Hausa novels

Haihuwa Da Hanji Page 22 Hausa Novel

Ga dumbin mamakinta dukkansu biyu kuka suke yi, Abeeha kam ma da sauti yayinda Mammi ke zubar da hawaye, ko kan tayi wani yunkuri Mammi ta miƙe ta iskota ta ɗago ta sai ta sanya ta jikinta ta rungume tana shafa bayanta, wannan dalili! wannan ɗumin jikin shi ya saka Afeefah fashewa da sassanyar kuka mai sauti.Sun fi mintuna goma a haka tana wannan kukan, tuna komai take yi tamkar yanzu ne ya faru ji take duk mace-macen yanzu ne suke dawo mata sabo, taji tana kewar mahaifiyarta da Aunty zee, wannan tausayi da kauna da ta gani daga Mammi sai ya tsaya mata a rai ta ji itama tana ƙaunar matar tamkar mahaifiyarta.Rayyan da tun kan tayi nisa ya lumshe idanunshi bai buɗe ba sai da ya ga kukan na yawa, duk tsikar jikinshi jinshi yake a tashe, ko da ya miƙe zaune sai da ya ji kanshi ya sara ya ɗan runtse idanunshi ya buɗe kan ya ja tsaki ya sauka daga gadon, ya taka ya dafa kafadar Mammi da har lokacin take rike da Afeefah.Mammin gabanta ya faɗi tuna yana ɗakin ta tuna labarin Afeefah sai tayi sauri ta saki Afeefah ta waiga tana kallon yanayinshi, idanunshi ya sauƙe kasa a hankali yace “Mammi please ki bar kukan nan, you are sick already kukan nan bashi da amfani, dole ne sai mutum ya rayu da dangi? Dole ne sai sune kaɗai za su baka farin ciki da kulawa? Na Allah na nan dayawa Mammi…”Yankewa maganan yayi ya ɗago garin kaucewa idanun Mammi sai nashi suka sarƙe cikin nata, sama da seconds huɗu yana kallonta kan kawai ya juya ya bar ɗakin.”Saraki.! Saraki….!!”Bai juyo ba ya fice, ta duƙar da kanta tana ambatar sunan Allah… Chan ta sauƙe numfashi ta waigo ga Afeefah da tunda taji sauƙar muryarshi da yadda yake magana da amo kukanta ya tsaya chakk, haɗa idanun da suka yi ya matuƙar Dakar zuciyarta idanunshi abin tsoro ne a gareta amma a yanzu sai taga ya zama wani iri duk yadda zata fassara ma’anar kallon nashi ta kasa, maganan Mammi ne ya dawo da ita tunaninta.”Lallai Afeefah kin ga rayuwa, haƙiƙa na kaɗu da labarinki abin mamaki kika iya daurewa kika cije kika tsallake wannan jarabawa duk da kananun shekarun ki, Afeefah rayuwar nan duk jarabawa ce kuma ko wani lokaci yana da karshen sa, za mu yi ta shan wahala a duniya amma sakamakon yana hannun Allah kuma ya fi jarabtar wanda ya fi kauna daga cikin bayinsa, Afeefah ina so ki san idan dai har ni, Abeeha, jidda ko Saraki muna raye a wannan duniya kin gama kuka, zan cigaba da rikeki har karshen numfashi na haka zan yi musu umarnin cigaba da kula da ke da baki kariya har nasu karshen numfashin, in shaa Allahu kin gama zubar da hawayen baƙin ciki Afeefah… Sannu! Sannu da juriya”Sabon hawaye ne suka cigaba da silalo mata ta sake rungume Mammi tana fashewa da kuka, Abeeha ta taho ta ɗago ta tana riƙe hannunta “In shaa Allahu ba za mu taɓa kyamatarki ba Afeefah ai duniya ce idan wani ya ƙi ka dole wani ya so ka haka Allah yayi rayuwar, ni na yarda ki ƙirani Addah don ko kowa zai guje ki in shaa Allahu ni ba zan taɓa gudar ki ba”Sossai take kuka, a ranta Adu’a take tana tuna irin kaunar da Aunty zee ta nuna mata a ƙarshe ta tafi ta barta, anya ta zama mai adalci? Anya zamanta a gidan zai haifar da ɗa mai ido? Karshen wahalar kenan ko kuma akwai saura? Duk ta bar wa Allah.Sossai suka rarrasheta ta natsu kan Mammi ta miƙe tayi sashen Rayyan don duk yana cikin ranta tun ɗazu, a kwance ta same shi hallau dai idanunshi a lumshe, kai tsaye ta je ta sa hannu a goshinshi ganin jijiyoyin kanshi raɗa-raɗa a waje, jin hannunta ya sa ya buɗe idanun da suka sake sauyawa ya zuba mata “Saraki ciwon kai ne? Ko za ka je asibiti?”Girgiza kan yayi kaɗan yana yamutsa fuska “Ba sai na je ba Mammi””Saraki in na barka haka dare ba zaka iya bacci ba, ka taimakeni ka je ka ga psychiatrist din ka”Shiru yayi bai ce komai ba. Ta sauƙe numfashi ta fara duba wayanta cikin mintuna kaɗan sai ya ji muryarta tana magana da likitarshi, buɗe ido yayi ya kalleta bata damu ba har suka gama wayan.”Za ta zo, don Allah ka tashi ka saka wani abu a jikinka mu je parlor”Ta faɗa cikin kulawa kaman yadda yake damuwa da ciwo da damuwarta, shi ma bai san yadda zai yi bane, bai san ya zai yi ya hana kwakwalwarshi tsayar da tunanin baya ba, bai san ya zai yi ya cire tsananin nauyi da damuwar da ke kwance a ƙasan ranshi ba, a duk lokacin da ya samu sassauci to fa a tsakanin da yake ganin farin ciki da walwala a fuskar Mamminshin ne saboda baya so yake sakata cikin damuwa amma yaya zai yi? “Zan zo!”Ya faɗa a hankali.Ta juya ta fice da damuwa a fuskarta, bai yi bacci ba a daren jiya dama ya saba da rashin isashen baccin dare, tun tana kwana dashi har taga yayi girman da bai kamata su cigaba da kwana ba amma ko bacci take tana tunanin yadda yake tafiyar da nashi daren, ba’a yi mishi adalci ba amma kuma to ya suka iya ne? Da kyar ya miƙe ya saka armless vest mai fadi da three quater da ya kai mishi gwiwa, a bakin gadon ya zauna yana dafe kai har lokacin fuskarshi jazir babu ɗigon fara’a a kan fuskar tashi, ba’a jima sossai ba sai ga Mammin ta dawo ta kama hannunshi suka fito, a zaune kan kujera ya ga Dr. Ɗin tashi macece babba da a haife zata haife shi, ganin sun haɗa idanu ya sa tayi mishi murmushi ya ɗauke idanu, ajiyar zuciya ta sauke har ya zauna ya kishingida ya ɗaura kafa daya kan daya Mammi ta fita bata ce komai ba.”Malam Rayyan! Barka da warhaka”Ido ya ɗan buɗe ya kalleta kan ya amsa.”Whats happening? Na zaci mun wuce wurin nan duka..! Mafarkin ne?”Shiru yayi chan dai ya gyaɗa kai “Am having a sleepless night for almost a month now””Me ya faru? Are you taking your pills?”Gira kawai ya ɗaga don kan ya mishi nauyin da ba zai iya dagawa ba.Ba don ma ya san darajar likitar ba ba zai kula ta ba, tayi ta janshi da magana dai har ya ɗan sake ta bashi magani cikin kulawa da kwarewa a aiki.”Mammi wants me to get married, tana tsoron ta mutu….” Ya ɗan yi shiru zuciyarshi babu daaɗi sam kan ya cigaba “ba ta so ta bar ni ni kaɗai ba tare da mata ba and i hate the idea… Me yasa take yawan zancen mutuwa? Yana damun zuciyata da kwakwalwata kina tunanin zan rayu bayan bata nan?”Idanu ta zura mishi, Rayyan a cikin patients ɗinta da take gani sama da shekaru talatin yana daga cikin na daban da take jin damuwarshi tamkar ɗan cikinta, tana tsananin tausayinshi gashi kuma Allah sai ya sake aiko mishi wata jarabawar akan wata na rashin lafiyar Mammi da fargabar mutuwar a kowani lokaci, sam bata so Mammin tashi take kawo mishi zancen tunda a ranshi ya riga ya san kowa zai mutu idan ajalin shi ya zo amma kuma ta taya ta duba raunin da yake danne wa a cikin zuciyarshi he was already traumatized, yana fama da insomia for so long ciwon Mammi kuma ya haifar mishi da anxiety tsoro da fargabar barin shi da zata iya yi.Lallaɓa shi tayi tayi har ya ɗan sake, maganin da ta bashi kuma ya taimaka mishi don kafin ta tafi ma yayi bacci a kan kujerar, Mammi ta samu “Don Allah Maman Rayyan ki taimakeni a kan Rayyan, ki daina mishi maganganun da zai ji a ranshi kaman wasiyya ne, kin san matsalar shi kin san da ya ya girma in ba Allah ba babu mai iya kawo Rayyan matakin da yake kai yanzu””Dr. Ya zan yi ne? Ina faɗa mishi hakan ne saboda ya shirya, ya kamata ya shiryawa hakan dole zata kasance amma bana Fatan hakan ya kasance bashi da wani kafaɗar, bana Fatan hakan ya kasance ba shi da inda zai iya bayyana damuwarshi shiyasa nake so yayi auren””Amma kin san matsalar da niyyar auren nan ya jawo a baya, a maimakon ya gyara sai tabargaza da yayi mana har ya zama for months Rayyan baya aiki baya kuma fita ko ina, bakya tsoron abin da ya faru ya sake faruwa?”Shiru Mammi tayi itama duk damuwa a kan fuskanta kan ta ce a hankali “Zan san yadda zan yi likita, na gode sossai da taimakon ki ina fata zai ɗore ko da bana nan”Murmushi kawai tayi ta taso ta dafa kafadar Mammin ta ɗan bubbuga kan ta fice bata iya ta ce komai ba.Hawaye ne ya silalowa Mammin, ita kadai ta san me take ji, ita kaɗai ta san tsoro da fargabar da bawa kan shiga a duk sadda aka ce maka ga wa’adin mutuwarka Dukda bata yarda ba amma hakan ya tsaya mata a rai tun shekaru bakwai baya, Dukda ta wani gefen hakan ya matuƙar bata kusanci da ubangijinta sai dai tsoronta yadda zata tafi ta bar Rayyan, bata jin yaranta matan saboda basu da matsalar komai amma Rayyan fa? Raunin shi sabo zai dawo bata son hakan bata Fatan hakan don haka dole ne a gareshi ya nemi abinda zai tallafeshi a bayanta.****Ta ɓangaren Dr. Sulaiman neman duniya ya saka an yi wa Afeefah sai dai babu ita babu alamunta, police station har uku daban daban ya kai report sai dai babu ko duriyarta.Tun yana ciwon kai a tsatsaye har sai da ya kwanta don da gaske ya matuƙar damuwa, a ƙarshe haƙuri umma tayi ta bashi akan ya fawwalawa Allah ya karɓi auren da aka bashi don Abba ya nuna mishi babu gudu babu ja da baya.A dole daga ita har ƙannenshi suka fara shirye shiryen auren tunda sati biyu kachal ya saura a yanzu.****A ɓangaren saleem ma duk ya ƙare a tsaye saboda damuwa da tunani, a kullum adu’ar shi a kan Afeefah ne Allah ya tallafeta ya hanata faɗawa halaka Allah yayi riƙo da hannayenta ya bata uwar ɗaki na ƙwarai, har yanzu iya gaisuwar ƙannenshi kawai yake amsawa wanda abin ya dame su sossai ya zura musu ido kawai musamman mommy da ke ta shirye-shiryen aure ka’in da na’in ita uwar amarya kuma uwar ango.Sameera na zaune a kan plastic chair a wurin parking lots saleem ya shigo da motar shi ya zo yayi parking ya sauƙa, bai mata magana ba don ta gaisheshi da safe kuma ya amsa har zai wuce tace “Yaya!”Ya juyo ya kalleta duk tayi wani iri da ita “Yaya don Allah kayi hakuri da abubuwan da muka yi maka, wallahi na gane kuskurena tun da jimawa na tuba don Allah””Me kuka yi min Sameera? Ai ni dan uwanku ne ba zaku iya min komai ba ko? Sai bare ne zaku iya yi wa… Babu komai Allah yana gani”Kuka sossai take yi.”Allah ya riga ya nuna min iyaka ta ko a haka na gane kuskurena, Yaya in na tuna abin da muka yi wa Afeefah sai Naji tamkar jayayya muka yi da ubangiji… Za ka yi mamaki yaya idan na ce maka na san abin da kake ji a ranka, na san zafi da raɗaɗin rashin masoyi domin Allahnta ya saka mata, a sadda take nan ina samun sauƙi ne kawai da kallonshi amma a yanzu ko arzikin kallon babu tunda Afeefah bata nan haka kawai ba sakayya bane?”Idanu ya zura mata duk ta zama wani iri ta rame,”Sameera wa kike so? Rayyan?”Ta girgiza kai “Sulaiman?”Tayi shiru ya ɗan yi jimmm, kan ya matso ta.”a haka kawai Allah ya barki ya rama mata, ba yafiyata za ki nema ba ita za ki nema ta yafe miki”Yana kai nan ya juya ya fice.Ta saukar da kai tana hawaye, tana bibiyar Sulaiman sossai Dukda bai sani ba a haka ta san auren shi wadda hakan ya sake daga mata hankali amma ya zata yi? Jarrabawarta kenan, ashe Afeefar ma ba laifi tayiwa ubangiji ba ya zaɓi jarabtar ta ta hanyar da ya so, ba zata taɓa cewa Sulaiman tana son shi ba amma zata yi Adu’a Allah ya sassauta mata ya kawo karshen shi.****Rayyan yayi kwana biyu yana jinya kan ya ɗan sake Dukda ba sossai ba, sam ko a hanya basu sake haɗuwa da Afeefah ba don bata zauna ba shima kuma ba shiga mutane yake yi ba idan bashi da lafiya, Abeeha ta ɗauke ta suka yi sayayya sossai wadda Mammi ce duk tayi mata, suka je aka sama mata makaranta sun ma ƙi karbar ta sai da kyar aka barta SS1 za ta yi waec kawai SS2, idan tace hankalinta ya taɓa kwanciya irin na kwana biyun nan tayi ƙarya, wani irin so da kulawa suke nuna mata.Bata aikin komai don gidan ma’aikata har sun yi yawa sai ka ga daman zuwa kitchen, uniform da ake jira ɗinka mata bai samu da wuri ba saboda uniforms ɗin school din ba’a Kasar nan ake yi ba kuma tsakiyar term ne ya ƙare already wanda suke dashi ba’a kawo wani ba, don haka kullum suna tare da Abeeha kusan duk wanda ya san Abeeha sai ya san Afeefah matsayin ‘yar uwarta.Gidan Jannah suka je suka sha yinin su itama bata da damuwa kaman dai Abeeha don duk sun samu nagartaccciyar tarbiya daga mahaifiyarsu.A yau monday Afeefah ta fito sanye da uniform ɗinta mai dauke da bajin KIS(Kaduna international school) tayi kyau sossai a uniform din sai kuma tayi kankanta, murmushi ne sossai fuskarta tana yiwa Mammi sallama Abeeha ce zata sauketa in an tashi sai Driver ya je ya ɗauko ta, har tana shirin fita Mammi tace “Afeefah kin mance lunch box ɗin ko kunyar dauka kike?”Abeeha tace “Ana kunya da ciki ne? Oya maza yi sauri ki sameni a mota”Da sauri ta juya bata ankara da akwai mutum ba kawai ta ji ta buga goshinta a kan kirjin shi, kamshin turarenshi ya sanar da ita waye tun bai ɗago ba a razane tayi baya baya tana ɗago ido sai suka sarƙe cikin nashi fuskar nan tamau, uban Harara da yake zabga mata ya sa ta nemi rikecewa…”Ba ki da hankali ne? Ko ba kya abu da natsuwa ne?”Dakakkiyar muryarshi ya sauka a cikin kunnenta ai sai….

Back to top button