Halysaah Page 160 By Khaleesat Haydar
HALYSAAH PAGE 160…Khaleesat na zaune kusa da Ajay tana kallonsa har suka gama magana da Ammi sannan ya mika mata wayar, Ta amsa ta ƙara yi ma Ammi ta’aziyya daga haka suka yi sallama, Khaleesat bata mayar masa da wayar ba, shi dai kallonta kawai yake ganin ta shiga contact dinsa, cikin few seconds ta rubuto sunan da yayi saving numberta da shi don yana nan a ranta sannan ta nuna masa tace “What’s the meaning of this?” Bai san sanda yayi murmushi ba, yace “Kamar ya?” Ta wani kallesa tace “Meye wannan ka rubuta?” Rungumota yayi har sannan yana murmushi ya lumshe idonsa yace “Me kika ga an rubuta?” Tace “Kai zan tambaya ai” Ya kai bakinsa kunnenta murya can kasa yace “Slushie” Tace “To meye shi din?” Yace “Baki san Slushie ba?” Tace “Wanda na sani wani frozen drink ne….” a hankali yace “That was how I froze ur love in my heart for many months Milady, you are my Slushie” Khaleesat ta ɗaga manyan idanuwanta ta kallesa, tayi murmushi tace “Since when did u save it that way?” Cikin sanyin murya yace “Few months after you became my wife” shiru tayi bata sake cewa komai ba, ya bude wayarsa ya shiga wani private folder ya mika mata wayar, amsa tayi taga hotuna ne a wajen, Khaleesat ta dinga kallon wani hoton ta tana tsaye kitchen a sabon apartment dinta kamar girki take yi, tana sanye da doguwar riga mara nauyi, and she was backing the camera kuma hoton ya fito ras, ta daga kai ta kallesa da mamaki tace “How?” Yayi shiru at first yana ta kallonta, can yayi kasa da murya yace “You were cooking that day” Tace “Shi ne ka daukeni hoto?” Yayi murmushi yace “Yea, na je bakin kofar kitchen din baki sani ba, and I snapped you” Tayi murmushi tace “May be that is because of the aroma of the food, if not ai kana zuwa waje nake sani saboda kamshin turaren ka” shafa gashinta yayi shi ma yana murmushi ya tafi hoton gaba, Khaleesat ta zaro ido tana kallonsa wondering how he snapped the picture cause she was looking at the camera, tun bata ce komai ba ya dora fingers dinsa biyu a lips dinta alamar kar ma tace komai, haka ya dinga shiga pictures dinta wanda duk unaware yake mata su, gasu very clear, kuma duk yawanci a apartment dinta ne sauran kuma can gidansu dake Maryland, tunani ta dinga yi sau da nawa sau da nawa ma suke haduwa da shi har ya samu yi mata wannan pictures din masu uban yawa a wayarsa, wasu tana kitchen, wani parlor, wani stairs, Kai har da wani tana compound din gidansu kamar driver take jira, a dakinta ne kawai bata ga ya mata hoto ba which was because babu ta yanda za su hadu a daki tunda baya shigar mata dakin, Khaleesat ta sauke boyayyen ajiyar zuciya bayan ya gama nuna mata duk hotunan ta, ta kwantar da kanta jikinsa ta lumshe ido a hankali tace “But, let me ask you….” Ya daura fuskarsa a gashinta murya can kasa yace “I am all ears Milady” Tace “Tell me, how did you feel when i was in a relationship with ur brother and almost married to him” Ajay yayi shiru kamar bazai ce komai ba, har sai da ta dago kanta, lumshe ido yayi yace “I don’t know what to say Jeeddah, i feel i don’t even want to talk about it, why not forget about the question My queen” Ta girgiza masa kai tace “No plss, tell me” Ya bude idonsa a hankali yace “I won’t lie to you, at a point I gave up totally and nursed my heart…. Sai nake ganin kamar sharrin shaidan ne ta yaya zan ji ina ci gaba da sonki bayan ga Jawwad, but Jawwad bai nuna yana son ki da wuri ba, don sanda ku ke old apartment dinki I was like ta yaya zai yi betraying Hadiyah bayan ya saka mata rai sannan ya zo yana kula wata, and he swore babu abinda ke tsakaninku kawai Housemate dinsa ce ke, bai taɓa saninki from anywhere ba sai a wannan apartment din, and he is just being nyc to you, no strings attached after that, and I believed him don nasan bazai min karya ba, may be wannan ne yasa har zuciyata ta yaudareni na fara sonki, don da tun asali nasan akwai wani abu tsakaninku da Jawwad my heart will never start loving you, shi yasa ma har na nuna he is betraying Hadiyah don inji me zai ce game dake, sai da zuciyata ta kamu da sonki sannan ya nuna yana sonki shi ma, before then da kansa yake gaya min how nice and lovely you are na dinga ignoring dinsa, he even gisted me about ur Ex and how he is maltreating you, like he is trying to create a bond between us amma naki bada fuskan hakan don bana son ya gano ni da wuri, akwai sanda yayi min text mu hadu a eatry ashe tare da ke zai zo, he want me to see you….” Khaleesat dai kallonsa kawai take babu ko kiftawa, Ajay yace “Still at that I tried my best to ignore what i am feeling about you in my heart, don ni ban gane so bane at first, I was confuse, har sai sanda kika zauna dakina na few days and u left ur ribbon, I do look at that ribbon every morning at the front of my mirror before I begin my day….” Matse ta yayi a hankali yace “Shi ne kika dauke ribbon din ko?” Ta zaro ido tana dariya tace “To ba nawa bane? kawai ganinsa nayi na dauka ai” Ya lumshe ido yana jin wani sabon sonta na shiga ransa cikin sanyin murya “Jay queried me for that ribbon, but i have no choice than to pretend i know nothing about it, and you know what Milady?” Girgiza masa kai tayi tana kallonsa, cikin sanyin murya yace “Till the end I ignore my feelings for you Jeeddah, ban taɓa nunawa ba saboda Jay ya riga ni nuna sonki, and I supported Jay back to back wajen neman auren ki….” Shiru yayi for almost a minute Khaleesat ta daga kai ta kallesa a hankali tace “Ina jin ka” Murmushi yayi yace “Za mu ci gaba wani lokaci, for now, let’s go to bed” Yana fadin haka ya dauketa sai saman gado. Khaleesat and Ajay’s 8-days stay in Zanzibar will forever be a memorable one to them, don soyayya me sanyi da sanyaya zuciya babu wanda basu gwada ma juna ba kamar zasu hadiye juna, wani irin closeness ne ya shiga tsakaninsu a yan kwanakin nan, they became so obsessed with each other, komai tare suke yi, they were always clung to each other ko cikin dare ma suna makale da juna suke bacci, ranan da za su bar Zanzibar kuwa tana zaune da sassafe tana kallonsa yana rufe mata box dinta bayan ya gama shirya mata kayanta don suna isa Tanzania za su yi boarding flight zuwa Abuja Nigeria duk a ranan, ya mike yana kallonta ganin yanayinta yace “Are you okay?” Ta sauke idonta a hankali tace “I am surly going to miss here” Ya ɗan yi murmushi ya karasa ya zauna kusa da ita yana kallonta yace “Ana kan processing maki Maldives visa din ki, can za mu je for our next trip in sha Allah my queen….” Ta ɗan yi murmushi a hankali tace “Da gaske?” Yace “Sure in sha Allah, in few months time” Mikewa yayi ya dagota yace “We have a flight to catch by 9 wife….” Ta dau handbag dinta a sanyaye, a ranta tana ji har ta fara kewan Zanzibar and the beautiful things it gat, she wish they will be there forever, the peace of mind in Zanzibar was top-notch, lokaci daya jikinta yayi sanyi sosai, mood dinta ya canza bayan da ta tuna wannan Emirate din nasu fa za su koma yanxu, hannunsa ta kamo cikin sanyin murya tace “We still have time Mi Vida, please Ina son in maka wata magana….” Ya kalleta yace “Alright My Lady” Zaunawa yayi kan kujera ta zauna kusa da shi tana kallonsa kamar yanda shi ma yake kallonta babu ko kiftawa, jawota yayi jikinsa murya can kasa yace “Maganar me za ki min wife? Kina son wani abu ne?” Ta sauke idonta a hankali tace “Don Allah kar mu koma gidan Sarki wallahi bana son zama gidan, pls we should stay far away from the Emir’s palace, do this for me my prince” Ajay yayi shiru yana kallonta yana jin ina ma hakan zai zama possible don bata kai sa rashin son zaman masarautar nan ba, ta daga idonta jin yayi shiru, ya kamo hannunta calmly yace “Nima bana son zaman gidan Jeeddah but i have no choice because of my father, Mai martaba bai son mu yi nisa da Emirate din, but idan mun koma yanxu i will try speaking to him ko zan yi convincing dinsa” Ta marairaice masa tace “Plss do….” ya gyada mata kai yace “I will in sha Allah” Bayan sun fita daga Le Mersenne Beach resort Khaleesat ta juya ta kalli resort din for the last time, she will surely miss all their beautiful moment that started here, she will never forget all that happened here, cause it is the best thing that have happened to her so far, har suka isa airport bata sani ba don tayi nisa tunanin da take duk da kanta na kwance ne saman shoulder dinsa suna zaune kamar zata shiga jikinsa a cikin motar, damuwarta yanxu bata san kuma what next za su je Emirate din nan su tarar ba, a haka suka shiga cikin Airport din yana rike da hannunta. Bayan magrib Ajay yayi parking dai dai kofar gidansu Khaleesat, basu jima da sauka Kano ba ya karbi mota wajen driver ya kawota gida ta gaisa da su Umma, sosai Khaleesat ta ji dadin kawota gida da yayi don tana son amsan maganin nan wajen Nenne cause har suka baro Zanzibar bai yi komai da ita ba tunda yaga da gaske bazata iya dauka ba, amma kullum sai ta samar masa nutsuwa ta hanyoyi daban daban, Khaleesat na kallonsa a hankali tace “Minti nawa zan yi a ciki?” Ya ɗan yi murmushi ya jinginar da kansa jikin kujeran motar yace “You can spend the night here Milady, gobe da rana sai mu tafi Bauchi, Ko kina son ki kwana biyu a nan kafin mu koma Bauchin?” Khaleesat ta girgiza kai tace “A’a, yanda kace haka za ayi” Yace “Alright Milady ki shiga, bari in je masallaci inyi sallah tunda nayi alwala….” Khaleesat ta gyada masa kai sannan ta bude motar ta sauka, ya bi ta da kallo har ta shiga cikin gidansu, da sallama Khaleesat ta shiga parlonsu, nan ta tarar da su Mama Shatu da Mama Zubaida da wata makociyarsu ana kallo a parlon ga yara zazzaune kan carpet, yaran suka mike da gudu suna mata Oyoyo, duk ta rungumesu sannan ta zauna kan kujera ta gaida su Mama Shatu dake ta kallonta da makociyarsu, daga haka ta mike ta karasa dakin Ummanta, tunda ta shigo Umma da Aunty Farida ke kallonta, tana murmushi ta karasa har inda suke ta zauna kasa ta rufe fuskarta a kafar Umma tace “Ummana” sai kuma ta dago ta kalli Aunty Farida har sannan tana murmushi tace “Aunty” Mamaki yasa Umma sai kallonta take, wai Khaleesat ce yau ta shigo masu a nutse ba a guje ba, Aunty Farida ita ma mamaki ne ya cikata, Umma tace “Ikon Allah, daga ina haka Khaleesat?” Khaleesat na murmushi tace “Yau muka dawo Umma” Gaishesu tayi, duk suka amsa, Aunty Farida tace “Ke da shi ne?” Khaleesat ta gyada kai tace “Ya shiga masallaci ne, Umma ina su Islam?” Umma tace “Suna dakin Nenne” Khaleesat ta mike tace “Bari in je in gaisheta” Suka Bi ta da kallo har ta fita daga dakin, Umma ta kalli Aunty Farida tace “Ikon Allah”





