Fitacciyar jarumar kannywood Rahma Sadau ta bayyana yadda ta tsallake rijiya da baya a harin jirgin kasa a Kaduna.
Jarumar ta bayyana cewa sai da su ka shirya tsaf ita da yar uwar za su hau wannan jirgin amma sai wani uzuri ya gitta har su ka yi latti, lamarin da ya jirgin ya tafi ba tare da sun samu shigarsa ba.
Sai dai kuma jarumar ta bayyana cewa abun ya rutsa da su ta wata hanyar tunda akwai yan uwanta da ke cikin jirgin.
Rahma Sadau ta bayyana cewa ya kamata gwamnati ta maida hankalinta wurin baiwa talakawan ta tsaron da ya dace domin rayukan su da dukiyoyinsu na da matuƙar muhimmanci.
Daga karshe dai jaruma Rahma Sadau ta yi kira ga talakawan Nigeria da su gaggauta dauko katin zaben su su aje shi a kusa da su domin yin amfani da shi wajen zaben shugabannin da suka dace a zaben 2023 mai karasowa.
A cewar ta hakan ne kawai zai basu damar nemawa kawunansu salama da kuma shugabanci na gari. Har wa yau kuma jarumar a bukaci yan kasa da su bi cancanta wajen zaben 2023 ba akida ko jami’ya ba.
Wannan dai ya biyo bayan wani bom da aka sanya a kan hanyar layin dogo da ya taho daga Kaduna zuwa Abuja wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane da yawa inda wasu da dama suka yi raunuka. A yanzu haka dai wadanda abun ya rutsa da su na asibiti na amsar kulawa a hannun likitoci.
Muna fatan wannan ya kasance karo na karshe da wasu tsageru za su samu damar yiwa mutane irin wannan taaddancin. Domin jin ra’ayin masu bibiyar shafin mu na na AiHausanovels.com.ng
Muna kallon dukkan ra’ayoyin ku a ƙarƙashin comment section na wannan shafin mai albar, mun gode da kasancewar ku a tare da mu, mu huta lafiya.