Halysaah Page 58 By Khaleesat Haydar
HALYSAAH PAGE 58…Safiyyah ta gama saka Jacket dinta da neck warmer tana kallon Khaleesat da ta kasa tashi daga inda take zaune tace “C’mon Khaleesat, yana fa waje yana jira, and the weather is very cold outside, don Allah ki tashi mu je” Da kyar Khaleesat ta tashi tana jin bugun zuciyarta na tsananta ta dau Veil din Abayan jikinta ta yafa kanta a hankali, gaba daya jikinta a sanyaye yake don bata san ta yaya zata fara hada ido da Jay ba, Safiyyah na kallonta tace “Baza ki saka rigar sanyin ki ba?” Khaleesat ta girgiza mata kai kawai, Safiyyah tace “Saboda room heater ne fa yasa kike jin kamar ba sanyi sosai a garin, amma wallahi azababben sanyi ake a waje idan kika fita” Ita dai Khaleesat bata ce komai ba don bata ma san me Safiyyah ke cewa ba, duk tunaninta ita dai da wani idon zata kalli Housemate dinta, Safiyyah ta tabe baki ganin Khaleesat taki tanka mata kamar ma bata san me take cewa ba, Safiyyah ta nufi kofa Khaleesat ta bi bayanta tana tafiya a hankali kamar mara lafiya, a haka suka fito parlor, Safiyyah bata ko kalli Surayyah dake zaune parlor tana ba yaronta abinci ba ta nufi kofar fita, ita dai Khaleesat na bin ta a baya walking slowly fuskarta dauke da damuwa, Surayyah ta bi su da wani shegen kallo har suka fita daga parlon, Khaleesat na hada ido da Housemate dinta dake jingine da motarsa ya rungume hannunsa taji wani kuka na neman taho mata from no where, amma ta dake ta sunkuyar da kanta tana biye da Safiyyah har suka iso dai dai inda yake tsaye, sau daya ya kalli Khaleesat ya dauke idonsa ya mayar kan Safiyyah dake gaishesa, ya amsa gaisuwanta da murmushi fuskar sa yace “Ya hanya?” Safiyyah tace “Hanya Alhamdulillah” Ita dai Khaleesat gefe ta koma ta tsaya har sannan ta kasa hada ido da shi tana wasa da veil dinta, nan kuma daurewa kawai take kar ta fashe da kukan dake cin ta, bayan sun gama gaisawa da Safiyyah, ya juya ya kalli Khaleesat for the second time, calmly yace “Housemate” Kamar jira take ta fashe masa da kuka sosai, ya sauke idonsa yayi shiru, after some seconds… walking slowly ya karasa har inda take tsaye yayi kasa da murya yana kallonta yace “Ina Jacket din ki?” Ta kasa cewa komai tana kuka a hankali tana girgiza masa kai, cire tsadadden rigar sanyin jikinsa yayi yana kallonta ya zaga ta bayanta yace “Wear this, the weather is cold” Ta gyada masa kai kawai wasu hawayen na sauka idonta ta amshi Jacket din nasa ta saka, lokaci daya kamshin turarensa da ta dade bata ji ba ya cikata ta ko ina ga kuma warmth din jikinsa from the Jacket, ji tayi kamar an yaye mata duk wani damuwar dake tunkushe a ranta, Ita dai Safiyyah na tsaye tana kallonsu, har cikin ranta take jin tausayin Khaleesat don tana jin ta ne kamar er uwarta ta jinin, Jay ya cire neck warmer din wuyansa ya daura mata kan Jacket din, ita dai Khaleesat ta kasa barin su hada ido, taji daddaden kamshin turarensa na kara mata wani irin nutsuwa da relieve, Ya juya ya kalli Safiyyah yace “Za mu je tare da ke can apartment din nata yanxu ko?” Safiyyah ta sauke ajiyar zuciya tace “Ohk, let me get her luggages” Daga haka ta juya ta koma cikin gida, ya bude ma Khaleesat gaban motarsa yana kallonta, ita dai ta kasa hada ido da shi wasu hawayen na taruwa idonta ta shiga motar ya kulle gently, after some minutes Safiyyah ta fito da akwatin Khaleesat guda biyu ya bude booth ya saka a ciki, Safiyyah tace “Let me get the rest” Daga haka ta juya ta koma cikin gidan ta dauko sauran kayan su ma ya amsa ya saka a booth, Safiyyah ta shiga back seat sannan ya zaga ya bude driver seat ya shiga, the ride was so silent ga snow da aka fara yi, after almost 20 minutes suka iso sabon Apartment din da Jay yayi renting ma Khaleesat, parking yayi a garage din apartment din yayi shiru, sai kuma ya jinginar da kansa da driver seat ya lumshe ido bayan ya tuna makullin apartment din na can gida ya bar sa, after some seconds ya ɗan shafa kansa yace “Sorry… i think na mance makullin apartment din a can gidanmu” Reverse ya fara yi bayan ya fita garage din ya dau hanyar gidansu, ita dai Safiyyah tayi murmushi kawai bata ce komai ba, dai dai sanda wayarta ya fara vibrate ta duba taga Mustapha ne ke kiranta, hade rai tayi, tayi silencing kiran sannan ta kife wayar a cinyarta, wato ya dawo yaga bata gida shi ne zai fara doka mata kira, Jay na isa gidansu yayi parking a waje ya juya ya kalli Khaleesat da tayi nisa tunanin da take, yace “Let me get the keys Housemate” Bata bari sun hada ido ba ta gyada masa kai kawai, ya bude motar zai fita, ta kalli snow din dake sauka sai kuma ta kallesa, da sauri ta fara kokarin cire Jacket dinsa dake jikinta tace “Should i give you the Jacket? Naga akwai sanyi” Ya juya ya kalleta, sai a sannan suka hada ido all this while, taji kamar kasa ya bude ta shige tayi saurin sauke idonta, ya ɗan yi murmushi yace “Don’t worry, i will get another one idan na shiga gida yanxu” Daga haka ya sauka daga motar ya shiga gidansu. Bayan kusan minti goma sai ga shi ya fito daga cikin gidan yana sanye da wata rigar sanyin, Khaleesat dai kallonsa kawai take, ganin ya tsaya bakin gate din gidan nasu yana kallon direction daban yasa ta kalli direction din da yake kallo, sunkuyar da kai tayi bayan ta hango Ajay yana tahowa tare da katon karensa Legend yana rike da Leash din karen, Safiyyah tayi kasa da murya tace “That is Ajay, and ya kamata ki gaishesa gaskiya Khaleesat” Khaleesat ta ɗan kalli Safiyyah, a hankali tace “Baza ki gane ba Sophie wallahi kunya nake ji” Safiyyah tace “To ya za ki yi? Dole dai haka zaki ajiye kunyan ki sauka ki gaishe sa, ni dai nasan baxai taɓa barin Jay yayi duk wannan hidimar da yayi maki shi kadai ba, tunda kan su a hade yake, nasan dole Jay zai yi shawara da shi before anything, Kuma tare za su yi komai…” Khaleesat ta kasa cewa komai amma har cikin ranta she is so ashame of speaking to him, har yau maganganun da Abdul yasa tayi masa ta waya na yawo a kanta, Safiyyah ta hade rai ganin Ajay ya kusa inda Jay ke tsaye tace “Pls Buckle up kiyi abinda ya dace Khaleesat, ni na tsani wannan halin kauyancin da kike yi wallahi, to meye a ciki gaishesa fa kawai zaki yi, ai ko ba komai kokarin da shi ma yayi maki ya kamata ki gaishe sa, abinda ya faru ya riga ya faru so forget that and do the needful” Jiki a sanyaye Khaleesat ta kai hannu zata bude motar, amma Ajay ko kallon inda suke bai yi ba ya wuce Jay dake tsaye yana jiransa yayi shigewarsa cikin gida, Jay ya bi bayansa, a sanyaye Khaleesat ta fasa bude motar ta juya tana kallon Safiyyah, Safiyyah ta sauke wani ajiyar zuciya tace “He is still angry at what you did to them, nasan zai huce definitely” Ita dai Khaleesat tayi shiru bata ce komai ba, after some minutes sai ga Jay ya fito daga cikin gidan ya bude driver seat ya shiga yace “Sorry for keeping u waiting, makullin apartment din na aljihun jacket dina ne, and Ajay wore the Jacket out for a walk” Safiyyah na murmushi tace “It’s fine” Ita dai Khaleesat tayi shiru bata ce komai ba, wajen karfe biyar da rabi suka iso sabon Apartment din, ya kashe motar yana kallon Khaleesat a hankali yace “This is ur new apartment Housemate, i hope you will love it” Daga haka ya bude motar ya sauka, Safiyyah ma ta sauka tana kallon gidan tana murmushi don sama da kasa ne, Khaleesat ta goge hawayen dake makale idonta sannan ta sauka daga motar, bude masu kofar apartment din Jay yayi ya jira suka fara shiga sannan shi ma ya shiga, yayi switching din light din parlon da Heater, Safiyyah na murmushi tana bin parlon da kallo ganin yafi na tsohon Apartment din girma tace “Waow, this is soo beautiful” Jay ya zauna kan kujera yana duba wayarsa dake vibrate alamar kira, Safiyyah ta bude kofar da ta gani a parlor taga kitchen ne, ita dai Khaleesat na tsaye bayan kujera tana kallon Jay ta kasa cewa komai, Safiyyah ta fito daga kitchen din ta nufi sama zata duba dakunan gidan, after some seconds Jay ya gama sending message din da yake a wayarsa ya juya suka hada ido da Khaleesat, sauke idonta tayi tana wasa da gefen Veil dinta, Calmly yace “Housemate” Da kyar tace “Um” Ya mike ya dawo gabanta ya tsaya yana kallonta, a hankali yace “You like the new apartment?” Ta gyada masa kai tana kokarin ganin bata fashe da kuka ba, bai sake ce mata komai ba don yana kallon fuskarta yasan kuka zata fara masa, Safiyyah ce ta sauko downstairs tace “Ya Jawwad wallahi gida yayi kyau Maa sha Allah, Allah Ubangiji ya saka da alkhairi yasa kafi haka, my frnd is really grateful ba ma ta da bakin yi maka godiya shi yasa nake magana on behalf of her, mun gode sosai, Allah Ubangiji ya kare ka da sharrin mahassada, thank you so much Housemate we are really grateful” Ɗan murmushi yayi bai ce mata komai ba, Khaleesat ta goge hawayen da taji ya silalo idonta, Safiyyah tace “Toh ni zan tafi yanxu, yayana sai doka min kira yake, ya kirani yafi sau goma ban dauka ba” Jay yace “Ohk, to bari in yi dropping din ki” Da sauri Safiyyah tace “A’a wallahi ba sai ka ba kanka wahala ba Yaya Jawwad, har nayi order din Lyft gashi nan zuwa” Yace “Ohk then, my regards to everyone back home Safiyyah” Safiyyah na murmushi tace “In sha Allah” Sai kuma ta kalli Khaleesat tace “Toh mu je ki rakani kawata” ta kama hannun Khaleesat suka fita daga parlon, suna barin apartment din Safiyyah ta kalleta tace “If you like kar ki dena wannan kukan ki bude baki kiyi masa godiya sosai, shi yasa ma nace ki rakani don nasan halinki in kika fara kuka ba lallai ki masa godiya ba, in mutum yayi kukan sau daya ba shikenan sai ya rungumi kaddara ba yayi abinda ya kamata yayi move on, amma ke kiyi ta kuka kamar me takaba, i understand you are lost of words amma kiyi composing kanki kiyi appreciating dinsa plss, wallahi ban taɓa ganin mutum with kind heart like Jawwad ba, kuma shi tsakani da Allah yake abun sa ba don komai ba” Khaleesat ta fashe da kuka muryarta na rawa tace “I don’t know where to begin Safiyyah, ban san ta inda zan fara masa godiya ba, i am just confuse” Safiyyah ta rungumeta tana patting bayanta a hankali tace “I understand Khaleesat, i understand you, nasan you are confuse, but just start from anywhere, tell him anything that means appreciation zai fahimce ki” Khaleesat ta gyada mata kai hawaye masu zafi na sauka idonta, a haka Lyft din Safiyyah ya karaso, Khaleesat ta kamo hannunta da kyar tace “Thank you for everything Safiyyah, thank you for always being by my side through thick and thin, thank you for being supportive, nagode Allah ya saka da alkhairi” Tana magana hawaye na zuba idonta, Safiyyah ta hade rai tace “C’mon Khaleesat, ni kar ki sake min godiya, don na dauke ki tamkar sister din da bani da ita ne, i care so much about you” Safiyyah ta zame hannunta ta bude bayan motar ta shiga ta kulle kofar sannan ta daga ma Khaleesat hannu, kai kawai Khaleesat ta gyada mata tana share hawayen da yaki tsaya mata sannan ta juya tana tafiya a hankali ta koma Apartment din, tana bude kofar parlon Jay ya juya ya kalleta sai kuma ya ci gaba da danna wayarsa, walking slowly ta nufesa har inda yake zaune ta durkusa kasa tana kallonsa, Kafin tace komai ya dakatar da ita ba tare da ya kalleta ba yana magana softly yace “I don’t want ur thanks Khaleesat, bana bukata, ba don ki gode min nayi duk abinda nayi ba, nayi ne saboda Allah, nayi ne saboda kinyi deserving in yi maki, so bana bukatar godiyan ki pls, instead ki gode ma Allah” Khaleesat ta kasa cewa komai kanta a kasa hawaye na zuba idonta daurewa kawai take kar ta fashe masa da kuka, ya mike yace “Let me show you round the house before i leave” Tana goge fuskarta ta mike ta fara bin sa tana tafiya a hankali, kitchen ya fara kai ta, ita dai tana tsaye daga bakin kofa take bin kitchen din da kallo, hatta foodstuff duk ya siya mata, fridge din kitchen din ma was fully stocked up, ga cookies kala kala a kitchen din saboda yasan tana son cookies, ta kasa daurewa bata san sanda ta kamo hannunsa ba muryarta na rawa tace “Ban san ta inda zan fara maka godiya ba….” Ya ɗan bude ido cause he never saw that coming, lkci daya yayi saurin janye hannunsa daga nata, yana murmushin karfin hali yana komawa baya ba tare da ya bari sun hada ido ba yace “Nace maki bana bukatar godiyan ki, let me show you other places” Daga haka ya fita daga kitchen din, ta jingina da kofar kitchen din bayan ya fita tana kuka a hankali, sai da tayi me isarta sannan ta fito daga kitchen din tana jan kafa da kyar, tsaye ta gansa dai dai staircase yana danna wayarsa alamar ita yake jira, yana ganin ta fito daga kitchen din ya mayar da wayar aljihunsa ba tare da ya kalleta ba yace “The rooms are upstairs” Sai da ta karaso har inda yake sannan ya fara haura stairs din ta bi bayansa, ya fara nuna mata spare rooms guda biyu, sannan ya bude kofar nata dakin, calmly yace “Ur room” Ita dai tana tsaye bakin kofa tana kallon dakin babu ko kiftawa, ba abinda babu cikin dakin nan na comfortability, duvets ma manya hudu duk sababbi cikin case dinsu ta gani a dakin, the room look so beautiful sai wani sparkling yake, a hankali ta juya ta kallesa ya sauke idonsa bai dai ce mata komai ba, sai kuma ya juya ya bar bakin kofar dakin ya sauka downstairs ta bi sa da kallo, jingina tayi da kofar dakin for almost 5 mins tana kallon cikin dakin, a hankali ta juya ta bar bakin kofar dakin ta fara sauka downstairs cikin rashin kuzari, tsaye ta gansa bakin kofar fita daga parlon, yana ganin ta sauko yace “I will take my leave now Halysaah, amma dai sai jibi zaki shiga school, cause i see you look stressed” Ta gyada masa kai a hankali, yace “Ohk, here are the apartment key” Ta karasa ta karbi bunch din makullan da yake mika mata, sai kuma ta kallesa tace “Baka cire spare key ba?” Yace “A’a ki ajiye su kawai a wajen ki” Ta gyada masa kai kawai bata ce komai ba, ya bude kofar parlon without looking at yace “Text me ur Skin care set via WhatsApp” Yana fadin haka ya fita daga parlon yace “Good night Halysaah” Tana kallo ya kulle kofar parlon, after some minutes ta ji alamar tafiyar motarsa.*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u send ur evidence of payment 07087865788 👈🏻, it’s better ki ji tsoron Allah ki sauke nauyi kiyi karatunki cikin kwanciyar hankali don littafin na kudi ne, in kika karanta with no payment i owe you 500*
