Hausa novels

Halysaah Page 7 By Khaleesat Haydar

Kwanan Khaleesat hudu yau a garin kano, kuma har a sannan babu wanda yasan da zuwanta a cikin yan gidansu, ko nan da can bata fita a gidan Baaba Gaje don ma kar tsautsayi ya sa ta hadu da daya daga cikin yan gidan nasu, a kwanaki hudun nan sau biyu Ummanta da Aunty Farida suka zo gidan Baaba Gaje dominta, zuwa sannan Umma ta warware gaba daya tafiyarta ya dawo normal, tun kwanaki biyu da suka wuce ta gama amsan treatment dinta a hospital sai magunguna da take sha kawai, har zuwa ranan kuma Abdul bai kira Khaleesat ba, ita kuwa kawai taji ko a jikinta da ya kira da kar ya kira, there wasn’t an atom of disturbance a tattare da ita, ko ta WhatsApp bata yi gigin yi masa magana ba Unlike before da bazata iya hakuri ba sai ta masa, tana bakin murhu tana dafa shinkafa da wake ga turmi gabanta tana ɗaka yajin da za ayi amfani da shi wajen cin shinkafa da waken, Su Ummanta da Baaba Gaje kuma na can uwar ɗaka, tunanin yanda zata fara shirye shiryen komawa USA take don suna da wani presentation nan da kwana uku, daxu da safe ta duba available flight da farashinsu online and she is hoping in ta canza dollars din da Housemate dinta ya bata zai isheta ta koma, Khaleesat ta bar daƙan yajin da take yi bayan taji Aunty Farida na kwalo mata kira, mikewa tayi ta wuce dakin tana amsawa, tun da ta zo gidan Baaba Gaje ta sakar mata aikin komai, hatta jikokinta ita ke masu wanka kan su tafi makaranta, ita taga kamar har ta ɗan yi duhu tsabar girki cikin rana da take yi tun zuwanta, Aunty Farida tace “Ana kiran wayarki” nan da nan mood din Khaleesat ya canza ta karasa gun wayar without much interest, duk tunaninta Abdul ne cause she isn’t expecting any call from anybody, Number mutumin da ya tarbeta a Airport din Lagos ta gani a gaban Screen din wayarta, ta dinga kallon number bata ko kiftawa, duk da bata yi saving ba amma ta gane nasa ne, daukar wayar tayi ta fita daga dakin ta koma bakin murhun sannan tayi picking ta kai kunne, sallama yayi ya gaisheta da ladabi, tace “Ina yini?” Yace “Alhamdulillahi Hajiya, ya jama’ar gidan?” Tace “Alhamdulillah” Yace “To maa sha Allah, dama na bugo ne inji ko zaki kara kwanaki nawa nan gaba kan ki koma America?” Khaleesat tayi shiru trying to understand why he is asking her that, yace “Hello?” Tace “Ina jin ka, ban gane tambayar bane” Calmly yace “Aa so nake in san ranan da zaki koma ne Hajiya, in ya kama ayi rescheduling din ticket dinki sai ayi hakan in sha Allah” Khaleesat was speechless, a ranta tace Ticket kuma? Kasa cewa komai tayi with surprise, taji ta ma kasa ci gaba da tsayuwa, jin ya sake cewa “Hello” ta kifta ido da kyar ta duka kusa da turmin da take daka yaji tace “Ina ji” Yace “Ina ga a bari duk sanda kika shirya zaki nemeni ta waya ko Hajiya?” Sauke idonta tayi kasa, lokaci daya jikinta yayi sanyi sosai, cikin sanyayyen murya tace “Ranan Lahadi nake son zan koma idan Allah ya yarda” Yace “To Maa sha Allah, dama booking din ranan aka maki da zaki taho, flight din karfe daya ne, za ku tashi ta Airport din Abuja in sha Allah” Ita dai Khaleesat ta kasa cewa komai, yace “Sai kin ji ni in sha Allah Hajiya” A hankali Khaleesat tace “Nagode” Khaleesat na zaune dakin Baaba Gaje tana jujjuya shinkafa da waken dake gabanta da cokali, gaba daya ta kasa cin abincin, ita kanta ta rasa dalili, ko tsabar yanda jikinta yayi sanyi ne tun bayan da suka yi waya da mutumin daxu da ya sanar mata da ticket dinta na komawa America sannan tana gama aikin da take ta bude WhatsApp taga ya aiko mata da Flight Ticket dinta which was also business Class kamar dai yanda ta zo, this made her so weak, gaba daya ta ma rasa gane feeling din dake ranta a lokacin, bata taba tunanin Housemate din nata zai mata ticket din komawa ba, Duk Ummanta na lura da sauyawanta lkci guda, Aunty Farida ta gama shafa powder din da take zata leka gidan wata kawarta Maman Fu’ad a nan hotoron, ta dau jakarta da mayafi tana kallon yayarta tace “To sai na dawo Umma” Umma tace “Amma kar ki dade don Allah Farida” Aunty Farida tace “Haba ai yamma tayi bazan zauna ba Umma” Daga haka ta fita daga dakin tayi ma Baaba Gaje dake waje tare da bakuwarta sallama sannan ta fita daga gidan, Umma ta daga kai tana kallon Khaleesat tace “Menene kika saka abinci a gaba kika kasa ci Khaleesat?” Khaleesat ta daga kai da sauri tana kallon kyakkyawan fuskar Ummanta, babu wanda zai ce Umma ce ta haifeta sai dai ma yayi tunanin yayarta ce don kama suke ba na wasa ba kamar an tsaga ƙara, Khaleesat tayi murmushin yake ta kai shinkafa da waken baki tace “Babu komai fa Umma” Umma tace “Yaushe za ki koma? Kuma yaya za ayi da batun kudin jirgi? Har yanzu Abdul din bai san kina nan ba?” Khaleesat ta girgiza kai tace “Umma ai nace baya nan kuma ba a samunsa ta waya, ranan lahadi zan koma in sha Allah” Umma tace “Ranan Lahadi? To ina za ki samu kudin komawa?” Khaleesat ta gyara zamanta tace “Makocin nawa ai tare ya biya min na zuwa da dawowa” Kallonta Umma ta dinga yi da alamar tuhuma ga mamaki kwance fuskarta, Khaleesat taki yarda ta bari su hada ido sai tura abincin gabanta take, Umma tace “Khaleesah” Da kyar Khaleesat ta daga kai gabanta na faduwa, Umma tace “Meye tsakaninki da wannan mutumi da ya biya maki kudin jirgin zuwa har da na komawa?” Khaleesat ta hadiye sauran shinkafar da ya makale a throat dinta da kyar tace “Wallahi Umma babu komai, makocina ne kawai shi, kuma don yaga yanda na daga hankali baki da lafiya shi ne yasa yayi hakan, ni kaina sai bayan da ya biya min na sani, amma ki yarda dani Umma babu komai tsakanina da shi” Kamar zata yi kuka ta kare maganar, Ummanta ta sauke ajiyar zuciya tayi shiru, bayan some seconds tace “Toh shikenan, amma dai kinsan in Abdul ya samu labarin nan da matsala ko?” Khaleesat ta sunkuyar da kanta bata sake cewa komai ba, jin Umma tayi shiru alamar ta fada duniyar tunani Khaleesat ta daga kai a hankali tace “To ai Umma babu wanda yasan na zo kano har yanzu, don haka bazai sani ba” Umma ta sauke wani ajiyar zuciyar tace “To gudun kada hakan ya sake faruwa kar ki sake yarda ko wata mu’amula ta hadaki da shi makocin naki Khaleesat, ki rufa mana asiri” Khaleesat bata ce komai ba sai kuma ta jawo handbag dinta ta ciro dala dubu dayan da Housemate dinta ya bata ta nuna ma Umma cikin sanyin murya tace “Wannan ma shi ya bani da zan taho” Umma ta dinga kallon kudin duk da bata san ko nawa bane ta dai ce “Ki kula don Allah Khaleesat kar ki ja mana magana kin dai san wanene Abdul kin san kuma waye Babanki” Khaleesat dai tayi shiru, tasan Umma bata san har nawa bane Dollars din in an canza zuwa Naira, ita dai tayi shiru bata gaya mata ba kar ta kara daga mata hankali. Washegari da wuri Khaleesat ta shirya ta saka Nikab dinta ta fita don zata je canza dollar din nata ta dan yi siyayya, bayan ta canza dalolin taga har ya wuce yanda take tunani a Naira, nan ta fara zuwa inda zata siyi waya, ta siya ma Ummanta da Aunty Farida sabbin wayar Android iri daya na dubu dari da hamsin each, Ganin Baaba Gaje ma bata da waya kuma ba iya amfani da Android zata yi ba ta siya mata karamar waya na dubu ashirin, daga nan ta karasa kasuwa tayi siyayyar yan abubuwan da zata koma USA da shi, ta siya ma siblings dinta twins mata sabbin school bag da schl shoe da socks, ta siya masu atamfofi kala uku each da mayafai da takalma masu kyau da inner wears, jikokin Baaba Gaje ma ta siya masu takalma da inner wears gaba dayansu, pharmacy ta shiga da takardan da aka rubuta magungunan Ummanta ta siya mata na wata biyu duk da tsadar magungunan, kusan Azahar ta koma gidan Baaba Gaje ta tarar su Ummanta basu zo ba. Washegari asabar Khaleesat na shanya kayan jikokin Baaba Gaje da ta wanke, Baaba Gaje kuma na shirin fita kasuwa Ummanta suka shigo gidan tare da Aunty Farida da Siblings dinta yan biyu Islam da Noor that are just 11 years old, da gudu suka tafi suka rungumeta suna mata oyoyo, sosai kannin nata ke kama da ita, Khaleesat was so happy seeing her twins Siblings wanda su uku kawai Ummansu ta haifa, Baaba Gaje tace “Basu tafi islamiyya bane?” Umma tayi kasa da murya tana kallon Gaje tace “Sun ma kwana biyu rabonsu da zuwa, ba a biya kudin wata ba” Baaba Gaje tace “Ikon Allah to Alin ca yayi bazai biya ba kenan?” Umma tace “Cewa yayi in dora masu talla kamar yanda yan uwansu ke yi tunda su ba ‘ya yan Gwal bane, dama ba fa shi ke biya masu ba wannan karan ne bani da kudi duk jarin ya lalace shine nace su tambayesa” Baaba Gaje tace “To Allah ya kyauta, amma Ali dai haƙƙin ‘ya ya da kyar ya bari ya jiyo kamshin aljanna balle yaje kusa da ita” Ita dai Khaleesat a sanyaye ta kama hannun kannin nata zuwa dakin Baaba Gaje, tana jin Baaba Gaje na cewa “Amma de suna zuwa bokon?” Umma ta sauke ajiyar zuciya tace “Ina fa, islamiyya ma da ya zama dole ba aje ba sae wani boko” Aunty Farida ta girgiza kai cike da takaici tace “Allah de ya kyauta, shi fa bakin cikin bata dora ma yaran talla kamar yanda sauran matansa ke dora ma nasu ‘ya yan talla ba yake” Sosai jikin Khaleesat yayi sanyi don duk sanda ta tambayi Ummanta ko kannen nata na zuwa boko da Islamiyya ta wayar Sha’awa sai tace mata eh suna zuwa, ashe basa zuwa, Umma dai bata ce komai ba suka shiga dakin gaba daya, Baaba Gaje tace “Kun ga bari inje kasuwa in dawo” Su Umma suka mata Allah ya kiyaye ta figi gyalenta ta fita daga gidan, Khaleesat ta fiddo duk siyayyan da tayi jiya, daga Ummanta har Aunty Farida kallonta suka tsaya yi, Aunty Farida ta rike haɓa tace “Haka kudin suke da yawa da kika canza? Kuma wa ya aike ki kashe kudi haka mu da muke da sabga a gabanmu Khaleesat? Maimakon ki bada a ajiye maki ko kujeru da setin gado ne da kudaden? Kin de san ko tsintsiya mahaifinki ba lallai ya siya maki da sunan a kai ki dakinki da shi ba ko?” Khaleesat tayi murmushin karfin hali bata ce komai ba, Umma dai ta ma rasa abun cewa, Aunty Farida tace “Ni da kin yi shawara da ni duk baza ki yi wannan siyayyan ba, iyaka ki siyi abinda zaki koma can Amurka da shi, in suka tado da maganar aure me garemu da za a kai ki da shi Khaleesah?” Khaleesat na murmushi tace “Allah zai rufa asiri zuwa sannan Aunty” Aunty Farida tace “Yanzu duk kudin sun kare kenan?” Khaleesat ta girgiza kai tace “Aa, saura dubu dari biyar” Daga Aunty Farida har Umma bude ido suka yi sosai suna kallonta with shock, Aunty Farida ta gyara zama tana zaro ido tace “Har nawa ya baki haka? Ko dai baki da hankali ne” Khaleesat ta kauda zancen ta hanyar cewa “Har fa da kudadena duk na canxa” handbag dinta ta jawo ta bude ta ciro sauran kudaden da suka rage don har wanda Safiyyah ta bata ta canza, ta kirga dubu dari a ciki ta ware, sannan ta kirga dubu dari da hamsin shi ma ta ware, kallonta kawai Umma da Aunty Farida suke, ta ba Aunty Farida dubu dari tace “Aunty kiyi kudin mota da wannan idan zaki koma Lagos sannan ki kara jari” Ta ajiye ma Umma 150k tace “Umma ki rike wannan a biya kudin makarantar su islam da Noor a kuma canza masu Uniform” Umma tace “Ko dai baki da hankali ne Khaleesah? baki ji shawaran da Farida ta kawo bane halan?” Aunty Farida ta mayar mata da 100k din tace “Aa gaskiya ban ga alamar da kan nan ba Umma, ina ga hakoranmu za mu je mu jera mata a gida idan bikin ya tashi….” Khaleesat bata san sanda tayi dariya ba tace “Akwai fa kudade a account dina wanda Abdul ke bani kuma suna da yawa za su isa ayi duk abinda za ayi sannan Aunty” It took Khaleesat almost an eternity to convince her Mother and aunt akan su rike kudin da ta basu, nan kuma bata da wani kudin a zo a gani a account dinta sai miliyan 10 na Abdul da ya ajiye a account din wanda nashi ne ba nata ba, iya kudin foodstuff kawai yake tura mata duk karshen wata sai kuma kudin Uber na zuwa makaranta, sai house rent dinta da yake biya at due time, iya abinda kawai yake mata kenan amma naira biyar dinsa baya bata a matsayin kyauta, instead sai dai ya siya mata kaya masu tsada, monthly kuma yake mata subscription a waya, apart from this bai bata kudi da sunan kudin kashewa, a haka dai ta samu tayi convincing Umma da Aunty Farida suka amshi kudin da ta basu, Aunty Farida na kallon Umma tace “To kinga sai kiyi kaffa kaffa da wayar nan kar su sace maki tunda sun saba maki haka, kin dai ga ba dan karamin kudi aka siyo wayar da shi ba” Umma na kallon Khaleesat tace “To shi Malam din me kika siya masa?” Aunty Farida ta wani kalli yayarta, Khaleesat ma dai kallon Ummanta tayi bata ce komai ba, Aunty Farida ta kyabe baki ta kauda kai, Umma ta kalli Aunty Farida tace “Wai saboda hakki, naga ta siya min waya shima da sai ta nemi abinda ta siya masa kwatankwacin wayar, kuma bashi da wayar shi ma wallahi” Aunty Farida na kallon yayarta da kyau tace “Umma in kinsan zuwa za kiyi ki kyautar da wayar nan da ta siya maki to gwara dai ki bar mata kayanta, ina ce kwanaki can matansa ya siya ma Atamfa yar gadagalle lkcn bikin Salisu ke ya siya maki?” Umma tace “Aa ba ruwanta da wannan Farida, ai ubanta ne, kuma don ta siyi abu ta basa ai ba faduwa tayi ba” Aunty Farida bata sake tanka Umma ba ta fara harhada ma Khaleesat kayayyakin abinci da ta siyo waje daya, Sai kusan la’asar su Umma suka bar gidan kuma har sannan Baaba Gaje bata dawo ba, a boye Khaleesat ta ba Siblings dinta 50k wanda ta saka a karamin jakar Islam tace masu in sun je gida su ba Umma kuma ta ja masu kunni sosai kan daukan sabon wayar da ta siya ma Umma kar su lalata mata. Washegari da safe Khaleesat ta fito wanka wayarta ya fara ring tana dauka taga mutumin nan ne dai, bayan ta daga suka gaisa sannan yace “Hajiya nan da karfe tara da rabi wani driver zai kiraki sai kiyi masa kwatancen inda zai zo ya daukeki ya kai ki airport, don flight dinki zuwa Abuja na karfe sha daya ne, in kun iso Abuja kuma jirgin da zaki bi zuwa Amurka jirgin karfe biyu saura ne” Khaleesat tace “To ba damuwa Nagode” Aunty Farida kadai ce ta zo gidan Baaba Gaje yi ma Khaleesat sallama, Khaleesat bata ji dadin da Umma bata biyo ta ba, duk jikinta yayi sanyi sosai, a haka drivern da zai kai ta airport ya iso, Baaba Gaje ta dinga sa mata albarkan wayar da ta siya mata da abubuwan da ta siyo ma jikokinta, bayan an kai akwatin kayanta cikin mota su Aunty Farida da Baaba Gaje suka rakata har bakin motar, bayan Khaleesat ta shiga motar ta daga masu hannu a sanyaye tana murmushin karfin hali, har cikin ranta bata ji dadin da bata yi sallama da Ummanta ba, a haka suka kama hanyar airport da drivern da ya zo daukarta, suna sauka Abuja karfe daya da minti 40 jirgin su ya tashi. The flight to the United state was so comfortable for Khaleesat in her business class seat, don throughout bacci tayi, karfe hudu saura na asuba jirginsu ya sauka Maryland, It was soo cold in Maryland gashi bata da sweater a kayanta, bayan ta fito da luggages dinta tana duba Uber da zai kai ta gida tana rike da wayar kamar ance ta daga kai taga motar da yayi parking, kallo daya tayi masa sai kuma ta sauke kai kasa, ya karaso har inda take yace “Jirgin ya dade da sauka ne?” Sai a sannan ta kara kallon Sleepy face dinsa, sai kuma ta girgiza kai tace “Aa” Yace “Ohk let me drop you home” Daga haka ya koma gun motarsa ta bi bayansa with both of her luggages, ya bude booth ya amshi daya trolley dinta ya sa a booth, ita ma ta sa dayan, ya zaga ya shiga driver seat, tana jan kafa ta karasa front seat ta bude motar sannan ta shiga tana kallonsa da gefen ido, jinginar da kansa taga yayi da kujeran motar idonsa a lumshe, ta kulle motar gently, after few seconds ta sake kallonsa ga mamakinta sai taga kamar fa bacci yake, kallonsa ta dinga yi, and they seated for almost 3 minutes a haka ita dai bata tashesa ba kuma bata ce komai ba, Vibration din wayarta ne ya sa ya bude ido, ya wara ido ya fara kokarin tada motar, bude jakarta tayi to stop the alarm din da ya sa wayarta ke vibrate, bayan ya ja motar sun bar wajen, still not sounding normal yace “Ya jikin Mama?” Ta sauke idonta tace “Alhamdulillah, You shouldn’t have bothered coming tunda akwai Lyft ko Uber” Without looking at her yace “The house key is with me, shi yasa na taho, cause i estimated when u are arriving” Bata sake ce masa komai ba shi ma haka, a haka har suka iso gida yayi parking, ya sake jinginar da kansa da kujeran motar, ita dai ta bude motar gently ta fita, jin fitarta ya sa ya bude ido, shi ma ya sauka daga motar, Entrance din shiga gidan ya nufa ta bi bayansa, Pajamas ne jikinsa sai Jacket da ya saka saboda sanyi, yana isa kofar ya kai hannu aljihu alamar zai ciro makulli, still taga yayi a bakin kofar, ita dai kallonsa kawai take, after some seconds ya juya yana kallonta, zuwa sannan his eyes are very clear gaba daya baccin ya gudu jin babu makulli jikinsa, ko bai gaya mata ba ta fahimci baya tare da makullin gidan, ya ɗan sosa kai yace “I think…. I think, i left the key at where i am coming from, i am sorry about that Halysaah” Sauke idonta tayi without saying anything, ya juya ya nufi motarsa ta bi sa da kallo, sai da ya isa gun motar ya juyo, da sauri ta dauke kanta daga kallonsa, yace “Mu je in dauko makullin, ba wani nisa zuwa can, kinga it’s cold out here baza ki iya tsayawa cikin sanyi ki jirani in dawo ba” Bata yi musu ba ta koma gun motar don yanzun ma sanyin take ji sosai, sai da ya shiga sannan ita ma ta shiga, his car was so warm, ya tada motar suka bar garage din, inda yace mata babu wani nisa taga sunyi tafiyar kusan 15 mins basu kai ba, nan taji gabanta ya fara faduwa, lkci lkci take ɗan satan kallonsa ta gefen ido, wani unguwa suka shigo wanda ko wani gida da gate dinsa unlike some houses in US, daga karshe taga yayi parking ba tare da ya kashe motar ba yace “Let me get the keys” Bude motar yayi ya sauka ta bi sa da kallo taga gate din kusa da su ya bude ya shiga, tsaf take iya kallon hadadden gidan dake ta cikin gate din don ba irin gate dinmu na gida bane, ita dai sai bin unguwan take da kallo wanda ko ba a fada maka ba kasan na masu hannu da shuni ne a Amurka din, ba a wani dau lokaci ba sai gashi ya fito da wani Huge Dog dake biye da shi yana shisshige masa, wani faduwa gabanta yayi don a duniya tana mugun tsoron kare, ya duka yana patting Dog din yana masa magana at the same time, wani matashi ne dogo just like him ya fito daga cikin gate din gidan sanye da Pajamas shi ma, Khaleesat ta dinga kallonsa as if ta taɓa saninsa amma kuma bata san sa from anywhere ba, tana kallonsa tana gyara mayafin kanta kar ma ya kalli direction dinta su hada ido da shi, gabanta kuwa sai faduwa yake kamar mara gaskiya, matashin ya jingina da gate crossing his both legs yana kallon Housemate dinta taji yace “Daga ina kake?” Ƙin basa amsa Housemate din nata yayi instead ya mike yana tura masa ƙaton karen don karen tsaf zai ce zai bi sa, Calmly matashin yace “Ina za ka?” Housemate dinta ya kallesa yace “You have any issue with that?” Matashin ya ɗan kalli motarsa calmly yace “Is that a lady in ur Car?” Housemate dinta yayi kamar bai ji sa ba still pushing the Dog to him, Matashin ya sake kallon motar, Khaleesat tayi saurin kauda kanta, tabe baki yayi yace “Enjoy” Daga haka ya ja karen suka koma cikin gidan, Khaleesat da duk taji conversation din nasu taji ranta ya baci, House mate dinta ya dawo cikin motarsa ya kulle without looking at her yace “Sorry for keeping u waiting Halysaah” Yana fara driving ta hade rai tace “Mene yasa bazaka gaya masa i am just ur housemate ba da kuma dalilin da yasa ka kawo ni nan din?” Housemate dinta yace “Never mind, ba wai yana da hankali bane”07087865788✍🏻

Back to top button