Halysaah Page 134 By Khaleesat Haydar
HALYSAAH PAGE 134…Sau hudu Mami na kiran Jay no answer, kuma tasan baya saka wayarsa a total silent sai dai vibration, ita dai Khaleesat na tsaye parlon kanta a kasa tana wasa da fingers dinta, Mami tace “Ki koma can bangaren ina zuwa” Khaleesat tace “To” Juyawa tayi ta nufi kofa ta fita daga parlon, Mami ta mike ta fita zuwa part din Jay tayi knocking, ta kusa minti biyar bakin kofar tana knocking daga karshe Jay ya bude yana gyara jallabiyan da ya saka, yana kallon Mami da mamaki yace “Mami hope all is well?” Hadiyah na tsaye daga bakin kofar Bedroom dinsu sanye da wasu shegun kayan bacci fuskarta daure, ko kunyar Mami ta ganta bata yi ba, don sarai tasan Mami ke knocking din kofa don ko da ta kira wayar Jay dama wayar na kusa da ita vibration din ya tasheta bacci, tana dubawa taga Mami ke kiran ta saka wayar a total silent ta kife a bedside drawer, duk da Mami ta hango Hadiyah amma sai tayi kamar bata ganta ba tana kallon Jay tace “Ka je bangaren Junaid ba shi da lafiya….” Jay ya sauke idonsa yayi shiru jin abinda Mami tace, can ya daga kai ya kalleta yace “How did you know?” Mami tace “Matarsa ce ta zo bangarena yanxu take gaya min” Jay yace “Sai dai a bada pain reliever a kai masa cause iya shine abinda ke available da daddaren nan, zuwa gobe da safe sai likita ya duba sa yayi masa proper treatment” Mami tace “Sai ka kai masa pain reliever din ai” Tana kai wa nan ta juya ta bar bakin kofar, Hadiyah ta murguda baki ta juya ta koma cikin daki. Khaleesat na komawa bangaren Ajay ta shiga dakin ta zauna gefensa tana kallonsa ta kai hannu goshinsa that is so hot, cire hannunta tayi a hankali still looking at him, can ta mike ta shiga bandaki ta debo ruwa a karamin abu ta saka towel ta dawo dakin ta ajiye bowl din gefen gado, cire duvet din jikinsa tayi, ya bude idonsa da har sun kada yana kallonta murya can kasa yace “Ke” Bata ce masa komai ba ta sauke idonta daga nasa ta fara unbuttoning din masa shirt din jikinsa ya rage singlet sannan ta dau towel din ta matse ruwan jiki ta fara goge masa jikinsa da shi a hankali, he didn’t resist cause he was weak, kofar parlor da taji alamar an bude yasa ta ajiye towel din hannunta, sai kuma taji sallaman Mami a parlon, rufa masa duvet tayi jikinsa ta sauka daga kan gadon ta tafi ta bude kofar dakin tana amsa sallaman, Mami tace “Yana ciki?” Khaleesat tace “Eh yana ciki” Mami ta shiga dakin da sallama ta karasa inda Ajay ke kwance tana kallonsa, hannu ta kai forehead dinsa, shi dai idonsa na lumshe, after some seconds tace “Allah ya sauwake, za a kawo masa magani yanxu” Khaleesat tace “To” Mami tace “Sai ki dinga tofa masa addu’o’i kuma” Khaleesat ta gyada kai tace “To in sha Allah” Juyawa Mami tayi ta fita daga dakin, Khaleesat ta koma ta zauna kusa da Ajay tana kallonsa ta ci gaba da goge masa jikinsa da towel, bayan fitar Mami da minti biyar taji ana knocking kofar parlor, sauka tayi daga kan gadon bayan ta ajiye karamin towel din hannunta ta ja masa bargon a jikinsa ta fita zuwa parlon, tana bude kofar suka hada ido da Jay dake tsaye, sauke idonta tayi ya mika mata magunguna biyu yace “Two each….” Amsan maganin tayi without raising her head, ya juya ya bar bakin kofar, ta bi sa da kallo sannan ta kulle kofar parlon, wani tea ta sake hada ma Ajay kadan a cup ta dau bottle water sannan ta koma cikin dakin, ta cire duvet din jikinsa tace “Ga maganin” Ya bude ido, iya maganin ya sha kawai yaki shan shayin ya koma ya kwanta, har karfe uku Khaleesat ko gyangyadi bata yi ba a kusa da shi, addu’o’in da Mami tace ta dinga tofa masa kawai take ta yi, in ta gaji ta huta sannan ta ci gaba, da ya bude ido zai ganta kusa da shi a zaune, duk motsin sa idonta na kai, zuwa sannan temperature dinsa ya dan sauka ba kamar daxu ba, kuma ya dena jolting da yake, and he was just sleeping. Khaleesat bata san sanda bacci barawo ya dauketa ba ta kwantar da kanta a gefensa lying down horizontally shi kuma yana kwance straight, a firgice ta farka wajen karfe biyar ta juya kanta a hankali jin something is holding back her hair, ganinsa tayi ya bar position din da kansa yake ya dawo kusa da ita ya cusa kansa cikin dogon gashinta bayan hularta ya fita, hada ido suka yi don ba bacci yake ba a lokacin, ya mirgina ya koma position dinsa, ta mike zaune tana packing gashin nata da ribbon dinta da ya zame, sauka taga yayi daga kan gadon ya shiga bandaki. Bayan sallan asuba ko azkar Ajay bai yi ba ya koma ya kwanta cause he was very weak, ta idar da nata azkar din ta koma kusa da shi ta zauna tana kallonsa tace “Ya jikin?” Ya dan kalleta yace “Waye bai da lafıya wai?” Ita dai kallonsa kawai take, can tace “Ni” Taga ya lumshe ido bai sake cewa komai ba, bacci ne ya kuma daukesa a haka, ita dai tana ta zaune taji ana knocking, ta mike ta fita, tana bude kofar taga Jay a tsaye, ta sunkuyar da kanta a hankali tace “Ina kwana” yace “Lafıya lau, how is his body?” Ta gyada kai still not looking at him tace “Da sauki” Sai kuma ta koma gefe don bata san ko shigowa zai yi ba, shiga parlon yayi ganin ya tsaya tace “Yana daki” Jay bai ce komai ba ya karasa Bedroom din, tsaye yayi kawai kusa da gadon ganin bacci Ajay yake, after some minutes ya juya ya fita daga dakin, Khaleesat na tsaye inda ya bar ta har sannan, ba tare da ya kalleta ba yace “Likita na hanya zai zo dubasa” Ita dai Khaleesat bata ce komai ba har ya fita, a hankali ta zauna gefen kujera, tana ta zaune har likitan da Jay yace yana hanya ya iso, bayan tafiyar likitan Khaleesat na zaune kusa da Ajay don drip Dr din ya sa masa yayi masa allurai, Sallaman Mami da taji a parlor yasa ta tashi daga kusa da shi ta tafi ta bude kofar dakin tana amsa sallamarta, Mami na tsaye parlor tace “Ya jikin nasa?” Khaleesat ta duka nan kasan carpet ta gaisheta sannan tace “Da sauki” Mami tace “Har yanxu baccin yake?” Girgiza kai Khaleesat tayi tace “A’a ya tashi” Mami tace “Ok” Ta karasa cikin Bedroom din, ita dai Khaleesat bata mike daga inda take durkushe ba, Mami ta karasa har kusa da gadon dakin tana kallon Ajay da ya mike zaune ganinta, tace “Ya jikin?” Ya gaisheta sannan yace “Da sauki” Mami tace “Allah ya sauwake” yace “Ameen” After some minutes ta Juya ta fita daga dakin ta koma parlor tana kallon Khaleesat tace “Yaushe Jawwad ya sa masa drip din?” Khaleesat ta girgiza kai tace “A’a ba shi yasa masa ba, wani Drine” Mami tayi shiru bata ce komai ba, can ta nufi kofa, Khaleesat ta bi ta da kallo har ta fita daga parlon sannan ta mike a hankali ta koma cikin Bedroom din, jingina tayi jikin gadon tana ta zaune har bacci ya dauketa a haka, Ajay ya juya yana kallonta, sai kuma ya mike zaune yayi disconnecting din drip din hannunsa ya dau pillow ya ajiye kusa da ita, da hannu daya yayi using yayi laying dinta down the bed, ta bude ido da sauri, sai kuma tayi lamo kan pillown tana kallonsa, ya maida drip din hannunsa, lumshe ido tayi bacci ya kara dauketa. Sai kusan karfe tara Khaleesat ta farka taji yana wanka a bandaki, ya cire drip din da ko rabi bai kusa ba, ta cire duvet din da ya rufa mata ta sauka daga kan gadon ta fara gyaran babban dakin, Ajay na fitowa bathroom ko goge jikinsa bai yi ba taga ya kwanta kan gadon da ta gama gyarawa covering himself with duvet, ta ajiye turaren wutan hannunta da ta saka a burner ta koma kusa da shi tana kallonsa tace “Me yasa zaka yi wanka yanxu…” Juyawa tayi jin sallama a parlor sai kuma ta kalli Ajay that was shivering, ta tashi da sauri ta tafi ta bude press din kayansa, ta dauko masa one among the many jallabiyas she saw in one part of the press, ta dawo kusa da shi ta cire duvet din jikinsa ta mika masa jallabiyansa sannan ta fita daga dakin jin wani sallaman, Walid ta gani tsaye parlor taji gabanta ya fadi sosai, ta dan koma baya ta sauke kanta kasa cike da karfın hali tace “Ina kwana” Shi dai kallonta kawai yake daga sama har kasa da idanuwansa kamar wanda ya sha wani abu, sai kuma taji yace “Tare mu ke da Mai martaba, he is here to check on ur so called Husband….” Ta gyada kai without saying anything, Walid ya dan yi murmushi still looking at her ya juya ya fita daga parlon, ita kuma ta koma daki tana kallon Ajay da ya daure ya saka jallabiyansa tace “Mai martaba ne zai shigo Daga haka ta koma parlor ta tsaya gefe tana jiran shigowan Sarki, after almost 3 minutes suka shigo parlon, da Mai martaba da Walid sai Jay da Mukhtar, ta duka har kasa tana gaida Mai martaba ya amsa yana tambayarta me jiki, kanta a kasa tace “Da sauki ranka shi dade” ita dai tana durkushe inda take har suka karasa cikin Bedroom din. Throughout ranan haka Khaleesat ke zaune gefen gado kusa da Ajay Wanda baccinsa yafi rashin baccin nasa yawa, abinci kusan kala uku ta dibar masa a wanda aka kawo masu part din amma bai ci ko daya ba sai fruits kawai da ya sha, da rana Mami ta sake shigowa dubasa bata yi minti uku ba ta fita, sai Mukhtar da shi ma ya shigo bayan la’asar, amma bata ga Jay ya dawo bangaren ba tun bayan da suka zo tare da Mai martaba wajen karfe tara, Yakumbo ma na ta shigowa bangaren ta tambayi Khaleesat ya jikinsa, Khaleesat sai tace mata da sauki, wajen karfe shidda ta sake shigowa Khaleesat ta fito parlor tana kallonta don wannan shi ne shigowarta na kusan goma kenan ranan, Yakumbo ta zauna kasa ta sinne kai da ladabi tace “Allah ya taimake ki, har yanxu Yariman bacci yake?” Khaleesat tace “Ehh bacci yake” Yakumbo na dan kame kame tace “Dama idan ba damuwa ina son wata er magana dake ne, Allah ya sa bazai bata maki rai ba kuma Allah sa ki fahimce ni ranki shi dade” Khaleesat tace “To ina ji, ki zauna kan kujera mana Mama Yakumbo ta girgiza kai da sauri tace “A’a nan ma ya isa ranki shi dade, ni dai fatana Allah sa ki fahimce ni don a dar dar nake son maki wannan maganar, kuma ki dubi Allah maganar nan ya zama tsakaninmu ki gafarceni ranki shi dade ban san ko maganata ta karshe tayi tsauri ba, Allah ya taimake ki” Khaleesat ta zauna gefen kujera tana kallonta tace “To ina ji Mama” Yakumbo tayi kasa da murya tace “To Nagode Gimbiya, ni dai kamar yanda na gaya maki kwanaki kwarai a gidan nan na taso tun ina karamata, a lokacin mahaifiyata na da rai tana matsayin jakadiyar marigayiya mahaifiyar Yarima, don haka hatta ni mahaifiyarsa ta nuna min soyayya sosai, a magana ta gaskiya ranki shi dade duk abinda ke faruwa gidan nan kusan babu wanda ban sani ba, na dade ina son sanar maki cewar ciwon nan da Yarima yake da zarar ya shigo gidan nan a gaskiya har da sa hannu ba ciwon tsakani da Allah bane, jifa ne, tun wancan lokacin da aka kawo ki nake son inyi maki maganar nan amma ina tsoron yanda zaki dau maganata, to a takaice abinda nake son ce maki yanxu shi ne a duk sanda ya dawo masarautar nan idan baya da lafıya kai koma da lafıyarsa ni ke kawo masa abinci ko kuma na kawo masa kayan shayi da ruwan zafı kuma akasari ni ke hada masa abun shan sa saboda yarda da yayi da ni, ki gafarceni ranki shi dade ni dai a duk sanda bai da lafiya nakan zuba masa wannan a shayinsa….. Yakumbo na magana ta fito da kullin maganin tana nuna ma Khaleesat, amma fa duk a tsorace take tana kallon Khaleesat dake ta kallon kullin maganin, sai kuma tayi kasa da murya ga tsoro kwance fuskarta karara tace “Wallahi ranki shi dade ba komai bane illa itatuwa na kaikayi koma kan mashekiya, kuma hadi ne na musamman wallahi, duk naje garinmu nake amso masa wajen kanina don lakani ne da kakanmu ya bar mana, to in sha Allahu Yarima na shan shayin nan kafın kwana biyu zaki ga ya mike kamar ba shi ba, wani lokacin a ranan ma zaki ga alamar samun sauki tattare da shi, bai taba sanin wannan abu da nake yi ba kinsan dan boko ne ina fargaban yanda zai dau lamarin duk sanda ya sani shi yasa nake kaffa kaffa ban taba gaya ma kowa wannan sirrin ba, to yanxu tunda kece matarsa kinga ke ce ke hada masa shayi ko wani abu da zai sha don ba hurumina bane hakan yanxu, idan ma baki yarda ba yanxun nan sai in zuba a ruwa in sha, wallahi bana nufinsa da komai sai alkhairi, da mugun abu ne kin san bazan zo in gaya maki ba kuma duk hanyar da zan bi in zuba masa a abinci to zan bi in zuba babu kuma wanda zai sani” Khaleesat dai sai kallon kullin maganin take yi babu ko kiftawa, har cikin ranta kawai taji ta yarda da Yakumbo, can ta amsa maganin tace “To shikenan zan hada masa shayin da shi in sha Allah Mama” Sosai farin cikin fuskar Yakumbo ya kasa boyuwa tace “To Allah ya kara girma ranki shi dade tun jiya nake son maki magana amma ina tsoron yanda zaki dau maganar, na fi shekara uku ina ma Yarima haka, duk ranan da na tabbatar zan zuba masa maganin sai in dafa shayin da kayan kamshi sosai ta yanda bazai ji kamshin maganin ba, Yarima zagaye yake cikin makiya da mahassada bai da wani masoyi da ya wuce Mai martaba sai Jawwad a gidan nan, rayuwarsa na cikin mugun hatsari a gidan nan, ba sai na bude baki na gaya maki wasu abubuwan ba da kanki duk zaki fahimta daya bayan daya” Khaleesat dai ta sauke idonta bata ce komai ba, sallama aka yi kofar Parlon, Khaleesat ta maida maganin bayanta da sauri ta boye ganin har za a bude kofar parlon, Yakumbo kuwa sai zare ido take a dan tsorace, Hajiya A’isha da Kilishi ne suka shigo parlon sai Hajiya Habiba, suka dinga bin parlon da kallo a walakance, Yakumbo kuwa ta daga hannu daya sai jero masu kirarin ban girma take daga inda take zaune kanta a kasa, Khaleesat ta gaishesu babu wanda ya amsa mata cikinsu suna tafiya cike da kasaita da gadara suka nufi dakin Yarima suka shiga suka kullo kofar, Yakumbo ta kalli Khaleesat da sauri tayi kasa da murya tace “Ranki shi dade ki dinga kulle kofar da makulli sai ki ce masu shi ya kulle kayansa daga ciki in dai ba idonsa biyu ba, shigar wasun su cikin dakin nan ba alkhairi bane wallahi, babu abinda baza su iya yi ba, yanxu da kiyi dubara ki bi su ciki Khaleesat dai tayi shiru, sai kuma ta gyada kai tace “To Mama” Yakumbo ta mike still murya can kasa tace “Kiyi kokarin hada masa shayin yau da maganin don Allah, shi yasa ma na taho da matacin da zaki ta ce shayin da shi in kin zuba Daga haka tayi ma Khaleesat sallama cikin girmamawa ta fice daga parlon, Khaleesat sai kallon kofar dakin take ganin har yanxu basu fito ba, kasa daurewa tayi ta mike ta nufi cikin dakin ta bude ta shiga, duk ta samesu tsaye sun zagaye gadon suna kallonsa, shi ko yaki bude ido duk da shigowarsu dakin sai da ya tashesa daga baccin da yake amma he still pretends he is sleeping, duk suka juya suna kallon Khaleesat da ta shigo, da wani expression Kilishi tace “Ko baki da hankali ne yarinyar nan, muna ciki zaki shigo saboda rashin kunya? Ba a koya maki ladabi bane a gidan ku? Ko mu din sa’an iyayenki ne?” Khaleesat ta sunkuyar da kanta, Ajay ya bude idonsa ya mike zaune fuskarsa daure to stop them from saying more to her, Kilishi bata sake cewa komai ba ganin ya tashi zaune, Khaleesat dai ta juya a hankali ta fita daga dakin, Hajiya Habiba na kallon Ajay tace “Sannu ya jikin?” A takaice yace “Na ji sauki, Alhamdulillah” Hajiya A’isha tace “Allah ya sauwake” Daga haka ta juya ta fice daga dakin, Hajiya Habibah ta bi bayanta, Kilishi ma tayi haka, duk suka koma parlorn, Hajiya A’isha na kallon Khaleesat strictly tace “Idan kika ce a haka zaki zauna cikinmu wallahi sai zaman gidan nan ya gagare ki, this house will be nothing but a living hell for you tunda naga alamar ke din mara tarbiyya ce mara kunya er kananun mutane baki san na gaba da ke ba, ke har er gidan uban wacece ma tukun kike neman goga kafada da mu, ko ‘ya yanmu har ki mutu baki isa goga kafada da su ba balle mu, amma mu zuba da ke a gidan nan” Hajiya Habibah tace “Gaskiya sai an gyara mata zama yarinyar nan naga tana da rawan kai, kin san dan talaka sannan gata bazawara, don sabuwar amarya bazata taba wannan rashin da’an ba” Daga haka duk suka fita daga parlon, Khaleesat dai bata dago kanta ba, can ta mike a hankali zata hada masa shayin da Yakumbo tace ta hada masa.

