Halysaah Page 95 By Khaleesat Haydar
HALYSAAH PAGE 95…Aunty farina na zaune tsakar gida da umma da malam Ali,umma dai tayi tagumi ko bakin magana bata dashi idanuwanta duk sun kumbura saboda kuka,Aunty farida sai jira take malam Ali yace masu ga yanda sukayi da maimartaba a waya amma yaki cewa komi,Nenne ta fito daga cikin gida tana rike da wayar aunty farida Don har ita sai da maimartaba yayi magana da ita,Nenne tace,” inba adalin sarki ba waye zaiyi haka sai kunga yanda ya ajiye izza da girman kai irin ta sarakuna yana ban hakuri,har saida kunya ta kamani wallahi,yana bani hakuri ina basa hakuri,to ni ai inba shegiya bace ai dole In hakura,Amma zance na gaskiya na tsorata da lamarin uwar Ahamad,taban tsoro sosai banga alamar akwai abun arziki a tattare da itaba,naji kuma ina tsoron auren nan,ace khaleesat tayi auren farko bataji dadi ba nabiyu ma yazo mata a haka? Kunga ai bazamu bari ayi na biyu ba yarinya da karancin shekarunta tayi ta walagigi gidan aure har sai wani cutar yaje ya sameta,gaskiya nidai nasha jinin jikina gaskiya da auren nan gara kawai duk a hakura dan babu alamar alkhairi a cikinsa,tunda har uwar sa ta nuna bata sonta bazata taba sontaba har abada kuwa, sannan fa duk a yau mukejin ashe ba ita daya ma ashe zai aura ba,harda yar uwarsa budurwa itama jinin sarauta kuma duk a rana daya za a daura auren,Ina khaleesah ina kishi da jinin sarauta inba dai hallaka akeson jefa yarinyar ba ga uwar miji tun baayi auren ba ta nuna bata sonta gaskiya jikina ya mutu,akan abun duniya bazamu sake salwantar da rayuwar er mu ba” Cikin sanyin murya umma tace” Damani auren ya fice man arai gaba daya Nenne,Hakura zatayi Allah ya fiddo mata da wani mijin kawai Don babu Alkhairi a wannan auren dama aikowa tayi akazo da sauki akan ta tako da kanta tazo gidannan tayi abinda tayi gwara a hakura kawai…..Nenne ta katseta da sauri tace”Ai bazamu bari wannan ya fito daga bangaren mu ba Zahara’u duba da yanda sarki duk yabimu yayi mana magana ta waya, in bama shi dinba wane sarkin ne zaiyi haka? Ai iyaka saidai yasa na kusa dashi su kiramu su bamu hakuri a gantale Amma badai yayi waya damu muji muryarsa ba,Ki duba lokacin daya dauka yana waya da farida,Sannan yayi waya da malam Ali ma,nima kuma yayi magana dani duk yana kokarin sanyaya mana zuciya akan tijarar da er iskar mata tazo har gida ta mana,kinga ko Don wannan bazamu yarda ace daga wujen mu mukace mun fasa bada yarinya ba,nasan kuma wannan matar er bariki ba hakura zatayi ba gwara ace ita ta ruguza zancen Auren da kanta da dai ace mu muka ruguza,Sam Ahamad baiyi dacen uwa ba gashi yaro mai hankali da nutsuwa ga kirki amma uwa er duniya,mu bazamuce komai ba Albarkacin mai martaba saidai in su suka ce sun janye batun auren shikenan yazo ma kowa gidan sauki ,Aunty farida ta sauke ajiyar zuciya tace”hakane Nenne” Nenne tace Atoh,kai meye shawararka malam Ali?Ana magana sai kayi shiru kamar wani bare a cikin mu,sai a sannan malam Ali ya daka kai a karo na farko yace” Shawara ta shine zuwa gobe ko jibi mu tattara mu koma mariri tunda har an kusan gama gyaran da akeyi gidana baaba,idan mun koma to koma me zai biyo baya me sauki ne….. A mugun fusace Nenne tace “Toka tattara ka koma mana Ali wani ya rike ka ne? Mudai muna nan babu inda zamuje tunda bamu bude baki mun roki yaron nan ya siya mana gida ba,kuma takardun gida na hannun mu balle ace zaa kwace gidan,ko kuma mu siyar da gidan mu tashi mu koma wani wajen mu siya ba shikenan ba,Amma wallahi babu shegen daya isa ya rabamu da gidannan,ko shi Ahamad din bazai fara tunkarar mu da zancen gida ba tunda saboda Allah yayi kuma jinin marigayi sarki Ahmadu na yawo a jikinsa,mahaifinsa kuwa kowa ya shaida mutumin arziki ne “Nenne na kaiwa nan ta Mike rai bace tana kallon Aunty farida tace” Taso mu shiga ciki muyi shawara parida ” Ali da matarsa in kace zaka zauna cikinsu kayi maganar Arziki ranka ne kawai zai baci a banza,ban taba ganin sumbudaddu matsorata irin su ba “washegari har gida maimartaba ya tura akaje ba malam Ali hakuri akan abinda mami taje tayi,Shidai malam Ali Allah ya sani he is not longer comfortable with his daughter getting married to the royal family, Sam hankalinsa bai kwanta da auren ba amma nauyin me martaba yasa ya kasa nuna hakan,gashi wanda sukazo basa hakurin sunce ranar jumaar nan zaa daura auren,shi kansa me martaba ya sanar masa da hakan a maganar da sukayi jiya,gaba daya ya rasa ta inda zai bullo ma lamarin gashi yasan nenne bazata taba tsayawa ta fahimcesa ba balle suyi abinda ya kamata dan ceto rayuwar Khaleesat,baya fatan abinda ya samu ersa a baya ya sake samun ta yanzu,bayan wakilan me martaba sun bar gidan wajen karfe takwas da rabi na dare ya dau wayarsa ya zauna tsakar gida yayi dialing number khaleesat,yana fara ringing khaleesat dake shafe shafe bayan tayi wanka ta daga Kiran,bayan ta gaishesa ya amsa yace “yaushe zaki dawo jiddah”?a hankali khaleesat tace Nenne tace kada su bari in dawo yanxu amma ni ina son ranar Friday indawo ,malam Ali ya danyi shiru sai kuma yace”kina jina jiddah?tace inaji baba,yace farida sun fada maki abinda ke faruwa kuwa?Sosai khaleesat taji gabanta ya fadi ,ta ajiye kwalbar turaren hannunta tayi shiru ta kasa cewa komai,Har saida babanta yace “hello ta kifta ido cike da karfin hali tace “inaji baba,baa gaya min komi ba meke faruwa baba,?Cikin nutsuwa malam Ali ya fara sanar mata duk abinda mahaifiyar Jay tazo har gida tayi,babu abinda yayi mata excluding,daga karshe ya sauke ajiyar zuciya yace you know why I decided to call and inform you about this jiddah?Saboda nasan Nenne zatace kar a sanar maki,Ni kuma abinda yasa nike gaya maki ina son kiyi deciding duk abinda kikaga ya dace da rayuwar ki tunda ba wani zai maki zaman auren dashi ba jiddah,quite alright I knew Ahmad is a good man but come to think of the life you may find your self in with his mother as your in-law,Ni ina jin nauyin sarki ina matukar jin nauyin Ince bazan bada auren kiba beside har gida ya aiko aka ban hakuri akan abinda ya faru bayan Kiran da yayi min ta waya ,bazan iya ja in ja da me martaba ba jiddah amma ina jiye maki wannan auren,hankalina bai nutsu da auren ba bana son abinda ya faru dake a baya ya sake maimaita kansa saboda muna jin nauyin kwatar maki yancinki for the second time kamar wancan lokacin,sarki ba mutumin da zaa tsaya ayi ja in ja dashi bane Don girma da martabarshi ya wuce ayi masa haka koda kuwa bai turo wakilansa ba iya ta waya kawai mukayi magana,balle bayan munyi magana ta waya still ya sake aikowa har gida a bamu hakuri …..tunda ya fara magana khaleesat ke kallon kofar dakin aunty murja babu ko kiftawa dan mutuwar zaune rayi kawai a inda take,sosai maganganun babanta sukayi mugun girgizata taji wani sanyi na shigarta wannan shine dalilin da yasa taketa Kiran housemate baya picking call dinta tun jiya kenan,har take tunanin ko wani laifin tayi masa bata sani ba,daga karshe taji muryar babanta yace hope kin fahimceni jiddah?da kyar ta nemo muryarta dako fitowa sosai bayayi tace “Toh bana,yace kiyi abinda kikaga ya dace for your betterment dear,I want nothing but the best for you,nobody is in the rightful position to decide for you for the second time daughter “kai ta gyada mashi cike da karfin hali har ya katse wayar,sannan taji wasu hawaye masu zafi sun zubo idonta,whatsapp dinta ta bude ta shiga DM din Jay cikin minti daya ta gama rubuta masa abinda zata rubuta hannunta na rawa tayi sending,sannan ta kashe data ta kwanta hawaye masu zafi wasu na bin wasu a kuncinta, ji tayi kamar komi na duniyar sun tsaya mata cak tsabar confussion ,ko minti biyu baayi ba saiga kiranshi ya shigo wayarta,silencing Kiran tayi bata daga ba sau uku yana kiranta bata picking ba daga karshe tayi switch off din wayar gaba daya tana sheshshekar kuka tana jin zuciyarta na mata zafi,karfe goma da rabi na dare aunty murja ta gama shimfide yaranta da sukayi bacci tun dazu,ta tafi ta dauro Alwala ta dawo dakinta ta kashe fitila zata kwanta saiga wani Almajiri yana sallama bakin kofar dakinta tace waye? Yace wai Ana sallama da halysah a waje,aunty murja tace khaleesat da daddaren nan? Wai inji wa? Almajirin yace a mota yake,Duk khaleesat najin aunty murja da Almajirin amma ko motsi batayi ba,Aunty murja ta dau hijab tasa ta fita Don ganin wanda ke Kiran khaleesat a wannan lokacin bayan minti uku sai gata ta dawo dakin tana tashin khaleesat ,tace khaleesat tashi Ahmad na jiranki a waje,meyasa bakice masa yazo da wuri ba yanzu ai dare yayi khaleesat taki juyowa tace, na Riga nayi bacci ace nayi bacci,Anty murja tace haka nan zaki daure ki fita amma karki dade ,kar babansu ya dawo ya tarar dake a waje kije yace sako ya kawo maki,khaleesat taki tashi aunty murja tafi minti biyar tana fama da ita amma fir taki tashi,har saida kishiyar Aunty murja ta leko dakin tasa baki Don tana jinsu,khaleesat ta tashi zaune da kyar ta sunkuyar da kanta Don bata son suga idonta da yayi ja saboda kuka,banda tanajin nauyin kishiyar Aunty murja da babu abinda zai sa ta tashi harta fita kofar gida,hijab dinta ta saka har kasa akan kayan baccin jikinta Aunty murja na mika mata torchlight taki amsa ta fita daga dakin kanta a kasa ta isa kofar gidan ta tsaya daga jikin motar tana jinsa ya bude motar ya sauka sannan ya zagayo inda take tsaye yana kallonta ita dai wani wajen daban take kallo sai kuma ya bude mata back seat pleadingly yace pls ki shiga Halysah ita dai taki ce masa komi kuma taki kallonsa lallabata ya shigayi yana hadata da Allah ta shiga motar yafi minti biyar yana Abu daya ita dai taki cewa komai hawaye na sauka a idonta ganin anata wucewa Ana kallonsu yasa kawai ta shiga motar ya kulle sannan ya zagaya ya shiga ta dayan side din motar ya ajiye wayarsa ya matsa kusa da ita yana kallonta cike da damuwa yace why will you send me such txt halysah?da wanne kikeson inji pls? Meyasa zaki man irin wannan message din? Ta sauke idonta tana jin wasu hawayen na zubo mata kasa daurewa tayi kawai ta fashe da kuka sosai nan da nan ya kara rikice mata yace stop this pls halysah why are you doing this to me? Kuka kawai take taki ce masa komai taji ya jawota kusa dashi yace halysah kiyi min Alkawari ko ban aureki in this short period of time ba bazaki taba auren wani da namiji ba kiyi min wannan Alkawarin pls halysah ni kuma nayi maki Alkawarin zan aureki no matter the circumstances surrounding our marriage,koba yanzu ba ni nasan zan aureki insha Allah halysah nasan akwai sanda mamina da kanta zata amince man in aureki and this is not going to take long yanzu ma ban cire rai ba am hoping we will get married cikin satinnan insha Allah dan Allah kada ki bari a rabamu halysah I don’t know what will become of me idan na rasaki kuka kawai khaleesat takeyi ta kasa cewa komi tana jin zafi a ranta kamar zai mata kukan shima yace say something pls halysaah kice wani Abu dan Allah,bata ankara ba kawai sai gani tayi ya rungumota jikinsa cikin zafin name, nan da nan ta hadiye kukan da take ta fara turasa tana son kwace kanta daga jikinsa amma yaki sakinta bata kara gigicewa ba saida taji yana lalubanta through hijab din jikinta at the same time attempting to kiss her jikinta ya dau rawa tana kauda kanta tana turasa tace pls housemate ka bari stop it pls,sosai khaleesat ta tsorata ganin da gaske yake jikinta na rawa tace walahi zan maka ihu kiris ya rage yayi kissing dinta wayar sa ya fara vibrate slowly ya saketa daga rikon da yayi mata Trying to control his breathing ya juya yana kallon wayarsa yaga Ajay ke kiransa ita kanta tasan ba karamin ceton ta me Kiran yayi ba a wannan lokacin Don badan Kiran ba babu abinda zai hana Jay kissing dinta deeply ko ina na jikinta rawa yake ta matsa ta koka karshen seat din motar tana zare ido takai hannu ta bude motar yana ganin haka yayi saurin miko hannun sa zai rikota kar ta fita amma tuni ta fice daga motar ko waigawa batayi bata hada harda gudu ta shige cikin gidansu aunty murja jikinta na rawa kife wayar Jay yayi bayan Kiran Ajay ya sake shigowa ,yafi minti goma zaune bayan motar har sai da yadan samu nutsuwa sannan ya sauka ya koma driver seat ya tada motar.washe gari Jay na dawowa masallaci ya tarar da mami zaune a bedroom dinsa sau daya ya kalleta ya sauke idonsa ya karasa cikin dakin ya gaisheta ba tare daya kalleta ba ta amsa tace ka zauna ina da magana dakai jawwad,zaunawa yayi baice komai ba. jawwad,zaunawa yayi baice komai ba mami tace jwwad ban taba tunanin akwai ranar da zaizoba Ince maka bana son Abu ka kafe kace sai kayi abunnan ba saboda me martaba na goya maka baya wanda hakan da zaiyi a banza tunda nidai nasan ba son tsakani da Allah yake makaba ,da yana sonka son gaskiya bazai ware nasa dan ya gwadama duniya shine asalin jininsa sannan magajinsa ba,banyi tunanin akwai ranar da zaka nuna ban isa dakaai ba bayan duk sadaukarwar danayi a kanka domin in ganka cikin farin ciki da walwala na toshe maka duk wata kafar da zaisa kayi maraicin mahaifinka na jajirce na zamar maka uwa na zamar maka uba sakayyar da zakayi man kenan After all this ahmad?Jay ya daka kai a karo na farko ya kalleta cike da karfin hali yace ,mami sorry to say amma ban gane me kike nupi ba,ni nasan baki nuna man bakison aure na da yarinyar ba kin nuna man kin amince kin kuma yi min fatan Alkhairi kin min addua har yanzu akan hakan nike, All I know mahaifiyata ta amince min da maganar auren Dana kawo mata har ta min fatan Alkhairi,ban kuma san reason dinki na nuna ma me martaba da sauran mutane baki amince ba bayan ni kin nuna man you are okay with that har mun gama magana ,so ni har yanzu akan amincewarki nike mami maybe kina da dalilin ki na nuna musu baki amince ba shiyasa hakan bai dameni ba dan nasan komi da dalili kike yinsa,amma dani dake munsan kin amince da batun auren so yanzu kuma ban fahimci maganar da kike minba in har kinzo bangarena ne domin ki canza maganar da kikayina farko akan amincewarki then I will be highly disappointed and heartbroken don ban sanki da magana biyu ba.infact I don’t even know how I will take it Don harna fara jin zuciyata na man ciwo yanzu even though I don’t want believe abinda ya kawoki kenan ki canza maganar da kikayi a farko saboda na yadda dake mami na yadda da duk maganar data fito daga gareki baki taba man magana kin canza maganar ba ko bayan shekara nawa ne duk abinda kika nuna man kin amince to har abada kin amince da abun nan and nothing can ever change that,shiru mami tayi tana kallonsa ganin yanda ya daureta da jijiyar jikinta after some seconds ta sauke wani boyayyar ajiyan zuciya tayi kasa da murya tace “kasan me nikeso dakai jawwad? Ya daga kai ya kalleta taga har idanuwansa sun canja launi cikin kwantar da murya tace kayi hakuri jawwad tace kasan duniyar nan babu wanda ya tsani yaga bacin ranka ko kuma ya ganka cikin damuwa sama dani,yanzu ma bazan yarda injefa ka cikin damuwa ba amma ina son I baka shawara kuma nima I will be highly disappointed idan idan baka dau shawarar nan da zan baka ba na kuma yi Alkawarin shawarar nan bame cutar dakai bane to ya tauyeka ya hanaka abinda kakeso in anyway,Amma fa dole kadau shawarar nan tawa,Jay dai kallonta kawai yake babu ko kiftawa yana jin zuciyarsa na bugawa……
