Hausa novels

Mejo Najeeb Page 44 By Autar Alheri

“Cikin sauri ummi tafice daga pert ɗin..shiko yaci gaba da wayarshi dayakeyi cikin nutsuwa yana lunshe kyawawan blue eyes ɗinshi…sosai anty hawwa tashagala da kallonshi yadda ɗan ƙaramin bakinshi kejuwa yana magana cikin aji kamar ba namujiba, ita kanta datake macen seda tarena kanta agabanshi, jitakeyi kamar taje yarungumeshi kozataji sanyi aranta,,,harya gama wayar yaɗago yana ƙare mata kallo batasan yagamaba tanacan talula duniyar shauƙinshi gaya atufe bashida riga sedai dogon wando kawai faffaɗan girjishi awaje sumar dake kwance akai se sheƙi takeyi gwanin sha’awa…ganin gaba ɗaya tamutu da kalloshi yasa yaɗan taɓe bakinshi yana ɗauke kanshi daga gareta. Kusan minti 10 suna ahakan kafin yamiƙe zuwa bedroom ɗinshi yabartanan a tsaye….bata Ankara daya tashiba seda taji ƙarar rufe Ƙofa dayayi…wuri tasamu tazauna tana sauke numfashi se matsar ƙafa takeyi dan masifa😹daganin ɗan kyakkyawan sauri seki ɗarsawa kanki lalura haba anty babba🤩 najeeb kam bayan yashiga bedroom ɗin seda yaɓata kusan awa ɗaya befitoba yanacan kwancinshi suna tattaunawa akan wannan shugaban ƴan ta’addan domin kuwa mejo tanimu yaje binciken inda suka kaishi amma an hanashi shiga a dokar wurin duk wanda ya ajiye mailaifi shine kawai keda damar shiga, wannan abun kuwa yaƙonaran Alhaji tanimu shiyasa General Aliyu yace dasun dawo daga Gombe zasu fiddashi sumakashi koto kar wani abun yabiyo baya, seda suka gama zancensu tukkunna yamiƙe yaƙara yin wanka yafita…anan yasameta inda yabarta ko kallon inda take beyiba yafice warshi…itako Jakar ko ajikinta tunanin matakeyi maybe yana saurine shiyasa bemata magana, hakan yasa tagyara kawai tayi kwanciyar ta akan kujera( nikuwa nace kina ruwa anty hawwa)Mejo nafita Captain jameel yataso yabuɗe Mishi mota suka fice segidansu general Aliyu…koda yashigo gidan bakowa a perlor se TV kawai dake kunne. Jin motsi a kitchen yasa yaƙarasa can aiko habbey naciki tana aikinta kamar yadda yayi tunani,,gaidata yayi cikin girmama, takuwa amsa Mishi cikin sakin fuska tare da yimusu murnar samun nasara a aikinsu. Dazefita ne yaɗauki plate yazubo farfesun naman rago da babbey tasauke daga wuta kana yaɗauki donut ɗaya yafito. “Yeee yah najeeb oyoyo mufeedah tafaɗa cikin farin cikin ganinshi tanayowa kanshi…murmushi yasakar mata batareda yace komaiba. “Yah najeeb kundawo lpy? “Lpy qalau rigimammiyar habbey y kk y school? “Ɗan turo bakinta tayi cikin shagwaɓar dasuka saba mata da ita tace “nidai Allah ba rigimammiya bace, yawwa garama da kadawo yau bazaka fitaba seka kaini gun anty Maryam.. tafaɗa dede lokacinda suka shigo perlor general Aliyu “Au haba? Yafaɗa yana zama kusan general Faruk..Allah kuwa yah najeeb. “Ohh Allah shikenan naji zan kaiki amma Please kibari naci abinci yunwa nakeyi antyn taki duk takwashe abunda ke cikina, yafaɗa shima cikin shagwaɓa kamar yadda takeyi, domin idan kaji bakin mejo indai ba su general Aliyu bane to auta siyana ce ko mufeedah….ido tawaro waje cikin mamaki tace “ita anty Maryam ɗin? Garin yaya zata kwashe Abinda ke cikinka yah najeeb?? “Ɗan murmushi yayi kana yace “to taɗauke abincin da mama tabani kuma ita bata dafamin waniba, yanzu dai jeki kihaɗa min coffee kafin nagama cin abincin..”to yah najeeb tafaɗa cikin zumuɗi Takoma kitchen.”Ɗan renin hankalin aida seka gaya mata yadda akayi Maryam takwashe abunda ke cikin naka ɗin takwashe ko dai kajuye mata…cewar general Aliyu…banza yayi Mishi kamar bejiba.”Ni wlh tunda naga kawani maƙalƙale yarinya acikin mutane nasan akwai ta asar dazakayi ashe kai fitinace ka kwaso darashin imani kazo kayiwa yarinya fata’fata, wlh Ziyad yabani haushi dabe lallasama bakiba kaje kasha daɗinka kazo kana yiwa mutane wasu muzurai. “Ohh sheath uhhm please kadena zancen nan Aliyu wlh ƙara maidani ruwa kakeyi karkasa nakasa cin abincin nan please, yadda kace wai nasha daɗi se daɗin yadawo min kamar yanzu ne nake jinshi, wayyoo my AK-47 I’m very sorry your sweet she’s coming back very soon ohh Allah sarki my sweet lifeee, yafaɗa yana ɗora hannu akan wandonshi tareda lumshe Blue eyes ɗinshi yana murmushi…wani irin duka general Aliyu yakai Mishi yana fadar hoo ɗan iska muzaka yiwa karuwanci anan? Waye to zakayiwa kurin mece? Ou nufinka muma katada mana hankalin kagudu kabarmu da jarabako? Dariya sukeyimishi yau hadda ƙyaƙyatawa daga general Faruk har mejo ɗin daya goce lokacinda ze dukanshi, domin sosai yabasu dariya, sunjima sunayin kafin su tsagaita mejo yace “au kuzanyiwa mana waye yakeda macen acikinku?? Haba yara wlh bakumasan minene ake kira daɗi ba labarinshi kawai kukeji kuyi aure idan zakuyi domin niyanzu ba tsaranku bane, yaƙarasa zancen yana sakin murmushi.”Kam bala’i lallai guy ɗinnan dagaske yake yi general Aliyu kawai munemi matan aure shine mutuncinmu a idon wannan dudda cewar nidai nasamu wadda Nakeso saura abani kawai,, cewar general Faruk. “Humm ai shikenan akwai Allah, general Aliyu yafaɗa yana barin perlor. Dukkansu dariya suka Mishi, mejo zetambayi general Faruk aina yasamu wadda yakeso kenan mufeedah tashigo da coffee ɗin data haɗa Mishi….karɓa Yayi yasha bayan ya gama cin abincin yafice warshi tare da jadda damusu gobe Abba tace dasafe zasuje Gombe sushirya da wuri…..tare da mufeedah yafita yakaita shopping sosai yayi mata sayayya itada isseta daganan yaje yasiya musu kayan ƙwalam tukunnah yanufi gida…suna zuwa mufeedah tawuce part ɗin Hajiya mama gun Isseta shiko yahaura pert ɗinshi”assalamualaikum anty Maryam kina inane gani nazoo, mufeedah tafaɗa cikin zumuɗin son ganin isseta juwaira ce kawai zaune a perlor hakan yasa tayi kamar bataga mufeedah ba, itako tayi kamar bataga mutunba domin mufeedah ko iskanci yasanda zamanta, bedroom ɗin mama tanufa anan sukaci karo da ummi. “Yee yammatan habbey kece hakan gaske duka gidan yaɗauke da ƙamshin yah najeeb ashe yar lelenshi ce agidan, Ummi tafaɗa cikin tsokana. Dariya mufeedah datayi cikin barkwancinta tace “anty ummi please Ina anty Maryam yau ita nakeson gani nakawomata kayanda heron ta yasiya muna. Damm daram hakan gaban juwaira yafaɗi hakama anty hawwa da shigowarta kenan daga pert ɗin mejo taji wannan zancen, cikin ranta tace “dama siyayya yaje yiwa waccan banzar shine yashanyani yanzukuma yadawo shine zekoroni, atake wata muguwar tsanar isseta taƙara rufeta.. “itakam mufeedah dariya tasaka kana tace “aibaki saniba anty ummi maƙalƙale shi nayi sabida nakwashe turarenshi amma be ganeba gaya kuwa nakwaso kinsan yaƙi siyamin irinshi danace inaso sedai wani yabani, ɗazuma fa damukaje shopping nace yasiyamin secewa yayi wai ai turarenshi na anty Maryam ne kawai tafaɗa tana turo baki gaba. “Ikon Allah wai mufeedah kece anan ina hajiyarki tana lpy? Cewar Hajiya mama dafito yanzu. “Rungume Hajiya umma tayi cikin farin ciki tana faɗar lpy qalau take mama? Itama Hajiya mama murmushi tayi tana ƙara rungumeta domin idan dasabo tasaba da halin mufeedah. Daga hakan tashige cikin bedroom ɗin tasamu isseta zaune tana shan farfesun naman rago me kayan haɗin mata da Hajiya mama tadafa mata. Cikin zumuɗi tarungume Isseta tana murna, itama murmushi tayi domin tagane mufeedah sarai itace sukaje shopping aranarda Abba yazo dasu gidan, sosai isseta ma tayi farin cikin ganinta domin balaifi itama tashiga ranta sabida mufeedah batada matsalar komai arayuwarta ita mutunce me habahaba dakowa natane sedai idan kace kai shegen kaine to zata nunama tafika zama shegen kan…..sosai suka shiga fira tsakaninsu ita da isseta dakuma ummi se dariya sukeyi kamarcan sunsaba da juna cikin farin ciki mufeedah tashiga nunawa isseta kayanda mejo yasiya musu itada ita hadda ummi ma, aiko sabuwar fira taɓarke tsakaninsu. Daga ƙarshe dai anan mufeedah ta kwana taredasu. Washe kari tunda sassafe akayi shirin tafiya Gombe inda ummi da mufeedah ne yau suka haɗa musu abun breakfast. Misalin ƙarfe 9:00am kowa ya fito akayi shirin tafiya. Mota ɗaya aka shiga ummi isseta dakuma mufeedah datace seta bisu Gombe…mejo cika kawai yakeyi yana batsewa domin aikin Hajiya mama ne tahana sushiga mota ɗaya tareda isseta…. general Aliyu da general Faruk kuwa atare suka shiga Mota ɗaya da shi mejo ɗin se tsokanarshi sukeyi…Abba kuwa da dady wato Alhaji Abubakar mota ɗaya suka shiga yayinda anty hawwa da juwaira suka shiga Mota ɗaya domin koda suka fito tuni motarsu ummi ta ɗaga saura ta mazajen kawai se su Abba..ahakan suka ɗauki hanyar Gombe kusan mota goma, huɗu nasu shida na security ɗinsu sedoka jiniya sukeyi ahanya.Gombe Yau tunda safe ammin isseta tacewa innar halima, itadai tana cikin farin ciki kila yau taga ƴarta domin tanaji ajikinta kamar Maryama zatazo yau…sosai innar halima ke dariyarta. Halima tace Ammi inaga dan kesaka son ganin isseta arankine kikejin hakan, amma dazatazo aida maah tagaya min jiya danaje wurinta…ido suka zuba mata atare sukace “tayaya kike zuwa wurinta ƴarnan??? Dariya halima tayi kana tace “da ƙafa mana aitun Isseta na nan atare muke zuwa wurinta musha fira muci hadda abinci tukkunnah mudawo.. “ikon Allah lallai yaran nan bakuda tsoro koda yake itace ai ba abar tsoroba kuda mamarku dan yanzu komu ai bamajin tsoronta balleku hadde gimbiya mardeeya ko Umaima sudake zuwanan…Ammi tafaɗa cikin murmushi.. “gaskiya kam cewar innar halima.A bakin ƙofar megarin Gombe motocin suka farayin Perking..anan take wurin yacika anata yimusu maraba…su Abba ne suka fito daga cikin motarsu sa’anan su anty hawwa…acan cikin motarsu mejo kuwa picture ɗin da megirma shugaban kasar Niger yaturowa general Faruk ne suke kallah awaya, cikin mama mejo yace “kai my wife itace yake nema koyaya? Dukkansu kallonshi sukayi, general Aliyu yace kamarya matarka wannan yarinyar ce Maryam? “Humm kawai yace tare da buɗe motar yafice sabida kiranda Abba yayi Mishi….duk wanda ke wurin da kallo yabi zaratan samarin su duka ukku domin kuwannensu babu makusa musamman mejo daya wani haɗe rai amma kasan zuciyarshi na ƙara jadda Mishi cewar matarshi ce acikin wannan picture ɗin.Ƴammatan ne suka buɗe motar suka fito ummi ce agaba se mufeedah daga karshe isseta tafito. Gata tayi wani irin kyau da haske tayi ƙiba ɓulɓul da ita. “Isseta cewar yaya shamsu daƙarfin gaske hakan yasa duk wanda ke wurin hankalinshi yakoma kanta..shiko mejo yaya shamsu yake kallah. “Ikon Allah Maryama ce Alhaji aina kuka sameta wanda ke makaranta cewar megari….murmushi kawai Alhaji Abubakar yayi yana zama awurin da aka tanadar musu, dukkansu kowa zama yayi hadda su isseta..aka shiga gaishe gaishe..Da mugun gudu yah balah yashigo gidan yana faman kiran Abba Abba wlh ga isseta nan angani gatacan sunzo itada wasu mutane a faɗar megari…ai tunkamin yaƙarasa mlm Musa ya fito daga ɗakinshi Karaye kamar wanda aka koro yayi wani biji’biji dashi abun tausayi..hakama mama bintu tafito mayafinta ahannu tanufi faɗar megari batama jira umurnin megidan nataba, shima ɗin dai ahakan yafita. Ganin duk dunficene yasa mama salmu ɗibar mayafinta tabisu, ai cikin sauri mamansu ya balah da iyya hassi suma suka mara musu baya kar ayi basu..Acan Kofar gidan megari kuwa bayan duk angama gaishe gaishe aka nutsu..anan Alhaji Abubakar yace “baba maganace me mahimmanci takawomu kamar yadda mukayi alƙawari awaccan ranar nacewar idan ɗayar tadawo zamu saka yaronmu yasaki ɗayar tunda bazeyu yazauna dasu dukaba. “Haka ne Alhaji tabbas hakan akayi, cewar megari. “Masha allah to yanzu dai gamu dasu dukkansu agabanmu ga yaron da’aka aurawa sunan yafaɗa yana nuna mejo. Kana yace gakuma yaran dukkansu sabida hakan zeɗauki ɗaya wadda zezauna da ita seya sawwa ƙewa ɗayar Allah yabata wani ta aura. “Nisawa megari yayi kana yace ikon Allah wannan gaskiya ne Alhaji amma senaganku duka hadda Maryama dama da ita aka kai awancan ranar?? “A’a bada ita aka kaiba mukanmu acan muka sameta itada yaron shiyasa muka yanke shawarar zuwanan dukkanmu inda aka fara anan yadace aƙarasa. “Wannan gaskiya ne Alhaji Bara natura Akira mahaifin nasu ayi komai agabanshi inaga zefi ko? “Eh wannan gaskiya ne kam..megari yadubi sarkin faɗa yace aje gidan mlm Musa akirashi yazonan. ‘aigama yanan ƙarasowa ranka yadaɗe cewar Sarkin fada dayatsinkayo mlm Musa takalmi ahannu yana doso wurin kamar wani zararre…kafin megari yayi magana mama bintu taƙaraso wurin domin itace agaba. Sam idonta yarufe bata ganin kowa awurin se Yar Tata, tana hangota tace “Maryamaa Maryama kece dagaske? Allmdllah Allah Maryama kindawo gareni tafaɗa tare da sakin kukan da kecinta..azabure isseta tamiƙe tana faɗar”mama nicee wlh sekuma tasaki ƙasa sabida zaburar datayi daƙarfin gaske ta tako ta fama ɗinkin dake jikinta. Dukkansu bawanda yaga tashin mejo kawai ganinshi sukayi rungume da ita yana faɗar “sorry my maryam kibi hankali mana sannu. Yariƙeta sosai amma tana miƙawa mama bintu hannu…hakan yasa ya kalli mama bintu a marairaice yace”please kizonan bazata iya tafiyaba batada lafiya yayi maganar kamar zeyi kuka. Cikin sauri akashiga bawa mama bintu hanya harta zo gun Isseta aiko suka rungume juna suna sakin marayan kuka atare wanda daga ganinshi kasan daga ƙasan zukatansu yake zuwa. Sunɗauki tsawon lokaci ahakan kafin mama bintu tasaki isseta cikin kuka tace “Maryama miyasa zakimun hakan? Miyasa baki gayamin abinda yafaruba awancan ranar? Maryama ba inda bannemekiba aranar bangankiba ina kikaje acikin duhun dare Maryama? Itama isseta kukan takeyi sosai kafin tace “dan Allah kiyi haƙuri mama a wannan lokacin zuciyana tarigada tarufe bana ganin kowa se maah wurinta naje nazauna da ita acikin daren kafin dasafe kuma tabawa yah najeeb ni mukaje gidanshi acan nake rayuwa haryanzu mama kuma ina cikin aminci da ƙoshin lafiya abisa kularshi….Kuka mama bintu taƙara sakawa tama kasa magana, ahakan mlm Musa ya isa garesu domin tun ɗazu shima yana wurin kuma duka matan gidan suna nan tsaye…cikin karayar zuciya yace “Maryama…!

Back to top button