Uncategorized

Tubali Book 1 Part 9 Complete Novel

NA
AISHA ALIYU GARKUWA

Ya harba ya fara aiki. 

Ajiyar zuciya Dr. Sulaiman Dr Fatymah, da kuma Dr. Imran suka sauk’e, tare kuma dajin wani irin farinciki saboda, taimakon da Allah ya basu iko da dama wajen iya ceto rayuwar Jannart d’in. 

Dr. fatymah ce ta soma treating duk inda Jannart din taji ciwo, bayan ta kammala ne kuma, Dr. Imran yayiwa Jannart din wasu allurai, wanda zasu taimaka mata wajen samun ingantaccen bacci, da kuma k’warin jiki idan ta farka. 

Bayan sun kammala yi mata duk wani abunda ya dace ne kuma, Dr. Sulaiman da kansa ya turo gadon da Jannart din ke kwance, zuwa wani d’aki dake gefen Emergency’n na musamman. 

Fitowarsu daga Cikin Emergency room dinne kuma, yasa Barrister Kabir ta sowa, cikin sauri ya nufesu, hankalinsa amatukar tashe yace.

“Dr. Yaya ya jikin Jannart din? Dan Allah ku fadamin halin da take ciki, kada ku b’oyemin.”

Ya kare maganan yana me hade hannayensa biyu, waje daya alaman roko.

Dr. Sulaiman ne ya dan matso tare da cewa.

“Calm down jikinta da sauki sosai, Domin da taimakon Allah munyi nasaran samo numfashinta, yanzu dai haka tana dakin hutu.”

Wani irin kakkarfan ajiyar zuciya Barrister  ya sauk’e, tare da d’aga hannunsa sama cikin matsanancin farinciki yace.

“Alhamdulillah Allah Nagode ma, Yah Allah ina rokonka da ka cigaba da bawa Jannart kariyarka akoda yaushe.” 

Dr. sulaiman kuwa kallon Barrister  din yayi, cikin kuma tausasa murya yace.

“Idan babu damuwa zan iya ganinka a office dina, saboda akwai maganar da nakeso muyi.”

Kai Barrister Kabir din ya jinjina, tare da cewa babu wata damuwa.

“Dr muje.”

Hakan kuwa akayi inda Dr. Sulaiman ya shige gaba, shi kuwa Barrister Kabir ya take masa baya. 

*Alhaji Idi Saleh Dakata House.*

Dr. Lukman ne ya d’ago da kansa ya kalli Alhaji Idi Sale Dakata dake tsaye, fuskarsa dauke da bacin rai da kuma zallan rashin jin dadin abunda ya faru yace.

“Alhaji Idi Saleh Dakata, kana ga abunda k’aninka yayimin yau, ya hanani duba Jannart,  bayan yafi kowa sanin cewar nine likitan da yake dubata tun tana yarinya, kana ga fa har tsawa yayimin wai kada nayi kuskuren tab’a ta, har yana cewa wai yasan abunda nake shiryawa takarkashin k’asa.

To Meya sani kenan? Yanaso yace ban iya aikina bane?” 

Dr. Lukman din ya tambaya yana sakin hucin iska.

Shikuwa Daddy hannu ya d’agawa Dr. Lukman di, Domin ayanzu kwata kwata baya bukatar jin korafin kowa, abun dake cikin zuciyarsa kawai ya ishesa. 

Wani irin numfashi mai zafi ya fesar, tare da d’agowa ya kalli Alhaji Abdu Tababa, da kuma Dr Lukman din. 

“Kuje zan ne meku daga baya.”

Yana gama fad’in haka ya juya, zuciyarsa amatukar hasale ya nufi cikin falonsa. 

Ganin hakanne kuma yasa Alhaji Abdu Tababa kama hannun Dr Lukman suka shiga mota, bayan maigadi ya wangale musu gate ne kuma, kaitsaye suka fice daga cikin gidan.

Daddy kuwa Koda ya karasa cikin falon nasa, Sam kasa zama yayi, shi d’ayansa yake ta safa da marwa atsakiyan falon,  Yayinda ya had’e hannayensa duka biyu awaje d’aya.

Lallai Tabbas akwai aiki babba a gabansa, wanda kuma dole saiya tashi tsaye. 

Babban abunda yake tambayar kansa kuma shine, Tayaya akayi Dr. Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara yagane cewar, shine wanda yasa ake bibiyansa?.

Ya akayi ma yasan gidansa, har tsaurin ido irin na yaron ya kawosa? 

Tayaya akayi ya yi wannan saken?

“Wani irin shegen yaro ne wannan? Mai tsaurin ido da taurin kai da rashin tsoro?” 

Yayiwa kansa tambayar, yana me sharce gumin daya keto masa.

Dai-dai lokacinne kuma Mom ta shigo, cikin falon, hankalinta amatuk’ar tashe, batare kuma da fahimci  din da Daddyn yake ciki ba tace. 

“Alhaji Ina Jannart d’in, Ina aka kaita wanni hali take ciki dan Allah ku fadamin.” 

Amatuk’ar fusace Daddyn ya juyo, cikin tafasan  zuciya ya dann wani tsawan daya saka hanjin cikin Momn kad’awa yace.

“Waya baki izinin shigomin falo kai tsaye? Kifita daga harkata fa Maryam, da kike tambayan Jannart kinfini sonta ne? Ba’ayata bace, Ina ruwanki da inda aka kaita? Ko kece kika haifa min ita? Fice min daga falo, tunkafun na aikata abunda zai bata miki rai!!!” 

Daddy’n ya fad’a fuskarsa babu alaman annuri asamanta. 

Hakan kuwa shiya sanya, gaba d’aya jikin Mom yayi sanyi, kamar kuma yanda ya buk’ata cikin sauri ta juya ta fice daga cikin falon. 

Abdull dake tsaye awaje kuwa ganin Mom nasu tafi to jiki asanyaye ne yasashi rufa mata baya.

Bayan sun isa nasu falonne ya kalli mahaifiyar tasa cikin sharce hawaye yace cewa.

“Ki kwantar da hankalinki Mom, Insha Allah Aunty Jannart ako Ina take Allah zai kula da ita, kuma naga Abba Kabir nema da kansa ya d’auketa, nasan kuma asibiti zai kaita.”

Jin abunda Abdull din ya fad’ane kuwa yasa Mom sauke ajiyar zuciya, lokaci guda kuma taji hankalinta ya d’an kwanta.

Wayarta ta dauka tare da lalub’o lamban Barrister Kabir din, saidai kuma amma kwata kwata wayartasa bata shiga, hakanne kuma yasa ta hakura tare da ajiyewa akan anjima zata sake kira.

      *Mainasara hospital*

Cikin yanayin tashin hankali Barrister Kabir ya zauna bisa kujerar dake gaban babban table ɗin dake gaba Dr Sulaiman.

Gyara zama Dr Sulaiman yayi tare da d’an sauk’e numfashi, kana ya fuskanci Barrister Kabir, murya a tausashe yace.

“Babanta ne kai?”.

Cikin sauri Barrister Kabir ya gyaɗa mishi kai alamun eh kawai.

Shi kuwa Dr Sulaiman, kai ya jinjina tare da ci gaba da cewa.

“Kuna sane da cewa tana ɗauke da chronic Asthma, wanda yayi worst sosai ajikinta ko kunsan hakan?”

Kai Barrister Kabir ya jinjina, kana cikin bada tabbaci yace.

“K’warai Dr. munsan da hakan.”

Ajiyar zuciya Dr. Sulaiman din yayi, kamar kuma zaice wani abu saiya fasa, rubutu ya danyi ajikin wata takarda.

Bayan ya mikowa Barrister Kabir din takardar ne kuma yace.

“Way’annan sune magungunan da zata sha idan ta farka, sannan kuma Dan Allah ana kiyaye yawan bacin ranta please dan  abubuwan sunyiwa zuciyarta yawa, har ta fara samun raunin harbawar jini.”

Kai Barrister Kabir din ya jinjina, tare da cewa.

“Insha Allah Dr. Nagode sosai, amma ya kake gani shin zan iya zuwa na Ganta kuwa.” 

“K’warai kuwa saidai kada kayi wata magana mai karfi da zai disturbing nata, saboda akwai alluran da mukayi mata, wanda akwai buk’atar dole saita huta.”

Kai Barrister Kabir din ya jinjina, tare da mikewa tsaye musabaha suka sakeyi da Dr. Sulaiman din. 

Bayan kuma ya gaya masa numbern dakin da  Jannart din ke ciki ne ya juya yafice daga cikin office din. Kaitsaye dakin da aka kwantar da Jannart din ya nufa,   

Koda ya shiga tura kofar dakin yayi, inda ya Sameta kwance tana bacci, an daura mata drip ajikinta.

Karasowa Cikin dakin Abba Kabir din yayi, cikin tsananin kulawa hadi da tausayawa ya sa hannu ya shafi goshin Jannart din dake bacci Cikin kwanciyar hankali. 

“Insha Allah Jannart farinciki yana nan zuwa acikin rayuwarki, Domin ba zaki tabbata acikin kunci ba har abada, Tabbas watarana makiyanki sai sunji kunya, kunya irin Wanda ba zasu taba iya daga Ido su kalleki ba, Insha Allah watarana zaki zama y’antacciya nan bada jimawa ba.” 

Abba Kabir din ya fad’a, cikin tabbaci da kuma sanin lokacin hakan na k’aratowa sabida yasan dole watan-wata rana gsky zatayi halinta. 

Sanin da yayi kuma cewar Dr yace abarta tasamu ishashshen hutu ne yasa shi matsawa can gefe, tare da zaro wayarsa kaitsaye ya dannawa lamban Dr  Sajo Kira. 

Cikin sa’a kuwa bugu uku kacal Dr Sajo ya d’aga wayan.

Bayan sun gaisane kuma Abba Kabir din ya gyara zamansa tare da cewa. 

“Yaya Sajo  jikin d’iyarku Jannart ne ya tashi,  yanzu haka muna cikin Mai-nasara Hospital an bata gado, saidai kuma ba Dr. Rayyern ne ya duba ta.” 

Daga can b’angaren Dr. Sajo yace.

“Subahanallah yanzu Ina fata jikin natan da sauki.”

“Eh.” Abba  ya bashi amsa.

Dr. Sajon kuwa cewa yayi.

“Karka damu Barrister Kabir Indai kuna Cikin Mai-nasara Hospital, koba Dr. Rayyern bane ya duba ta, To Ina tabbatar maka da zata samu isashshen kulawa, Domin gaba d’aya likitotin dake cikin asibitin sunsan aikinsu, kuma dukansu k’wararrune kamar yadda suke da lafiyayyun kayan aiki, sannan maganar Dr. Rayyern dinma zaku samu ganinsa Idan kukayi booking Insha Allah.

Cikin samun karfin guiwa yace.

“In Sha Allah kuwa zamuyi booking”.

“Yauwa sai munzo”.

To yace kana sukayi sallama da juna.

 Yana katse kiran ne  kuma ya kira Matarsa Aunty Dijat ya Sanar da ita halin da ake ciki, nanfa tace gatanan zuwa ta k’are mgnar da cewa. 

“Yanzu ya jikin nata?”.

Juyowa yayi  ya d’an  ya kalleta.

a hankali take fesar da numfashi alamin baccinta yayi zurfi.

“Da sauki.”

Ya bata amsa, Domin kuwa harzuwa lokacin Jannart din bacci take bata farka ba. 

“Allah ya ƙara sauki”.

Amin yace kana sukayi sallama.

K’arfe 5 dai-dai ne kuma yana nan zaune, kiran Yayan nasa, wato Alhaji Idi Sale Dakata ya shigo cikin wayarsa. 

Bayan ya d’aga wayarne kuma Daddy da hankalinsa ke tashe yace. 

“Wai Kabir ina kuka shiga ne? Wani asibiti ne ka kai Jannart, duk na karad’e asibitoci mafi kusa damu amma babuku babu alaman ku, kuna Ina sannan ya jikin Jannart din?” 

Daddyn ya had’ewa Barrister Kabir duka tambayoyin awaje d’aya. 

Barrister Kabir kuwa ajiyar zuciya ya sauk’e, tare da cewa.

“Kayi hakuri Yayah, gaba daya sha’anin ciwon Jannart dinne ya rudar dani, shi yasa bankira na sanar dakai komai ba, yanzu dai haka muna Cikin Mai-nasara Hospital, kuma jikin nata da sauki sosai Dan tun da doctors suka duba ta take bacci har yanzu kuma bata farka ba.”

Shima Daddyn ajiyar zuciya ya sauk’e, nan take kuwa yace.

“Okay ganinan zuwa Mai-nasara Hospital din” 

Yana gama fadin hakan kuwa ya kashe wayan.

Mom dake kallonsa ne kuma tace.

“Bari na dauko mayafi na muje, Domin dama na gama abinci, Idan yaso saina tafi musu dashi.”

Kai kawai Daddyn ya jinjina mata, Domin kuwa hardai yanzu, Jin zuciyarsa yake a Jagule. 

Koda Mom ta d’auko mayafin nata, kitchin ta wuce tare da daukan basket din da ta shirya food flask acikinsa.

Kaitsaye waje ta nufa, saboda tuni Daddyn ya fice. 

Tana fita compound din gidan kuwa ta sameshi zaune acikin motarsa, bayan ta shiga  kana driver yaja suka fice daga cikin gidan. 

6:12 pm dai dai suka iso cikin asibitin, wanda kuma zuwannasu yayi dai dai da zuwan Aunty Dijat.

Domin kusan atare ma suka shiga cikin d’akin da Jannart din ke kwance bisa jagorancin Barrister Kabir. 

Bayan sun gaggaisa da junansu ne kuma, Aunty Dijat ta zubawa Barrister Kabir din kunun data dama musu ya sha kasancewar itama tayi girki na musamman ta taho dashi.

A lokacin da aka soma kiraye kirayen Sallah magriba ne kuma, Daddy da Abba suka fice dan zuwa masallaci.

Yayinda su Aunty Dijat da Momy kuwa anan cikin d’akin asibitin sukayi nasu sallan. 

Dawowar dasu Barrister Kabir din sukayi a masallaci kuwa, yayi dai-dai da shigowan wasu nurses guda biyu. 

Ledan ruwan dake jikin Jannart din, wanda ya k’are nurses din suka cire, tare kuma da sake yi mata wasu y’an gwaje gwaje.

Bayan sun kammala duba lafiyar Jannart d’inne kuma, suka juyo inda d’aya daga cikin nurses din tace.

“Kuyi hakuri patient din batason hayaniya sosai, kuma ak’a’idar aikinmu Idan dare yayi, bama barin kowa acikin Hospital din sai masu kula da majinyata, saboda haka dole duk zaku tafi, saidai za a bar mutum guda d’aya kawai da zaina kulawa da ita, ma’ana wanda zai kwana da ita.”

Kai Duk suka jinjina, cikin gamsuwa da bayanan Nurse din Aunty Dijat tace.

“Shikenan To Abban Hafeez kuje, Idan yaso ni zan kwana da ita”

Saurin girgiza Kai Mom tayi tare da cewa.

“A’a Dijat baza’ayi haka ba, duk kuje ni zan kwana da ita, Domin ba wani d’awainiya ne akaina sosai ba, ke kuwa nasan dole su Hafeeza zasu nemeki.”

Murmushi Aunty Dijat din tayi kawai, saboda tasan maganan da Mom’n ta fad’a gaskiya ne.

Hakan kuwa akayi kamar yanda Momy tace, ita dince ta zauna awajen Jannart din , yayinda Barrister Kabir, Daddy, da kuma  Aunty Dijat suka koma gida. 

Mom na zaune kuwa har wajajen k’arfe 11 zuwa 12 amma Jannart bata farka daga nannauyan baccin da takeyi ba,  wanda kuma hakan ya samo asaline saboda, k’arfin alluran dasu Dr. Sulaiman sukayi mata. 

Acan gidansu Rayyern kuwa, gaba d’aya babu wani wanda zaka kalla kace yana cikin farinciki, musamman ma da ayanzun suka ga, Rayyern din ya kwashe sama da awanni bakwai bai farka daga baccin daya daukeshi ba. 

*11:30 pm*

Dai-dai ahankali ya soma bud’e idanunsa da sukayi masa nauyi.

Inda yana gama waresu kuwa ya sauk’esu, tarwal akan Abbansa dake zaune agefe, ya k’ura masa ido,  da dukkan alama kuma jiran farkawan nasa yake. 

Idanun nasa ya sake bud’ewa da kyau, cikin kuma dan kuzarin da ya saura masa, ya soma yunkurin tashi zaune. 

Ganin hakanne kuwa yasa Abba sakin numfashi, tare da cewa.

“Alhamdulillah Rayyern ka tashi ko, sannu ya jikin naka? Ya kakeji yanzu?”

Idanunsa ya d’an lumshe tare da k’ak’alo murmushin karfin hali, kana murya asanyaye yace.

“Alhamdulillah Abba, yanzu banajin komai naji sauki.”

Murmushin Jin dadi dukansu sukayi, Yayinda Riyyam da har yanzu yake cikin gidan, ya matso kusa da Rayyern din da sauri.

Hannun Rayyern din ya kamo, tare da d’an langwab’ar da kansa gefe, kana cike da soyayya hadi da kulawa yace.

“Masha Allah Hamma Rayyern, Naji dadi daka ji sauki, sannu ya jikin naka?”

Kansa yad’an jinjinawa Riyyam din, tare da dan gyara zamansa, Ahankali yace.

“Da sauki.” 

“Hamma Rayyern sannu ya jikin naka?.”

Cewar Ramadan daya taso ya matso kusa da Hamman nasa.

Kai Rayyern din ya jinjina alaman da sauki, dai-dai lokacinne kuma idanunsa suka sauka akan agogo.

Ganin lokaci ne kuma yasashi dan fiddo idanunsa, tare da Kallon Abba da Mamynsa cikin marairaice fuska yace.

“Abba 11:30 pm, narasa sallan  magriba, da Isha, Ayyah Abba mai yasa baka tasheni ba.”

Kai Abban ya girgiza tare da cewa.

“Tayaya zan tasheka Rayyern? Ai rashin lafiya ya kauda komai, yanzu ba gashi ka tashi ba, kuma Alhamdulillah ciwon naka da sauki, sai kaje ka rama sallolin da ake binka, tun kafun 12 am ya cika.

Kansa ya jinjina alaman “To.” 

Inda Kaitsaye Ramadan ya wuce sama ya had’a masa ruwan wanka acikin bathtub. 

 Da taimakon Ramadan din kuma ya haura sama yayi wanka.

Koda ya fito daga wankan, wani brown din jallabiya ya saka, tare da shumfud’a sallaya ya tada sallah.

30mn kuwa cas ya dauka yana sallan, bayan ya gama biyan duka sallolin nasa ne kuma ya sauk’o k’asa. 

Inda har yanzu suna zaune a falon.

Gefen Abbansa ya zauna ya d’an kallon mamynsa dake cewa.

“Sam Rayyern, baka kula da kanka saboda kwata kwata bakacin abinci, d’azu ma haka kafita bakasa komai acikinka ba sai kayan zak’i.”

Kaitsaye kitchine Mamyn ta wuce, batare kuma da taji ta cewarsa ba, ta hado masa ferfesun kaza, da kuma gasashshen kifi, hadi da ruwan tea mai kauri. 

Ganin kuma yanda iyayen nasa suka sakashi agaba ne yasa shi dagewa yaci, duk da cewar bayajin dadin bakinsa, amma haka yaci sosai. 

Koda ya kammala cin abincin sama ya haura, saboda still wani sabon bacci yakeji a idanunsa. 

Haurawansa sama dinne kuma yasa, Riyyam-nsra mik’ewa tsaye.

Cikin alamun bacci da kuma gajiya yace.

“Abba Mamy Yah Ramadan ni zan tafi, dama na zaunane kawai saboda inason naga tashin Hamma Rayyern.” 

Kai Ramadan ya dago tare da Kallon Riyyam din, Cikin nuna damuwarsa ga Riyyam din kuma yace.

“Gaskiya ba zaka tafi yanzu ba Riyyam, ka ko san k’arfe nawa? Yau kam dai ka kwana anan kabari gobe da safe Idan mukayi breakfast saika tafi.” 

“K’warai kuwa Riyyam dare yayi yanzu shabiyu fa, Ina zaka samu abun hawa ma, ka kwana anan kawai, yanzu ai duk munzama daya”

Cewar Mamy da ta cab’i zancen. 

Abba dake zaune, kuwa baice musu komai ba.

Ganin hakanne kuma yasa Ramadan kama hannun Riyyam din suka haura sama.

Koda suka isa saman direct dakin Ramadan din suka nufa

*Mainasara hospital*

Abba ne da Aunty Dijat suka turo kofar d’akin da Jannart take, a nitse suka kutsa kai ciki.

Dai-dai lokacin kuma Jannart ta ɗan fara motsa kwayar idanunta.

Wanda kuma ganin hakan yasa dukansu cikin sauri suka k’arasa shigowa cikin dakin.

Barrister Kabir da farin cikinsa ya kasa buya ne yace.

“Alhamdulillah Masha Allah Jannart ta farfad’o, Alhamdulillah.”

Jannart kuwa jin sautin Abban nata acikin kunnuwanta ne, yasaka ta kara Ware idanunta tare da yunkura ta tashi zaune. 

Kallon Abban nata tayi tare kuma da sakin sassayan ajiyan zuciya mai cike da burbushi kuka, kana Ahankali tace.

“Abbana.”

“Na’am Jannart ya jikinki? Ina da Ina keyi miki ciwo?.” Abba Kabir din ya amsa mata yana me shafa kanta.

“Babu inda yakemin ciwo Abba saidai banajin karfi ajikina.”

Jannart din ta fada tana me Zuro kafafunta k’asa.

Dai-dai wannan lokacinne kuma Daddy ya turo kofar dakin ya shigo. 

Yana Ganin Jannart din azaune ya saki murmushi, tare da karasowa cikin dakin, kaitsaye wajen Jannart din ya nufo, cikin nuna so da kauna hadi da tsantsar kulawa yace.

“Allah abun godiya Jannart ya jikin naki?.”

Murmushi Jannart din tayi tare da langwabar dakai cikin sanyi tace.

“Daddy jikina da sauki sosai.”

Kanta Daddyn ya ci gaba da shafawa, cikin kuma muryar dake bayyana rararrashi yace.

“Kiyi hakuri kinji Jannart, kwata-kwata bansan me yake damun Yayanki Junaid ba, Sam Junaid baida wadataccen hankali,  duk lokacin daya shawo giyarsa akanki yake huce duk wani haushinsa, bansan ya zanyi dashi ba Jannart, amma na d’auki samunsa amatsayin k’addarata wacce bazan taba iya sauya taba.” 

Ya kare maganar yana mai matsan k’walla daga cikin idanunsa. 

Wanda hakanne kuma yasa Jannart girgiza masa, Kai kana cikin sanyi tace.

“Karkayi kuka Daddy kaifa mahaifinmu ne, kuma zubda hawayenka asanadiyar Yah Junaid ba karamin masifa zai haifar masa ba.” 

Shiru gaba daya dakin ya dauka,  inda hakanne kuma yasa Momy zubawa Jannart din abinci.

Saidai kuma bataci abincin ba saida taje tayi brush tare dayin wanka kana ta kimtsa kanta da kayan da Aunty Dijat ta kawo mata wanda harda pand. Anan cikin toilet din dake cikin dakin ta gama kimtsawanta.

Bayan ta fito ne kuma ta zauna taci abincin, Duk da cewar batajin dadin bakinta kuma haka ta daure taci sabida yadda iyayen nata suka matsanta.

Kafun ta gama cin abincinne kuma Momy, tayi shirin komawa gida, acewarta zata je ta dawo.

To shima dai Daddyn kasancewar ba jimawa zaiyi bane yasa Mom’n na tafiya shima ya tafi ba jimawa, acewarsa akawai wani aiki da zaiyi. 

Hakan yasa dakin ya rage daga Jannart sai Abba Kabir da Aunty Dijat da kuma Hafeeza.

 

Wanda Hafeezan ne kuma ta kamo hannun Dijat, tare da cewa 

“Momy taso muje kiga waje.”

Yadda take tajan hannun tane tana d’aga sautin cewa su fitane yasa Dijat din ta mike kasancewar tasan ba’a son cika hayaniya kan mara lfy. 

Koda suka fito harabar wajen kuwa, akan wani kekkyawan kujeran silver Dijat din ta zauna. 

Ko mintuna 3 ba ayiba da  fitar tasuba.

Barrister Kabir ya gyara zamanshi tare da jawo kujerar da yake kai ya ƙara matsowa kusa da Janbart 

Zama yayi agefen Jannart din.

Wanda hakan yasa ta d’ago Idanunta dake cike tab da hawaye ta kalleshi.

Kai ya fara jujjuya mata yana mai jin rauni.

Gaba daya fuskarta ne ya sauya, Yayinda rauni da kuma matsanancin damuwa ya bayyana akan fuskarta.

Cikin kuna da kuma ciwon da takeji acikin zuciyarta ta ɗan gyara konciyar da tayi murya a sanyaye tace.

“Abba”.

Cikin tarin kulawa yace.

“Na’am Jannart”.

Ɗan yunƙurowa tayi ta ɗan tashi ta jingina da jikin gini.

Murya can ƙasa hawaye na kwaranya tace.

“Abba Yah Junaid ya tsaneni. Yah Junaid shine babban matsalata aduniya, Yah Junaid baya k’aunata Koda kad’an, Abba sai yaushe ne nima zan zama y’a kamar kowa? Sai yaushe ne zan samu ingantaccen farinciki? Sai yaushe zuciyata zata huta da kuncin rayuwa?  Yaushe Daddy zai fara daukan mataki akan abubuwan da Yah Junaid keyi min Abba ka rabani da gidan Daddy mana dan Allah ka medani gidanka…”

Dan tsagaitawa da maganan tayi tare da dafe saitin kirjinta dakeyi mata zafi. 

Cikin kuma muryar kuka tace.

“Abba zuciyata tana gab da bugawa, matukar rayuwata taci gaba da tafiya ahaka,Abba mutuwa zanyi, Domin wata kilan hakan shine zai zamo silar farincikina.” 

Saurin rufe  mata baki Barrister Kabir yayi, cikin kuma muryar dake bayyana tsananin takaicinsa da tausayawa da son fara fahimtar da ita wani abun da bata saniba sabida fara shirin kawo mata sauyi a rayuwarta yace.

“Bazaki tabbata ahaka ba Jannart Insha Allah haske yana nan zuwa, sannan  ki rabu da maganan Junaid dana Daddynki.

 Domin kuwa Dadynki *HANKAKA NE*…!!!”

TUBALI 18

NA

AISHA ALIYU GARKUWA

Shiru Jannart tayi tare da zuba mishi idanu, tana mai nanata kalmar daya suffanta Daddy’nta dashi.

“Hankaka!!!?”. Ta faɗa can ƙasan zuciyarta tana mai son nazartar ma’ana da  tushen kalmar a hausan ce.

Gyara zama Abba yayi tare da fuskantar ta da kyau cikin tsananin kulawa, tausayi ƙauna, jinƙai.

Murya a sanyaye yaci gaba da cewa.

“Bazaki fahimta ba Jannart kada ki tsauwalawa kanki tafiya nazari ko tunanin sarƙaƙiyar dake cikin rayuwarki.

Bazaki ganeba sai an ganar dake, ina cikin matuƙar damuwa mai tarin yawa.

Na yadda zan samu in zama GARKUWAR ki, ina tunanin kamar yarda da kikayi min tana da rauni bazan samu amincin da nake buƙata daga garekiba. Na amsar umarni na sawa ko hanawa!!!”.

Hawayen dake kwaranya bisa fuskarta tasa hannun ta ta share kana a take wasu suka kwaranyo.

Hakan kuma baya rasa nasaba ne da yadda taga idanun ƙanin mahaifin nata yana kwaranyo da hawaye.

Tana hango tsananin tausayinta cikin kwayar idanunshi.

Numfashi ta fesar a hankali tare da danne shessheƙan kukan dake son kumbce mata cikin aminci da dukkan yarda da yaƙini murya na rawa tace.

“Abba kana da ƙarfin iko a kaina.

Ni ɗiyace a gareka, kuma zan zamo mai biyayya akan dukkan umarninka, zan kuma nitsu in fahimci abun da kakeso in fahimta bani da wani katanga jigo majingini sai kai, Abba inada kekkyawan yaƙini kaine TUBALIN farin cikina”.

Wani zazzafan numfashi Barrister Kabir ya fesar kana ya ƙara jawo kujerar ta matso kusa da ita, cikin sanyi ya kama tafin hannunta murya can ƙasa yace.

“Yadda na riƙe hannunki haka.

Ana haifoki mahaifiyarki ta damƙa min amanarki.

Tana mai jaddada min cewa in zama Garkuwanki inyi miki zaɓi mijin na gari wanda naga ya dace dake, in gaya miki ke marainiyace tace in faɗawa duk wanda zan bawa aureki cewa ke marainiyace dan ya duba maraicinki.”

Ina shessheƙan kuka wanda yake tafe da zazzafan tsohon dafi mai ciwo a zuciyarsa ya danne mgnar.

Itama kukan ta farayi.

Wanda Har Aunty Dijat dake woje ta fara jiyo sautinsu.

Cikin tsananin rauni ya kalleta murya na rawa yace.

“Jannart in nayi miki zaɓi da miji kamar yadda mahaifiyarki ta roƙa, zaki amince dashi, zaki yarda da duk tsarin da zan zo miki dashi dan mu cika fatan mahaifiyarki!!! In Kuma samar miki ƴanci!?”.

Cikin kukan ta gyaɗa mishi kai.

Hannunshi yasa ya sharce hawayen sa kana ya tsareta da ido tare da cewa.

“Zaki iya amincewa in ɓoyeki, in bada ajiyarki a killataccen wurin da zaki tsira da ranki da lfyarki tun kafin wa’adin da suka tsara a kanki ya cika”.

Zuwa yanzu kanta ya ƙara ɗaurewa, duk da ta saba jin waɗannan zantukan a bakin ƙanin mahaifin nata, amman har yau ta gaza samar musu muhallin ajiyewa.

Cikin rashin fahimta tace.

“Abba na amince”.

Kai ya gyaɗa kana yayi ƙasa da murya yace.

“Har Daddynki fa zaki bari bazaki kuma sanar mishi komaiba, bazai san inda kikeba”.

Hannu tasa ta dafe ƙirjinta tare da zaro ido kana tace.

“Abba in na dawo Yah Junaid zai kasheni, kuma Daddy na zai shiga tashin hankali!”.

Numfashi ya fesar kana a hankali yace.

“Lokacin da zaki dawo, zaki dawo da encinki mai ƙarfi, Junaid ko farcenki bazai taɓa ba, Daddy kuwa kunya zata makantar da idanunshi sabida ya gaza zama uba kuma Garkuwa a kanki.

Sai dai hakan bazai faruba sai da amincewarki da sahalewarki.

Kuma sai haka ta faru zaki gane kurman baƙin dake cikin rayuwarki.

Shin kin amince!!!?”.

Cikin zulimi tace.

“Abba har na tsawon wani lokacin zaka ɓoyeni? Kuma ina zaka ɓoyenin?”.

Da sauri yace.

“Bana tantance lokacin ba, amman zan ƙiyasta wata takwas zuwa shekara ɗaya.

Sannan inda zan ɓoye ki kuma shine ban gama tantancewa ba, amman ki aminta dani GARKUWA zan nema miki”.

Ajiyan zuciya mai nauyi ta sauƙe kana a hankali tace.

“Abba na aminta da kai nasan baza cutar dani ba”.

Da sauri yace.

“Toh ki adana wannan mgnar amanace tsakaninmu kada ki gayawa kowa, duk faɗin duniyar nan.

Nan kusa kuma zan samu wurin adanaki mai inƙanci”.

Cikin sauƙe numfashi tace.

“Toh Abba”.

Shigowar Aunty Dijat ce yasa suka katse zancen.A nan gidan nasu kuwa.

Mom na komawa ta shiga Kitchen aikin ta farayi yayinda Abdul ke gefenta yana tayata kana yana mgna, da Yah Azeez ɗinshi wanda.

Kwanan ya koma Macsow kasan cewar acan yake aiki.

“A jikin da sauƙin Yah Azeez yanzuma Mom ta dawo anjima in munje zan haɗaku a waya”.

Abdul ya bawa Azeez amsa.

Cikin tausayawa Azeez yace.

“Toh shi kuma wawan ina yake”.

Mom ce ta ɗan ja tsaki tare da cewa.

“Yoh waya sani tun jiya da abin ya faru daya fita bai dawo ba”.

Kwaffa yayi tare da cewa.

“Allah zai saka mata”.

Daga nan dai sukaci gaba da mgnar suna aikinsu.

Saida suka gama  aikin ta shiga Bathroom Dan yin wonka.

_Dan Allah daga wannan PAGE din kada a fidda wani_

A can Gidansu Dr Rayyern Mai-nasara kuwa kasan cewar yau jumma’a.

Basu dawo masallaci da wuriba,

Sai kusan ƙarfe takwas suka shigo

A jere da ma’aikatan gidan baki ɗayansu.

Yayinda suka gaggaisawa suna tambayar jikin Rayyern.

A hankali ya kalli Baba Mauɗo tare da cewa.

“Alhamdulillah Baba Mauɗo na saumu sauƙi banjin komai sai baccin da nake ji bai isheni ba”.

Cikin jin daɗi Baba Mauɗo yace.

“Alhamdulillah Allah ya ƙara mana lfy”.

Amin Amin sukace baki ɗayansu.

Abba ne ya ɗan kalli Ramadan dake cewa.

“Eh kasan mgnin ne zai ɗan saka jin bacci”.

Kai suka gyaɗa alamun gamsuwa.

Dai-dai lokacin da suka shiga falon ne Riyyam-nsra ya lumshe idonshi sabuda sabida ƙamshin masar da Mamy ke toyawa wanda duk ranar jumma’a take yinshi bisa umarnin Rayyern za’a cika manya-manyan kuloli kana ta dama kunun gyaɗa suna kaiwa tsangayar al’majirai”.

Da sauri ya nufi Kitchen din yana cewa.

“Mamy Barka da safiya”.

Murmushi tayi tare da sauƙe kaskon tuyan dan tun ƙarfe huɗu take farawa in lokacin salla yayi sai taje tayi kana tazo taci gaba.

So yanzu ta gama.

“Barka dai Riyyam-nsra kun dawo ko”.

Kai ya gyaɗa mata yana kallon tukunyar ferfesun data sauƙe.

Shaƙan zazzafan ƙamshi yayi tare da cewa.

“Wow special Mamy girkinki da daɗi”.

Juyowa tayi ta da sauri jin ƙamshin turaren Rayyern.

Ƙarasowa yayi cikin Kitchen din.

Gefenta ya ɗan tsaya, tare da buɗe manyan kulolin.

Ita kuwa foodflask  ɗin da ta zuba musu breakfast ɗinsu a ciki ta nunawa Riyyam-nsra tare da cewa.

“Kai manasu Dinning”.

Da sauri yace to kana ya ɗauka ya fita.

Juyowa tayi ta kalleshi tare da cewa.

“Rayyern ya jikin naka?”.

Kai ya jinjina tare da cewa.

“Na worke”.

Cikin jin daɗi tace.

“Alhamdulillah, Allah ya ƙara mana lfy”.

Amin Amin suka amsa shida Riyyam-nsra.

Ramadan kuwa da Abba suna can falo, da alamu mgnar aure Ramadan keyiwa Abba duk ya marairaice.

Cikin haɗe fuska Abba yace.

“Kai da Allah tafi daga nan, Yayanka ma baiyi aureba sai kai ai dole dai ka jira sai yayi ko”.

Fuska ya kwaɓe tare da longobar da kai kana cikin girmamawa yace.

“Toh Abba”.

Yana faɗin hakan kuma ya miƙe ya nufi Kitchen ɗin.

Da ido ya bishi yana mai jin zafin tsawar daya daka mishin a ransa Allah ya sani baya son yin abinda zai b’atawa yaranshi rai more especially Rayyern.

“`Special people group 1k ne karamin group kuma 500 BABBANCINSU a yawan posting ne“`

Rayyern kuwa dake gefen Mamy cikin nitsuwa yace.

“Mamy kada Ramadan ya kai masar tsangayar malam Babayo.

Ya bari yau tsanƙayar Malam Mai-nasara zan kaishi, in Abba ya amince”.

Juyowa tayi ta ɗan kalleshi tare da cewa.

“Toh Allah yasa ya amincen”.

Amin yace yana mai bin bayanta suka fito.

A Dinning area Suka haɗu da Ramadan da yayi fuskar tausayi,

Ɗan zuba mishi ido yayi kana ya kauda kanshi ya nufi tsakiyar falon.

Mamy kuwa gefen Ramadan da Riyyam-nsra da suka zauna bisa Dinning table tayi kana ta kalli Riyyam-nsra tare da cewa.

“Baka kaiwa su Baba Mauɗo nasuba”.

Da sauri Riyyam-nsra ya miƙe tare da cewa.

“Toh”.

Kana ya ɗauko kulolin da plate cups and spoons. Ya wuce.

Shi kuwa Rayyern a nitse ya zauna gefen Abban nasa, cikin sanyi yace.

“Abba”.

Numfashi ya ɗan fesar kana yace.

“Na’am Rayyern, ya akayi”.

Yayi mgnar cikin tsananin kulawa.

Cikin yanayin neman al’farma yace.

“Abba sadakan nane  nace, dan Allah yau ka amince mu kaishi tsangayar Mai-nasara”.

Ga mmkinsa sai yaji Abba yace.

“Toh Allah ya bada ladan”.

Cike da mmki yake kallonsa yana kuma muƙewa,

Numfashi ya fesar fahimtar Abba yana cikin zurfin tunanine shiyasa ya amsa a sauƙaƙe.

Hakan yasa da sauri ya dawo Dinning area.

Cikin bada umarni ya kalli Ramadan da Riyyam-nsra da ya shigo yanzu yace.

“Yauwa taso maza ku ɗauki womas ɗinan ku kai min cikin mota”.

To sukace kana suka fara ɗauƙa.

Shi kuwa da sauri ya haura sama ya ɗauko car key ɗin nasa.

Koda ya sauƙo a hankali yace.

“Toh Abba na tafi”.

“Sai ka dawo”.

Ya bashi amsa da alamun har yanzu yana cikin nazari ne.

Yana fita su Ramadan na fita da kulolin ƙarshe.

Riyyam-nsra ne ya buɗe mishi gate ya fita.

Kana ya rufe sannan suka dawo cikin gida.

Bayan duk sun zauna kan table.

Mamy ta kalli Ramadan tare da cewa.

“Kira Abbanku”.

To yace kana ya miƙe ya sauƙo steps ukun tare da cewa.

“Abba breakfast is ready”.

Wani dogon numfashi mai nauyi yaja ya sauƙe a hankali kana yace.

“Toh”.

Sannan yazo saida ya zauna ya kallesu cikin kulawa yace.

“Rayyern fa!?”.

Cikin nitsuwa Riyyam-nsra yace.

“Abba ba yanzu ya fita kai abincin al’majirai ba”.

Kai ya jinjinawa Riyyam-nsra.

Ita kuwa Mamy cikin fahimtar halin da yake ciki ta zuzzuba musu breakfast ɗin kana suka fara ci.

Mai-nasara Hospital.

Suna cikin hirar Jannart ta ɗan gyara konciyarta tare da lumshe idonta lokaci ɗaya bacci yayi awon gaba da ita.

Hakanne yasa Abba koma gida.

Aka bar Aunty Dijat.

Abba na tafiya ba dadewa Mom da Abdul suka iso.

Kasan cewar tana baccine yasa suka koma gefe suka zauna suna ɗan taɓa hira sama-sama gudun kada su tasheta.

Yayinda Abdul yake riƙe da wayarta.

Yana mgna da Salman.

Nan ya gaya mishi suna asibiti.

Koda Dr Sulaiman yazo ya dubata.

Ganin tana bacci ya shaida musu jikin da sauƙi sosai.

Shi kuwa Dr Rayyern Mai-nasara.

A hankali yayi parking a gaban tsangayar malam Mai-nasara.

Kana ya fito, 

Cike da Mamiki Uncle Mustapha da shima yanzu ya iso da abincin al’majirai da yake kawowa daga gidansan.

Dan al’majiran malam Mai-nasara basa yin Bara shi da yaransa suke ciyar dasu.

Da sauri ya nufi Dr Rayyern cike da mamaki yake cewa.

“Ikon Allah wa nake gani kamar Dr Rayyern Mai-nasara?”.

Da sauri ya juyo suka fuskanci juna, musabiha sukayi cikin jin daɗi yace.

“Ya Malam da jiki?”.

Cikin jin daɗi yace.

“Masha Allah mu isa ciki, malam na nan jiki yayi lfy sosai fa!.”

Ya ƙare mgnar yana miƙawa wani Gardi key ɗin motarsa tare da cewa.

“Yauwa Yayana gashi fito muku da abincinku”.

Da sauri Dr Rayyern Mai-nasara shima ya miƙa masa key ɗin motarsa tare da cewa.

“Ga wannan ma ka duba baya ka fito muku da abincin”.

Cikin jin daɗi Wanda Uncle Mustapha ya kira da yaya ya amshi key ɗin. Tare dayi musu godiya.

Shi kuwa Uncle Mustapha jagora yayiwa Dr Rayyern Mai-nasara,

har cikin gidan Malam Mai-nasara.

Kana suka nufi wannan falon.

Yana mai cewa.

“Duk ranar jumma’a Malam bai fiye amsar baƙiba, amman nasan kai na musamman ne, mu shiga”.

Ɗan guntun Murmushin yayi kana suka kutsa kai tare da sallama a baki.

Can Dr Rayyern Mai-nasara ya hango Malam Mai-nasara, zaune tsakiyar falon.

Yayinda wata kekkyawar tsohuwa ke gefenshi, da alamun abin karin kumallo take zuba mishi.

Ganin Dr Rayyern Mai-nasara ne yasa Malam yunƙurawa ya tashi zaune.

Cikin yalwataccen murmushi ya miƙo mishi hannu tare da cewa.

“Masha Allah. Wa nake gani kamar Dactana mai Nasara”.

Hannunshi ya miƙa mishi ya jawoshi ya zaunar dashi kusa dashi.

Yayinda ya kalli Uncle Mustapha dake cewa.

“Ai kuwa  shine dai Malam”.

Hannunshi ya ɗaura tsakiyar kan Dr Rayyern Mai-nasara tare da cewa.

“Lallai.kuwa yau ka amsa sunanka Mai-nasara dunda kayi nasarar ganina da safiyar jumma’a.”

Cikin son dattijon yace.

“Alhamdulillah Nasara ta haɗu da nasara kenan”.

Murmushi sukayi baki ɗayansu.

Yayinda tsohuwar nan kuma ta zuba mishi ido tana mai mishi wani irin kallo.

Kai ya juyo ya kalleta tare da cewa.

“Barka da safiya”.

Gyara zamanta tayi tare da sauƙe numfashi kana cikin kulawa tace.

“Barka dai Mai-sa’a. Yau dai da Malam zakayi karin kumallo”.

“Sosai ma kuwa”.

Malam Mai-nasara yace yana mai gyara zamanshi.

Ita kuwa tsohuwar kekkyawan akoshin dake tururin danderun naman ragon ne, ta turo tsakiyarsu.

Kana ta jawo ɗayan kuma tuƙeƙen tuwon alkmana ne mai kyau.

Da miya a kanshi miyar ɗanyar kuɓewa mai kyau tana ƙamshin man shanu, da ƙamshin ɗumamen.

Sai kuma bread mai kyau na masu ciwon sugar sai flask. Da cups biyu.

Misa alamu dai da basu zoba da tare zasuci abinci da tsohuwar.

Kai Rayyern ya ɗan jinjina tare da cewa.

“Alhamdulillah fa malam kaci kawai”.

Cikin kula Malam yace.

“Ina muci dai, ai dole kaci, tunda ba giya bace, ko kyamar tsoho kakeyi ne?”.

Da sauri ya jujjuya kanshi alamun a a.

Ita kuwa tsohuwar nan ɗan ƙaramin kwaryar dake gabanta da ruwa a ciki ta tura masa tare da cewa.

“Toh wonke hannunka kuci”.

Abu kamar wasafa dole suka matsa mishi.

Allah ya sani yana son tsohon haka yasa ya ɗan gyara zamanshi,

cikin nitsuwa yace.

“To a bani tea”.

Da sauri ta haɗa mishi tea.

tare da amsar akoshin danderun da Malam ke miƙo mishi.

Dole yasa hannunshi cikin kwaryar ya wonke.

Kana ya gyara zamanshi tare da kallon Malam yace.

“Malam ya jikin naka kuma?”.

Loman tuwon daya sa a baki ya haɗiye kana yace.

“Alhamdulillah Rayyanu naji sauƙin jikina sosai sai yawan ci”.

Juyowa yayi ya kalli Uncle Mustapha dake cewa.

“Dan Allah Dacta kaci girkin Innayinmu, zaka jishi da banne dana sauran matan duniya”.

Ya ƙare mgnar yana miƙewa tsaye.

Yayinda ita kuwa Innayi tayi murmushi tare da cewa.

“Kwarai kuwa har matarsa ma”.

Murmushi yayi tare da cewa.

“Toh ki bari a yaba miki mana”.

Dariya sukayi duka.

Kana su suka fita.

Ya rage dagashi sai Malam Mai-nasara.

Wanda ya maida hankali kan cin abinci.

Shi kuwa tea ɗin ya ɗan zuƙa a hankali.

Idanunsa ya lumshe tare da buɗe su.

Tabbas Mamynshi ƙarshece a girki amman daga shayin tsohuwar nan yaji da ban.

A hankali ya ɗago kanshi ya kalli Malam dake cewa.

“Dan Allah Rayyanu kaci naman nan zakaji dadinshi”.

Kai ya jinjina kana yasa hannunshi cikin akoshin.

A nitse ya ɗan yagi tattausan tsokar kana ya kai bakinshi.

Wani irin tsinkewa yaji yawunsa yayi tare da amsar saƙon ɗanɗanon naman nan mai cike da ƙamshi.

“Ya Salam”. shine abinda  ya faɗa a zuciyarshi.

Tea ya kurɓa kana ya ɗan kalli Malam cikin hikima yace.

“Ni ko Malam sunan kakanka ne Mai-nasaran ko?”.

Kai malam ya jujjuya mishi alamun a’a.

Cikin jin daɗi ya gyara zamanshi tare da ɗan ture akoshin gefe.

Sosai naman ya mishi daɗi to amman matsalar bazai iya cin abincin nama da sassafe hakaba.

In yasha tea ɗin kawai ya gamsu sai irin 11-12 haka zai iya cin wani abu kuma.

“Kaci mana”.

Malam yace.

Kai ya gyaɗa kana ya kafe kofin a baki ya zuƙe team ɗin kana ya ajiyeshu gefe, tare da cewa.

“Toh Alhamdulillah na ƙoshi”.

Murmushi kawai malam yayi tare da wonke hannunshi.

Shi kuwa a hankali yace.

“Toh Malam menene Tubalin sunan naka”.

Toro mishi kwaryar malam yayi tare da yin dariya sosai.

Hannunshi yasa yana wonkewa yana kuma kallon tsohon yana murmushi ganin yadda yake dari.

Cikin tsagaita dariyar Malam yace.

“Lallai kam ka nemi jin tsohon lbri”.

Sai kuma ya ɗan kishingiɗa.

Da sauri Dr Rayyern Mai-nasara yace.

“A’a Malam tashi zaune, ba’ason mutun ya kwanta bayan cin abinci a take, anfi son ka ɗan zauna koma motsa jiki, ko ga masu lfy kwanciya da zaran an gama cin abinci yana haifar da cutar sugar.”

Da sauri Malam yace to kana ya zauna tare da cewa.

“Tubalin sunana ya samo asaline tun ina yaro ɗan shekaru tara a duniya, da aka kaini al’majiranci.

Anan na samu sunan Mai-nasara nawane na kaina bana Babana bane ko kakana”.

Sai kuma ya ɗanyi shiru ganin hakane yasa Dr Rayyern cewa.

“Tah yaya aka sama sunan?”.

Numfashi ya ɗan fidda kana yace.

“Asalina ɗan jihar Adamawa state ne, yankin Jada al’majiranci iyayena suka kawoni jihar Kano.

Nazo kano bani da kowa sai Allah sai malamina, wanda a ƙalla yakeda ɗalibai sun kai ɗari biyu,200 baya shayar damu bare ci damu.

Mafi akasari ranaku ɗalibai kaso 100 cikin 200 da yunwa suke kwana da wuni.

Wasu kan shiga gidaje 7 ba’a kirasu ba, cikin ikon Allah ni kuma duk gidan dana shiga sai an kirani kuma sai an bani abinci.

Haka yasa abincin da nake samu yafi ƙarfin cikina, sai nake rabawa yara kamata.

Yayinda wasu manyan ma ke zuwa suna roƙata inje musu Bara, duk wanda ya bani akoshinsa sai na cika mai nake dawowa.

Toh fa daga nan ɗalibai suka samin Mai-nasara. Cikin ikon Allah kuma nasarar ta bini. Nayi karatu na tsawon shekaru goma sha biyu na haddaci al’ƙur’ani mai girma da tarin littattafai.

Daga nan kano ta zamemin uwa goya marayu, malam ya bani yarsa itace wannan data tafi yanzu na aura.

Kana na fara kasuwanci Allah cikin ikonsa ya samin al’barka a harkar kasuwanci na.

Na ƙara mata biyu ƙannena suka dawo gareni da iyayena.

Allah ya azutani da yara sama da 37.

Kaga ai nasara ta yiwu, duk da bayan nasarar na fuskanci ƙalubale akan d’a mafi soyuwa a gareni”.

Cikin gamsuwa Dr Rayyern Mai-nasara yace.

“Allah sarki”.

Da sauri ya katse shi da cewa.

“Kai kuma menene TUBALIn sunan naka”.

Murmushi yayi tare da cewa.

“Nima ɗalibai ƴan uwanane suka samin shi.

Sabida duk jarranawar da zanyi bana faɗunwa.

Kuma duk abinda nasa gaba sai na cimmasa”.

Shigowar Uncle Mustapha ne yasa suka tsagaita da hirar, kana akaci gaba da hirar dashi.

Har sai tara dai-dai suka sallami Malam suka tafi

A bakin gate suka samu wannan gardin ya basu keys ɗin su suka tafi.

Daga nan kai tsaye gida ya koma

A can MAI-NASARA Hospital kuwa.

Ma’aikatan Arewa 24 TV ne, kusan su shida ke cikin ɗakin da Jannart ke konce.

A hankali ta kalli Aisha Lawal dake ta gyara mata gashin kanta dake kan kafaɗunta.

Salman ta ɗan kalla cikin nitsuwa tace.

“Yah kiraka kuwa?”.

Cikin yanayin tausayawa yace.

“Keda baki da lfy me ruwanki da kiran wani”.

Hajia Rabi’ah ce ta ɗan yi murmushi tare da cewa.

“Yoh keda ma gaki a asibitinsa”.

Aunty Fauziyya D Sulaiman kuwa cikin kula da nagarta ta ɗan shafa goshinta tare da cewa.

“Ai dukkan uzuri bayan lfy yake, kada ki damu kinjiko Jannart MD da kansa yace a gaidaki da jiki”.

Cikin jin daɗi ta kalli Fauziyya D Sulaiman tare da cewa.

“Ngd matuƙa My Aunty”.

Mom kam dake gefe sai godiya takeyi musu.

Sun jima anan kana suka ajiye ledodin Fruits da suka kawo mata,

Kana suka fita.

Har sunje bakin ƙofar fita Salman ya juyo jin tana cewa.

“Salman kada ka manta fa saura kwana  biyar  kacal”.

Murmushi yayi tare da cewa.

“In dai ina raye to kisa a ranki kinada GARKUWA”.

Yana faɗin haka suka fita.

Kasan cewar yau jumma’a haji babbar ranace yasa, dukkan Al’ummar musulmai suke cikin yanayi na musamman duk kan maza nata shirin zuwa sallan jumma’a tako ina.

Sha biyu da rabi dai-dai haka take a gidansu Dr Rayyern Mai-nasara ma.

Yayinda hakama Barrister Kabir kasan cewar duk a Nassarawa G.R.A suke yasa gaba ɗaya masallacin Al’furƙan suke da niyar zuwa.

A hankali ya kalli Mamy dake ce mishi.

“Toh Rayyern me kake so in dafa maka ne? Ni bana son zamanka da yunwar nan fa”?.

Yana mai haurawa saman yace.

“Mamy yanzu lokacin jumma’a ya ƙara to, bari inje inyi shirin salla in na dawo zanci abincin”.

Da ido kawai ta bishi ganin tuni ma ya haura sama.

A hankali ya ɗan juyo ya kalli ƙofar Bedroom din Ramadan jiyo muryarsa shida Riyyam-nsra alamun suma shirin tafiya jumma’a sukeyi.

Dan yana jiyo muryar Riyyam-nsra na cewa.

“Nima fa mai gare zaka bani in saka Hamma Ramadan”.

Kai kawai ya jinjina ya wuce Bedroom ɗinsa.

Kai tsaye Bathroom ya wuce.

Bayan 15mn ya fito ɗaure da towel.

Gaban dreesing mirror’nsa ya nufa cikin yanayin sauri-sauri ya busar da sumar kanshi tare da shafa mai kana ya miƙe ya nufi gaban ƴar ƙaramar Driver’n’shi na glass dake gefen babban durowar.

A hankali ya buɗe, ido ya ɗan zubawa ƙananan kayanshi dake kimtse a ciki.

Wata tattausan boxer  and single ya zaro masu ɗan karen taushi.

A hankali ya meda marfin ya rufe, sauri-sauri yasasu kana ya zare towel din ya cilla gefe ganin ɗaya ta kusa cika.

Babbar durowar ya buɗe,

Wasu kayan ya zaro Getzner fara ƙal mai masifar kyau da sheƙin maiƙo.

Riga da wondo.

Sauri-sauri ya saka su.

Kana ya koma gaban Driver’n’shi na glass din hula damanga ya zaro Royal blue kalan zaren surfanin da akayi wa Getzner aikin rigar.

Sunkuyowa ya ɗanyi toms masu masifar kyau samfarin Italy ya zaro suma Royal blue.

Kana ya dawo gaban dreesing mirror’nsa.

Kafa hular yayi irin kafin nan da matasa ke cewa.

Babu ruwanka da duniya.

Wato ya ɗan ture hular ta koma baya kaɗan hakan yasa tattausar sumarshi ta fito tana zuba sheƙi sajenshi ya kwanta lib sai sheƙi yake siraran lips dinsa suma suna sheƙin taushi.

Sai kuma ya sunkuyo yasa fararen sawunsa cikin takalman.

Agogon Daimond dake kan mirror’n ya saka.

Turarensa Oud Zauji mai masifar daɗin shaƙa ya fesa.

Kana ya zari car  key ɗinsa Dan lokacin ya ɗan so ƙure mishi.

Da sassarfa ya sauƙo kan steps din har yana takawa bibbiyu.

Ba kowa a falon yasa da sauri yasa kai ya fita, ko su Baba Mauɗo duk sun tafi sai Ari.

Haka yasa ya buɗe mishi gate kana Suka tafi tare haka nan yake ta jin tsinkewan zuciya da faduwan gaba.

Numfashi ya ɗan fesar lokacin daya shiga cikin masalacin sabida har yanzu huduba akeyi.

Inda ake hudubar akan illar cin riba.

Sosai aka nitsu, bayan an ida hudubar ne kuma aka kabbarta sallan…

Bayan sunyi raka’a biyun, an zauna zaman tahita.

Sun ida zasuyi sallama sunyi gefen dama sun juyo hagu.

Kenan Barrister Kabir ne dake gefen daman Rayyern ɗin ne  ya ɗan leƙo fuskar Dr Rayyern bayan ya sallame.

Wata iriyar sassayar ajiyar zuciya mai nauyi ya sauƙe tare da ɗaga hannunshi sama ya fara yiwa ubangiji kirari cikin zuciyarsa yana ƙara neman zaɓin Allah kan manufarsa da addu’a in al’khairi ne Allah ya nufeshi da ida nufinsa a wannan lokacin.

Yayinda shima Rayyern da mafi akasarin mutane hakan sukeyi.

Bayan an idar da salla ne, Dr Rayyern na fita yaji an riƙo hannunsa tare da ce masa.

“Assalamu alaikum”.

Da sauri ya juyo tare da cewa.

“Wa alaikassalam”.  Fuskarshi ya ɗan yamutsa alamun tunani kana a hankali yace.

“Lfy”.

“Lfy lau Alhamdulillah Dakta”.

Barrister Kabir ya faɗa yana mai jawo hannun Dr Rayyern ya nufi can kan titi wurin motarsa.

Ba tare da ya ƙara mgna ba yabi bayansh.

Suna zuwa ya buɗe suka shiga….!

Anan asibitin kuwa, da Yamma Dr Sulaiman ya bawa Barrister Kabir takardar sallama, sabida sosai jikin Jannart yayi sauƙin.

Ya ƙara da cewa.

“Idan an barku kun ƙara kwana tofa sai ranar Monday za’a sallameku. Toh kuma tunda jikin da sauƙi gwara kuje gida zaifi”.

Dr Sulaiman yayi mgnar bisa bin umarnin da Dr Rayyern ya kidanya mishi a waya.

Cikin jin daɗin samun lafiyar nata Barrister Kabir yace.

“Toh Alhamdulillah Dr Sulaiman mun gode matuƙa Allah ya bar zumunci”.

Amin Amin yace tare da juyawa ya fita.

Su kuwa biyar dai-dai Barrister Kabir ɗin ya ɗauki Jannart da Mom ya nufi gida dasu.

Suna kan hanya ne Daddy ya kirasu yazo bai samezu ba.

Nan yake ce mishi ai an sallamesu gasu a hanyar gida.

Nan dai suka koma gida Barrister Kabir ya bawa Mom magungunan tare da cewa ta kula da Jannart da shan mgnin.

Ba tare da yayiwa yayan nasa mgnar Junaid ba ya sallamesu ya tafi.

Toh a hankali dai  abubuwa ke juyawa suna wakana.

Yau Monday kwana biyu kenan da sallamo Jannart Alhamdulillah kuma jiki yayi sauƙi sosai.

Junaid kuma har yau bai zo gidaba.

Barrister Kabir kuwa duk cikin kwanakin nan bashi da zama yana yawan zirga-zirgan da Aunty Dijat ta gaza gane na menene.

Yau Monday misalin biyar na yamma.

Dr Rayyern Mai-nasara ne dake zaune a yar barandarsa balcony dake sama can jikin Bedroom ɗin sa.

Sanye yake da wasu tattausan riga da wondon iya guiwa rigar kuma irin mara hannun nance.

System ɗinshi ne bisa stoll ɗin dake gabansa sai plate da chocolate sai Bootle water a gefenshi.

Sosai ya dugufa kan aikin da yakeyi.

A hankali ya ɗago kansa cikin tarin gajiya ya juyo ya kalli farfajiyar gidan nasu can bakin gate.

Wani irin juyowa yaye tare da tashi tsaye da masifar fargaba ya zubawa fuskar Barr….!

Back to top button