Sama da mutane Miliyan Uku (3) ne aka sace wa NIN dinsu, bayan da wani mai kitsen da aka fi sani da Sam ya kutsa NIMC.
Dan kitsen ya yi ikirarin cewa ya samu damar shiga shafin na hukumar gwamnatin Nigeriya, kuma yana iya ci gaba da yin duk abin da ya ga dama tare da wasu muhimman bayanai dake hannunsa.
Kutsen da aka yi wa hukumar NIMC ba wai kawai ya fallasa raunin tsaron yanar gizo na Najeriya ba ne, har ma ya nuna irin haɗari da mazauna ƙasar ke ciki a halin yanzu.
Harin da aka kai wa internet ya zo ne ƙasa da watanni biyu da hukumar sadarwa ta Nijeriya a watan Nuwamba 2021 ta yi gargaɗin cewar wata ƙungiyar kutse ta Iran na shirin leƙen asiri ta internet a faɗin Afrika.
A sanarwar da hukumar ta fitar ta kuma bayyana cewar masu satar bayanan na kai hare-haren a kamfanonin sadarwa, da masu samar da internet, ma’aikatun harkokin wajen Nijeriya da kuma wasu ƙasashen Afirka.
KARANTA WASU LABARAN
✓ Yadda za ku kula da fatarku lokacin sanyin hunturu.
✓ Scholarship Ƙarƙashin Ma’aikatar Ilimi Ta Ƙasa Da Kuma Hukumar Samar Da Lamunin Karatu Ta Ƙasa.
✓ Gwamnatin Tarayya zata dauki karin Matasa 400,000 aikin N-Power
✓ Yan Kannywood Sun fara yin Blue Fim
Har ila yau, lamarin ya zo ne watanni bayan da gwamnatin Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a lokacin da ta umarci ‘yan Najeriya da su yi rijistar lambar dan ƙasa, hukumar ta yi ikirarin cewa zata dakatar da duk wani layi da bashi da rijistar NIN.
Da yake jawabi a yayin kaddamar da tsarin inganta harkokin yan ƙasa a ɓangaren sadarwa na Najeriya da kuma sake fasalin manufofin ƙasa na yin rijistar katin a watan Mayun 2021, shugaba Buhari ya ce, “NIN zai rufe ɗaya daga cikin raunin da ke tattare da tsarin tsaro. Za mu iya gano da sanin halin da yan Nijeriya suke cikin sauƙi. Sannan zamu dinga kama yan damfara cikin sauƙin.”
Da yake tabbatar wa da ‘yan Najeriya muhimmancin sabon tsarin, ministan sadarwa da tattalin arziki na Digital, Isa Pantami, a watan Yunin 2021, yayi ikirarin cewa al’amuran ta’addanci irinsu ‘yan fashi da garkuwa da mutane sun ragu matuƙa a cikin ƙasar sakamakon haka dagewar da gwamnati ta yi mutane a Najeriya su yi rijistar NIN.
Pantami ya ci gaba da cewa, ingantaccen tsarin tattara bayanai zai kare ‘yan Najeriya fiye da ko wanne lokaci.
Sai dai duk da wannan tabbacin, sabon harin nan ya fallasa gazawar gwamnatin Shugaban ƙasa Buhari wajen kare ‘yan Najeriya daga masu aikata laifuka ta yanar gizo.
Sama da ‘yan Najeriya miliyan 60 ne aka adana bayanan sirrinsu, a cewar hukumar NIMC.