Hausa novels

Kurkukun Kaddara Takun Farko Chapter 55 By Hafsat Bature

💋KURKUKUN ƘADDARA💋

daga alƙalamin hafsat Boss Bature

E55

💋PRISONERS💋

Kwakkwance suke saman gadajensu, Sarah kaɗai ce kwance a ƙasa ta shimfiɗa bargonta kamar yarda ta saba.

Mutun É—aya ce ta rage acikin É—akin idonta biyu, sam ta kasa runtsawa sai juyi take yi saman gadonta, tarasa meke mata daÉ—i acikin duniyar nan, komai ya tsaya mata cak, babu alamun zata runtsa a daren yau, Yayin da take fuskantar ceilling, Jikin ta na asanye da tsoffin uniform É—inta da suka maida kayan baccin su, É—akin nasu yayi tsit sai sautin minsharin masu bacci, basu kashe hasken floor lamps É—insu ba, Saboda yau majnun bai yi musu haukan dare ba, tun da suka tsamo shi daga cikin trash can suka lalla6a shi ya kwanta bacci ya É—auke shi, Har dare bai sauko daga saman gadon shi ba, Ya ji jiki da alama.

Kamar an tsunkule ta, ta zabura ta miƙe ta zauna saman gadonta, hannunta dafe da saitin zuciyarta da ke ta harbawa da sauri sauri, sakamakon tunawa da ƴar uwarsu batool da ta yi, zuciyarta sam ba daɗi, sai yanzu ma take jin haushin damuwa da tayi akan ƴar gidan daddy, Sun saki jiki suna ta rayuwarsu batare da sun ta6uka komai ba, akan ƴar uwarsu.

Saukowa ta yi daga saman gadonta, ta É—aura eyes É—inta akan shimfiÉ—ar Danish, Ya rungume pillow abun shi sai sharar baccin sa yake yi, Cikin sanÉ—a ta nufi tsakiyar É—akin tana tunkarar sabbin gadajen da su parveen suka gaje, don har yanzu basu daina kwana saman su ba, tun ranar da aka kawo su Jamima, aka koma da mutun goma, su ka ci gaba da kwana saman su, Mutun biyar ne ba su kwana saman tsaffin gadajensu, Ita da Danish sai haris da Deeja, da kuma naufal, Amma sauran kowa ya samu sabon gado.

Agaban gadon Unaiza ta tsaya tana kallon wani sabon salon kwanciya, ta tura hannayenta cikin short É—in jikinta, saboda jaraba Cikin bacci tayi wurga da bargonta Æ™asa, Tana numfashi boobs É—in ta na yin sama da Æ™asa, Ta6e baki angel ta yi, Ji take kamar ta sanya hannu ta maida su cikin Æ™irjinta su shafe, A nemesu arasa, ko sun huta da guyabarta, ” Guntun tsoki taja tunawa da abunda ya taso da ita daga saman gadonta, da sauri ta nufi Æ™opar shiga sashen toilet É—in su, bakomai take son gani ba face furen batool tana so taga awani hali yake ciki, Tana Æ™oÆ™arin shiga toilet É—in taji motsin shigowar mutun ta bayanta, a firgice ta juya don taga wanene, lokaci É—aya ta sauke ajiyar zuciya ganin Danish ko me ya tada shi daga bacci, rayawa tayi aranta may be yayi tsamanin zata Æ™ara dura tagar ne shiyasa yabiyo bayanta.

Harara ta shiga jefa mashi, Yana daga tsaye ya goya hannayenshi saman ƙirjinshi, red vest ɗin Jikin shi ta fiddo mashi da hasken fatarshi sosai, Idanuwanshi da alamun bacci acikinsu,

“Halan Ka biyo ni ne don kaga me zan yi acikin toilet? in banda sa ido, mutun na jin bacci amma ya kafe sai ya takura rayuwar wani, ni nasan saboda ni kazo nan” ta yi maganar tana murgaÉ—a mishi Æ™aramin bakinta.

Bai tanka mata ba har sai da ya tako zuwa gabanta ya tsaya ya É—an duÆ™o da kanshi saitin fuskarta, Cikin Cool voice ya furta mata”abunda kika faÉ—a gaskiya ne, Saboda ke nazo nan” ta6e mashi tausasa la66anta tayi tare da cewa”Kasan dai baka isa ka hana ni yin abunda na yi niya ba, zaifi ka daina wahalar da kanka akaina” Æ™ayataccen murmushi ne ya bayyana akan fuskarshi, ganin yadda take mishi magana tana jifar shi da harara hadi da murguÉ—a mishi baki, a Æ™arshe ma taja mishi tsoki ta juya zata shige toilet, da sauri ya damÆ™o damtsen hannunta ya dawo da ita jikin bango yayi mata rumfa, mamaki ne ya kama ta, Ta zuba mishi ido tana jiran ganin me zai yi mata.

“Saboda na damu dake ne shiyasa na biyo bayan ki ba don wani abu ba” yatsina fuska tayi tare da cewa”Ni ban damu da kai ba don haka kaima ka daina damuwa dani, pls ka koma ka kwanta ni ka bani hanya in wuce ka na 6aramin lokaci” Hada bubbuga Æ™afa irin ya takura ta É—in nan,

Hakan ba ƙaramin dariya yaso ya bashi ba,
“Kince ba ki damu dani ba, but why kike hana idonki bacci don ki roÆ™i Allah akan ya baki abunda zai faranta min raina”! Har saida gabanta ya faÉ—i jin abunda yace, wani irin kallo ta soma binshi dashi, gaba É—aya ya kashe mata ba.”

DaÆ™yar ta iya buÉ—e baki tace “Danish kana nufin duk time da nake farkawa tsakar dare ina addu’a idon ka biyu? why ka sanya min ido, ko time dana É—aukar maka alÆ™awarin na faÉ—i ne kawai don in kawar maka da tunaninka akan wancen yarinyar, kuma ni nayi hakanne gudun kada ta 6ata maka tarbiyar ka, saboda Nifa basa burgeni, bata su nake ba” tana magana tana hura hanci, Hannu yasa yaja tsinin hancinta tare da cewa”Nafa san me nake yi angel, ki daina Æ™oÆ™arin nuna kamar ba donni kike yi ba, kina 6oye min irin Æ™aunar da ki ke yi min,” ranta a6ace tace”waya ce maka ina Æ™aunarka ni? To wai ni akan me ma xan yi addu’ar Allah ya bani su….” ya bata amsa da cewa”Saboda inaso” fuskarshi a É—aure ya bata amsa, kamar tasa hannu ta shaÆ™e wuyanshi haka take ji, muryarta a fusace tace”Dallah ni bani wuri na wuce, kunnuwana ba zasu juri sauraran waÉ—annan kalaman naka ba,”

tana Æ™oÆ™arin janye shi don ta wuce yae saurin cewa”Its okey, kin bani damar in cigaba da kallon nata kenan”? Girgiza mishi kai ta yi alamar a’a,

“nifa bance bazanyi bane, maganarce ke bana so,” ta faÉ—i hakan tare da sanya hannayenta ta ture shi gefe, Ta nufi Æ™opar shiga toilet, har ta kusa shiga sai kuma ta É—an dakata da alama wani abu take tunani ba tare da ta juyo ta kalle shi ba tace”Ni abunda ban fahimta ba, me zakai dasu da kake son su fito min? Ka san dai bana manya bane, Na jarirai ne, don haka ka daina murna, iya kallo ne shima ba koda yaushe zan bari kana kallan min abuna ba, da zarar Mun rabu da unaiza, zan haramta maka ganinsu,” ta Æ™arasa maganar tare da faÉ—awa cikin toilet din hada sanya jamlock ta datse Æ™opa, ta kifa kanta jikin Æ™opar tana

Kanga kunnuwanta ta yi ajikin Æ™opar don taji idan yana nan ko ya tafi, ba zato ba tsammani taji saukar hannun shi saman bayanta, a firgice ta juyo tana kallon shi, Yayin da shima yake kallonta, Ba ta yi mamakin ganin shi acikin toilet din ba tun da ba yau bane rana tafarko da ya fara Yi mata irin hakan ba, runtse idanuwanta tayi tare da bubbuga Æ™afa tace”Nashiga uku! Wai meye ruwanka dani ne eye? Ba mun shirya ba, kuma nace maka nima zanyi irin nata to me kuma kake so”? Fuskarta a hautsine tayi mishi maganar, wani irin kallo yake binta dashi idanuwanshi kamar zasu lumshe saboda baccin da yaje ji,

“Angel, kin É—aga min hankalina why zaki ce wai na jarirai ne, menene haka ba daÉ—in ji, kuma kince da zarar mun rabu da unaiza shikenan ko kallon su ma bazan Æ™ara yi ba, Ni na yi tsammanin duka zaki mallaka min su, tun da donni zakiyi su, idan kika min hakan baki min adalci ba,” muryarshi asanyaye sautinta ke fita, Lamarin yayi matuÆ™ar É—aure mata kai, har wani zazzare mashi ido take yi don ma yasan cewa ba wasa take yi ba, a cikin zuciyarta kuwa tunani take yi Anya Danish bai da ta6in hankali? Taya zai tsareta akan abunda ma basu da tabbacin zasu fito ko ba zasu fito ba.

“Kin yi shiru baki ce komai ba”? Muryarshi ce ta dawo da ita cikin hayyacinta, Ganin yana Æ™oÆ™arin dagula mata lissafi yasa ta ruÆ™o hannun shi acikin nata, Tace mishi”muje mu kwanta,” bata jira amsar shi ba, ta buÉ—e Æ™opar toilet É—in, taja shi suka fuce har zuwa cikin dakinsu, Abakin gadon shi ta tsaya tare da kallon shi tace”nasan damuwarka, yanzu mu kwanta mu yi bacci, zamuyi magana zuwa gobe” ba don yaso ba ya Æ™yale ta ya hau saman gadon shi ya kwanta itama ta wuce nata gadon ta haye, tana faman sauke ajiyar zuciya, ganin yana kallonta yasa ta janyo bargo ta rufe har kanta, lumshe idanuwanshi yae tare dajan nashi bargon ya lullube jikinshi, kowannansu da abunda yake saÆ™awa acikin ranshi, gani take kamar akwai shaiÉ—anu ajikin danish, waÉ—anda ke sanya shi yana yin abubuwa, Da farko yace yana son yi mata wanka yasa naci taÆ™i amincewa yanzu kuma so yake Æ™irjinta sun fito ko uban me zaiyi dasu, Anya kuwa Danish bada biyu yake yi mata wasu abubuwan ba? Ta fara kokwanto akanshi, da wannan tunanin bacci yae awon gaba da su.

A washe garin ranar, majnun ne ya farkar dasu daga bacci, Tun da ya farka daga bacci ya sauko daga saman gadonshi yana miƙa da hamma, ya nufi gadajensu ɗaya bayan ɗaya ya dinga bubbuga ƙafafuwansu, yana faɗin su tashi ayi wasa, One by one su ka soma farkawa idanuwansu a kumbure fuskokin su duk a yamutse an sha bacci, su parveen hada miyan bacci a gefen baki, sun ji haushin tada su da ya yi, sai faɗa su ke yi mishi amma ko ajikin shi.

tsotai ne yakai Majnun gadon Unaiza Æ´ar gidan daddy, Ya sanya hannu yana bubbuga Æ™afafuwanta don ta farka yaga ita kaÉ—ai ce bata tashi ba, can cikin bacci ta dinga jin bugun da akeyi mata, a hautsine ta farka tare da miÆ™ewa fuskar nan tayi jawur da ita babu annuri, suna haÉ—a ido da majnun Ya washe mata baki, ranta ya 6aci sosai dama ta tsani yaron, zabura tayi ta damÆ™o wuyan rigarshi, Haris da Danish har suna haÉ—a Baki wurin Æ™oÆ™arin dakatar da ita akan karta ta6a lafiyar jikin shi, ko kallo basu isheta ba, ta daddaga ta kwakkwasa mashi zafafan maruka saman fuskarshi, azabar zafi yasa yaron ya dafe kuncinsa ya fashe da kuka, parveen hada cewa”Allah shi Æ™ara maka, Ae kaine da shegen jan faÉ—an tsiya,” duk sun yi tunanin za ta sake shi ne tun da ta mare shi, amma sai suka ga ta sanya hannu ta shaÆ™e wuyanshi da Æ™arfi kamar zata kashe shi, idanuwanshi suka firfiro waje, A gigice Danish ya yunÆ™ura tare da angel hada deeja suka nufi gadonta, Suna Æ™oÆ™arin Æ™wace shi daga hannunta amma taÆ™i sakin shi, rai a6ace Danish ya daddage ya watsa yatsun hannayenshi biyar saman kuncinta, ji kake tass! Abun da bata ta6a tsammani ba, Da sauri ta saki Wuyan majnun idanuwanta akan fuskar Danish, tun da take arayuwarta bata ta6a jin azabar mari irin wanda Danish yayi mata ba, har wani jiri take gani acikin idanuwanta da suka cicciko tab da Æ™walla, hannayenta bibbiyu dafe kuncinta.

Su azeeza dake kallonta, dariya ce ƙumshe acikin bakunansu, Musamman da ta dinga binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya, kamar tana tunzurasu ne akan su yi dariya, Angel ce ta rungume majnun ajikinta, tana lallashinshi, Sai kuka yake yi, Wuyan shi hada sahun akaifar Unaiza wurin yayi ja sosai jini ya kwanta abunka ga zabayyana dama ya lafiyar giwa.

“Wani ya samo min ruwa in bashi” angel ce tae musu maganar, da sauri parven ta sauko daga saman gadonta, ta nufi Æ™arÆ™ashin gadon batul ta É—auko bottle water cikin wanda suka ajiye taje ta miÆ™a ma Angel tasa hannu ta kar6a tare da cire murfin ta kwafa mishi abaki, sosai yasha ruwan har yana shaÆ™ewa, kusan rabin robar ya shanye, kafin ya janye bakin shi, Yana faman tatta6e fuska ya kalli unaiza a lokacin ta dawo da kallonta kan Danish, da alama bakinta ya gama mutuwa saboda marin da yayi mata ba.

Cikin shessheÆ™ar kuka Chinonso Ya nuna ta da yatsa yana faÉ—in”I hate u, mai idon dodo, bana son ki,” Dama ranta a6ace yake, azabure ta yunÆ™ura ta sauko daga saman gadon da niyar ta sake bugun chinonso, a tsorace yaron Ya yi saurin faÉ—awa jikin angel ya Æ™anÆ™ameta, Wata irin gigitacciyar tsawa Danish Ya daka mata, wadda tayi silar dakatar da ita, Da kakkausar murya yace mata”kada ki kuskura kice zaki Æ™ara ta6a shi, ke baki da hankali ne baki ga yaro bane? Ko so kike ki kashe shi ne shiyasa kika shaÆ™e mishi wuya” yae maganar idonshi akan fuskarta, wani irin Æ™ululun baÆ™in ciki ne ya tokare mata maÆ™oshinta, la66anta har kerme suke yi wurin faÉ—in”Ni ka mara? Sannan ka rufe ni da faÉ—a sai kace wata Æ´ar cikin ka, To ni ko ubana bai ta6a É—aga min murya ba, balle har yayi gigin ta6a lafiyar jikina, rana ta farko da mahaifiyata ta fara yi min tsawa akan idona daddyna ya kwashe ta da mari, Amma zuwana Cikin ku, kun maidani kamar wata jaka, Wai me kuke nufi dani ne? Na kasa ganewa……..” daÆ™yar ta Æ™arasa maganar, hawaye ta ko’ina saman fuskarta, Still idonta akan fuskar Danish, su Deeja sun kasa kunne suna sauraronta babu wanda ya tanka mata, hakan ba Æ™aramin Æ™ona mata rai yai ba.

tana magana jijiyoyin wuyanta duk sun firfito ruɗu ruɗu saman fatarta, Sautin muryar ma daƙyar yake fita

“Ni bazan cigaba da zama acikin wannan Munafukin Ginin ba, nafara kokwanto akan ku, Kun Æ™i ku sanar dani ina ne nan, wai me ake nufi dani ne? So ake dole sai nayi rayuwa kamar dabba! to nagaji! nagaji!! bazan Iya cigaba da zama acikin Ƙuntataccen dakin nan ba, wlh ban yarda da kowa ba, so ake akashe ni, Ni ku faÉ—a min me ake aikatawa acikin ginin nan? Kowa ya maidani jaka, Ni da nazo É—aukar karatu? Ance min school ce but why har yau ba’a kai mu class room ba? Na yi shiru ne don inga ko akwai wani shiri da ake yi mana amma naji shiru har yau, babu zancen zuwa aji mu É—auki karatu, nayi expecting É—in zan samu abunda nake so shima kun hanani saima neman kassara rayuwata da ku ke yi, ta ko’ina kun Æ™untata min, Nifa ban saba da irin wannan rayuwar kullen ba, Ni school din ma na fasa amaidani gidan daddy na, wlh bazan zauna ba!!! ” tana magana tana matsar hancinta, fuskar tayi jaga jaga da hawaye,.

Da alama marin Danish ba ƙaramin zaburar da ita yayi ba, sai sambatu take yi tana zazzaga masu masifa ta inda ta shiga bata nan take fita ba.

“magana fa nake yi maku, duk kunyi min shiru sai kace kurame, Ku faÉ—a min ina ne nan? Kuna Æ™ara jefa ni cikin ruÉ—ani! Abubuwa dayawa suna neman rikita min lissafin Æ™waÆ™walwata! meyasa tun da nazo babu wani sauyi, ni fa ba haka daddyna ya faÉ—amin ba, yace min school É—in akwai wuraren shaÆ™atawa acikinta, amma ni bangani ba, shi fa ya faÉ—amin hada lunch room da garden da swimming pools ga zoo irin na gidan mu, hada cinema but why are we always locked in the same room like an animal? Nifa na saba agidan mu, Ina yin duk abunda nakeso, ban saba da wahala ba, duk rana saina fita yawon buÉ—e ido, Har night club ina zuwa sometimes a hotel nake kwana tare da friends É—ina, Taya rana É—aya za’a kawo ni wannan gurin me kama da Gidan Yari!”

a hargitse ta Æ™arasa maganar, Cikin raunin murya da sagewar gwiwa ta zube saman Æ™asa tana ci gaba da yin kuka tamkar ranta zai fita, basu ta6a jin tausayinta ba irin na yau, ganin yadda duk tabi ta burkice, tsawon lokaci babu wanda Ya tanka mata, da zarar angel ta yi yuÆ™urin buÉ—e baki ta yi mata magana, da sauri Danish ke dakatar da ita, ta hanyar girgiza mata kan shi alamar karta fada mata, tuntuni take son faÉ—a mata gaskiyar zance akan daddynta mugune sadaukar da ita yayi kuma nan É—in kurkukun Æ™addara ne, da komai da suka sani dangane dashi wata’Æ™il ta dawo hayyacinta, ta gane cewa Allah É—aya ne! Sai dai Danish yaÆ™i bari a sanar da ita.

Sosai take yin kuka babu mai lallashinta, Gefen fuskarta inda Danish ya mara hada sahun yatsun hannun shi ruÉ—u ruÉ—u, Tamkar da bulala aka shafi wurin, shi kanshi sai daga baya ya yi danasanin marinta da yayi duk da laifinta ne itace taja ma kanta,.

Saukowa gabriel yae daga saman gadon shi, gaba É—aya hankalinsu ya koma kan shi, Bai nufi ko’ina ba sai wurin da Unaiza take zuÆ™unne tana kuka, ZuÆ™unnawa yayi tare da sanya hayyanshi biyu ya rungumota jikin shi yana lallashinta, sai ya dinga ganin kamar twin sister É—in shi ce take kuka, muryar shi Æ™asa Æ™asa yake faÉ—in”its okey unaiza, Stop shedding ur tears, ina atare da ke” kallon kallon sauran Æ´an uwan nasu suka somayi atsakaninsu, sun yi mamaki ganin yana lallashinta, bayan shima yasan halinta na dabbanci da rashin kamun kai, dakatawa tayi da yin kukan tayi lamo ajikin shi, dama Gabriel akwai Æ™ira, Ta samu wurin zama, kamar zata shige cikin shi, jin tayi shiru yasa shi É—agowa ya kalli su Danish dake atsaye suna kallon su, Magana ya soma yi musu

“Nima na jima ina so in tambaye ku game da kurkukun nan amma nakasa, Mu tamkar baÆ™i ne acikinsa, ina so insan komai agame da shi, Tsawon kwanaki, Banga an dawo min da Æ´ar uwata ba, kuma ni banga ana fidda mu waje ba, kullum muna kulle a room É—aya, sannan waÉ—annan mutanan dake zuwa wanda ku ke kira da giants sam basu kwanta min araina ba, meyasa koda yaushe suke zuwa cikin shiga ta baÆ™aÆ™en kaya? Suna 6oye kan su don kada mu gansu, na fara zargin wani abu, it seems like something strange is going on in this prison. I wonder what they’re hiding from us.”

Shiru suka yi babu wanda ya tanka mashi, A ƙagare yace

“Na yi magana anyi shiru ba’a tanka mini ba, hakan na nufin hasashe na ya zama gaskiya kenan? Akwai wani abu dake faruwa wanda ba’a so mu sani, pls ku faÉ—a mana abunda ku ka sani tattare da gidan kurkukun Æ™addara, ku wayar mana da kanmu Ni da Unaiza! ni Æ´ar uwata ma itace damuwata, bansan Ina aka kaimin ita ba, awani hali take! Idan naci gaba da 6ata lokaci za’a iya cutar min da ita batare da sanina ba

(Mu haɗu next page, Yanzu zan ɗaura maku shi, saboda ina busy mantawa nake, Don haka idan kun gama karanta wannan ku bincika page 56, Masu so karanta middle Step book 2 whatsapp suyi min magana 08103884440 masu son facebook paid group Ga link ku danna shi za kaiku ga wadda zaku yi ma msgana👇

(Masu so karanta middle Step book 2 whatsapp suyi min magana 08103884440 masu son facebook paid group Ga link ku danna shi za kaiku ga wadda zaku yi ma msgana👇)

 

Click Here To Download Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete

 

 

( mu hadu next page In Allah yakaimu da rai da lafiya, masu yi mun ya jiki ina godiya)

Back to top button