Zamantakewar Aure

Hanyoyi Uku Da Namiji Zai Gamsar da Mace Har Taji Babu Kamar sa

Mace ba koyaushe take iya bayyana abin da take so ba, amma ko da ta yi, ba lallai ne ta iya fada maka ba.

Gina dangantaka mai karfi da mace yana da mahimmanci idan har ka gane abinda mace ke son a yi mata. Yayin da dangantakarku ke bunkasa, za ka kara fahimtar ta kuma ka kara sanin yadda zaka gamsar da ita.

Karanta>>> Maganin Kurajen Gaba Da Kaikayin Gaba Na Mata

Duk mace na son a nuna mata kauna, ana kulawa da ita, kuma ana daraja ta yadda ya dace. Suna bukatar mafi girman matakin kulawa da nuna soyayya. Amma, kalilan ne daga cikin maza suka fahimci wadannan abubuwan dake gamsar da mace.

Karanta>>>  Ingantaccen Matsi Da Bashi Da Illa, Kuma Da Kanki Zaki Hadashi.

Mace ba koyaushe take iya bayyana abin da take so ba, amma ko da ta yi, ba lallai ne ta iya fada maka ba. Sakamakon haka, ana daukar su a matsayin halittu masu rikitarwa.

Karanta>>> Tsumin Matan Aure Na Musamman Domin Inganta Zaman Aure

Hanyoyi Uku Da Namiji Zai Gamsar da Mace Har Taji Babu Kamar sa 

A wannan rubutun, zan bayyana hanyoyi uku da suka fi burge mace.

1. Kada ka rika kushe ta, amma koyaushe ka rika yi mata gyara; Idan kana so mace ta gamsu da kai, dole ne ka iya mu’amala da ita cikin kulawa da sauki. Idan ba za ka iya zama mai hakuri da nuna kauna da ita ba, zai yi maka wuya ka mallake zuciyarta. Sanin abinda mace ke so da wanda bata so zai iya taimakawa namji yasan yadda zai yi rayuwa da ita cikin aminci da kaunar juna.

Karanta>>> Amfanin Kubewa Musamman Ga Ma’aurata

Saboda haka, duk lokacin da kake jin bukatar ka horar da matarka, yi kokarin yin hakan cikin soyayya maimakon hanya da za ta iya cutarwa ko bata mata rai. Idan ka gyara ta cikin soyayya, akwai yiwuwar za ta iya karbar shawararka kuma ku duka za ku kasance farin ciki.

Karanta>>> Ina Mata Masu Fama Da Rikecewar Al’ada Ga Magani Da Izinin Allah

2. Bata damar ta yi magana game da yadda take ji a ranta (ma’ana ka bata damar bayyana rayyinta); Ba za ka taba samun nasara a matsayin namiji wajen faranta wa mace rai ba idan ka hana ta damar bayyana ra’ayin ta kanta ba. Idan kai ne kadai ke yanke shawarwari da ba ta umarni, ya kamata ka ba ta sarari ka kuma saurari abin da take cewa. Bari ta yi jawabi a fili.

Idan kana son sanin abin da matarka ke so, dole ne ka ba ta damar ta fada maka. Wannan zai sa ya zama mai sauki a gare ka ka biya bukatunta.

Karanta>>> Tusar Gaba Da Abinda Ke Kawota Yana Da Kyau Ku Karanta Wannan Bayanin

3. Yaba mata; Don faranta wa mace rai, ya kamata ka nuna kaunar ka gare ta da godiya ga kokarinta. A fili, ya kamata ka yi mata kalaman nuna godiya ka kuma yaba mata. Wannan zai sa budurwarka ta fi saukin jin gamsarwa game dakai.

Karanta>>> Amfanin Hulba Guda 21 Ga Lafiyar Jiki Musamman Yan Mata Da Matan Aure.

Back to top button