Halysaah Page 146 By Khaleesat Haydar
HALYSAAH PAGE 146…Ajay dai ya kasa ce ma Mami komai gashi yaki daga kansa, gaba daya he look very worried and confuse, tsawa Mami tayi masa tace “Baka ji na ne wai Junaid? What is wrong with her?” Ya girgiza kai ba tare da ya yarda su hada ido ba, muryarsa dauke da tsantsan damuwa yace “Bata da lafiya ne” kafin Mami tace komai kawai ya koma cikin dakin don duk hankalinsa na can gaba daya, yana shiga dakin yayi saurin covering zanin gadon that was stained with blood da duvet, yanda Mami ta gansa a birkice yasa ta kasa hakuri kawai ta bi bayansa da sauri zata shiga dakin taji muryar Kilishi da ta taho daga side din Hajja tace “Lafiya me ke faruwa Aunty Aseeyah? Ko iska ta tayar? Mu mun zata ma Hadiyah ce wallahi” Mami ta juya tana kallon Kilishi don sai a sannan ita ma tunanin hakan ya zo mata bayan Kilishi ta fada, ko dai tana da iskokai ne, Mami bata ce ma Kilishi komai ba ta shiga cikin Bedroom din kawai, har kusa da gadon ta karasa da sauri ganin yanda Ajay ke rike da ita with confusion yana kiran sunanta worriedly amma ko motsi bata yi, sai ga Kilishi ta biyo bayan Mami har cikin dakin ita ma, Mami ta zauna edge din gadon tana kallon Khaleesat that was still unconscious ta fara tofa mata addu’a, Kilishi ta wani kalli Ajay tace “Amma kai dai sauna ne Ahmad, idan iskoki gareta dama sunanta zaka zauna kana faman kira kana jij ko ko addu’a ya kamata ka dinga tofa mata?” Sal a sannan Ajay yayi realizing abinda ya kamata yayi in the first place da yaga she is unconscious, da sauri ya sakar ma Mami Khaleesat ya shiga bandaki immediately zai debo ruwa, Kilishi ta bi sa da wani kallo baki bude ganin yanda duk yake a rikice ya daburce kamar ba shi da ta sani ba, dama akwai abinda ke rikitasa har gigice ya kasa boye hakan, haba ta rike tana kallon Khaleesat a ranta kuwa tana cewa har sun fara mallakesa kenan irin wannan gigicewa da rawan jiki kamar zai masu kuka, Mami dai sai gyara ma Khaleesat duvet din jikinta take bayan ta lura babu riga jikinta at the same time tana tofa mata addu’o’i, Kilishi ta tabe baki ta fara komawa baya a ranta tana addu’an Allah ya sa iskan su kara tashi ta shake Mami, ita banda Hajja da ta tasheta ta taho taga abinda ke faruwa da yake a bangarenta ta kwanta yau ai da baza ma tasan wani abu na faruwa ba a gidan, Hajjan ma tayi tunanin Hadiyah ce, Ajay ya fito bandaki da ruwa ya karasa kusa da gadon da sauri har ruwan na zubewa a hannunsa, duk tunanin Mami addu’a zai yi a ruwan ko wani abu, sai kuma taga ya zauna daya side din yana shafa mata a fuska, Mami zata yi magana Khaleesat ta fara juya kai a hankali, da sauri Kilishi ta koma can bakin kofa ta tsaya tana fatan ta makuro Mami a rasa me kwatanta, a hankali Khaleesat ta bude idonta da suka rine, Mami ta dafa goshinta cikin kwantar da murya tace “Sap Halysaah, sannu kin ji” Khaleesat ta kasa komai tana kallon Mami Kamar tana son tabbatar da ita din ce ko kuma idonta ne suke mata gizo, nan ta fara kokarin mikewa zaune amma ta kasa daga ko hannunta, gashi duk jikinta sai rawa yake, Mami zata gyara mata kwanciya tayi saurin kamo hannunta tana girgiza kai muryarta ko fita baya yi sai ga hawaye masu zafi na sauka gefen idonta a wahale tace “Don Allah ki tafi da ni Mami, don Allah ki tafi da ni” a nan ne idon Mami ya sauka kan bedsheet din kan gadon don a sanda Khaleesat take kokarin tashi ta janye duvet din da ya rufe wajen jini, shi dai Ajay ya mike a hankali ya koma daya bangaren dakin ya tsaya looking guilty, Mami tace “Innalillahi wa Inna ilaihi raji’un, meye wannan?” Kilishi ma sai kallon kan gadon take da mamaki, Mami ta kalli Ajay da ya sauke idonsa kasa, sai kuma ta kara kallon Khaleesat that was still struggling to get up tana rike da hannun Mami muryarta na rawa tana cewa Mami ta tafi da ita don Allah, Mami dai sai rufa mata duvet din jikinta take ganin cirewa ma take kokarin yi gaba daya not minding she is naked, mamakin jinin meye a kan gadon Mami ke yi with confusion, gashi sai bin dakin take da kallo ko zata ga wani makami or anything sharp, Kilishi kuwa ta kasa daurewa ta kalli Ajay tace “Wannan kuma wai jinin meye haka kwance a kan gadon Junaid? Fada ku ka yi da matar taka ko me?” Ajay dai bai daga kansa ba, kawai suka ga ya nufi kofa walking slowly ya fita daga dakin don ji yayi kafafuwansa sun ka gaba da daukansa ga wani sanyi da yake shigarsa sosai, Mami ta bi sa da kallo cikin rudani, Khaleesat na kuka da kyar har Ikcn muryarta bai fitowa sosai tace “Don Allah ki tafi da ni Mami, pls take me away, wallahi mutuwa zan yi….” A hankali Mami tace “Ina hijab din ki?” Da sauri ta yunkura zata mike ta nemo hijab amma tayi wani kara me karfi ta rike Mami idonta kamar za su fito ta fashe da wani kukan tace “Bazan iya tashi ba wallahi….” Kilishi ta bude baki tace “Baza ki iya tashi ba? Yanka ki yayi da makami a kafar ko me?” Mami ta cire duvet din jikinta a hankali tana dubata, mamaki tayi sosai and she was shock at the same time amma fa ta rasa gane ma’anar hakan, after a while ta mike ta fice daga dakin ta fita har parlor, kofar dakin da ta gani a bude ta shiga ta gansa zaune gefen gado ya dafe kansa da hannu biyu, Mami na masa wani kallo tace “Meye haka kayi ma yarinyar mutane Junaid?” A hankali Ajay ya daga kansa yana kallonta da idanuwansa da suka kada sosai, sai kuma ya sunkuyar da kai yayi shiru, Mami ta daka masa tsawa tace “Ba magana nake maka ba, me kayi mata haka?” Dakewa yayi murya can kasa yace “Mami ba da gangan bane…” Mami tace “Ban gane ba da gangan ba, meye kayi mata ba da gangan ba?” Cikin sanyin murya ya daure yace “Ni ban san she is a virgin ba” Mami ta dinga kallonsa babu ko kiftawa da wani expression tace “Virgin? Kamar yaya Vy Ajay ya kasa cewa komai kawai sai ga hawa idonsa, Mami tayi still a tsaye kamar an dasa ta a dakin tana kallonsa babu ko kiftawa virgin din da yace na mata yawo a kal, ta dade bata shiga shock irin na moment din ba, a hankali ta juya cikin rashin kuzari ta fita daga dakin, but how is she a virgin yarinyar da aka ce ta taba aure?? A corridor ta hadu da Jay da Hajja sun zo part din, Hajja tace “Aseeyah ke ma zuwanki kenan ko? ni wallahi na zata Hadiyah ce tun da ta saba ta kurma ihu ba gaira ba dalili saboda tabara” Hajja ta shiga parlon tana cewa “Ko dai iskokai gareta ne Jiddan? ina Ahmad din?” Jay bai shiga parlon Junaid ba yana kallon Mami yace “Me ya sameta Mami? Hope she is okay?” Mikewa Ajay yayi jin muryar Jay ya shige bandaki, Mami bata yarda ta kalli Jay ba tace “She is fine, I think she had a nightmare” Tana fadin haka ta shiga parlon ba tare da ta jira me zai ce ba, shi dai bai bi ta zuwa cikin parlon ba ya tsaya bakin kofar, Kilishi dake tsaye bakin kofar dakin Ajay taki zuwa kusa da Khaleesat ta fita parlor da sauri jin muryar Hajja a parlon, Mami dai ta wuce Bedroom ta bar su a parlon, Hajja ta kalli Kilishi tace “Na ji shiru shiru baki dawo ba, lafiya dai ko? Me ya sameta? Kuma ina Ahmad din? Halan tana da mutanen boye ne?” Kilishi tace “A’a ba lafiya ba Hajja, ina ganin Junaid dai fada yayi da ita, gashi can ya yanyanke ta wallahi, don saman gadon kaca kaca da jini, mun tambayesa me ya faru yaki bamu amsa ficewarsa, ita kuwa tana can kan gado” tashin hankali sosai Hajja ta dafa kujera tace “Innalillahi wa Inna ilaihi raji’un, ta mutu??” Kilishi tace “Ga ta can dai a dakin, amma kam ta zubar da jini sosai, zanin gadon ya jike jagab da jini” Hajja tayi karfin halin karasawa cikin dakin jikinta na bari tana salati a zuciyarta, tana shiga ita ma idonta ya sauka kan zanin gadon tace “Innalillahi wa Inna ilaihi raji’un” Kallon Mami da ta fito daga bandaki bayan ta tara ruwan zafi a bath tub tayi tace “Aseeyah me ya faru?” Mami bata kalli Hajja ba, tana magana da kyar tace “Ta samu rauni ne Hajja” Hajja tace “Rauni? Wani irin rauni?” Karasawa tayi kusa da Khaleesat hankali tashe, Mami dai ta fita daga dakin zata tafi kitchen ta dauko gishiri hawayen dake makale idonta ya fara zuba, Hajja tayi shiru tana ta kallon stain din zanin gadon kamar warce ta fahimci wani abu, sai kuma ta kalli Khaleesat da ta rasa inda zata sa kanta cause she was soo weak and in pain, ta kasa kwanciyar haka zaman ma ta kasa sai Umminta take kira, a hankali Hajja ta rufe dai dai inda yayi staining a zanin gadon sannan ta kalli Khaleesat tace “Sannu Jiddah, Allah ya maki albarka…..” Sai kuma ta juya ta kalli Kilishi tace “Idan Aseeyah ta kintsa ta a kawota sashi na komin dare” Hajja na kai wa nan ta fita daga dakin, Kilishi ta bi bayanta zuwa parlor with confusion, ba tare da Hajja ta kalleta ba tace “Wannan ai jinin budurci ne a saman gadon Kilishi” Kilishi ta wani gwale ido “Hajja ai ba budurwa bace wallahi” Hajja tace ко ma dai menene ga dai jinin budurci na gani akan gado, a linke zanin gadon a ajiye tukun” Hajja na kai wa nan ta fita daga parlon, Kilishi ta kasa barin inda take tsaye baki bude abinda Hajja tace na mata yawo a kai, jinin budurci kuma yarinyar da kowa yasan Bazawara ce, Mami ce ta shigo parlon bayan ta dauko gishiri a kitchen, da wani expression Kilishi tace “Aunty Aseeyah ki ji Hajja da wani zance wai jinin budurci ta gani a kan gado, wai dama boye ma Hajja aka yi bata san Bazawara bace yarinyar nan ashe?” Cike da karfin hali Mami tace “Abinda Hajja ta fada haka ne Kilishi, budurwa ce Halysaah…. Ga kuma shaida nan kan gado” Mami ta shiga daki ta bar Kilishi da sakakken baki a wajen, da sauri ta bi Mami zuwa dakin with shock tana kara kallon zanin gadon, ganin irin dagan da Mami suka yi da Khaleesat Kafin su je bandaki don ta kasa tashi tsaya wannan ya kara tabbatar ma da Kilishi gaskiya Hajja ta fada, Kilishi na jan kafa da kyar ta fita daga bangaren gaba daya, to amma ta yaya za ta zama budurwa bayan hatta iyayenta basu boye cewar Bazawara bace da aka je neman aurenta, ko dai wani salon yaudara ne wannan don su dena ce mata bazawara a gidan? Kai inaa yaudaran nan bai yaudaru ba don ko duk jikinta kunnuwa ne bazata yarda ba, ta yaya warce kowa ya sani a Bazawara overnight ace ta zama budurwa kamar wani wasan kwaikwayo, wato su Junaid zai ma hankali tunda yaji yanda ake kiranta Bazawara now and then shine bari ya zo da plan, Jay was still standing outside of the main parlor don kawai ya kasa tafiya so yake Mami ta fito tace masa she is fine duk da Hajja da ta fito yanxu tace masa kawai iskokinta ne ya tashi ba komai ba ya tafi yayi kwanciyarsa she is fine now, shi kuma fin shekara daya da yayi da Khaleesat bai taba ganin alamar iskokai a tare da ita ba, don ko yaya ne ai da wataran za su tashi ko kuma su dan tabata barin lokacin da take cikin tension din Abdul, take cikin bacin rai kullum, why all of a sudden za ace tana da iska dare daya, bacci yake amma farat daya ihun da tayi ya tashe sa daga baccin kuma yasan sarai muryarta ne, kuma duk yanda ya so kin zuwa yaga if everything was alright ya kasa daure zuciyarsa, yana fitowa Parlonsa sai ga Hajja that was thinking Hadiyah ce don ita bata ma san Khaleesat bace, nan yace mata ba Hadiyah bace, shi ne suka taho part din Ajay tare, Kilishi ta fito daga babban parlon tana kallon Jay da ya juya yana kallonta ta karasa har inda yake babu kunya babu tsoron Allah tace “Jawwad wai don Allah wannan yarinya Halysaah take ko waye sunanta? Budurwa ce ko Bazawara? Ina ga duk wanda zai san matsayinta to a bayanka yake don da kai aka fara sanin yarinyar kafin Junaid Jay ya dinga kallon Kilishi still trying to process what she is saying, Kilishi tace “Dole ka kalleni haka Jawwad, mu dai mun san tun farkon neman auren yarinyar nan da kayi iyayenta basu boye matsayinta na bazawara warce ta taba aure ba, to wai kwatsam dare daya mijinta ya maidata budurwa zai raina ma kansa hankali ba mu ba, sannan ace duk tsawon watannin da suka yi tare sai yau ya fara saninta idan ba raina ma mutane hankali zai yi ba, to kansu suka yi deceiving da wannan jinin saman gadon da Hajja ta lakaba masa suna jinin budurci, na fi karfin yaron da aka haifa a gabana ya yaudare ni” Jay dai ya sauke Idonsa bayan ya gama jin duk abinda Kilishi ta fada, ta juya tayi wucewarta zuwa bangaren su Gimbiya Firdausi ta kai masu labari, Jay stood there for almost 20 mins sai ga Mami ta fito zata je kiran Yakumbo ganin ita kadai bazata iya da Khaleesat da taki bata hadin kai ba kwata kwata, Jay ya daga kai yana kallon Mami da ta sauke idonta bayan sun hada ido, tace “Baka tafi ka kwanta ba?” Bai ce mata komai ba, tace “Ka je sai da safe, sun lafa mata ai tuntuni” Daga haka ta bar wajen ba ta ta kallesa ba……….


