Ruwan Zuma Page 30 Hausa Novel
(30) Wunin ranar Haydar bai je ko’ina ba yana tare da Laila wacce take harkokinta cikin sanyin jiki babu walwala. Bai matsa mata dole sai ta washe fuskarta ba domin yasan tana cikin damuwa sosai wanda barkwancinsa ba zai fito da ita daga ciki ba. Sai dai yana iya bakin k’okarinsa wajen ya kwantar mata da hankali don ta rage damuwa. Har yamma suna zaune a gida babu labarin Abul, sau biyu Mas’ud na zuwa yana fad’a musu halin da ake ciki na cigiyar Abul wanda duk magana d’aya yake kawowa wato ‘babu wanda yasan inda ya shiga.�? Bayan la’asar Mas’ud ya dawo gidan Laila ya sameta tare da k’awayenta Hajiya Maryam da Hajiya Shatu wanda Haydar ya kirasu don su tayashi bata baki. Bayan ya gaishesu ya maida dubansa kan Laila wacce ke waya da Sabrin, “Ban ga amfanin zuwan naki ba Sabrin, ko kin zo ba samunshi za’ayi ba. Kiyi zamanki a gidanki, kin ji?�? Haydar da a lokacin yake fitowa daga d’aki yayi shirin fita yace, “Ki barta tazo Laila, tana buk’atar kasancewa dake a wannan lokacin.�? “Shikenan ki zo.�? A nan Mas’ud ya nemi Haydar ya fito su tafi wanda dama zuwa yayi ya d’aukesa. Sallama suka musu suka fita Laila ta biyo bayan Haydar zuwa bakin k’ofar falon. Kallon fuskarta kad’ai da yayi ya gane cewa she’s grateful daya kira su Hajiya Maryam. “Yaushe zaka dawo?�? “Sai nine ko nine thirty.�? “Ina zaka je haka?�? Hannunshi ya d’aura a kan kumatunta yace, “Take care.�? Ya shiga motar Mas’ud suka tafi. Jikinta a sa6ule ta koma ciki gurin su Hajiya Shatu suka cigaba da kwantar mata da hankali tana sauraransu har Sabrin ta zo. Daga gidan Laila su Haydar suka wuce gidan Madu inda zasu yi magana da Ummii. Kai tsaye sashenta suka nufa. Mas’ud ne ya shige d’akinta don yayi kiranta Haydar kuma ya samu guri a k’asa ya zauna yana jiran fitowarsu. Basu jima ba suka fito tare Ummii na masa barka da zuwa. Bayan ta zauna ya gaisheta, sai a lokacin Mas’ud ya bata labarin halin da ake ciki wanda aka k’i fad’a mata tun jiya. “Ina jira ne inga waye mai hankali a cikinku da zai fad’a mini abunda yake faruwa.�? “Mun d’auka zamu sameshi ne tun a jiyan shiyasa bamu fad’a miki ba Ummii.�? Mas’ud ya bata hak’uri. “Tun a jiyan Madu ya fad’a mini. Allah ya tsareshi ya kuma sa ya bayyana cikin aminci.�? “Ameen.�? Suka amsa duka. “Dama ina son zan kira Khalii Abdi ne kan maganar Abul sai kuma na fasa domin kinsan yanzu sai ya d’aura laifin a kan Laila ba tare da ya saurari me yake tafe dani ba. Shine nake son ki kirashi ki fad’a mishi halin da ake ciki ko akwai abunda za’a yi.�? K’arfe tara da wasu mintuna Mas’ud ya ajiye Haydar a gida ya shiga ciki. A kwance a d’aki ya samu Laila amma bata yi bacci ba, sannu da zuwa ta mishi ba tare data tashi ba. “Kinci abinci?�? Ya tambayeta yana zama a gefenta. “Bana jin yunwa.�? Bai ce komai ba ya tashi ya fita falo ya d’ebo abinci sannan ya dawo ya k’ara zama a gefenta yana cewa, “Tashi kici abinci.�? Matsa mata yi dole taci sannan ya koma falo ya barta a d’aki domin ta fad’a masa bacci take ji. Wannan karon shi d’inne ya kasa cin abincin domin ya rasa appetite d’insa baya marmarin komai. Zama yayi yana tunanin hanyar da zai bi a ga Abul hankalin Laila ya kwanta, domin idan tana cikin damuwa shima ba zai ta6a yin walwala ba. Bayan kwana biyu da haka Laila tayi wankan sallah Haydar ya nuna kamar bai gani ba ya cigaba da sha’anin gabanshi. Sannan har a lokacin ba’a ji labarin inda Abul yake ba. A daren ranar bayan sun kwanta Laila ta kira sunanshi, “Haydar.�? “Na’am.�? “Nayi wanka.�? “Na gani.�? Ya k’ara jawo bargo ya lullu6a. Daga nan suka yi shiru har bacci ya fara d’ibanshi ta tashi ta zauna, a fusace tace, “Baka ji mena fad’a maka bane?�? Juyowa yayi a kasalance yace, “Laila naji mana, kuma na baki amsa.�? “So?�? “So? Ban gane me kike so in fad’a ba bayan nan.�? Komawa tayi ta kwanta shima ya k’ara juyawa wannan karon har yana gyara pillow yace, “Sai da safe.�? Bata ce komai ba har yayi bacci tana jin minsharinshi yana fita a hankali. Tashi tayi ta zauna ta dafe kanta da hannunta biyu tana jin zuciyarta na zafi domin har yau tunanin Abul na ranta. Ita ta haifeshi, ta raineshi ta bashi tarbiyya daidai iyawarta sannan ta bishi da addu’ar Allah ya shirya mata shi, amma lokaci d’aya, cikin k’ank’anin lokaci al’amura sun canja wanda har halayyar Abul ma ya canja. Ina yake? A wani hali yake? Hannun wa yake? Me ya sameshi ko me zai sameshi? Duk bata sani ba. Sannan zuciyarta na kawo mata images kala iri daban-daban wanda take hasko mata Abul a cikin yanayin maye yana fad’a da mutane wanda watak’ila su masa illa ko su kasheshi gaband’aya. Tana cikin tashin hankalin da babu mai iya gane yanda take ji sai wanda hakan ya faru dashi. Hawaye ne ya sauk’o kan kumatunta tana tausayin rayuwarta da kuma ta Haydar wanda a yanzu yafi kusanci da ita a kan kowa. Ta san ba k’aramin hak’uri yake yi da ita ba, kuma tana ganin k’ok’arinsa da dattakunshi. “Haydar.�? Ta kira sunanshi wanda hakan yasa ya farka ya fara lalu6arta cikin duhu. “Meya sameki Laila? Bakya jin dad’i ne?�? Kuka ne ya ku6uce mata don Haydar is too good for someone like her, meyasa ya kasance mara son kai? Meyasa yake da hak’uri kuma yake son mace irinta? “Why me?�? Ta tambayeshi a lokacin da yake tashi zaune ya kunna bedside lamp kana ya ganta a zaune babu alamar rashin lafiya a tattare da ita. “Kin tsoritani, I thought baki da lafiya ne.�? Ya matsa gurinta yana jawota jikinshi ta dakatar dashi. “Why me?�? Daburcewa yayi domin bai gane inda maganarta ta dosa ba. “Ban gane ba Laila.�? “Meyasa ka za6eni a matsayin wacce kake so ka kuma yarda ka aureni bayan duk red flags d’in da ka gani kafin hakan?�? “Saboda hakan ne zai kasance.�? “This is not enough.�? Ta share hawayenta tana kallonshi ido cikin ido. “Because I love you Laila, damn it woman. Me kike so nace? In fad’a miki cewa ke nake so nake kuma burin samu kuma Allah ya kar6i addu’ata ya bani ke ko yaya? Ko kuma so kike in fad’a miki ke cewa ke kad’ai nake da burin yin rayuwa har abada kuma I don’t give a fuck wace rayuwa kike ciki ko kike fuskanta ba?�? Wuyanta ya rik’o ta baya ya tashi ya d’aura guiwoyinsa a kan gadon ya sassauta muryarshi yace, “Once I’m in, I’m in for better and for worse. I love the whole you Laila, I know you are not perfect but you are fucking perfect to me, ina son kayana a haka. Kuma I’m not going anywhere ina tare dake har abada till death do us part.�? Bakinsa ya d’aura a nata yayi kissing d’inta na wasu sakanni sannan ya tashi ya sassauta rik’on da yayiwa wuyanta tace, “Why?�? “Because I love the whole package and what comes with it.�? “Haydar…�? “Shssshh.�? Ya d’aura yatsunsa kan lips d’inta wanda suka fara yin ja dalilin kissing d’inta da yayi. “I love you.�? Yace da ita yana had’e goshinsu guri d’aya. “I love you too.�? Itama ta fad’a tana sak’ala hannayenta a wuyashi yayi hugging d’inta yana shafa bayanta. Sun jima a haka sannan suka rabu suka tsaya kallon juna fuskarsu d’auke da murmushi. Sunkuyar da idanunta tayi k’asa tace, “Nayi wanka.�? “Munyi maganan Laila.�? A fusace ta d’ago da kanta har ta manta da abunda ya faru yanzu tace, “Don meyasa ba zaka nemi hak’k’inka?�? “Saboda baki shirya ba, kuma bazan miki dole ba. And I want you to need me ba wai ki bani kanki don sauk’e hak’k’ina dake kanki ba. Kin fahimceni?�? Bata ce komai ba amma ta fahimceshi tsaff, gyad’a kai tayi ta koma ta kwanta shima yabi bayanta yana jawota jikinshi. “Ki samu kiyi bacci kinji? Ki barwa Allah komai shi zai gyara a lokacin da bakya tsammani.�? Hannunshi daya mak’ala a k’ugunta ta d’ago tayi kissing kana ta rungume a k’irjinta. Shima kissing d’in tsakiyar kanta yayi yana murmushi sannan yace, “Good night matar Haydar.�? “Good night Ruwan Zuman Laila.�? Washe gari da safe Haydar ya tafi aiki kamar kullum Laila kuma ta wuce shagonta domin ta fara zuwa bayan mijin nata ya hanata zaman gida. Bai jima da zama a office d’insu ba aka fad’a mishi wai Alhaji Abdul na kiransa. Wannan ne karo na farko da zasu had’u bayan aurensa da Laila. D’an aikan yana fita shima yabi bayanshi fuskarsa a had’e domin baya so ko kad’an wata magana ta k’ara had’ashi da Alhaji Abdul, ya dawo yin aiki k’ark’ashin shi ne domin rashin samun aiki da kuma Ammi da Laila, the most important people in his life da zai iya yin komai domin ganin farin cikinsu. Sai dai yayi alk’awarin da zarar ya fad’a mishi magana wacce bata gamsheshi ba zai bar aikin, in yaso ko gadi zai fara a kantin daya bari. Yana shiga office d’in ya sameshi yana waya ya bashi baya, a gefe ya tsaya yana kallonshi har ya gama sannan ya juyo da murmushi a fuskarsa yace, “Ashe har ka shigo. Ga guri ka zauna.�? Haydar ya zauna fuska ba yabo ba fallasa yace, “Morning sir.�? Wata irin dariya Alhaji Abdul yayi kana yace, “Morning Aliyu Haydar. Sorry bamu baka hutu na aurenka ba saboda abun yazo mana a k’urerren lokaci ne, kuma baka jima da fara aiki damu ba.�? Shiru Haydar yayi yana kallonshi, Alhaji Abdul ya gyara zamanshi kana yaci gaba, “Dama a farkon fara aikinka mun fad’a maka cewa da zarar mun ga yanayin jajircewarka zamu k’ara maka matsayi. Bayan duba da muka yi da k’ok’arinka yasa muka baka matsayin Assistant Manager na wannan company.�? “Bana buk’atan hakan.�? Ya amsa masa flatly kana ya mik’e tsaye zai tafi. “Ban sallameka ba Aliyu Haydar, sannan baka fad’a mini dalilin da yasa baka son k’arin girman ba, wanda nasan mutane da dama jira suke yi su samu wannan damar su kar6a.�? “Ba nine na dace da wannan seat d’in ba saboda ban jima da fara aiki daku da har zaku d’auki babban matsayi irin wannan ku bani ba. Sannan akwai wad’anda suka cancanta wad’anda suka jima suna muku aiki tuk’uru. Zai zama tamkar na shiga gonar da ba tawa bace idan na k’ar6i wannan k’arin girma.�? Shiru Alhaji Abdul yayi yana kallonshi shi kuma yana tsaye yana jiran a sallameshi ya tafi. A ransa kuma haushi yake ji da yana da wani hanyar samun aikin da ya bar wannan. Sannan bai gane manufar Alhaji Abdul ba, menene dalilinsa na k’ara masa matsayi alhali bai cancanci hakan ba? “Ka yarda da cewa ka cancanci hakan. Secretary na da manager zasu nuna maka sabon aikinka, sannan zaka saka hannu a wasu papers da zasu baka. Zaka iya tafiya.�? Fita Haydar yayi ba tare da yace komai ba, sai dai a maimakon yayi hanyar office d’insu sai ya fita daga company d’in baki daya ya hau achaba ya koma gida. “Sir ya fita daga company.�? Secretary Alhaji Abdul ta sanar masa. “Zai dawo. Zai dawo because I’m the one playing the strings now.�? Ko da Haydar ya isa gida bai samu Laila ba kamar yanda yayi tsammani, zama yayi a kan kujera ya dafe kanshi wanda yake jinshi kamar an d’aura masa dutse. Dalili irin wannan yasa tun farko ya nunawa Laila cewa ba zai koma aiki k’ark’ashin Alhaji Abdul ba, saboda yasan he will try to control him, wanda shi kuma ba zai d’auki hakan ba koda wasa. Ya kai minti talatin yana zaune yana tunani yaji an bud’e gate Laila ta shigo da motarta. Bai d’aga kanshi ba har ta shigo ta sameshi, a kusa dashi ta zauna kana ta dafa kafad’arshi tace, “Wai me yake faruwa ne? Kuma ina ta kiran wayarka ka k’i d’auka.�? “Babu komai.�? “To meyasa Alhaji Abdul yayi ta kirana? Sai daga baya yake cewa wai kunyi magana dashi ka tafi cikin fushi. Wace magana kuka yi?�? A fusace ya tashi tsaye yace, “Don meyasa zaki yi magana dashi? Na hanaki d’aukan wayarsa wanda sai da kika gindaya mini sharad’inki na yarda dashi, kuma shine zaki koma kuna waya dashi? Me yake fad’a miki? Meyasa kike d’aukan wayarsa?�? “Haydar….�? “No, karki fara. Kin karya dokata Laila, just doka d’aya dana saka miki kin kasa bi.�? Yana fad’in hakan ya fice daga gidan ya barta hawaye na taruwa a idanunta. Me ta mishi? Meyasa ba zai saurareta ba? Me yake damunshi? Me yake shirin faruwa dasu? Dama zai iya fushi da ita? Fitansa a gida ya rasa ina zai yi, hawa achaba yayi yace ya kaishi kantin su Nasir domin shi kad’ai ne zai iya fad’a masa matsalarsa a yanzu ba Ammi ko Laila da zasu bashi shawaran ya koma bakin aikinsa ba. Bayan ya gaisa dasu yake tambayarsu ina Nasir, “Kut! Bai fad’a maka ya samu aikin gwamnati ba? Ai kwananshi uku rabonshi da nan.�? “Inaga bai samu zama bane. Bari zan masa waya.�? Da haka ya fita yana jin ba dad’i a ransa, meyasa Nasir bai fad’a mishi wannan abun farin cikin ba? A waje yayi ta kiran wayarshi bai d’auka ba, daya gaji ya hak’ura ya k’ara hawa achaba zuwa gidan Ammi. A rumfarta ya sameta tana d’aura ruwan zafi a kan camping gas. “Ali yau baka je aiki bane?�? “Naje, bana jindad’i ne na dawo. Ina kwana.�? Ya gaisheta yana shiga d’akinta. “Lafiya dai kam? Me yake damunka?�? Ta biyoshi tana tambayarshi. “Ammi kaina yake ciwo ina so na kwanta nayi bacci.�? “To, meyasa baka koma gidanka ba?�? Kwanciya yayi a kan gadonta yace, “Laila bata gida kuma bazan ji dad’in zama ni d’aya ba.�? “To Allah ya sauwak’e.�? Da haka ta fita ta barshi shi kuma ya gyara kwanciyarshi ya rufe idanunshi. An fara kiran sallah azahar Ammi ta tasheshi kan lokacin sallah yayi. Duba wayansa da zai yi yaga missed calls d’in Laila dana Nasir da yawa. Nasir ya kira yana fitowa daga d’akin Ammi, “Ina ka shiga haka?�? “Wallahi nayi bacci ne. Kana ina ne?�? “Ina gidanmu.�? “Ina zuwa.�? Ya kashe wayarsa ya dubi Ammi dake alwala yace, “Ammi na tafi. Sai anjima.�? Dakatar da alwalan tayi tace, “Anya kuwa lafiya kalau kuke? Ko dai fad’a kuka yi da Hajiya Lailan? Ali bana son saurin fushi fa, matar nan tana k’ok’arin yi maka biyayya don Allah karku fara samun matsala tun daga yanzu. Zaman aure hak’uri ya gada, dama zo mu zauna zo mu sa6a ne.�? “Ki yarda dani Ammi, ba fad’a muka yi da Laila ba. Sai anjima.�? “To ga abinci nayi da kai.�? “Na k’oshi.�? Yasa kai ya fita. “Allah ya kyauta dai.�? Ta bishi da addu’a. Bai bar unguwan ba sai da yayi sallah kana ya isa gidansu Nasir wanda babu nisa da gidansu akan abun hawa. A d’akinsa dake zauren gidan ya sameshi ya zauna yana fito da wayarsa wacce ke ruri, Sunan Laila ya gani kamar yanda yayi saving number ta da ‘Zuma�?. Kifa wayar yayi akan katifar Nasir yana jin d’aci a ransa idan ya tuno wai har yanzu tana magana da Alhaji Abdul a waya. “Mutumina yaya dai?�? Nasir ya tambayeshi. “Babu komai. Sai naji ka samu aiki, ya aka yi ban samu labari ba?�? “Wallahi a bazata na samun aiki shiyasa tunda na fara zuwa ban samu kaina ba, su ‘yan kantin ma Maigidanmu ne ya fad’a musu da yake shi ya sama mini aikin. Kayi hak’uri, amma dama niyyata yau idan na dawo in je gidanka in fad’a maka.�? “Na tayaka murna sosai da alama kai ma zaka ci fruit d’in boko. Ni kuma aikina zan bari.�? “What? A dalilin me?�? Nasir ya tambayeshi cikin mamaki. “Yau ya bani k’arin girma wanda ban cancanta ba Nasir, sannan har yanzu bai daina kiran matata a waya ba wanda nake jin na tsani hakan har cikin zuciyata. Barin aiki a k’ark’ashinsa shi zai sa ya daina kiranta yana fad’a mata magana a kaina. Idan Maigidanka zan yarda ya mayar dani tunda ka daina.�? “Ai ina barin gurin nace ya bawa Nunu k’anina aikin, kasan zaman banza yake yi gashi yak’i karatu.�? Kafad’un Haydar suka sauka cikin rashin jin dad’in wannan labarin, ina zai sa kanshi? Yaya zai yi? Yasan duk irin neman aikin da zai yi yanzu ba zai samu ba domin yayi a baya kuma ba’a dace ba. “Na tsani mutumin, bana ko son ganin fuskarsa.�? “Bari in baka shawara ko zaka d’auka.�? Nasir ya gyara zamanshi. “Ina jinka.�? “Me zai hana ka kar6i aikinka kaci gaba da zuwa, nan da wani lokaci idan ka tara kud’in da zai isheka yin wani business sai ka ajiye?�? Girgiza kai Haydar yayi bai ce komai ba. Nasir ya dafa kafad’arshi yaci gaba da magana. “Ka dai yi tunani, idan ka bar aikin wa zai ciyar da iyalinka da Ammi? Ina zaka samu wani aikin cikin ‘yan kwanaki kad’an kafin kud’in aljihunka su k’are? Kar zuciya ta d’ebeka ka aikata abunda zaka yi dana sani daga baya. Shawara ce.�? “I hate it da yake iya controlling rayuwata. Zan d’auki shawararka Nasir ba don ina da za6i ba.�? Bayan sun gama magana Nasir ya shiga gidansu ya kawo musu abinci suka ci, suka cigaba da hira wanda yawanci Nasir ne ke fad’a masa yanayin aikinsa. Bai bar gidan ba sai k’arfe takwas na dare, a falo ya samu Laila tayi tagumi tana jiransa domin har ta gaji da kiran wayarsa tunda ba d’auka yake yi ba. “Sannu da dawowa.�? “Yauwa.�? Kawai yace da ita ya shige d’aki ta bishi da kallo. Minti kad’an da haka ta bishi d’aki ta samu ya shiga wanka ta zauna zaman jiranshi. Ko da ya fito bai kulata ba har ya gama shirin bacci ya kwanta, “Ga can abinci akan dinning table.�? “Na k’oshi.�? “A ina kaci abinci?�? Ta tambayeshi cikin 6acin rai. “A wani guri.�? “Don meyasa zaka ci abinci a wani guri alhali kasan zan dafa maka?�? “Don Allah Laila bana son hayaniya.�? Shiru tayi tana kallonshi mamaki a fuskarta ba kad’an ba. Wai ita Haydar yake cewa baya son hayaniya? Hayaniya take mishi daga tambaya? Fita tayi daga d’akin tana jin zafi a zuciyarta, shima zafin yake ji a tasa zuciyarsa amma dole ya nuna mata laifinta. Yana sonta yana kuma mugun kishinta da zai iya yin komai don ganin hakan bai sake faruwa ba.
Mum Fateey 👌



