Ajiya A Duhu Book 1 Page 17 Complete Novel
🅿️➖1️⃣7️⃣…….Sai da suka gama gaisawa da Shahidah sannan ta ɗan kallesa ta ce, “Yaya Yazeed ina yini”. Sai da yaja kusan minti ɗaya kafin ya amsa da, “Lafiya lau. Yaya jikin naki?”. “Alhamdullahi”.“Masha ALLAH”. Ya faɗa yana maida kallonsa ga Shahidah. “Shine aka sallameku Shahidah ban sani ba. Sai da naje asibitin yanzu akace kuna gida”. “Kayi haƙuri Yaya Yazeed anyi kuskure kam. Amma banyi tunanin zaka dawo yau bane, azatona kuma kasan da sallamar ne ma wlhy. Tunda muma munje kai musu breakfast Nene ke sanar mana ai doctor yace zai sallemeta yau, da daddare yake sanar musu.” “ALLAH ya ƙara lafiya to, ya kuma kiyaye gaba. Ina su Nenen?”. “Nene ai yanzu na tabbata suna gab da shiga Kaduna. Mijin Amal ne ya wuce dasu gaba ɗaya”. “Kai da sauri haka?. Ita Nene ko ɗan hutawa bazatayi ba”. “Aikam bazata zauna ba. A hakama dan zaman asibiti ne. Yau kam muna dawowa tace bafa zata sake kwana a garin nan ba”. Murmushi kawai yay da faɗin, “Shike nan zan sameta har gida ai. To kema sai ki shirya mu wuce da safe ko, tunda yanzu yamma dai tayi kam”. Ya ƙare maganar idonsa akan Maanal. “Ni Ammie tace ai na zauna anan”. “Anan kuma? To saboda mi?”.Shahidah ce ta bashi amsa da, “Bana zaton wani abune gaskiya. Inaga dai tana son ta ɗan ƙara murmurewa ne dan suma likitocin sunyi gargaɗi sosai akan ta huta a waje mai ƙarancin jama’a da hayaniya. Amma tana ƙara murmurewa zata dawo Yaya Yazeed”. Badan ya gamsu da bayanin Shahidahn ba ya ce, “Okay shike nan ALLAH yasa kaffara ne. Nima dai ina nan Abujan har zuwa jibi in sha ALLAHU, dan akwai abinda zanyi”. “ALLAH ya taimaka ya bada nasara”. Shahidah ta faɗa cike da girmamawa. Dan suna matuƙar giramam yazeed, koba komai suma yana girmama musu Ammien su. Su kansu yana mutuntasu, dan bazasuce ya taɓa musu wani abu na ashsha ba tun daga zamansu gidansu har zuwa aurensu. Hasalima a auren nasu ya zame musu tamkar babban yaya ne a komai. Tashi tai ta bar musu falon. Hakan yasa shi tashi ya koma kujerar kusa da Maanal shima. Cike da kulawa murya can ƙasa ya ce, “Baki jin komai dai zuwa yanzu?”. Kanta ta jinjina masa alamar eh. “Alhamdullahi haka ake so ai. Nasan kece kikacema Ammie baki son komawa KD ko?”. Cikin marairaice fuska kamar zatai kuka ta ce, “Ni ALLAH babu ruwana.” Kallonta kawai ya tsaya yi, sai kuma ya ɗan murmusa tare da duƙo da kansa kaɗan murya ƙasa-ƙasa ya furta, “Adana shagwaɓar nan ba yanzu ba”. Kanta ta duƙar ziciyarta na gudu da sauri-sauri a ƙirjinta kamar zata fito waje. Sai kuma ta yunƙura zata tashi. Cikin bada umarni ya ce, “Koma ki zauna”. Babu yanda ta iya dole ta koma ta zauna ɗin tana ɓata fuska…. _______________★ “Da alama wannan karon mijinki yana son nai matuƙar cin mutuncinsa Sadiyya. Ki taho gida tsahon kwanaki goma amma bai biyo bayanki ba saboda yana son nuna min iyakata. Ban san yaushe Usman ya fara maida kansa sakarai a gidansa ba. Ace mace ke juyaka yarinya ƙarama”. Hawaye Hajiya Yaya ta sake matsowa tare da duƙar da kai kamar ta ALLAH. Muryarta na rawa ta ce, “Baba wlhy yamafi yanda kake zatonsa a yanzu. Ni shiyyasa ma nace kawai kasashi ya sakeni na gaji da wannan zaman ƙuncin, ai ba haka mukai da shi ba. Shi da kansa yace min duk macen da zai kawo gidan nan sai dai ta kasance a ƙarƙashin ikona da umarnina. Amma duk ya manta da wannan alƙawuran da girmana agaban ƴaƴana da matansa yake tozartani. Wai har yake iya gaya min sai dai matarsa idan ta juya naga bayanta amma ba’a zaman gidansa ba, wai ni Usman ke tarema mace faɗa a gabana Baba”. Ta fashe da kuka. “Kinga ya isa kukan haka kinji, barni da shi ai nasan maganinsa. Shi kuma Yazeedu daketa kai kawon ki koma saboda baida kishin uwarsa shima zan gyara masa zama. Share hawayenki abinki zakiga matakin dazan ɗauka jeki kwanta”. Kai Hajiya Yaya ta jinjina tana miƙewa hannunta a saman ido tana share hawaye kamar wadda akacema baban ne ya mutu. Sai da ta gama ficewa mahaifiyarta dake zaune a falon bata tofa ko a ba a maganar tasu ta nisa a hankali. Tsohuwar kirki mara yawan son hayaniya kenan. Idanunta akan Baba ta ce, “Nikam da zakaji shawarata dattijo da baka goya bayan Sadiyya ba a wannan karon. Kai kanka kasan halin yarinyar nan sarai da abinda zata iya. Tunda kaga kuma Usman ya watsar da ita a wannan karon wlhy ba banza ba. Dan haka ka kirashi cikin dattako ka zaunar dasu su duka kaji bakin kowa. Idan ta kama ma can gidan nasa zakaje ka tasata gaba ka haɗasu har abokan zaman nata. Karfa dan ka raini Usman ya zama kana tauye masa hakki akan ƴar da ka haifa.” “Ai ke kinji matsalarki, idan har abu zai taso akan yaran nan sai kin nuna ban iya ba ke sarkin tawakkali da gaskiya ko”. “Ba haka bane Dattijo. Masu iya maganafa sunce kaso naka duniya ta ƙisa, ka ƙisa duniya ta soshi. Usman na maka matuƙar biyyar da kosu ƴaƴan da ka haifa ba kowa ke maka irinta ba. To bai kamata a cigaba da ƙasƙantar da shi ba akan abinda ya isa da shi. Wannan fa rayuwar aurensu ce. Kuma shine shugaba a gidan, yin kutse a al’amarin kamar ƙasƙantar da shi ne. Dan ALLAH kada ka biyema yaran nan ana ganin ka da kima da mutunci irin na uba kuma shugaba”. Shiru yay na kusan minti biyu, sai kuma ya sauke ajiyar zuciya. “Hakane kuma Adama nagode da tunatarwa. In sha ALLAHU gobe zan tasata gaba muje gidan. Sai dai ance min shi Usman ɗin baya ƙasar, amma dai inada tabbacin kamar yau ne da dare zai dawo”. “To Alhmdllh gobe idan ALLAH ya kaimu ɗin sai kuje, ALLAH ya taƙaita al’amarin kuma ya daidaita su”. “To Amin ya rabbi. Yarane sai addu’a kawai yanzu, sun maida aure wasan yara”……__________★ Isowar dare Daddy da Hajiya Basariyya sukai ma gidan. Tafiyar kwana goma har sunyi fresh abinsu. Babu wanda yasan da dawowar tasu, dan ita Ammie ma harta kwanta abinta. Cikin barci taji wayarta na ƙara. Da ƙyar ta buɗe ido ta jawota dan ta manta ne ma bata kashe ba. Ɗagawa tai takai kunne tare da sallama. Sai dai Muryar wanda ya amsa mata da umarnin daya bata ya sata watsakkewa sai kuma ta tashi zaune. Jin abin tai kamar mafarki, amma dai ta miƙe ta ɗauka dogon hijjab ta saka sannan ta nufi kitchen. Tea ɗin daya buƙata ta haɗa masa. Sai ta haɗa da ɗan snacks da fruits da bata rabo da su. Haka ta fito gidan shiru alamar kowa ya kwanta ta nufi sashen maigidan. Takai hannu zatai knocking ta tsaya cak sakamakon jin muryar Hajiya Basariyya na tashi a sama cikin faɗa… “To amma dare yayi ai, ƙarfe nawa yanzu da zaka ɗaga waya ka kirata wai ta kawo maka abu. Ni banda hannune ko abinda zata kawo makan banda shi a sashena? Randa kuka dawo Abuja wayasan kun dawo ba sai tashi mukai muka ganku a gidan nan ba. Sai ni daka raina. Wai mi Asiya tafimu dashi ne? Mi take dashi na mata da mu bamu da shi da kake son ganin ka fifitata a kammu?!!…….” “Badariyya wai kina da hankali kuwa. Baki ganin dare yayi zaki zo kina min ihu a kaina. Da kike maganar miyasa zan kirata ta kawo min abu ke da kika dawo daga tafiya mizaki bani? Sannan batun fin sauran mata da kike sai yanzu kika san Asia tafi sauran mata ashe. To lallai kin makaro da kika kasa fahimtar hakan tun tuni. Ita da na saka kika bini a ranar girkinta kinji tayi wani ƙorafi ne. Kuma randa muka dawo Abuja ni Asia bata kwana a sashen nan ba, idan ma ta kwana ai matatace. Dan haka ki fice min anan shasha kawai tana girma bata san ta girma ɗin ba”. “Ni ce shashashar Daddy Huznah?”. Banza yay mata bai tanka ba. Sai maida hankalinsa yay a kiran Ammie. Da sauri ta danne wayar gudun kartai ƙara. Sai kuma ta daure tai knocking ƙofar. Umarnin shiga ya bata. Koda ta shigo kai tsaye a Centre table ta ajiye tray ɗin, sai kuma ta shiga gaishesu su duka a tare da yimusu barka da dawowa. Daddy ne kawai ya amsa mata. Zata juya tabar falon ya katse hanzarin ta. “Ina zaki kuma”. Juyowa tai ta kallesa. “Zanje na kwanta ne, kuma ku samu ku ɗan rintsa ku huta gajiya ko”. “Dawo ai anan zaki kwana”. “Anan kuma Daddyn Hameed amma ai….” Cikin katseta ya ɗaga mata hannu. Dole ta haɗiye abinda take son faɗar. Cikin ɓacin rai Hajiya Basariyya taja akwatinta da hand bag ta fice a sashen tana jan tsaki. Da kallo Ammie ta bita harta gama ficewa. Tai wani kalar masifar bugo ƙofar har sai da Ammie ta zabura. Cikin sanyin jiki ta maida dubanta ga Daddy dake ƙoƙarin fara shan shayinsa hankali kwance. “Daddyn Hameed dan ALLAH….” “Asia! Kin san bana son jan zance ko!”. Ajiyar zuciya Ammie ta sauke kawai, badan taso ba tabi umarninsa a yanda yake buƙata…….__________★ Washe gari kusan ƙarfe goma na safe sai ga baƙi. Ammie na tsaka da haɗama Daddy abinci zai fara ci maigadi ya isar da saƙon zuwan Alhaji Mamman sirikin na Daddy kuma uban gidansa. Da sauri Daddy ya miƙe tare da shiga ciki ya canjo kayan jikinsa zuwa jallabiya. Yayinda Ammie kuma ta fita ta ƙofar baya domin ƙaro abincin. Bata wani jimaba ta koma ɗauke da wani kayan abincin. Ta samu har Daddy ya shigo da shi falonsa shi da babban amininsa sai Hajiya Yaya. Ajiye kayan Ammie tai cike da girmamawa ta rissina ta gaishesu batare data damu da hararar da Hajiya Yaya ke mata ba. Sun amsa mata da kulawa. Dan haka kawai sai Alhaji Mamman ɗin yaji Ammien ta masa kwarjini da shiga ransa. Bai fi sau biyu ya taɓa ganinta ba. Lokacin ruguntsumin aurenta sai kuma da sukaje da Daddy gaishesa bayan sun dawo Hajiya Yaya ta dinga zuba tujara daga nan Ammie ta ɗau aniyar bazata sake zuwa gaidashin ba. Daga mutunci sai abu ya zama fitina da cin mutunci, tun daga nan ko Daddy yace tazo suje sai tayi yanda tai ta zame jikinta. Abincin ta shirya a gabansu sannan ta fita domin basu damar ci, duk da dai Baban yace sun gode bazasu ci ba sukam. Amma Daddy nata roƙonsu. Dole dai suka ɗan taɓa kaɗan, kafin Baban yasa Daddy kira masa su Ammie su duka. Dai-dai nan kuma Yazeed ya shigo falon daga gani isowarsa garin kenan. Dan tunda daren jiya Ammie ta tura masa sako akan dawowar su Daddy ɗin, tare da bashi shawarar ya taho da safen dan ta samesa a gida shiyyasa yay sakkon tahowa kafin ya sake guduwa. Yana fatan iyayen nasa su sasanta kansu komai ya wuce kada abun yayta ƙara girma. Sai kuma akai sa’a ya samu kakan nasa yazo tare da mahaifiyar tasa gidan. Cikin girmamawa ya gaida kakan nasa sannan ya gaida abokinsa. Sun amsa masa da kulawa da tambayarsa aiki tare da tsokanarsa akan ƙara zama tuzuru babu aure. Murmushi kawai yay ya maida hankalinsa a gaida Daddy sannan ya gaida Hajiya Yaya itama. Dai-dai nan Hajiya Basariyya da Ammie suka shigo suma. Gaidasu yayi suma da girmamawa. Ammie ce kawai ta amsa masa da kulawa. Hajiya Basariyya kam sama-sama dan tana cikin haushi ne. Ko su baba sama-sama ta gaishesu kamar an mata dole. Anan ma sai Baban ya sake karantar abubuwa da dama. Bayan an natsa da gaishe-gaishe aminin Baba da suke kira Alhaji Kallah ya buɗe taron da addu’a. Daga haka ya kalla Daddy cikin mutuntawa ya kirayi sunansa. “Usman!”. “Na’am Baba”.Daddy ya amsa masa da girmamawa dan shima yana ɗaukarsa matsayin uba ne. Kai duk ma abokan Alhaji Mamman a rayuwa Daddy na basu girma irin na uba ne. Alhaji Kalla ya cigaba da faɗin, “Mike faruwa tsakaninka da iyalinka ka turata gida har tsahon kwanaki babu wani bayani”. “Baba ni bani na tura ba”……….✍️
