Hausa novels

Haihuwa Da Hanji Page 20 Hausa Novel

Harara ya sakar mata da sauri ta mayar da idanun ta rufe ruff tsaki ya ja a fili, ya fara ƙoƙarin neman vain ɗinta… ‘Asshh’ ta faɗa a hankali jin ya soka allurar sai ta fara kokarin janye hannun.”Kina janye hannun nan sai na wanka miki mari akwai wanda yace ki yi ta tuna samarin ki kina kuka har ciwo ya kama ki?”Tsit tayi bata kuma motsan ba, kila Rayyan shine ajalinta wa ya sani don tunda ya daka mata tsawar nan ko numfashi mai kyau ba ta iya ja har ya gama ɗaura mata drip ɗin, bata ji fitan shi ba ita kam tun tana pretending har baccin gaske ya ɗauke ta a haka, don dama jiya ba baccin ta samu ba na kirki gashi yau ta yini a kan hanya tana galantoyi.Sashenshi kawai ya miƙa daga nan don ya matuƙar gajiya hutu kawai yake buƙata, wanka yayi ya fito da alwala ya zo ya shirya cikin wani morrocon jallabiya baƙi sidik mai sheki wanda ya fito da ainihin kyaunshi fatarshi ya haska jallabiyar, masallaci kawai ya wuce bai dawo cikin gidan ba sai da yayi isha, time ya kalla ya ɗauke ido ya nufi cikin main parlorn kai tsaye ɗakin da take ya wuce, ta miƙe zaune bayanta jingine da jikin gadon kafafunta na cikin bargo, idanunta sun kara girma sun dan sauya saboda kukan da ta yini yi ga kuma bacci da tayi tayi, hulan kanta ya zame sosai ya bayyana rabin gashinta mai sulbi, tunani take ya zata yi in ruwan ya ƙare sai taji an yi knocking seconds uku zuwa huɗu ya turo kofan ya sanyo kai da sallama wadda iya shi kaɗai ya san yayi kayanshi.Kanta tayi saurin mayarwa kasa Alamu sun nuna bashi da niyyar magana don har ya zo ya cire ruwan da ya ƙare ya bare wani allura ya fasa yayi mata a canular bai ce takk ba itama bata ce ba, kamshinshi duk ya cika ɗakin har ya gama ya juya zai fita ta furta “Na gode”Bai ce komai ba ya fice daga ɗakin, kai tsaye wurin Mammi yayi, tana daga parlor a zaune cikin kujera abinci ne a gabanta wanda ta gama ci yanzu cikin kula sossai da cimar tata ɗin don professional cooker ya samo mata wacce take kulawa da zallar abincinta kuma take da karatu na musamman akan cimar da ake ba wa masu ciwon ƙoda da kan tafi da diabetes, ba’a so ta ci late kuma da ta gama ta sha magani tana so ya ɗan saketa sai taje ta duba Afeefah.Bai yi magana ba kawai ya zo ya zauna gefenta, ta kalleshi tayi murmushi “Gajiya ne a jikinka sossai Saraki, ka ci abinci sai ka je ka huta”Kai ya gyaɗa kawai don bashi da niyyar magana, da intercom tayi amfani ta kira su a kitchen a kan a kawo abincin Saraki, simple abinci ne marar nauyi yake ci da dare suka kawo suka jere a gabanshi, har lokacin yana kishindige kusa da ita idanunshi a lumshe.”Tashi ka ci kar yayi sanyi babana ko in baka?”Ya buɗe ido a hankali ya ɗan yi murmushi kaɗan sai wani sirrin kyaunshi ya bayyana Dukda murmushin bai jima ba sai dai tabbas duk wanda yayi wa irin murmushin zai jima bai manta ba.Itama murmushi tayi don ita kam akwai fara’a masha Allah, abincin ya ɗan ci kaɗan ya kalleta jin tana cewa”Ina zuwa zan duba Afeefah”Da Kai ya amsa ta fice, ta samu Afeefar ta idar da sallolinta tana kokarin cin abincin da aka shigo mata dashi Abeeha na zaune cikin kujera daya daga cikin huɗu dake gefen ɗakin tana danna waya ganin Mammi ya sa ta taso “Afeefah ɗiyata ya jikin?”Murmushi ta saki a kunyace tace “Alhamdulillah da sauƙi sossai Aunty na gode””Bana son sake ji kin ce Auntyn nan baki ji Abin da su Saraki ke faɗa bane?”Murmushi tayi.”Abeeha ki kula da ita har tayi bacci zan je Saraki na jirana in na sha sauran magungunan kuma kin san bana iya taɓuka komai sai da safenku””Toh Mammi sai da safe Allah ya kara sauƙi””Allah ya baki lafiya sai da safe Mammi”Afeefah ta faɗa ta amsa da murmushi kan ta fice.”Na ga dai baki da niyyar sa abincin nan bari na zuba miki”Abeeha ta faɗa tana zuba mata Afeefar ke cewa yayi amma sai da taji ya mata a ranta kan ta bari kuma tace sai Afeefar ta cinye, sossai moment ɗinta a gidan na yan awannin nan yayi mata daaɗi in ka cire arangamarsu da Rayyan amma Mammi da Abeeha mutanen kirki ne da suka yi ƙarancin samu a wannan zamani.Mammi na komawa ta samu ya gama, ɗaki ta shige ta fara shirin kwanciya cike da dauriya take komai fuskarta dai baya nuna wa amma ita ta san me take ji, sai da ya bata mintunan da yake da tabbacin ta gama yayi knocking ya shiga ɗakin tana zaune bakin gado sanye da doguwar rigan bacci har ƙasa mai kauri, frigde yaje ya ɗauko mata ruwa tulin magungunanta da suke cikin wani basket guda mai kyau ya ɗauko ya zaɓi na daren ya bare ya sanya mata a tafin hannunta, babu musu ta sha yadda ya buƙata kan ta kwanta, ya ja mata bargo ya zauna daga gefenta tare da riƙe hannunta ɗaya.Adu’a yayi ta mata tun tana kallonshi tana danne hawayen da suke ta yunkurin zubo mata har tayi bacci, idanunshi da suka rine ya ɗan rintse yana jin azaban da zuciyarshi ke yi, da yana da yadda zai yi ya mayar da ciwon Mammi jikinshi da bata shekara takwas tana fama da kidney failure ba, da kuɗi za su yi mishi maganin ciwon Mammi da ko zai yi yawo tsirara sai ya samar mata lafiya, sai dai yana roƙon Allah a koyaushe yadda aka bata wa’adin watanni uku za ta mutu amma yanzu shekara har bakwai da abin ya san ba yin su bane ba kuma dabararsu bace Allah ne mai yadda ya so, sai dai a tsananin tsorace yake hakan ya sa sadaqa da duk adu’ar shi yake kan Mamminshi itama saboda rage mishi damuwa take danne wani abin.Sai da ya tabbatar komai intact kan ya fice daga ɗakin yayi Sashenshi, Saleem ya ƙira da har lokacin yana asibiti yana samun kulawa”Har yanzu babu labarin Afeefah ko Rayyan?”Ajiyar zuciya Rayyan ya sauƙe “Na ce ka daina ɗaga hankalinka za mu same ta, ina kan bincike dai in har tana cikin Kaduna ba zata ɓace ba just focus on your health”Kai saleem ya gyaɗa sai yake ganin kaman Rayyan bai yi niyya bane, da yayi niyya ba zai kai zuwa lokacin bai same ta ba, damuwarshi ya zata kwana? A ina zata kwana? Me ta ci? Duk ya kasa kwantar da hankalinshi a gefe ga damuwar rashin ganin mommy Dukda ta mishi abin da ya zama gyambo a zuciyarshi sai dai uwa ce babu yadda ya iya kuma yana ƙaunarta bata da mahadi a wannan duniya.A ɗan sanyaye yayi sallama da Rayyan, Rayyan ya bi wayan da kallo baya jin zai gaya mishi inda Afeefah take saboda yana son Saleem ɗin ya manta da ita once and for all yanzu in ya san tana nan zai cigaba da sa hope a kan samunta alhali mahaifiyarshi bata ɗaura wannan damara ba na mallaka wa yaron nata cikar burin shi hakan ya sa ya ɓoye mishi wanzuwar Afeefar a gidansu.Su Samha ko da suka zo sun ƙaraci zamansu ko ci kanku bai ce musu ba sun gaishe shi ma bai amsa ba, wani irin zafin su yake ji a lokaci ɗaya yana mamaki bai taɓa sanin inhumanity ɗinsu ya kai haka ba, suka gaji suka tafi.****Washegari Da misalin karfe bakwai na safe Sulaiman ya fito shirye cikin manyan kaya, sallama yayi wa umma tana ta adu’ar dacewa Baba Jummai ma Adu’a tayi ta mishi har ya fice. Gidan Yaya Zubairu ya fara zuwa ya ɗauke shi kan ya wuce gidan babban Yayansu Abban Yaya Ummaru, dattijai ne masu mutunci da kamala kuma duk suna da dukiyar su daidai gwargwadon.Anan suka kama hanyar kauyen su Afeefah yana ta Adu’a da Fatan ya same ta chan Dukda bai yi ma tunanin rashin samunta ba don ina zata koma in ba gida ba? Tafiyan awanni kadan ya kawo su kauyen yana jin hirarsu Yaya Zubairu da suke zaune a baya, sai da suka ɗan shiga cikin garin kan ya ɗan tsaya jikin wani shago matasa ne zaune su wurin huɗu ya sauƙe glass”Assalamu Alaikum barkanmu da warhaka””Barka dai Alhaji””Don Allah tambaya nake yi””To Allah ya sa mun sani””Gidan su Afeefah kamal”Tsittt suka ɗan yi wannan ya kalli wanchan wanchan ya kalli wanchan..”Kai ko me zaka yi gidan su Mayyar yarinyar nan? Ai Annoba za ka ce sai mun fi gane ta””Annoba”Ya maimaita sunan, abin da ta faɗa mishi kenan me yasa ake ce mata annoba? Dan kallon su Yaya Zubairu yayi duk fuskar su ya ɗan nuna mamaki.”Gidansu nake nema”Ya faɗa ba tare da ya ji daaɗin furucin su a kanta ba.”Ka ga kara gaba sai ka tambaya a chan, ba mu san ko laifi ta muku ba kun zo yi wa kawunta tijara abu ya shafe mu lalala bamu shirya rigimar Labaran ba”Babu wanda ya tanka a cikinsu har ya ja motan suka yi gaba, wasu yara ‘yan daidai ya samu ya kira su su biyu “Gidan su Afeefah kamal nake nema”Ɗayan ya ɗan kalli ɗayan “Mayyar nan fa suke nema ta gidan su Auwalu”Ɗayan ya zaro ido “Wacce ta cinye Amadun gidan malam yahaya ta gudu duniya?””Eh ita ce…”Sai ɗayan ya gyaɗa kai ya juya ga Sulaiman da kanshi ya sake mugun ɗaurewa.”Idan kayi gaba ka ɗauki Layin hagu gida na biyu in baka gane ba ka ce gidan su Annoba kake nema ajalin duk wanda ya raɓeki”Suna kai nan suka gudu.”Sulaimanu a wani irin gida ka nemo aure? Wace irin yarinya ce wannan bata da shaida mai kyau?”Shiru yayi shima amsar yake nema don kwata kwata ya kasa fahimtar komai.Gaba yayi don clearing doubt ya sake tambayar wata mata a yanzu annobar shima ya faɗa yana runtse ido aiko ta nuna mishi, Da gaske ne ko wasa? Ya kasa ba kanshi amsa, kaman mafarki yake kaman kuma duniyar halluscination ya shiga don abin ya fi yanayi da almara, wacece Afeefah? Tarin mutane da suka gani kofar gidan kawu ne ya ɗan basu mamaki, bayan yayi parking suka fito su uku suka tsaya suna kallon abin mamaki, dambe ake ci da Kawu da inna larai har kofar gida duk ana tsatsaye ana kallonsu don su in suna yi ba’a raba su in ma ka shiga karshe kai za ka ji kunya, kuma ba karamin dukan ta yake ba, Bakinta ya ƙi shiru duk yaransu na zagaye suna kwasar kallo.”Wani irin tsantsar jahilci ne wannan? Sulaiman a nan gidan ka ɗauko aure? Anya da hankalinka?”Kawu Zubairu yayi maganan kaman ya rusa kuka.Kawu Ummaru ne ya je ya janye kawu Labaran daga riƙon da yayiwa larai ya ce “Haba malam baka san wannan abin da kake yin ya saɓa shari’a ba? Musulmi ne fa kai sannan mutum ba dabba ba wannan ai ɗabi’ar dabbobi ne, ba matarka bace ta sunna?””Kyale shi ai ni wandon roba nake daidai da kugun kowa, wlh ba zan yi wahala in nemi kudina Labaran ya dinga bin dare yana sace min ba shi ba ciyar da mu yayi ba kuma muyi wahala mu samu ya zama ɓera, Toh ni ba Asabe bace da ka gama kassarata ta koma cima zaune babu abin da take ba, kuma wallahi sai ka biyani kudina””Ni kike cewa ɓarawo? Yau sai na ci ubanki Larai sai na zubar da hakwaran rashin da’ar nan Malam Sallau shi zai raba mu”Babanta yake nufi, ganin za su cigaba da rigimar su kawu Ummaru ya ja shi gefe.”Ashe baka san Annabi yayi mana hani da dukan matan mu ba? Yanzu kai ba abin kunya bane yaranka gode-gode suna tsaye suna kallon ku ba? Dambe har kan layi? Subhallah”Kwarjini mutumin ya mishi da sai ya yanko mishi magana amma sai ya Buge da cewa “Waye kai? Me kake so? In baka da abin faɗa zan kama gabana don ina da abin yi”Girgiza kai Kawu Zubairu yake Sulaiman kam ya mayar da kanshi kasa yana jin yadda zuciyarshi ke cigaba da tsitstsinkewa don tabbas da matukar wuya Su kawu su bari su yi surkuntaka da mutum irin kawu, yanzu wannan baban Afeefah ne? Innalillahi wainna ilaihi rajiun ya maimaita ya kai sau biyar.”Sunana Umaru Malami zuwan namu ya shafi ‘yar wurin ka Afeefah”Zaro ido kawu yayi “Ba dai a yawon tambaɗarta ba ne ta kashe muku wani kuka zo nemanta? Ni fa na jima da yanke alaqa da yarinyar chan ba zai yiwu a dinga zuwa ana ɗaga min hankali akan kashe-kashe da take ba””kashe-kashe?”Kawu Zubairu ya maimaita “Wai baku sani ba? Ai rikakkiyar Mayya ce da ta addabi al’ummar garin nan a ƙarshe korinta muka yi ta shiga duniya”Jiri ne ya kwashi Sulaiman yayi baya baya ya dafa mota, zuciyarshi na harbawa da karfin gaske tuni idanunshi suka sauya, kwalwarshi ya nemi tsayawa da aiki amma sai ya tuna farkon abin da ya kawo Afeefah asibitin su ta sha poison ne don ta kashe kanta! Afeefah tana da tarin damuwa da yake haddasawa jininta sauƙa sossai zuciyarta kuma na ta kokarin samun matsala, me kenan? Menene ke kunshe a rayuwarta haka? Duk ya rikice amsa yake buƙata sai dai ba daga bakin wannan kaskantaccen mutumin da ya kira kanshi kawunta ba.”Toh mun gode ko, sai anjima”Juyawa kawu yayi ya kada rigar shi yayi gaba.”Sulaiman wannan ƙasƙanci har ina? Yanzu inda ka zabi neman aure kenan? Toh ba’a zuriyar Malami ba”Kawu Zubairu ya faɗa yana bude mota ya shiga, kawu Ummaru ma ya shiga Sulaiman da kyar yayi composing kanshi ya zagaya ya shiga ya tada motar a hankali yace “Don Allah ku yi haƙuri kawu ku yi min uzuri, wallahi Afeefah ba haka take ba ita nake so ba kawu…””Sulaiman ko Afeefah ta fi kowa musulunci a duniya ba za mu nema maka aurenta ba, ba za.mu taɓa hada zuri’a da irin mutanen nan ba, ban damu don an ce mata Mayya ba duba da irin kauyen da tarin jahilci ya musu yawa amma a yadda ta shiga duniya danginta suka watsar da ita har suke ikikarin yanke duk alaqa da ita, da kuma yadda muka sami wannan gida ba gidan aure bane, kana da tarin mata masu nasaba da asali cikakku waenda suke gaban iyayensu zaune don haka ka tabbatar baka kara tado zancen wata Afeefah ba, a yau ka fara dubawa cikin sauran yaran da iyayensu suke maka tayin auren su za’a hada aurenka da Munir”Kawu Ummaru yayi maganan. Muryar shi na rawa ya ce “Amma ka..w…”

Back to top button