Haihuwa Da Hanji Page 11 Hausa Novel
Wani irin kallo ya watsawa Samha da ya sa ta koma ta zauna sai kuma ta fara hawaye, juyawa yayi ya kalli hajiyarsu da tunanin za ta yi mata faɗa sai ya ga ma kallon shi take da expression na mamaki a fuskanta.”Mayya fa ka ce Salim? Shi ne za ka tura ta ɗakin autana ta fara da ita? Me ya hau kanka da za ka kawo mana cutarwa gida after all faɗi tashi da muka sha don mu ga mun inganta rayuwar mu?”Kasake yayi yana cigaba da kallon mahaifiyar tashi bai taɓa tunanin zai fuskanci wani matsala daga Mommy ba, ya zaci ta san zafin ɗa kuma ɗan wani ma zai iya zama nata musamman idan ta ji cewa Marainiya ce don ta fi kowa danɗanar wahalar da maraici ke janyowa.”Mommy na ɗauka Afeefah Abar tausayi ce da muddin na ba ki labarinta za ki karɓeta hannu bibbiyu, ki rungumeta tamkar su Samha wallahi mu ma Allah zai dube mu ya ba mu ladar kula da ita””Dakata Saleem! Dakata min don Allah! Ka kawo yarinya kana ikirarin danginta sun guje ta saboda Mayya ce da tun tana ciki take cin maita ta ci har uwar da ta haife ta da ubanta ka kuma yi expecting in karɓeta? Ta cinye min ku kenan? Ko ni kake so ta cinye maka? To ba da ni ba salim… Ba a gidan nan ba maza maza tun dare bai ba tarkatata ka mayar da ita inda ka ɗauko ta tun muna shaida juna je ka fitar min da yarinyar nan a gida ba za mu taɓa shiryawa ba…”Hankali tashe ya ɗan kalli kofar ɗakin Samha kar Afeefahn ta ji ya matso ya riƙe hannun mommyn.”Mommy wallahi ba gaskiya ba ne duk fa zargi ne da Ƙazafi irin na mutanen duniya, wallahi Afeefah is innocent mommy ki tausayawa rayuwarta don Allah. Mu ma fa marayu ne ki saka ta a sawun su Samha idan da ɗaya daga cikinmu ne ake yiwa wannan kazafi za ki iya jura? Za k….”A hasale ta katse shi “Na rantse da Allah zan tsinka maka mari salim ka sake alaƙanta yarana da wanchan Abar, eh ku marayu ne amma da ba ku ci naman kowa ba uban wa yayi muku Ƙazafi? Bari ka ji ba’a taɓa yaɗa jita-jitar da bashi da kamshin gaskiya ba. Kafin na hasala na haɗa da kai ka je ka fitar min da yarinyar nan a gida…”Samha da har lokacin take hawaye tace “Innalillahi wainna ilaihi rajiun ni dai mommy wallahi ba zan iya sake shiga ɗaki na ba”Sadiqa tace “Ni dama daga ganinta na ji har ga Allah bata kwanta min ba, sai nuƙu-nuƙu take ashe babu gaskiya a lamarin ta”Sameera ta yi kwafa “Nan ma ba ki ga idanunta bane, duk abin tso…””Kun yi min shiru ko sai na sassaɓa muku? Da ku nake magana ne? Ko na kira sunan dayanku anan? Kun ga kun yi kama da waenda zan nemi izininku kafin aiwatar da abin da yake daidai? Duk cikinku akwai wacce ta isa ta hanata zama a gidan nan ne?”Ya daka musu tsawa Ranshi ya kai ƙololuwar ɓaci duk mommy ce ta ba su wannan ƙofa amma ya zai yi?Gaban mommyn ya koma ya kama hannunta idanunshi kaman garwashi don saura kiris ya fara yi mata kuka a yadda yake jin zuciyarshi ya ce “Don girman Allah mommy kar ki koreta, ba zan iya bari ta tafi ba mommy in ta fita a gidan nan ina za ta je? Musulma ce fa ‘yar uwarmu kuma mace, ko don aikina na kare lafiyar al’umma mommy ba zan iya tura Afeefah waje ba, Don Allah mommy ba don ni ba ki sake nazari akan hukuncin ki kar ki saka ni yin abin da zai yi hunting ɗina for life please mommy”Ganin zai kai gwiwar shi ƙasa yana cigaba da roƙon ta ya sa ta riƙe hannunshi suka koma zaune, wuri guda ta tsurawa idanu sama da mintuna biyu ta sake kallonshi duk ya marairaice yana roƙonta, Salim a yaranta yana da haƙuri yana kuma da kawaici don da wuya ya roƙe ta abu ko ya tambayeta ko da kuwa yana matuƙar bukata ko da kuwa buƙatar kuɗi ne, yana tausayinta ƙwarai gani yake har yanzu bata huta da ɗawainiya ba alhali, gidan gadon su ma ‘yan haya ne ciki bai san ya suke kashe kudin ba a haka shi yake daukar ɗawainiyar karatun ƙannenshi da cin su, tufafin su da ma sauran hidima na rashin lafiya bai taɓa gazawa ba tun da ya riƙe ƙasa to Meyasa za ta kasa yi mishi wannan alfarma guda? Amma kuma idan yarinyar ta kashe mata shi fa? Numfashi mai matuƙar nauyi ta sauƙe ta ji ana cewa Mayu sun fi cinye kurwan wanda ya taimaka musu ya ji tausayinsu kenan muddin yarinyar za ta zauna gidan sai ta cire wa salim tausayinta? Amma ta yaya?Ta sake jan ajiyar zuciya cikin gamsuwa da shawarar zuciyarta”Shikenan Salim na amince ta zauna amma fa ina da sharuɗɗa, sharrudan da zan gindaya maka wanda matuƙar ka tsallake Allah ya isa ban yafe maka ba”A firgice yake kallonta, zuciyarshi kaman zai fito waje jikinshi har yana wani rawa don ba ya wasa da Abin da ya shafe ta, me yayi zafi da Allah ya isa? Da kyar ya iya buɗe bakinshi da yayi masa nauyi ya furta”Allah ya isa mommy? Ni??”Ta gyaɗa kai cikin alamun tabbatarwa tana kawar da idanunta daga kallonshi kar ma ya bata tausayi kuma ta san muddin ya amince ba zai taɓa tsallakewa umarnin ta ba.”Sharuɗɗan su ne babu ruwanka da abin da ya shafe ta, za ta zauna zan bata abinci sau uku kaman kowa, za ta yi aikin da ya kamata a ce kowacce mace na yi saidai duk wani abu da ka ga na yanke a kanta babu ruwanka, do not question me a kan duk abin da ya shafe ta i repeat! Magana ta fatar baki tsakanin ku in har ya wuce minti ɗaya ban yafe maka ba, ni zan duba in ga cancantar saka ta makaranta ko akasin hakan idan zaman ba na ɗore bane dole za ta bar gidannan ka kuma yanke kowace alaqa tsakanin ku, ko da ko sannu ne”Ya yi jimmm kanshi ƙasa duk ya damu kan ya sauƙe numfashi “Shikenan mommy in shaa Allahu zan kiyaye umarnin ki”Yana kai nan ya miƙe ya bar musu parlorn Ranshi na ƙuna, da yana da mata babu abin da zai hana shi riƙe Afeefah tamkar ‘yar sarki ya ba ta ingantacciyar rayuwa, a yanzu ma bai fidda tsammani ba ya amincewa mommy ne da tunanin with time za ta sassauto daga kudurinta.Tuni suka cika parlorn da hayaniya bayan barin shi suna uzzurawa mommyn akan me yasa ta amince da zaman yarinyar gidan? “ku yi shiru ku bar ni da shi, ai in bata ga wurin zama ba da kanta za ta fitar da kanta daga gidan ba sai wani ya kore ta ba.”Ta miƙe ta nufi ɗakin Samha tana jin abin da zuciyarta ke gayamata daidai ne, duk suka rufa mata baya wane sarauniya da fadawarta.Suka sameta zaune inda take tun bayan idar da Sallar ta idanunta suna zube a farantin abincin da ko loma uku bata yi ba saboda tunani da ya ci karfin kwakwalwanta, tsoro ne sossai da fargaba suka danne yunwar da take ji don rabonta da abinci tun da suka karya da Baaba da safen a asibiti.”Ya ma Sunanki?”Mommyn ta tambaya tana sake ƙare mata kallo.”Afeefah” ta amsa a hankali.”Ban san wani kalar tsafin kika yi wa Saleem ba da har karo na farko ya zaɓi bijirewa umarni na a kanki, amma bari mu ga ko ke kin san hallaci? Zan ja miki federal warning akan yarana don ni karan kaina ban san abin da zan iya aikatawa ba a kansu, hawainiyarki ta kiyayi ramata idan kina cin ƙasa to fa ki kiyayi na shuri wallahi ko da wasa ‘ya’ya na suka yi ko da ciwon kai ne hmmmm”Ta kara hmm ɗin da wani irin siga na razanarwa, “ana magana ba za ki amsa ba?”Sadiqa tayi maganan tana hankada ta da kafar ta A ɗan razane ta gyaɗa kai.”Tashi in kai ki inda za ki zauna, ki ɗauki farantin nan don daga yau a ciki za’a na baki abinci har Allah ya raba mu da ke, kuma ba ki isa a saka miki abinci ki bar mana ba don a nan ba ma almubazzaranci da gumi muke nema don haka dole duk abin da aka saka miki haka za ki cinye. Shara, mopping da wanke-wanke su ne aikinki. Am I clear?”Sameera tace “Kai mommy ke ma ina wannan ina jin turanci? aka ce kin fahimta?””Eh na fahimta”Ta amsa cikin rawar murya.”Tashi mana ni ki bar min ɗaki, ko za mu tsaya muna jiran ki ne?”Dole ta miƙe da sauri ta ɗauki kayanta da plates ɗin ta bi bayansu, ta kofan baya suka fita suka miƙa har Boys quaters jin hayaniya da hira haɗe da dariya kuma Muryar maza ya sa ta sake tsorata, isan su varender ɗin Hajiya ta shiga buga cikin aihinin main building ɗin ɗaya daga cikin su ne ya leƙo ganinta ya sa ya koma da gudu ya ƙira sauran suka fito su uku. Ba manya bane chan matasa ne duka masu jini a jika da fafutukar neman halal, Ishaq shi ne ke musu wanki da guga sai iliya da shi ne driver sai mudi mai gadi, ganin duk maza ya sake tsorata Afeefah me hajiyar take nufi? A sama ta ji muryarta tana cewa “ke! Ga ɗakin ki nan”Tq nuna mata wani single room dake kan varender ɗin. Da gaske a waennan garadan za ta haɗa ta, ganin yadda suke kallonta kaman kura ya ga nama ya sa hawaye ɓalle mata a take tana ji hajiyar na cewa “Mudi wannan itace mai wanke-wanke da share share za ta zauna a ɗakin nan kar in ji kar in gani””To! To hajjaju in shaa Allah za mu kiyaye”Suka juya suka tafi suka barta nan tsaye kyam.”Sannu kyakyawa”Bata tanka ba sai shige wa ɗakin da aka kira da nata da tayi da gudu ta datse kofan tare da zamewa a jikin kofan tana fashewa da kuka sossai.Dariya suka sheke da shi don tayi mugun basu dariya suna shiga ɗaki kuma suka fara gulman kyaunta, kaman daga sama suka ga an turo kofa da ƙarfin gaske duk razana suka yi sai kuma a take suka wani irin zubewa ƙasan ganin Saleem riƙe da bindiga muraran, fuskan nan yayi Red babu wanda zai iya cewa ya taɓa ganinshi cikin wannan yanayin a take jikinsu ya tsume cikinsu ya shiga ba da ƙarar tsoro suna tunanin me suka yi?Iliya ke ta maimaita”Yau mun shiga uku mun lalace allurar ce wallahi ta tashi a kanmu ya Allah ga mu gareka..”Kuuuuu haka kowa cikinshi ke ba da sauti ganin ya sake haɗe fuskan nan tamau, ya samu hannun kujera ya zauna tare da ɗora kafan shi daya kan kujerar ya sa bindigar ya ɗan sosa goshinshi yadda za su sake gani da kyau su tabbatar, ya sauƙar yayi kooking ta ba da sauti tuni suka maƙale juna suna kakkarwa kaman kadangarun da suka faɗa wuta sai salati suke. Ya ce cikin dakakkiyar murya “Menene wannan a hannu na?”Mudi da yake jin yana shiru saleem zai iya fashe kanshi don an sha ce musu idan allurar sojojin ta tashi bata da hankali ana ɓata wa sojan rai sai kisa yayi carab ya ce murya na rawa “Abin kashe mutane””sunanta na tambaya!!”Ya faɗa a hasale da kuma gaske a mugun hasalen yake, Ishaq yayi saurin cewa “Sunanta bindiga wallahi bindiga sunanta””Kun dai san ni soja ne, kuma ina da lasisin harbata ko?” Sai kai suke gyaɗawa kaman kadangaru “Buɗe baki za kuyi ku amsa ni malamai”Tuni suka cika ɗakin da “Eh, tabbas! Haƙiƙa hakane!””To ku buɗe kunnuwanku da kyau ku ji ni, wannan yarinya da Hajiya ta kawo ta nan ko kallon da ya wuce na seconds kuka yi mata bare magana ta fatar baki ba tare da kwakwaran dalili baaaa…”Ya miƙe tsaye ya isa inda suke ya ɗodɗora bindigar kan kowannen su yace da ƙarfi”Toh tabbas sai ya kwana a lahira!!! Ina Fatan kuna ji na da kyau??”Suna zare numfarfashin tsoro da kaɗuwa suke amsawa a tare “Mun gane wallahi mun gane, ba za mu kuskure ba ranka ya dade yallabai”Ya ɗan matsa baya.”Kar ku ga kaman ban cika zama ba, gidannan ko ta wani ɓangare ina da abin ɗaukar video a ɓoye waninku ya gwada saɓa doka ta ya gani…”Yana kai nan ya juya ya fice bayan ya sake nunnuna musu bindigar a Goshi ai da gudu iliya da mudi suka fara rige-rigen isa bayi sai zawo…! Ko magana cikinsu babu wanda ya sake yi a haka baccin dole ya kwashe su dukunkukune da juna.Ya ɗan jima tsaye yana kallon kofan ɗakin nata bayan fitanshi kan ya wuce, yana tsaye a balcony ɗin shi na sama ya ga isar mommy da ita wurin abin ya matuƙar damun shi, ta ya mommy za ta haɗa mace da maza har uku waenda ba muharammanta ba? Tsoro ne ya mamaye zuciyarshi ba zama yake ba yana matukar tsoron wani abu ya sameta ba zai iya yafewa kanshi ba, wayanshi ya fitar ya kira Rayyan.Ringing na ƙarshe ya ɗaga da sallama “Ya aka yi ne man?””I need your advice, ni ne na kawo lu’u lu’u mai tsananin daraja da ƙima sai na rasa inda zan killace hakan ya sa dole na ajiye a inda ba ni da tabbacin za ta samu tsaro da kular da ta dace da darajar ta, ban gama nazari ba sai na kyalla ido na hango wasu kananun ɓarayi da basu kai ko da shakar numfashi ɗaya ba suna zagaye wannan lu’u lu’u da kallon da ban gamsu ba, idan ba zan iya tafiya da wannan lu’u lu’u ba kuma dole zan tafi wani mataki kake ga ya kamata in ɗauka?”Ryan ya ɗan yi shiru na seconds kan ya ce cikin dakakkiyar voice ɗin shi “Dukkan yanki ba’a rasa ɓarayi kuma ko wani ɓarawo yana da uban gida, idan har kai ne uban gidan wannan ɓarayi kana da dama da ikon gargaɗi mai zafi irin na asalin maza ba mata ba, ina mai tabbatar maka daga zarar sun tsorata da gargadin ka ko kallon hanyar da wannan tagulla take ba za su sake ba”Lumshe ido yayi”Na gode”Ryan ya kashe wayanshi.Ya ɗan sake nazari kan ya saki murmushi ya juya ya je ya ɗauko bindigar ya wuce sashen. Dariya kaɗan yayi tuna yadda suke ta zazzaro idanu suka jike jagwaf da gumin tsoro…



