Hausa novels

Mijin Marigayiya Page 56 Hausa Novel

Ba tare da wani musu ba ta mike ta tasa Nasreen da Shukra a gaba tana biye da su yayinda Mustapha da Habib suke biye da ita.Anti Wiyya ce a zaune a kan kafet da kwanuka a gabanta suna cin abinci ita da Rukayya yayinda Naja take zaune a kan kujera tana cin nata abincin suna hira. Da yake kicin a buda yake ana hango mai aikinta da goyon baby tana goge-goge.Shukra ce ta fara shiga tana surutu don haka a fusace Anti Wiyya tace ‘To sarkin tsurku, ba cewa aka yi ku zauna a kasan ba shine kika shigo kina….’A lokaci guda kuma Naja tace ‘Ai sai nayi maganin wannan yar…’Sallamar Hajia ce ta katse musu zantukan, ta karsa ciki yayinda Shukra ta zagaye ta koma bayan Abbanta. Suka karasa ciki suka zauna yayinda Naja da Wiyya suka diririce.Naja tayi wuf ta mike ta kwashi kwanukanta tana cewa ‘Bari na wanko hannu.’ Ta nufi kicin cikin sauri.Itama Wiyya ta kwashi nata kwanukan ta mike tana cewa ‘Sannu da zuwa Hajia, bari na kawo miki abinci.’Rukayya tace ‘Anti ban koshi da naman ba.’ Bata ko saurareta ba ta wuce kichin yayinda ita kuma ta tashi ta bi bayanta da sauri.Sai dai duk saurinsu kowa ya riga ya ga abinda yake cikin kwanukan nasu; farfesun kaji ne wanda suke hadawa da burodi da shayi suna ci.Bayan sun zauna Hajia ta dubi Mustapha sannan ta dubi Nasreen tace ‘Nas ku ina naku naman naga kuna cin gayan burodin.’Tayi darya tace ‘Ba a bamu ba, dama kullum abincin sama da ban da na kasa har garama idan Abban yana nan.’Hajia ta sake kalloshi tace ‘Allah ya sauwake.’Naja ce ta dawo parlor din ta zauna a kan kafet ta gaida Hajia, bayan ta amsa ta dubi Nasreen tace ‘Jeki kicin ki taya Anti Wiyya ta daukowa su Hajia abinci.’Hajia ta daga hannu tace ‘Ki ce ta barshi, ku barshi ma, abincin da naga bai isa an raba da yara ba ai ba zai isa har a bawa bako ba. Ni na ci abincina ku barshi na koshi.’‘A’a Hajia ai akwai, suma hawowa ne basu yi ba nake jira Jummai ta gama wanke-wanke ta mika musu.’‘To me zasu shigo suyi, su da zaki yi maganinsu. Ai sai dai kawai a cigaba da addua kada a wayi gari kin korosu daga gidan kamar yanda kika koro dan uwansu cikin dare.’ Hajia ta bata amsa.‘Wallahi Hajia babu wanda ya koroshi.’‘Allah ne kawai zai gane gaskiya, amma dai ke kiji tsoron Allah. Kin bani kunya, wallahi kin bani kunya! Ban taba zaton haka daga gareki ba. Gaba daya mun zata zuwanki gidan nan zai sa yaran nan su sami kulawa ta musamman ashe ba haka bane. Ke da uwarki da ‘yayanki kuna sama kuna cin kaji yaran suna kasa suna fama da burodi. Kuma ma har sharadi aka kafa musu cewa kada su hawo su dameki. Kamar dai ba gidan ubansu ba.’Suka yi shiru kamar ruwa ya cinyesu.Hajia ce ta karya shirun ta dubi Mustapha tace ‘Kai dai baka kyauta ba, yanzu rayuwar da kuke yi kenan? Su wadannan da uwarsu ta mutu kun barsu a kasa kuna sama kuna jin dadi. To kaji tsoron Allah. Kema kuma ki ji tsoron Allah. Bana jin sun taba ganin haka a wajen Khadeeja, ashe dama jira kike ku koreta daga gidan ki cuzgunawa marayun Allah.’Ta sunkuyar da kai kamar wadda zata dungura. Habib yace ‘Ai tunda suka dawo daga Saudiyya aka hanasu hawowa na, dakinsu ma da koamai nasu ya koma kasa.’Hajia ta dubi Mustapha duba na takaici har sai da ya sunkuyar da kansa cike da kunya. Ta mike tana cewa ‘Ai shikenan, amma tabbas ba zan bar wannan zaluncin ba. Kuma ko da kin ga kamar kin yi nasara to Allah yana kallonku gaba daya.’Yaran suma suka mike, Hajia ta dubi Mustapha wanda kunya ta hanashi mikewa tace ‘Za ka samu ka mayar da ni gida ko sai ta baka izini.’Ya mike kamar wanda aka tsikara.Naja tace ‘Don Allah Hajia kiyi hakuri. Wallahi ba haka abubuwan suke ba rashin fahimta kawai aka samu wallahi ana kula da su.’Ta dubeta tace ‘Allah ya sa, ai nima haka nake so. Sai dai kowa yayidon Allah ai ya sani ko, Allah kuma yana sane.’Ta wuce yaran da Mustapha suka bi ta a baya suka fice.Har suka isa gida tana faman caccakar Mustapha a kan yanayin da ta gani a gidansa kuma tana tuna masa girman hakkin yaran nan a wuyansa da shi da matarsa. Bashi da binda zai gaya mata sai hakuri kawai yake bata; shima baya jin dadin yanda gidan ya koma tun bayan rabuwarsa da Khadeeja. Ba da son ranshi ba ta mayar da yara kasa kuma wannan raba abincin ya sha yin magana a kai. Amma ta iya abun ganin ido ne kawai, idan yana nan sai tayi kamar komai normal amma da zarar ya fita sai ta tsawatarwa yaran kowa ya shiga hankalinsa. Abinci kuwa dama idan dai ba a gidan zai ci ba tabbas abincin da ake dafawa a sama da ban kuma abincin da take bawa mai aiki ta dafawa yaran da ban ne. Duk wani dadi a sama suke ci ita da yaranta da ‘yan uwanta su kansu yaran har sun saba. Gashi ta hanasu kula ubansu sosai, domin in dai yana saman nan bata barinsu su ganshi. Har sun gaji da yanda take musu sun hakura sun ma daina cewa suna son magana da shi.Haka ya karasa gidan ya ajiye Hajia a bakin gate ya dawo saboda baya son ya shiga ciki saboda ya san ba zai ji da dadi ba a wajen Alhaji.Suna fita Anti Wiyya ta fito daga kitchen jiki a sanyaye, ta zauna kusa da Naja ta kama haba tana cewa ‘Ikon Allah, kin ji mutane ko? Ko motsin shigowarsu bamu ji ba sai kace shiri.’Ta tabe baki ‘Hmmn! Su suka sani. Dama tafiya yayi ya kai rahoto shi yasa ya bi dare su kuma basu yi tunanin su kirawo mutane su sanar cewa ya isa can ba saboda sun shirya tsiya. A kansu zata kare in sha Allahu.’Ta mike kamar an tsikareta tana cewa ‘Bari ki gani na hada kayana na bar gidan nan kafin ya dawo ya koreni da kansa.’‘Haba Anti, saura sati biyu dama fa ki tafi tunda kin ce ba zaki yi mim arba’in ba. Kiyi zamanki babu abinda zai yi.’ Ta fada tana gyara zama.‘Wallahi tafiya zan yi, da wanne idon zan kalleshi ya riga ya gama rainani. Ina nan ina yagar kaza na bar masa yara suna fama da gayan burodi.’Ta marairaice ‘Anti idan kika tafi ma in ya dawo ai sai yace bani da gaskiya.’Ta nufo kasa don hada kayanta tana cewa ‘Ku kwashe kalau amma ni da mijinki ba zamu sake haduwa ba in sha Allahu, ko a kwararo balle ma a gidansa.’Tana ji tana gani Anti Wiyya ta fice ta bar mata gidan.Bata dade da fita ba Mustapha ya dawo.Yana shiga parlor din kasa ya tara da Afaf ta fito tana shan bakin shayi da burodi yayinda sauran yaran suke zaune suna kallon TV.Bayan ya amsa sannu da zuwansu ya karasa ya zauna a kusa da Shukra, ya kalli kofin shayin Afaf wanda ta ajiye a kusa da ita tana kokarin sake yago burodi. Yace ‘Ya kike shan bakin shayi Yaya?’

Back to top button