ya ce

“Hakika yau muke da nasara, sako ce ta isko mu daga yankin kwana! su na cikin bala’i shine suke bukatar taimako daga yankinmu, yanzu haka ga takwabi sarkin kwana wato Chubaɗo ya aiko mana da shi alaman sun sakar mana igiyar, munyi nasara su sun faɗi, wannan takwabi da Chubaɗo ya aiko mana da shi alama ce na sun duƙawa wannan yanki tamu” 

    

    Sarkin fulanin yankin ja’i ya ce

“Maga Isar da sako, zai fi kyautuwa da kayi mana bayani dalla-dalla, ko kuma ka buɗe wasikar da suka aiko da shi ka karantawa dukkan wanda yake zaune a wannan fada dan jin meke tafe da sakon”

      Ƙara russunawa Maga Isar da sako ya yi ya buɗe wasikar ya fara karantawa kamar haka.

     ” _ASSALAMU ALAIKUM, SAKO CE DAGA YANKIN KWANA IZUWA YANKIN JA’I, MUNA FATAN WANNAN SAƘO TA ISA GAREKA SARKIN FULANIN JA’I WATO SARKI JAWO TARE DA MAI UNGUWAR YANKIN JA’I WATO MAI UNGUWA SODANGI, A YAU MU YANKIN KWANA MUN WAYI GARI CIKIN RUƊU DA RUƊANIN TASHIN HANKALI DA RASHIN ZAMAN LAFIYA, WA HAKA NE MUKA RUBUTO SAƘO DAN YA YI TATTAKI ZUWA GA YANKIN JAMA’AR DA SUKE JA’I GABAƊAYA, AMADADIN NI SARKIN FULANIN YANKIN KWANA CHUBAƊO DA MAI UNGUWAR YANKIN KWANA ORI, DA ARƊO DA TSOHON SARKIN FULANI MANDI, DA MAGAJI BAWA DA DUK WANI WANDA YAKE YANKIN KWANA MUNA NEMAN TAIMAKONKU! MUN GAMU DA IFTILA’IN MACIZAI WANDA SUKE KASHE MANA MUTANE! AN KASHE DUK WASU MASU KAMA MACIZAI NA YANKINMU! MUN NEMI TAIMAKON YANKIN JIMO INDA SUKA TAIMAKA MUKA ROƘI ALFARMA DA JARMAN MACIZAI YA KAWO MANA DAUKI WANDA SHI MA AKA KASHESA KWANA BIYU DA YA WUCE, GA WANNAN TAKWABIN DA MUKA AIKO YANA NUNI NE DA MUN ZUBAR DA MAKAMAN YAƘIN GABAR DAKE TSAKANINMU NA TSAWON LOKACI MUN DUƘAWA YANKINKU, MUN YARDA KUNYI GALABA A KANMU! BA DAN KOMAI BA, SAI DAN MUNA NEMAN ALFARMA DA A TAIMAKA MANA DA TAIMAKON *INNU MACIJI* MUN SAN SHI KA ƊAI NE KAWAI ZAI IYA, TUNDA HAR TA ALJANUN MACIZAI DA MAYU DA ALJANU DUK YANA FAƊA DASU, DAN ALLAH SARKI JAWO DA MAI UNGUWA SODANGI A TAIMAKA MANA, KANMU A ƘASA! A YAU MUN YARDA YANKINKU YANA SAMAN TAMU, SAƘO DAGA YANKIN KWANA, SAI MUNJI DAGA GAREKU, MUN GODE_”

Download>>> Budurwar Mijina Complete Document

      Wani murmushi sarkin fulanin ja’i ya yi yana mai kallon Maga Isar da Sako,yayinda jama’ar ja’i suka hau murmushin nasara, dan sun jima suna neman cin galaba a kan yankin kwana amma sun kasa, hakan ya samu asali ne da nasabar da Baffa yake da shi,amma wai yau sai ga shi su da kansu suke cewa sun zubar da makaman yaƙinsu? Wannan ai nasara ce babba a garesu, wakilin yankin ja’i ya ce

“Allah ya taimakeka! Ai mu nasara ce ta tako da kafarta tazo mana har gida, wai shanu daga sama gasheshshe!” 

    Wazirin ja’i ya ce

“Ai ranka ya daɗe abunda muka jima muna nema ne, shine suka sakar mana shi yanzu,tun yaushe muke neman nasara a kan yankin kwana amma mun kasa samu sabida Magaji Bawa” wazirin fulanin ja’i ya karasa maganarsa yana murmushi, wakilin fulanin ja’i ya kuma cewa

“Ranka ya daɗe kar mu b’ata lokaci kawai mu amsa da cewa e mun amince da bukatarsu” girgiza kai garkuwan fulanin ja’i ya hau yi ya ce

“Shekara da shekaru ake ɗibi ba daɗi tsakanin yankinmu da yankin kwana, rana daya tak su aiko mana da sako su ce sun janye anya babu lauje cikin naɗi? A gaskiya ni ban yarda da yankin kwana ba, sai dai wani shirin kawai suke yi ta yadda zasu shafemu!” garkuwan fulanin ja’i ya karasa maganarsa yana haɗa rai sosai, sarki Jawo ya ce

“Bana tunanin haka! Idan ma kuma hakane karka manta muna da fidda kunyar gasa a yankin nan wato *INNU MACIJI* wanda a halin yanzu shi suke bukatar taimakonsa,Innu Maciji dai duk faɗin yankuna sun san shahararsa! Tunda shi ya lashe kambu na daya a gasar fidda gwajin macizai! Innu Maciji bai ci sunansa a banza ba! Tunda har aljanun maciji da mayu yana yaƙi dasu kuma ya ci nasara, dan haka idan muka tura Innu Maciji dan zuwa taimakawa yankin kwana kamar yadda suka bukata yaje ya dawo ya kake tunanin martaban da yankin ja’i zai samu tare da karramawa daga sauran yankuna?” 

    Ajiyar zuciya Garkuwan fulanin ja’i ya sauke tare da kallon Sarki Jawo ya ce

“Ranka ya daɗe bana so mu manta da abu daya, a lokacin da aka raba kambu Magaji Bawa ya jima da sauke duk wata gab’ob’in baiwa da yake da shi, na san idan har zaka manta da tarihin Magaji Bawa da Tsohon sarkin ja’i ya baka ba zaka manta da sunansa da ya shahara a sauran yankuna ba, *GWARZON DAFIN MACIZAI!!* ka tuna?” Garkuwan fulanin ja’i na furta wannan kalma sai da mutanen da suke wajan suka firgita, Wakilin Fulanin Ja’i ya ce

“A gaskiya na so na yarda da maganarka Garkuwan ja’i! Me yasa Magaji ba zai yi wani abu a kai ba da zasu dinga bukatar taimakon yankuna! A da shi Magaji a ina ne bai yi taimako ba, gaskiya maganarka abun dubawa ce” Maga Isar da sako ya ce

“Amma shekaru ashirin Magaji Bawa ya ce ya daina duk wani abu na yaƙe-yaƙe da yake yi, bayan ya sauka ne shine aka naɗa Firi jarumin yankin kwana ko ba haka bane? Ni a tunanina da ace Magaji Bawa zai iya wani abu a kai da ba za a zo neman taimakon Innu Maciji ba har su russunawa yankin nan”

     “Amma dai kun san da cewa duk wata shahara da Innu Maciji zai yi ba zai taba kamo ko da tsilen takalmin Magaji Bawa ba ko?” 

        Maga Isar da sako ya ce

“Ni dai bana tunanin haka gaskiya, da ace zai iya da ba zasu zo nan ba” Sarki Jawo ya ce “tabbas haka ne maganarka Maga Isar da sako, yanzu abunda za ayi,aje a cewa mai unguwa Sodangi akwai magana ta gaggawa, a biya a kira Innu Maciji, a rubutawa yankin kwana da cewa su tsumayemu zuwa gobe idan muka gama shawara da tattaunawa zamu tura musu da sako idan ma mun amince ko akasin haka” Sarkin fulanin Ja’i yana gama magana ya miƙe tsaye ya bar wajan.

Download>>> Darasi Book 1 Complete Document

     🍃🍃🍃🍃

*YANKIN KWANA*

Maga Isar da sakon yankin kwana ne ya gama karanta wasikar da yankin ja’i suka aiko musu da shi, sarki chubaɗo ya ce

“Ba komai yau da gobe duk daya ne a wajan Allah, Allah ya nuna mana” mai Unguwa Ori ya ce

“Amma Allah ya kara maka yawan rai, anya yankin ja’i zasu yarda su taimakemu kuwa? Gani nake kamar su na neman hanyar da zasu wofantar da bukatarmu ne, tunda mun sanar dasu yankin jimo sun rasa jarman macizai, da mun sani da bamu rubuta musu da cewa an kashe jarman macizai ba” Arɗo ya girgiza kai ya ce

“Maganar duniya bata b’uya, gwanda dai da muka gaya musu gaskiya zai fi, balle kuma abu babba irin haka ya faru ace manyan yankuna basu sani bane? Ai hakan ma ba mai yuwa ba ce, dan naji ance yankin gangare da yankin jauro da yankin ulela da yankin nasare duk sunje yiwa yankin jimo ta’aziyyar jarman macizai”

      Sarki Chubaɗo ya ce

“Mu jira har zuwa goben muji sakamakon abinda zasu ce” Arɗo ya yi murmushin karfin hali ya ce

“Bana tunanin yankin ja’i zasu wofantar da bukatarmu! Abunda muka jima da sanina suna neman yankin kwana ta duƙa musu, sai ga shi laluri tasa duk taurin kan da fulani ke da shi mun russuna musu da muka ji uwar bari, dan muna da bukatar mu san waye ba mutum ba a yankin nan! WAYE MACIJI! a yankin nan! Dole azo ayi gwaji dan a fidda zargin juna a zukata, gwanda a nuna mana inda matsalar take mu kuma mu san ta inda zamu shawota”

Aka amsa da haka ne,nan dai suka gama tattaunawa suka ajiye maganar tasu akan su saurari yankin ja’i.

       Bayan an watse a fadar Sarki Chubaɗo Arɗo da Baffa ne suke tafiya a hankali su na magana kasa-kasa,Arɗo ya ce

“Magaji, fatan kana sa a ido sosai a kan su AZIMA DA AZIZA?”

      “E Arɗo ina iyakar bakin kokarina wajan saka musu ido, ita Azima baka iya gane gabanta,gwanda Aziza, gasu dai a tare aka haifesu amma halayyarsu ta sha bamban, a kwana biyun nan basu kula juna, Jumala sai korafi take yi a kan nayi musu magana ko me ya haɗa su, amma ban dauki hakan da mahimmanci ba sabida ba shi ya kamata na kula ba, kare rayukan yankin nan shine abu mafi mahimmanci” Arɗo ya gya ɗa kai ya ce

“Tabbas hakane, ba mamaki sun ɗan yi faɗa ne tinda ana samun irin haka” Baffa yace

“Eh nima haka nake tunani Azima bata da dadi ko kadan, Arɗo barin wuce gida” 

“To a gaida Jumala da Azima da Aziza”

“Zasu ji” Baffa ya fada tare da yiwa Arɗo sallama.

     🍃🍃🍃🍃

Tun safe Aziza ke rafin jimulo tana wanke kayan Hajja da na Baffa, Azima kuwa dan Aziza na rafin jimulo yasa ita bata je ba tana gida, abinci Hajja ta ɗora amma Azima ta hana abincin dahuwa, har la’asar tana zaune a kan tabarma kaba tana saƙe wani igiyoyi, Hajja ta kalleta ta ce

“Wai ni kam Azima wannan saƙe-saƙen da kikeyi na miye ne? Tun safe kike zaune a wajan ba sallar azahar bare la’asar ki tashi kiyi sallah” ba tare da ta dago ta kalli Hajja ba ta ce

“BANA SALLAH!” 😏

Baki sake Hajja ta kalli Azima ta ce

“Kina fashin sallah ne?” kafin Azima ta bada amsa Aziza ta yi sallama da kaya a hannunta ta shige bukkan Hajja ta ajjiyesu sannan ta fito ta duƙa ta ce

“Sannu da gida Hajja”

“Yawwa sannu Azizatuna, kin dawo?”

“E Hajja na dawo”

“Ayya Aziza maimakon idan kin wanke kayan ki dawo gida idan ya bushe anjima a kwaso shine kika zauna har yamma a rafi ba tare da kin dawo gida ba? Ga shi haka kika fita ba ki ci komai ba” murmushi Aziza ta yi a ranta ta ce

“Idan na so zan iya wanke kayan nan na busar da shi a lokaci guda sabida karfin dafin da nake da shi,amma bana son hakan nafi son na samu ladar iyayena” a fili kuma ta ce

“Wlh ba komai Hajja bana jin yunwa ai”

“Allah ya miki albarka Aziza ke da yar uwarki, kinyi sallah ne?”

“Amin, E Hajja nayi sallolina a rafin jimulo ban bari lokaci ya shige ba” Hajja ta kalli Azima ta ce

“Azima kince baki sallah kina fashi ne?” da blus eyes dinta ta dago ta kalli Hajja ta ce

“Ni sallah ne kwata-kwata bana yinsa a rayuwata!” dam!dam!dam! Ƙirjin Hajja ya bada ta b’ata shuru tana bin Azima da kallo, da kyar ta buɗe baki zata yi magana amma Azima bata jira hakan ta faru ba dan kamar ƙiftawar ido ta tashi tare da tattare dogon igiyar da ta saƙa ta shige bukka, Aziza ganin yadda hankalin Hajja ya tashi da maganar da Azima ta faɗa ya sakata faɗin

“Karya take yi Hajja, kin san halinta bata damuwa da maganar da zata faɗi zai yi maka dadi ko akasin haka faɗi kawai take yi” sai a lokafin Hajja ta sauke ajiyar zuciya, Aziza ta ƙwaƙulo murmushi dan sallah kam Azima baya yi, ta ce

“Hajja ba a gama abinci ba?”

“Wollah Aziza ban san wani irin abinci yau nake dafawa ba, tin rana na ɗora kafin ayi azahar amma har yanzu ta ƙi nuna” shuru Aziza ta yi tana kallon tukunyar kasan na wani sakanni kafin ta ce

“To Hajja je ki ciki ki huta yanzu zan karasa”

“A’a Aziza yanzu fa kika dawo daga….”

“Ohh dan Allah Hajja ki je ki huta” murmushi Hajja tayi tana shigewa bukka, Aziza ta buɗe abinci ta ga rashin dahuwarsa yana da nasaba da sa hannu da Azima ta yi, rintse ido ta yi ta buɗe nan idonta ya koma fari sosai ta zaro harshenta ta hura wani hayaki a cikin tukunyan, nan kalar abincin ya canza alaman ya dahu, sannan ta rufe tana miƙewa tsaye ya yi dai-dai da shigowar Baffa da kuma fitowar Hajja daga bukka, sannu da dawowa suka masa, Baffa ya amsa yana zama a inda Azima ta tashi, kallon baƙin igiyar da Azima ta yi saƙa da shi ya gani guntun, dauka ya yi a fili ya ce

“Zaran saƙar dana? me yake yi a gidan nan? Wa ya kawo?”

      🍃🍃🍃🍃

COMMENTS AND SHARE

Back to top button