Halysaah Page 217 By Khaleesat Haydar
HALYSAAH PAGE 217…Daga sama har kasa Jay ke kallon Ajay yace “Dauko min roban drip din” Ajay yayi dariyar da bai yi niyya ba yace “You can check the waste bin, na riga nayi disposing dinsa, why will i leave it inside the room” On a serious note Jay yace “In dai kasan cire drip din nan ku ka yi kai da ita, to ka sa ta ta maida maka shi” Ajay dai kawai dariya yake, Jay yayi masa wani kallo ya juya ya fita daga parlon. Da safe har karfe goma da rabi Khaleesat na kwance a bedroom din Ajay cikin duvet, breakfast din da ya kawo mata ma bata taba ba, ya shigo dakin ya ajiye wayar hannunsa sannan ya karasa kusa da gadon ya zauna gefenta yana kallonta yayi kasa da murya yace”Jeeddah” Bude idonta tayi a hankali tana kallonsa, yace “Baki yi breakfast ba har yanxu wife” Tayi shiru bata ce komai ba, ya duka kusa da fuskarta yace “Or are you still angry?” Ta dan yi murmushi ta girgiza masa kai, a hankali tace “Kawai na gaji ne” Yayi shiru yana kallonta, ya kamo hannunta cikin nasa yace “Nayi stressing din ki jiya da daddare ko?” Tayi wani murmushin tana girgiza masa kai, yayi kasa da murya yace “Are you sure?” Ta kara gyada masa kai, tashi yayi ya tafi inda ya ajiye mata breakfast ya hada mata tea sannan ya koma kusa da ita ya dagota ta zauna, ya dauko mata tea din ya bata, ganin zai dibar mata wainar shinkafa ta girgiza masa kai da sauri tace “Zan gama shan shayin tukunna” Ya mayar da murfin warmer din ya rufe sannan ya dawo kusa da ita ya zauna yana kallonta, ita dai shan shayin take a hankali amma da kyar take hadiyewa, Ajay na kallonta a hankali yace “l spoke to a palace guard this morning about Baaba Yakumbo don naga suna mutunci da shi, shi ma tunda ta tafi yace bai yi reaching dinta ba ko ta waya, number dinta baya shiga, amma ta taba gaya masa garinsu, so na aikesa gobe zai je garin nasu in sha Allah, Allah dai ya sa ya sameta” Khaleesat ta ajiye cup din hannunta da sauri kan bedside drawer don ta kasa ci gaba da daurewan da take, yace “You want to throw up?” Bata tsaya basa amsa ba tayi cikin bandaki da sauri tana toshe bakinta, ya mike ya bi bayanta, duk sai da ta amayar da dan shayin da ta sha yana rike da shoulders dinta ta baya yana mata sannu, ya wanke mata baki ya fito da ita daga bandakir she was already shivering, ya rufa mata duvet ya zauna kusa yana mata sannu da damuwa a fuskarsa don duk tunaninsa he stressed her yesterday night, ita dai ta kasa amsawa tana rawan sanyi, kan kace me jikinta ya dau zafi, temperature dinta yayi sama sosai. Daga wannan rana Khaleesat tayi bankwana da lafiyarta, itada ta zo jinya sai ita aka bige da jinyarta, rashin lafiya sosai ta fara yi na laulayin ciki, a dan kankanin lokaci ta fice hayyacinta ta dawo kamar ba ita ba, bata iya cin komai, ko ruwa bata son gani kusa da ita, ba kadan ba take jin jiki, duk ta sa Ajay ya dawo wani iri shi ma saboda tausayinta, ya ji kamar ya zubar da cikin ta huta kawai, ko da yaushe zaka sameta ana mata karin ruwa, duk da ita ma Hadiyah ba lafiyarta ce da ita ba amma gwara ita sau dubu kanHalysaah tunda ita tana cin abinci tana komai, da yamma ne zazzabi ke rufeta shi ma tana bacci shikenan sai kuma gobe, Mami ce ke jinyar Halysaah don sosai take bata tausayi saboda ita ma haka ta ji jiki da ta samu cikin Jawwad kamar bazata yi rai ba, daga karshe Mami ta maidata part dinta gaba daya tana kula da ita, ba kullum Aunty Faridah ke shiga duba Khaleesat ba a part din Mami tunda babu abinda Mami bata mata beside ita ma is not as if she is okay, sannan yan gidan ma duk suna zuwa dubata a part din Mamin, Hajja kuma duk ranan Laraba da lahadi take shigowa gidan saboda Khaleesat. Ranan wata friday Ajay ya shigo dakin Mami don a nan Khaleesat take tunda Mami ta maidota part dinta, as usual tana kwance, ko juyawa bata yi ba taga wanda ya shigo dakin, yaga Jay bai sa mata drip ba ranan don duk shi yake mata karin ruwa idan na zuwa asibiti ne shi da Mami suke kai ta for scan and everything, Ajay ya karasa cikin dakin yana tafiya slowly yana kallonta don tun da ta fara rashin lafiya ta dena kwanciya saman gado sai dai a kasa, dukawa yayi gabanta yana kallonta, ta bude ido a hankali tana kallonsa, sosai ta rame har da kashin wuya, sosai zuciyarsa ke karaya a yanda yake ganinta, ya dagota yana gyara mata gashinta don hulanta ya cire, hawaye suka fara zuba idonta a hankali ta kwanta a jikinsa, cikin sanyin murya tace “Na gaji….” Zaunawa yayi kusa da ita ya rungumota yana patting bayanta ya ma rasa me zai ce mata, he wish zai iya maida abinda take ji zuwa jikinsa, a hankali yace “l am sorry for making you go through all this Jeeddah” ita dai hawaye kawai ke zuba idonta tana sauke numfashi a hankali, shigowar Mami dakin da Custard a cup yasa Ajay ya kwantar da ita kawai ya mike ya fita daga dakin yammacin ranan wajen karfe shidda saura Ajay sun dawo gidan Hajja shi da Jay sun je gaisheta, Ajay ya sa Jay ya tsaya a wani pharmacy don shi ke driving din, Jay na kallonsa yace “Me zaka siya?” Ajay yace “| think | am having sore throat zan siya magani” Jay bai ce komai ba yayi parking Ajay ya sauka ya shigazaka siya?” Ajay yace “I think 1 am having sore throat zan siya magani” Jay bai ce komai ba yayi parking Ajay ya sauka ya shiga pharmacy din, bayan wani lokaci sai ga shi ya fito, ya bude passengers seat ya shiga, ya ciro lozenges da ya siya for sore throat ya bude ya jefa daya a baki, Jay dai kallon aljihun gaban rigarsa kawai yake ganin Pouche din magani a aljihun, har ya tada mota kawai yayi taking din sa unaware yayi saurin ciro Pouche din dake aljihun, Ajay zai fixge Pouche din Jay ya mayar bayansa yace”Me ka siya kake boye min?” Ajay ya hade rai yace “Dallah ka bani, kai komai sai ka sa ma mutum ido” Jay dai kallonsa kawai yake, although yasan halin Ajay, yasan abinda zai yi da kuma wanda bazai yi ba, but at this point sai kawai yayi tunanin ko dai Ajay ya canza halin nasa ne dąga yanda ya san sa, babu abinda yaje mind dinsa dake ‘cikin Pouche din da ya wuce Prophylactic don shi dai bai ga alamar yana sore throat ba, kuma tun suna gidan Hajja ya kagu su bar gidan wai akwai inda zai je anjima, ya kuma ki fadin inda zai je din, Ajay zai amshi Pouche din hannun Jay amma Jay yaki basa, wani kallo kawai Ajay yake ma Jay, Jay yace “Kafin in duba menene a ciki gwara ka fadi menene da bakin ka” Ajay yace”To bazan fada ba” Jay ya bude motar ya sauka don ta haka nekadai zai duba takardan maganin ba tare da Ajay ya karbe ba, Ajay ma ya sauka, barin wajen Jay yayi gaba daya, Ajay ya zaga ya shiga driver seat ya ja motar yayi gaba ya bar sa a wajen, Jay ya bi motar da ido, har cikin ransa yake jin ya kasa duba abinda ke cikin takardan maganin da ya amsa a wajen Ajay, after some seconds kawai ya kai zuciyarsa nesa ya bude takardan yana kallon abinda ke ciki, a hankali ya fiddo maganin da mugun mamaki yana jujjuyawa yana kallo. Ajay na zaune parlonsa Jay ya shigo, Ajay ya kallesa sau daya kawai ya ci gaba da danna wayarsa, Jay ya zauna opposite dinsa yana kallonsa, after some seconds yace “Junaid me zaka yi da maganin da ka siya?” Ajay bai tankasa ba, Jay yace “| am talking to you Junaid” Ajay ya gyara zama yace “Ni zan sha” Jay yace “Ciki gare ka da zaka sha?” Duk da haushinsa da Ajay yake ji sai da ya basa dariya, can yace “Tunda matata na da ci duk daya ne” Jay ya girgiza kai yace “Zubar mata da’ cikin z kenan?” Ajay yace “To kai fisabilillahi baka ga wahalan da take bane?” Jay yace “And so? Ya kake abu kamar ba likita bane?” Ajay yace “Ni bazan iya ci gaba da jure ganinta a haka tana wahala ba, , ai haihuwar ma ba dole bace” Jay yace “lkon Allah, ji wani maganada kake kamar illiterate, to wallahi idan wani abu ya samu cikin Halysaah you will be held responsible, daga nan kuma Mami zan je in sama tasan me ke faruwa, har Mai martaba sai na sanar masa” Ajay dake ta kallonsa yace “Why not ka shiga Masallaci ka yi amfani da mic din ciki ka hutar da kanka bin sashi sashi kana sanarwa….” Jay yace “Ohk ka zuba ido kaga ikon Allah” Yana fadin haka ya mike, Ajay ya tare gabansa yace “Ka dai san ba da niyyar cutarwa na siya maganin ba dai ko? Ta yaya ma zan cuci matata” Jay yace “Ohk da niyyar mugunta ka siya tunda ba da niyyar cutarwa bace? Naga dai bata ce maka bata son cikinta ba, for more than 4 months now yarinya na shan wahala sai a sanda wahalarta ya kusa zuwa karshe sannan kace zaka zubar mata da ciki?” Ajay ya sauke idonsa yace “Kusan wata na biyar kenan fa har yanxu wahalan laulayi take, kaga dole in tasaya mata in rabata da cikin, ni ko bazata haihu ba i won’t bother as far as I have her” Jay yace”To sannu Sarkin masu tasayin duniya, kuma kai laulayin nan da take ba gwara shi akan fitinar da ta tsiro farko farkon cikin ba, kaga yanxu tana kwance ba sakawa babu hanawa sai dai ace mata sannu ta gyada kai, ko bakin magana bata da shi” Ajay ya koma ya zauna yaçe “Gwara min fitinarta sau dubu akan irin wannan laulayin, i wish fitinar ta ci gaba da yi har Allah ya sauke ta lafiya” Jay yayi murmushi yace “Fitinar da ka kasa enduring for just a day a Benue kake son a ci gaba da yi maka? Gwara dai wannan din da kake tausaya mata, amma zubar da cikin ba option bane kar ma ka sake kai tunanin ka can, nan da wani lokaci zaka ga ta dawo normal kamar bata yi ba” a hankali Ajay yace “But that is taking too long, kalla fa yanda ta koma….” Jay yace “Ni da nake treating dinta nake kula da lafiyarta ban yi korafi ba sai kai me zuwa dubiya kawai, to yanxu ka shirya jin gender din babyn?” Da sauri Ajay yace “A’a, nace maka bana son jin komai, don’t say anything about that to me pls….” Jay yayi murmushi yace “To mata biyu kake son zubarwa bari kaji in gaya maka, I can’t hide it from you anymore” Ajay ya dinga kallonsa babu ko kiftawa yace “Da gaske don Allah Jawwad?” Jay na murmushi yace “Gashi yau na gaya maka, dubu dari kawai nake so as tukuici na” Ajay yayi shiru ya kallon Jay, deep down he was grateful to God da bai basa daman aikata abinda yayi niyya ba na zubar da cikin, Jay dai kallonsa kawai yake cause he could see how his mood ligten up all of a sudden, Jay na murmushi ya zauna yace “Kasan me nayi tunaninka siya a pharmacy din nan?” Ajay Kallonsa kawai yake cause he was filled with excitement jin wannan labari me dadi da Jay ya gaya masa yanxu, Jay yace “All my thinking Prophylactic ka shiga ka siya a pharmacy din fa” Ajay ya dan bude ido yana kallon Jay yace “Iskanci na fara kenan kake nufi?” Jay yayi dariya yace “To na sani? Tunda yau wata nawa rabon ka da mace” Ajay yayi murmushi kawai yaki tanka Jay don farin cikin da yake ciki ma bazai sa ya biyesa ba, kawai ya dau wayarsa yayi masa transfer din katin dubu darin da yayi requesting as tukuici.4 months later….Khaleesat na kwance parlor bayan isha’i, suna cikin chat da Aunty Farida da bata kasar bacci ya dauke ta, a haka Ajay ya shigo parlon ya sameta, ta bude ido jin budewar kofa tana kallonsa, ya zauna kusa da ita yana yana gyara mata gashin kanta a hankali yace “Kin ci abincin kuwa wife?” Ta gyada masa kai tace “Na ci, don Allah gobe zaka kai ni asibitin da safe?” Ajay yace “She is been discharged” Kokarin mikewa zaune ta fara yi, ya dagota tana zaro ido tace “Da gaske an sallameta?” Yace “Yea tare muka dawo gida yanxu” Tana murmushi tace “Tana part dinta ne?” Yace “A’a tana bangaren Hajja” Dafa sa tayi ta mike tsaye da kyar with his help, tace “Zan je can” Yace “Za ki iya kuwa?” Wani kallo ta masa, ta dau hijab dinta ta saka ta fita daga parlon shi dai ya bi ta da kallo yana murmushi, Khaleesat na isa part din Hajja taga su Hajiya A’isha dukkansu zaune a parlor sun shigo barka, ta gaishesu gaba daya, suka amsa, Kilishi tace “To dai saura ke, Allah Ubangiji ya sauke ki lafiya ke ma haka” Ita dai tana murmushi ta nufi dakin Hajja don taga alamar a ciki Hadiyah take, su Hajiya A’isha duk suka bi ta da kallo, sai da ta shiga dakin Kilishi tayi kasa da murya tace “Na ji dadin ‘ya macen da Hadiyah ta haifa har cikin raina, dama har addu’a na dinga yi ta haifi macen, ita kuma Halysaah ina rokan Allah ya bata namiji sai in ga ta yanda zuri’ar Maimuna za su gaji sarauta a gidan nan, in Halysaah ta haifi namiji tsaf Jawwag maida shi magajinsa wallahi, uwar Hadiyah kuma bazata so ba, da yake taji mace aka haifo ai kun ga har yanxu bata kamohanya ta zo gidan ba” Kilishi tayi kwafa tana wani murmushi tace”Akwai Film a gidan nan fa nan gaba” Hajiya Habibah tace “Wallahinima naji dadi da Allah ya bata mace, in ta kara wani cikin ma Allahyan son mulki, yanxu da buzuwar nan Farida ke auren sarki ai mun samu ‘yan ci a gidan nan, takanas take sa Sarki yayi mana kyauta me gwabi wanda bamu saka rai ba, sam bamu ki buzaye su amshe masarautar nan ba ma” Hajiya Sumayya ta wani kalli Hajiya Habibah, shigowar Mami parlon ne yasa duk suka yì shiru, Khaleesat na zaune gefen Hadiyah a dakin Hajja tana ta kallon kyakkyawan babyn da Hadiyah ta haifa, sai take ganin kamar Mami jaririyar ke kama da, amma dogon hancinta sak irin na Jay, Ita dai Hadiyah na kwance ta juya baya bata cewa komai, Khaleesat ta kalleta ganin kamar she is not in the mood to talk yasa bata ce mata komai ba tun bayan da tayi mata barka, Hajja dake zaune dakin ta kalli Khaleesat tace “Kina shan maganin da na aiko maki da shi kuwa Jiddah?” duk da Ajay ya hanata shan maganin gargajiyan ya ma dauke daga kitchen da ta ajiye amma haka ta gyada ma Hajja kai tace “Ina sha Hajja” Hajja tace “To Allah Ubangiji ya sauke ki lafiya ke ma” Khaleesat dai ta sunkuyar da kanta, mutsu mutsun da babyn ke yi a hannunta har da kuka ne yasa ta mika ma Hadiyah tace “Ko yunwa take ji Hadiyah?” Hadiyah bata juyo ba tace “Ki ba Hajja” Hajja ta tashi don bata son Khaleesat tayi stressing kanta, ta amshi jaririyar daga hannunta, har karfe goma Khaleesat na dakin Hajja ga ciwon mara ya dameta, tana son tashi ta tafi amma ta kasa mikewa tsaye don duk jikinta yayi mata nauyi sosai, dama yawanci idan zata tashi Ajay ne ke dagata tunda cikinta ya tsufa, to yanxu bai kusa da ita balle mata haka.Dan Allah ku taya ni addua Allah ya bani saa exams dina in samu A’s duka😩


