Hausa novels

Wace Ce Ita (Who is she) Chapter 63 Hausa Novel

WACECE ITA⁉️(WHO IS SHE⁉️)

Unique Barakancy🌹

SIXTY-THREE📍

Kamo hannunta deen yayi cikin rarrashi yace;
“Stop crying zahrah, he’ll be fine”….
Har cikin zuciyarsa yayi maganar saboda shi kadai yasan yanda kukanta ke daga masa hankali, yasan khaleel din shima abun aji tausayinsa ne amma sam baya tausayinsa because he believe rago ne shi, irin first class dinnan ma dan bega abinda zesa kazo ka kwanta a gadon asibiti saboda mace ba, ko me ta maka kuwa, men are bound to be strong and women are to be fragile, so why being fragile sai kace mace? In aurenta yakeso a bashi basai yazo ya kwanta a gadon asibiti ba sannan, Afterall ita kanta ta nuna tana yinsa so meye na rapkewa kana kuka kamar mace kuma?…..

Ba iya su umm da suke mamakin zuwansa da furucinsa ba har shi kansa patient khaleel yayi mamaki saboda wannan shine karo na farko daya taba jin deen yayi magana a tsine ba fada, kuma yau deen da bakinsa yake cewa ta kwantar da hankalinta he’ll be fine? Kenan yanzu yayi approving relationship dinsu? Inko hakane da yafi kowa farinciki a duniya, amma meyasa ya gansu a wannan yanayin? Tabbas yana bukatar sanin dalili kuma ya tabbatar babu wacce zata warware masa wannan abun sai wifey……

Hannunta ya ruko suka karasa har gaban gadon da khaleel ke kwance, ya kalli khaleel blankly yace;
“Toh gatanan tazo sai ka warke ai”….
Shiru dakin ya dauka kowa ya kasa gane ko da wata manufa yayi maganar saboda yanda yayi maganar a nitse babu hargowa…….

Dauke kai khaleel yayi ko a jikinsa, ya kalli sauran mutanen dake dakin ya tabbatar duk abinda ya fada deen baze iya mishi komai ba irin ga dama ta samu dinnan sannan ya dawo da kallonsa kan baby tee yace;
“Wifey, in baki aureni ba zan mutu, rayuwata na cikin garari”…..

Hannunta tayi niyar zarewa daga cikin na deen ta kamo na khaleel, deen ya kankame hannun batareda da kowa ya lura ba, dole ta hakura ta maida masa martani a haka…..
“Bazaka mutu ba darling khal, bazaka mutu ba sai munyi aure, stop being sick please……

“Promise me you will never leave me”…
“I promise I’ll always be with you”…..
“And I promise to love you forever”….
“Me too”…..
Wani abu me daci deen ya hadiye a makogoronsa, sakin hannunta yayi yana controlling kansa gudin karsu gane halin da yake ciki……..

At that moment, after witnessing that scene yayiwa kansa alkawarin fita daga sabgarsu gabadaya, ze barsu su sake suyi rayuwarsu kamar kowane masoya, and he mean it this time around, saboda abinda ya gani ya tabbatar masa zahrah na san khaleel, and right now farin cikinta kawai yakeso, besides ita da shi will never get along gwara ya barta da khaleel dinta zata fi jindadi, and Allah yasoshi he was never really in love with her ba re abun ya damesa, dama sudais ne yayi pushing dinsa, ya kuma godewa Allah da bai fadi abinda yayi niya sunji ba ballantana kowa ya dinga kallonsa da abun koda be aureta ba…….
A hankali murya a shake yace;
“I’ll let go of you baby girl! Forever!”….
Da sauri baby tee ta juyo tace;
“Yaya are you talking to me?”….
Murmushi ya kakalo yace;
“No zahrah”…
Ganin yanda ya sakar mata fuska khaleel yaji karfin gwiwar yi masa tambayar da yakeso ya masa, cikin dan tsoro yace;
“Yaya kayi approving relationship dinmu kenan?”..
“Sure, I can’t wait for you two weddding, I just need you to take very good care of my sister!”…
Deen ya bashi amsa yana murmushi……
Da wani irin farinciki khaleel yace;
“I promise you, wallahi I’ll take good care of her, bazan saba umarninka ba”…..
“Good”….
Ya fada yana juyawa da nufin barin dakin, da sauri baby tee ta ruko hannunsa tace;
“Yaya saif ina zaka?”……
Zame hannunsa yayi be juyo ba yace;
“Zanje in dawo ne, enjoy your time okay?”..
Be jira amsarta ba ya fice daga dakin…..
Wani iri taji aranta, jiki a sanyaye ta dawo gurin khaleel, tayi murmushin yake tace;
“Kaci abinci kuwa?”…..
“Tinda na ganki naji na koshi, I don’t need any food wifey”….
Ya fada yana kokarin kamo hannunta, janye hannun tayi da sauri tana bata fuska tace;
“Yaya can come in anytime, in ya gani zeyi fada”…….
Kamar yace mata shi daya rikeki ai ba haka kikayi ba sannan da kanki ma kin rikosa, kawai ya share gudin kar ranta ya baci…….

Yana fita ya samu su mami zaune a reception, guri ya samu ya zauna be cewa kowa komai ba, suma kuma basu ce masa ba saboda mamakinsa suke har lokacin, gwarama su bappa da basusan dramar da akasha ba so ba lallai su kawo abubuwa kamar yanda su umm sukeyi ba, da Abby dayayi witnessing dukan da deen yayiwa khaleel, amma shine ya zauna ya saurari maganganunsu sannan ya fito hankali kwance kamar ba arrogant deen din da suka sani ba….. Su dama khaleel na fara magana suka fice gabadaya dan bazasu zauna ayi rashin kunya a gabansu ba…..
Taboshi bappa yayi yace;
“Saifu dazun kana magana wannan abu ya katsemu, me kake san cewa ne?”…..
Ajiyar zuciya ya sauke cikin dakiya yace;
“Dama cewa zanyi babu abinda ke tsakaninmu and tanada wanda takeso which is this patient”…….
Be jira sunce komai ba ya dora da fadin;
“Bappa mahaifinsa shine wanda ya rike zahrah, yana barrack in an islolated place tun ranar confession dinchan kuma tin ranar bamu je ba”…..
Gyada kai bappa yayi yace;
“Na fahimta, ya kamata muje inda suke, inaso inyi magana dasu”….
“Toh shikenan bappa, ko yanzu kakeso muje zamu iya zuwa”…..
“Eh muje, ya kamata yasan halin da dan shi yake ciki ma”…..
“Okay but wa zamu bari a asibiti? Be kamata mu tafi duka ba ko?”…..
Karap anna tace;
“ni zan zauna, ba san shiga barikin sojoji nake ba”…..
Ita haka Allah ya yita batasan abinda ze hadata da sojoji……..

Mami da bappa da Abby ne suka fara yin gaba sai umm data bi bayansu bayan bappa yace ta raka anna ciki, deen na tsaye a reception din har umm ta fito sannan suka jera tare…..
Tafiya suka farayi in silence deen naso ya mata magana amma gabadaya shakkarta yake musamman yanda taki ce masa komai, saida yaga sun fito farfajiyar asibitin kafin akai parking space sannan yayi shahada ya tsaya ya ruko hannayenta ya tsuguna a kasa ya sunkuyar da kai dake babu mutane a gurin…..
Kallonshi tayi na 30secs sannan ta girgiza kai tace;
“Tashi!”……
Kasa da kansa ya karayi yace;
“Bazan iya tashi ba in baki yafemin ba umm, fushinki a gareni masifa ne, dan Allah ki yafemin”…..
Sosai taji zuciyarta ta karye amma ta dake tace;
“Tashi mana saif, baka ganin akan hanya muke”…….
Be tashi ba yace;
“Umm nasan mu masu lefi ne a gurinki most especially me, I know I have disappointed you in many ways amma ki yarda dani wallahi wallahi babu wani illegal relationship tsakaninmu da baby tee, you have no idea how heartbroken I am knowing zarginmu kike”…….
Zame hannunta daga cikin nasa tayi sannan ta shafa kansa tace;
“Koda zan ganku a cikin yanayin dayafi wannan trust me bazan zargeku ba, saif koda bansan halin baby tee ba kai nasan naka, nasan abinda zakayi da wanda bazaka yi ba, I just said that punish you, but the thing is in mu munyarda daku sauran mutane fa? Saif kasan illar ayiwa mutum sheda kuwa? Da kazo wucewa a family ana nunaka ana cewa shine wanda yayi kaza da kaza? It’s clear biyewa baby tee kake which is very wrong, idan bazaka tsawatar mata ba ai be kamata ka biye mata ba, tashi muje! I don’t want to repeat myself!”……
Mikewa yayi kamar yanda ta umarta sannan yayi kasa da kansa yace;
“I’ve realized my mistakes umm and I promise you it’ll be the last time something of such will ever happen, kice kin yafe mana dan Allah”…..
“Na yafe muka saif, ku nemi yafiyar mami ma”……
“Insha Allah Doctor, thank you”…..
“Muje suna jiranmu”…..
“Yes umm”….
Ya fada yana murmurshi, tabbas sudais yayi gaskiya da yace one conversation with her can solve everything, and it really did…..
Umm na fita anna ta kalli khaleel da ya sake gabadaya daga zuwansu tace;
“Ja’irin da’ wato kaga abincinka ka warke ko? Inata cewa a kawomin kai in ganka ashe a gadon asibiti zamu hadu, shine kazo ka kwanta kanata bidar zara’u na, kaga kyakkyawar jikata ka makale ko? Allah ya taimakeka kaima ba baya bane, amma meyayi zafi haka kakesa kanka a cikin damuwa dan nan?”…..
Murmushi kawai khaleel ya keyi batareda yace komai komai ba……Chan anna tashige toilet ta barsu anan……
“Wifey tin dazu nake cewa ki zauna kinki”…
Cewar khaleel yana matsa mata kusa dashi…..
Batasan meyasa ba, haka kawai taji batasan kusanci dashi ko yaya shiyasa dazu taki yarda ya rike hannunta, janyo plastic chair dake chan gefe tayi ta zauna tana facing dinsa……..
“Fatima!”…..
Ya kira asalin sunanta…..
Da sauri ta dago jin ya kirata da ainihin sunanta abinda be taba yi ba……..
Numfasawa yayi yace;
“Fatima hankali na ya kasa kwanciya tin bayan abinda nagani, bazan boye miki ba I felt betrayed, played played and heartbroken, kuma shine abinda ya kawo ni asibitin nan”…….
Curiously tace;
“Me kagani?”……
Cikin yanayin na jin ciwon abun har lokacin yace;
“You invited me with emphasis, only for me to come and see you in an unpleasant manner keda yayanki, muka hada ido dake kikayi kamar baki ganni ba ya daukeki kukayi ciki, was it all a setup?”…..

Download>>> Sexxy Boss Lady Romantic And Comedian Novel Complete

Wani irin faduwa gaban baby tee yayi harda dafe kirji batasani ba, koda wasa bata taba kowawa abinda zeyi magana akai ba kenan, kuma Allah ya sani bata ganshi ba, dan da ta ganshi saidai tayi losing deal din, girgiza kai tayi tace;
“Wallahi tallahi kaji rantsuwar musulmi banganka ba khaleel, maybe mun hada ido amma hankalina baya kai, kasan ba ido ke gani ba hankali ke gani, and it wasn’t a set up at all, what actually happened is that I was feeling sick, jiri nakeji to be frank, then we clash so I held him for support, a lokacin ko bashi bane I’ll held anyone because I don’t know where my head is”…..
Nan ta bashi exactly labarin da deen ya bawa anna……
Ajiyar zuciya ya sauke yace;
“Then why didn’t you pick my calls, you were just rejecting, karshe ma kika kashe wayar”……
Shiru tayi tana tinanin yanda sukayi da deen, shi ya dinga zugata wai karta kira khaleel tinda shi be kirata ba, ashe khaleel yanata kira ba’a dauka ba, kuma dama ita tasan definitely khaleel ze kira kawai ta kasa yiwa deen musu ne……
“My phone was with siyama, inaga ta nemi bata ganni bane ta kashe wayar, this is all misunderstanding khaleel, it’s never what you’re thinking”…..
Ta samu kanta da kin gayamasa gaskiyar wanda ta bawa wayan……..
“It’s alright wifey, thanks for clearing the air, but sincerely I was so devastated, ban kara gane kaina ba after that incidence, nasan na daure na shiga mota amma bansan ina kaina yake ba, the only thing I can recall is na ganni a gidan Abby, from then I don’t know how I got here”……
Cikin tausayawa tace;
“I’m so sorry honey khal, Insha Allah irin haka bazai kara faruwa ba”….
“I trust you wifey”……
Anna dake toilet na jin duk abinda suka fada, hasalima abinda ya hanata fitowa kenan saboda taji karshen zancen, nan ta tabbatar da labarin da deen ya basu gaskiya ne tinda gashi baby tee ta sake bawa khaleel, ta kuma gane abinda ya kawo khaleel asibiti ashe shima ya gansu ne, tausayinsa ne taji ya kamata ta kuma fahimci mutum ne me raunin zuciya……..

Download>>> Anya Baiwa Ce Complete Novel 

Da sallama sudais ya shiga parlourn building din umm da aka sauki wasu baki a ciki, saida ya gaisa da kowa sannan ya tambayesu ina ilham take…..
“Tana chan dakin, wallahi mun kasa gane kanta, sumanta biyu yanzu, a tafi asibiti kuma taki, gashi likitocin gidan duk basa nan”…….
Daya daga cikinsu ta basa amsa……
Tashi yayi ya nufi dakin da akace tana ciki, knocking yayi tare da sallama aka basa izinin shiga sannan ya shiga……..
Tana kwance kawayenta sun zagayeta sai fifita suke mata ga ac ga komai amma sai gumi take kamar wacce ake zubawa ruwa, fadi take;
“Allah ya isa ban yafe ba, saboda budurwarsa ce shiyasa yabi bayanta aka siya balango da kudina, wallahi bazan yafe ba”…….
Daka mata tsawa sudais yayi yace;
“Dalla rufe mana baki shashasha mara hankali, inda shi yazo yaji kina wannan maganar da bakinki zakice akaiki asibitin da kika hana a kaiki kuma wannan magana tamkar a kunnensa”……
Sai ga ilham ta duro a guje, har kasa ta duka tana kuka tace;
“Dan Allah dan annabi ka min rai yaya sudais, ka taimakeni karka fadamasa dan Allah”…..
Harararta yayi yace;
“Dalla chan matsa, ashe karyar iskanci kikeyi, da wa kike yiwa Allah ya isa toh?”….
“Wallahi bada shi nake ba, da kaina nake”…..
Dungure mata kai yayi yace;
“Kedai kika sani, bani account number dinki”..
Jiki na rawa ta karanto masa, a take ya mata transfer din 1m dinta amma babu waya balle taga alert tasan kudi ya turo mata………
“Toh dama shi ya turoni, yace in baki last warning, idan kika sake kika kara irin wannan shirmen wallahi baze biya ba, sannan yace ki tattara ki tafi gidanku a yau dinnan, idan kika sake yazo ya sameki kuma kinsan sauran, ni na gama nawa”….
Ya fada yana zaro wayarta daga cikin aljihunsa sannan ya cilla mata….
Wani irin ihu tayi ta tashi ta rungumeshi tsabar farinciki tace;
“Nagode yaya sudais, wallahi bazan kara ba, yanzu kuwa zan wuce gida”….
Tureta yayi daga jikinsa ya fita daga dakin……
Kiran number Saif yayi da niyar ya fadamasa ya kammala aikensa sannan ya tambayesa yanda ake ciki, amma wayar tayita ringing ba’a dauka ba…….
Dama dazu ne bayan sun gama magana akan baby tee suna jiran kiran bappa deen ya gayamasa gaskiyar abinda ya faru tsakaninsa da baby tee, game sukayi ita da ilham, ya dai boye masa dalilin dayasa ya bata hadin kai sannan ya bashi wayar ilham daya karba a hannun siyama ya kuma sa aka mishi transfer yace ya kai mata wayar ya kuma bata kudin saboda in yaje da kansa yasan ze iya marinta sannan ya fada mishi ya bata warning ya kuma ce tabar gidan……
Fita yayi daga building din umm ya koma ya shiga na mami, karo sukayi da dad a compound din gidan wanda zuwansa kenan shima…… Da ladabi sudais ya duka har kasa ya gaishesa sannan ya sanar dashi su mami basanan sunje dubiya wai wani khaleel bashida lafiya, tambayarsa yayi asibitin da sukaje yace masa besani ba saidai ya kirawosu yaji, godiya ya masa ya koma cikin mota…..

Download>>> Yar Harka Romantic Hausa Novel – Aihausanovels

Number mami ya fara kira tanata ringing ba’a dauka, dama kuma yasan bazata dauka ba saboda kullum sai ya kirata yasan tana gani kuma amma bata taba dauka ba, mai da alakar kiransa zuwa number deen yayi, Allah ya taimakesa bugu biyu ya dauka, gaisawa sukayi sannan ya sanar masa yazo gida ance basanan duka ya kira mami kuma bata dauka, saida deen ya juya ya kalli mami yaga wayarta a hannunta, ya daga kafada ya gayamasa inda zasu, mu hadu achan kawai dad yace sannan ya kashe wayar…….
Deen na sauke wayar ya dan juyo ya kalli mami yace;
“Dad ne ya kirani yanzu, wai yanata kiranki bakya picking, why?”……
Banza tayi dashi badan bata da amsar da zata basa ba saidan mutanen dake cikin motar dake a mota daya suka tafi, a hakanma bashi yaci amma zasu gamu sai ya gayamata uban me yasa zeyi questioning dinta akan rashin daukan kiran ubansa a cikin mutane…….
Murmushi umm tayi a kunne ta rada mata;
“Ai gaskiya ya fada nima ido kawai na zuba miki, so why’re you not picking his father’s call?”……
Cikin sigar data mata magana ta maida mata da;
“Zamu gamu dashi! Zeci ubansa wallahi! And haka muka tsara dake? Naga kamar kun shirya?”……
“Wannan tsarin ke kika san shi, ni bazan iya fushi da da’na ba”……
“Shikenan dama in aka hada abu dake ai sai a slow, Allah ya kyauta”…..
Dariya umm tayi tace;
“Ameen hajiya justice”…..
Dauke kai mami tayi tana harararta……
Shiru ne ya biyo baya suka cigaba da tafiya in silence…….
Saida suka kusa isa barrack din sannan Abby yayi breaking silence din da basu labarin halin da khaleel ya shigo gidansa da yanda ya suma har ya kaishi asibiti……
Sosai suka jajanta abun har abun yaso bawa deen haushi saboda yanda suketa zuguiguita lamarin……
Isarsu barrack din yayi daidai da zuwan dad da securities dinsa, gaisawa sukayi cikin mutunta juna sannan suka shiga tare…..
Direct isolated area din da aka kai su daddy suka nufa, suna zuwa aka kaisu visiting arena suka zauna jiran a fito dasu daddyn khaleel………
Ana futo dasu gabadayansu suke mike a razane babu shiri……..

Back to top button