Halysaah Page 213 By Khaleesat Haydar
HALYSAAH PAGE 213…Khaleesat ta juya ta wani kalli Ajay jin abinda yace, mikewa yayi ba tare da ya kalli inda take ba, yana kallon Nenne yace “Sai anjima Kaka” Nenne tace “To zaka jira ta a waje kenan ko?” Yace “Eh zan jira a waje” Daga haka ya juya ya fita daga parlon, Nenne ta kalli Khaleesat ganin gyara kwanciyarta ma tayi tace “Ba gyara kwanciya za kiyi ba baiwar Allah, tashi za kiyi ki tafi ki shirya kar ki ɓata masa lokaci yana jiran ki a kofar gida” Khaleesat ta hade rai tace “To ai naga ba sau goma ake zuwa asibiti ba Nenne, ko ba tare da ke muka je asibiti ba har aka bani gado, to wani asibiti kuma za aje bayan ga magunguna sun bani ko gama sha ban yi ba, ni babu inda zan je gaskiya” Nenne ta saki baki tana kallonta a tsorace, kujera ta nema ta zauna cikin kidimewa tace “Innalillahi wa Inna ilaihi raji’una, na shiga uku jama’a, to ko dai ƙwaƙwalwarki ya taɓu ne Khaleesat? Shi mijin da kika dinga mana hauka akan sa shekaru biyu da suka wuce kike walakantawa haka kamar wani yaron gidan ki? Na shiga uku na lalace zargina ya tabbata” Khaleesat taki ce ma Nenne komai, Umma ce ta shigo parlon da sallama, Nenne ta mike da sauri ta daga hannu biyu sama tace “Gwara da Allah Ubangiji ya dawo dake gidan nan Zahra’u, yau gidan ba lafiya, kin hadu da Yarima a kofar gida ai?” Umma da sai da gabanta ya fadi tace “Eh mun hadu har mun gaisa, lafiya Nenne?” Nenne tace “A’a babu lafiya wallahi, Yarima dai ya fi awa daya a gidan nan zancen da nake maki yanxu haka, ya zo ne zai kai gantalalliyar yarinyar can asibiti a duba lafiyar ɗan cikinta ta ki fita tace babu inda zata je, kuma babu uban da ya isa yasa taje, banda bakaken maganganu babu abinda take jefa min tun daxu a parlon nan, ta dai ce babu wanda ya isa ya sa ta bi sa koma wanene” Umma ta juya tana kallon Khaleesat da mamaki, mikewa zaune Khaleesat tayi ta marairaice tana kallon Nenne, Nenne ta nemi waje ta zauna ta dafe kanta tace “Innalillahi wa Inna ilaihi raji’un, Allahumma ajirni fi musibati, Wallahi a yanda naga tana magana kamar ko son ganin mijin bata yi, anya bamu shiga uku ba Zahra’u, wannan abu gaskiya ba lafiya bane, akwai wani abu karkashin kasa, ita da ke son mijinta kamar ta mutu rana daya mu ga wannan abu, yanda kika san makiyin ta ne ya zo fa, ko gaishesa bata yi ba wallahi” Khaleesat ta mike ganin irin kallon da Umma ke yi mata ɓacin rai ƙarara a fuskarta, cikin fushi Umma tace “Zo ki fita kar in yi mummunan saɓa maki, dama ke mahaukaciya ce ban sani ba” Nenne tace “A’a mahaukaciya ce wallahi, babu wani dama, kawai kirata mahaukaciyarta kai tsaye, ta dauko hijabinta kawai ta rufa mana asiri ta fitar mana daga gida lami lafiya” Lokaci daya hawaye suka ciko idon Khaleesat ta juya ta tafi daki, Nenne tace “Mu dai kar ma ta dawo mana gidan nan tunda ta zama abar tsoro, daga asibitin ya tafi duk inda zai tafi da ita ba ruwan mu gaskiya, kar ma yayi zaton mu muka zugeta tunda dai lafiya suka sauka garin nan, sai yanxu ma na gane rashin walwalan da yaron yake yi duk kwanan nan yana da alaka da ita, kullum in ya zo fa sai dai in ce tana bacci duk zatona baccin Allah da annabi take, ashe ba haka ba Zahra’u, kinga ai sai ya fara min kallon tsohuwar banza, gashi sai tayi ta tadi da Abdul a gabansa, anya ba Abdul din bane yayi mata asiri kuwa Zahra’u” Umma dai ta kasa cewa komai ta nemi waje ta zauna don gaba daya jikinta yayi sanyi, duk bata san wannan abun ba sai yanxu da Nenne ke gaya mata, bayan wasu mintuna Khaleesat ta fito daga daki tana sanye da hijab har kasa, fuskarta a daure kamar zata yi kuka, Nenne ta dinga yi mata wani shegen kallo, Umma kawai Khaleesat tayi ma sallama ta nufi kofa, Umma ko amsa ta bata yi ba ta bi ta da harara har ta fita daga parlon, Nenne ta mike tace “Ni zuwa ma zan yi in samesa in ce kar ya dawo da ita gidan nan don tafiya za mu yi gobe da asuba za mu je ziyara kauye” Umma tayi stopping din Nenne daga fita daga parlon tace kar ta ce masa haka…. Khaleesat na isa kofar gida ta kara murtuke fuska, tana tafiya kamar warce bata son tafiya ta nufi motar dake parke kofar gidan, back seat ta bude ta shiga ta kulle ba tare da ta kallesa ba, ta kauda kai tana kallon waje fuskar nan nata a daure, shi ma bai kalleta ba ya tada motar ya bar unguwan. Har suka isa wani private hospital me tsada sosai Ajay bai ce mata komai ba a motar ita ma bata kalli inda yake ba sai cika take tana batsewa, yayi parking a compound din hospital din ya kashe motarsa ya sauka, ƙin sauka Khaleesat tayi daga cikin motar, shi dai yayi wucewarsa zuwa cikin hospital din, ta bi sa da wani kallo, bayan kusan minti goma wata nurse ta fito daga cikin asibitin ta nufo motar Ajay, Khaleesat dai kallon nurse din take har ta karaso gun motar ta kwankwasa back seat tayi sallama, bayan Khaleesat ta bude motar suka gaisa da Nurse din, sannan nurse din tace “Za mu shiga ciki ne Hajiya” Saukowa Khaleesat tayi daga cikin motar tana biye da nurse din suka shiga cikin asibitin, Ajay na zaune a reception Khaleesat suka shigo patient services din da nurse din da taje ta kirata, zaunawa tayi very far away from him a reception din, ba wanda zai san tare suke ma, after some minutes wata mata in her late 30s ta shigo reception din da alamar likita ce duba da shigar da tayi, kyakkyawa ce fara kamar Half cast, tana ganin Ajay ta zaro ido tana rufe bakinta da hannu ta nufesa da sauri tace “Omg, why didn’t you call me Ajay, tun yaushe ka shigo?” Ajay ya ɗan yi murmushi calmly yace “An hour ago, Dr Mai Jiddah, kin shanya ni har na bushe” Ta kara zaro ido tace “Subhanallah, Allah ya huci zuciyar Yallabai, wallahi mun shiga wani aiki ne fitowa ta kenan, ka kikkira wayata ba response ko? Ko da yake nasan Nurses din za su gaya maka ina theatre….” Still smiling yace “Just kidding, ban dade da shigowa ba, i called once baki yi picking ba” Tayi dariya tace “You will never change Ajay, where is Jawwad? Shi kasan sarkin basarwa ne a chatting, few days ago na yi replying status dinsa har yau bai min reply ba….” Ajay yace “Yana Bauchi” Ta kai hannu saman gashin kansa tana birkitawa tace “You look very much healthy akan sanda kake asibiti a Maryland few months ago, har wani kyau ka kara fa….” Ajay dai ya kauda kansa da sauri from her touch, yana murmushi yaki ce mata komai, Khaleesat sai kallonta take babu ko kiftawa, dai dai nan wani likita ya shigo reception din tace “Dr Salman ga coursemate dina as at then, ɗan uwan Jawwad, ai kasan Jawwad din ya taɓa zuwa nan” Dr Salman yace “Ohk yan Bauchi Emirate ko?” Tayi dariya tace “Exactly baka manta ba, we did our masters together in John Hopkins, muka sake hadewa yin PhD, field din mu daya da Junaid, shi kuma Jawwad kamar Cardiology ne bangarensa” Dr Salman yace “Maa sha Allah, amma bai taɓa zuwa asibitin nan ba sai yau” Dr Jiddah tace “A’a bai taɓa zuwa ba Jawwad ne ya zo, kasan ta dalilin Jawwad fa na san Junaid, a lkcin ina masa kallon me shegen girman kan bala’i, baya son magana da mutane yayi ta ma mutum wani gani gani, sai bayan da muka saɓa na gane ashe ya ma fi Jawwad kirki da sakewa sosai ba kadan ba, kawai dai in bai saɓa da kai bane zaka masa kallon mara kirki” Dr Salman yayi dariya yace “Dama it is bad to judge a book by it’s cover alone” Dr Jiddah tace “Amma fa tsoron ‘yan mata yake sanda muna America, kasan tsohon saurayina ne amma ni kadai ce cikin relationship din a lokacin, ni nake ta soyayyan ina bata lokaci ma” Ajay yayi dariyar da bai yi niyya ba, shi kansa Dr Salman sai da yayi dariya da few Nurses dake reception din wanda dukkan su kallon Ajay suke alamar dai ya burgesu, kana kallonsa zaka san ruwa biyu ne shi, gashin kansa kadai ya nuna hakan, Khaleesat dai ta rasa me yasa ta kasa tashi ta fita daga reception din kamar warce aka yi glueing kan kujeran duk da yanda taji zuciyarta yayi mata nauyi sosai, Dr Jiddah na dariya tace “Har ce masa nayi zan biya masa sadaki mu yi aure, kawai naga mutumi ya fara avoiding dina duk idan muka hadu sai ya sha kunu, kuma da wasa nayi masa don Daddy ma bazai bari in yi aure a lokacin ban karasa karatu ba” Ajay ya ɗaga kai ya kalleta yace “To yanxu ki bada sadakin ayi auren” Dr Salman yace “Ai ko ni sai in bada in dai a shirye kake, dama tun bayan rasuwan mijinta bata kula maza” Khaleesat bata san sanda ta mike a inda take zaune ba ta fita daga reception din, babu wanda yayi noticing ta fita, Dr Jiddah tayi er dariya tana kallon Dr Salman tace “A’a da matarsa yanxu gaskiya, kuma amarya ce, zan jira har sai ta mori amarcin ta tukunna sai ka bada sadakin” Ajay yace “Ashe ba da gaske kike ba” Tana dariya tace “Seriously in dai ba yaudarata zaka sake yi ba” Sosai Dr Salman ke dariya yana kallon Ajay yace “To kar dai a yaudari er uwata for the second time” Ajay na murmushi yace “Baka da matsala” Dr Jiddah tace “To kace zaka kawo amarya a dubata kuma naga kai kadai ka zo” Sai a sannan Ajay ya kalli direction din da ya ga Khaleesat ta zauna amma sai yaga bata wajen, Yace “Tare mu ke….” Dr Jiddah ta zaro ido tana bin reception din da kallo tayi kasa da murya tace “Na shiga uku Ajay, shine ka bari nake ta zuba kar ka sa ta kullace ni, where is she?” Dr Salman da shi ma ya zaro ido ya juya ya bar wajen within few seconds ya wuce sama, Ajay na murmushi yace “Ai bata da matsala ita, i think she is outside, na kawota ne kawai taga hospital din, zuwa gobe driver zai dawo da ita sai ki dubata, nan zata dinga zuwa Antenatal idan lokacin yayi in sha Allah” Dr Jiddah tace “Ohk dama a Kano ku ke, na zata ai Bauchi ku ke zaune” Ajay ya girgiza kai yace “Tana gidan su ne yanxu, but Bauchi mu ke” Dr Jiddah tace “Amma dai ba har ta haihu ba dai ko?” Ajay yace “If she chooses that it’s fine” Dr Jiddah tace “A’a gaskiya an dena haka Junaid, sai kace ba wayayyu ba meye zaka bar matar ka a gidansu saboda tana da ciki bayan kai din likita ne kuma na mata for that matter, ko laulayi me tsanani take gaskiya babu amfanin ta zauna gidansu ai an bar haka, you are capable of taking care of ur wife” Ajay yace “She prefer that Dr, so i am not stopping her from staying home, she can stay har zuwa sanda zata haihu if she wish…” Dr Jiddah tace “To yanxu dai mu je in gaisa da ita tunda kace tana mota” Ajay yace “Ke da za a kawo maki ita gobe, kawai ki bari goben sai ku hadu in sha Allah” Tace “To Allah ya kai mu Junaid, Daddy bai shigo hospital yau ba da kun gaisa da shi” Ajay ya ɗan yi murmushi yace “Wani lokacin idan yana nan sai mu gaisa” Tace “To babu damuwa in sha Allah” Sallama yayi mata tace “Ba daman rakiya kar matar ka tayi wani tunani in ta gan mu a jere, a gaida gida kawai” Ajay yayi dariya yace “Ke matsoraciya ce dama” Tace “Eh dai aje a haka sai anjima” Hannu ya ɗaga ma Nurses din dake kallonsa sannan ya juya ya fita daga reception din, yasan ba lallai ya fita ya tarar da Khaleesat ba shi yasa yace gobe za a dawo da ita asibitin, all the way from Benue ma ta kamo hanyar Kano balle yanxu da a cikin Kanon take, ai kam bai yi mamakin rashin ganinta ba alamar dai tayi tafiyarta, ya shiga motarsa kawail ya fita daga hospital din. Daga asibitin direct Khaleesat gidan Safiyyah ta nufa, sai da ta isa gidan ta shiga ta amso kudi wajen Safiyyah ta ba mai adaidaita sahu, tun da Safiyyah ta ganta ta san da matsala, bayan ta kai ma ɗan sahu kudinsa ta dawo parlor Safiyyah na kallonta tace “Gaskiya kina downgrading darajar da Allah ya maki Khaleesat, kina matar ɗan sarki amma ayi ta ganin ki a adaidaita sahu kina yawo” Khaleesat tayi banza da ita ta nemi waje ta zauna, mikewa Safiyyah tayi ta koma kusa da ita ta zauna tace “To me ya faru kuma?” Khaleesat ta fashe da kukan da take dannewa tace “Na gama auren Junaid, kuma nayi da na sanin duk abubuwan da nayi a kansa” Kuka take sosai, Safiyyah ta dinga mata wani kallo, can ta kyabe baki don sarai tasan definitely ba wani abu bane serious amma ta maida shi babba, Safiyyah tace “To me Junaid din yayi maki?” Cikin kuka Khaleesat tace “Walakanta ni kawai yake yi yanxu, ba shi da aiki sai walakanta ni, bayan duk walakancin da yayi min a Benue bai ishesa ba, shi ne yanxu ya daukeni ya kai ni wajen tsohuwar budurwarsa wata er duniya er iska, kilan ma ta girmesa, har tana cewa zata bada sadaki a daura masu aure” Safiyyah ta saki baki tace “Kai Khaleesat, kuma a gaban ki?” Khaleesat ta kara rushewa da kukan takaici tana jin kamar zuciyarta zai fashe tace “Wallahi a gabana Sophie, har fa tana shafa masa kansa” Safiyyah ta kasa yarda da wannan magana, sai take ganin kamar Khaleesat kishi yasa take exaggerating lamarin, ita abun ma kusan dariya ya bata, ta dake tace “Shafa masa kai fa kika ce Khaleesat, kuma a gaban ki? Ko dai aski take yi ne ku ka je shagonta?” Khaleesat ta jefa ma Safiyyah wani kallo cike da takaici tace “Ko ba aski ba, to asibiti muka je muka hadu da ita, wallahi shafa masa kai ta dinga yi” Safiyyah ta bude baki tace “Wai kuma a gabanki? Tasan ke matarsa ce kuwa?” A fusace Khaleesat tace “To ina ruwana da ko ta sani ko bata sani ba? Wallahi a gabana ta dinga shafa masa gashi tana narke masa Kinsan dai bazan zauna in shirya karya ba” Safiyyah tayi shiru still trying to process that, Khaleesat ta kara fashewa da kuka tana jin zuciyarta na mata wani zafi kamar an soka mata arrow gashi abun sai dawo mata yake yi kamar a lokacin ya faru, cikin rawan murya tace “Wallahi bazan iya zama da shi ba, nayi da na sanin aurensa ma ni, yana kallon tana tattabasa bai hanata ba sai murmushi yake” Kwanciya tayi jikin Safiyyah tana kuka kamar warce ake kara tunzurawa, Safiyyah ta sauke ajiyar zuciya tace “Allah me iko, to wai me ku ke je yi a asibitin har ku ka hadu da ita?” Khaleesat taki cewa komai tana kuka sosai, Safiyyah tace “Ni dai ki dena wannan kukan don Allah, shi ma Ajay bai kyauta ba gaskiya, me yasa bai taka mata burki ba” Khaleesat ta ɗago da sauri tace “Wallahi biyeta yayi, har yana cewa ta bada sadaki fa a daura masu aure, har da wani tsinannen baƙin likita a tsaye yana cewa shi zai bada sadakin, duk Allah ya isa tsakanina da su, shi kuma zai ga abinda zai faru, ta fa girmesa matar duk tayi bleaching ta kwaile fuska, uban me zai yi da ita ma” Safiyyah ta danne dariyarta bata dai ce komai ba, har yanxu ta kasa processing labarin Khaleesat, Khaleesat ta goge idonta tace “Ina wayar ki?” Safiyyah tace “Me za ki yi da waya?” Khaleesat bata tanka ta ba ta dau wayar ta wuce dakin baƙi, Safiyyah tayi murmushi don babu abinda ta gani a idon kawar tata sai tsantsan baƙin kishi, Khaleesat na shiga daki ta zauna tana duba number Jay a wayar Safiyyah, dialing number tayi har ya katse bai daga ba, ta kara kira bai daga ba, sai da ta kira a na uku sannan yayi picking, da kyar tace “Ya Jawwad” Jay dake driving a lokacin sun je hospital da Hadiyah suna dawowa yace “Halysaah” Hadiyah dake gaban motar ta juya ta kallesa, sosai Khaleesat ta sakar masa kuka kamar er yarinya, Jay ya nemi waje yayi parking yace “Me kuma ya faru Halysaah?” Cikin kuka ta fara koro masa duk bayanin da tayi ma Safiyyah, jinginar da kansa yayi da kujeran motar yana sauraronta, wato still da ya baro masu Kanon ma bai tsira ba, har ya gaji da settling case shi kam, Hadiyah dai murmushi kawai take don duk tana jin Khaleesat, Jay ya sauke ajiyar zuciya yace “Listen to me Halysaah, kina ina yanxu?” Cikin kuka tace “Ni bazan fadi inda nake ba wallahi” Yace “Kina gidan Safiyyah tunda da numberta kika kirani ai” Ta wani turo baki don ta ma mance da wayar Safiyyah ta kirasa, yace “Kinga ina hanya ne yanxu, idan na koma gida zan kira ki mu yi magana, ki kwantar da hankalin ki kinji” Hadiyah dake kallon Jay bayan ya ajiye wayar tace “Cikin ne fa yasa take abubuwan nan” Jay yace “Ba wani ciki, dama tun asali rigima halinta ne sai ya hadu da ciki” Hadiyah tayi dariya tace “Ni tausayi ma Ya Junaid ke bani wallahi” Jay yayi dariya yace “Ai ko kiranta bazan kara yi ba, su je can su yi settling kansu da kansu, don in ma nayi mata magana ba ji take ba ai”



