Uncategorized

Maciji Ne Page 69-70 Hausa Novel

Elegant online writers📚📚

Free book 

Page 69/70

___________Ahankali nanny ta fara magana  ,tana cewa”Ammi ba ita bace asalin mahaifiyar Adeeb,amma itace wacce ta rikeshi bayan ta kashe mahaifiyarsa.”

Dararrararaammm!!!gaban fattu ya bada ƙara, sakamakon jin maganar nanny datayi kamar saukar aradu,

Da sauri ta dafe gefen kujerar da take kai,dan ji tayi kamar zata faɗi.

Baki buɗe take kallon nanny cike da tsantsar mamaki,cikin rawar murya tace “nanny kina nufin ammi itace ta kashewa Hamma mahaifiyarsa?to amma me yasa Hamma yake mata kallon uwa?me yasa bai dauki mataki akanta ba?”fattu ta faɗa cikin rudani.

Download>>> Maraicin Nawaff Complete Document

Ajiyar zuciya nanny tayi kafin tace “saboda bashi da masaniya akan abinda ya faru,kuma ya yarda da ammi fiye da kowa,dan yana mata kallon uwa mahaifiyane,baya tunanin zata taba cutar dashi.ki saurare Ni da kunnen basira ,zaki ji abinda ya faru yanzun nan.

“Sarauniya Nazli,ƴace agurin ƙarin baban mai martaba uwa daya uba daya,wato kenan ita da mai martaba ,yan uwan juna ne ,dan kuwa auren zumunci akayi musu.

Suna kaunar juna matuka bayan anyi auren,suna zamansu lafiya cikin so da aminci, lokacin da akayi auren nasu,iyayen sarauniya Nazli duk sun rasu,hakan yasa take zaune a hannun mahaifiyar mai martaba ,dalilin hankali da nutsuwarta yasa mahaifiyar mai martaba ta zaba masa ita matsayin matar da zai aura inda ranar da aka daura musu aure aka naɗa shi matsayin sarkin misra.

Shekara guda dayin aurensu Allah ya azurtata da zamu yaro , kyakykyawa  abin so ga kowa, ranar suna aka rada masa suna adeeb.

Adeeb ya taso cikin so da kauna, agurin iyayensa, da ma duk wani wanda yake fadar nan,yana da matukar hakuri ,hazaka ,ladabi da kuma biyayya.

Nice wacce ke rainon Adeeb ,kasancewar mijina yana aiki acikin fadar nan,shine drivern dake tuka sarki da iyalinsa.

Lokacin ina goyon dana tareeƙ ,dan haka na hadasu duka ina rainonsu,saidai ko da wasa ban taba hada tareeƙ da Adeeb matsayi daya ba,duk lokacin da zanyi musu wani abu saina farayiwa Adeeb,sannan nake yiwa tareek,ko wasa suke yi nakan sanya Adeeb matsayin shugaba ne tareeƙ kuma bafadensa.hakan yasa suka taso cikin kaunar juna da  girmamawa,dan kullum nakan nusar da tareeƙ cewar Adeeb ɗan sarkine kai kuma dan bafaden sarkine,dan haka kada ka haɗa kanka da Adeeb .

Download>>> Tubali Book 2 Complete Document

Sosai shakuwa ta shiga tsakanin Adeeb da tareeƙ,dan kuwa ko gurin sarki Adeeb zaije to dole saida tareeƙ ,kuma tun lokacin ƙuruciya tareeƙ ke kiran Adeeb da yallaɓai.

Muna jin dadin zama da sarauniya Nazli,dan kuwa macece mai matukar girmama dan adam,ba ruwanta da nuna isa ko iko,akan kowa ,tana janmu ajikinta sosai ,hakan yasa kowa ke kaunarta cikin masarautar nan.

Kwatsam batun karin auren mai martaba ya taso,kuma auren zaiyi shine da mata biyu a lokaci daya, dayar ƙánwar abokinsa ce  wato amma,dayar kuma yar abokin babansa wato ammi. ko kaɗan sarauniya nazli bata tada hankalinta ba,koda mai martaba ya nuna tayi hakuri,shima bada son ranshi zaiyi auren ba ,nuna masa tayi ma tafi shi farin ciki tayi masu fatan alkairi ,duk da kuwa can ƙasar zuciyarta tana jin kishi da zafin abin aranta,amma haka ta daure ta nuna ba komai.

Bayan anyi bikin mai martaba da matansa guda biyu,da farko ana zaune lafiya kowa na ba kowa girmansa,sai kuma abubuwa suka zo suka fara lalacewa,yau kaji wannan maganar gobe kaji waccan.ammi itace wacce ke haddasa komai,sam bata son zaman lafiya ta cika gutsiri tsoma,amma sarauniya Nazli bata kulata ,dan kuwa lokacin tana fama da laulayin cikinta na biyu.

Amma ce ma ke dan maida mata martani,

Kullum amma na zuwa gurin sarauniya Nazli tana kula da ita, sosai suke zaman lafiya a tsakaninsu ba gutsiri tsoma ko kaɗan,hakan kuwa ba ƙaramin bata ran ammi yake ba ,dan ita burinta kawai ta farraka su.

Lokacin da sarauniya Nazli ta zo haihuwa kuwa ,cikin nasara ta haifi yaranta tagwaye duka mata, Masha Allah,karkuzo kuga kyau garin yaran nan,sosai kowa ke murna da samun yan yaran nan,

 Adeeb yana bala’in kaunar ya’yan nan,kullum yana kusa dasu yana musu wasa,shida tareeƙ ,wani lokacin hana daukar yaran ma suke,idan za’a daukesu suyi ta kuka kar’a  taba musu kannai.kuma daidai lokacin ne amma ta fara laulayi itama.

Sosai mai martaba yake jin dadin zama da matansa ,dan kowa na kokarin kyautata masa.koda labarin cikin amma ya sameshi yayi murna sosai .

Wayyo ai tunda ammi ta kyalla ido ta gano ciki jikin amma,hankalinta yayi magun tashi,ya za’ayi haka ?an aurosu tare amma ita har yanzu ko batan wata bata taba yi ba?ina da sake wllh saita zubar da cikin Nan.shikenan saisuyi ta haihuwa ,su gaje masarautar ita ko oho?

Ba irin abunda ammi batayi ba akan cikin rashad  ya zube,amma hakarta bata cimma ruwa ba.

Download>>> Dr. Eesah Complete Document

Haka aka haifi Rashad , kyakykyawa dashi ,suna matuƙar kama da Adeeb,Adeeb yana son Rashad fiye da yadda yake san twince husna da haseena,kullum yana tare da Rashad shida tareeƙ ,barci ne kawai ke rabasu.

Hakan yana dagawa ammi hankali,tun daga nan saita fito da sabon salo, wato ta fara jan yaran ajikinta,da farko sam Adeeb bai saki jiki da ammi ba ,dan shi irin yaran nan ne miskilai,idan Kinga dariyarsa to shida tareeƙ ne ko mai martaba da mommansa ,ko kuma ni,sai kuma Rashad da amma .

Saidai yana da yawan kyauta ,yanzun nan zai baka abu yace na kyauta na baka,hakan yasa kowa ke kauanarsa sosai, 

Kusan tunda ga lokacin wasu da yawa ke kiransa da magajin fada,ciki kuwa hardanki.ciki kuwa harda Ni.

Amma kasancewar ammi makirar mace ,ta san ta yadda zata ja hankalin mutum ,sai Adeeb ya fara yarda da ita,harta kai ta kawo yana kwana anan bangarenta.daga wannan lokacin ne kuma Adeeb ya fara tsiro da  wata halayyar  sam baya son Rashad yazo inda yake ,lokacin Rashad yana rarrafe,wai zai bata masa jiki,saidai idan shi yaga dama yayi masa wasa .

Wata rana mijina ya dawo gida hankalinsa atashe,koda na tambayesa lafiya ?meke faruwa?nagansa cikin tashin hankali .nan yake sanar dani cewar ,yau ya kai ammi anguwa ,yana zaune yana jiranta, bata fitina, kawai saiya dan zagaya dan ya ware ƙafarsa ,yana zuwa saitin window yaji tana magana da wani mutum, kuma suna tattaunawa ne akan yadda zasu kawar da Adeeb harda tareeƙ,sannan yaji tana sanar da mutumin cewar aiki yayi kyau,dan yanzu sam Adeeb baya kaunar Rashad,baya son Rashad yazo koda inda yake ne.yanzu abinda take so shine a cire musa mahaifiyarsu daga ransu,ta yadda sai abinda tace suyi zasuyi,

Tana son saita lalata musu tarbiyyar sun zama abin kwatance ,sun haddasawa iyayen su ciwon zuciya sun mutu,kafin ta kawar dasu,inya so ta gaji dukiyar mai martaba ita kadai.

Hankalina yayi matuƙar tashi lokacin dana ji wannan maganar ,nan take na fara kuka ,ya zama dole na sanar da iyayen yaran nan,su kula da ƴaƴansu,

Amma nasan sarauniya Nazli,koda na faɗa mata ,ita macece mai hakuri da tawakkali ba abinda zatayi akan hakan,zata iya cemin ma indaina kawo mata zancen wani,kowa yayi dai dai kansa.

Dan haka gurin amma na nufa,ina kuka nake sanar da ita komai da mijina ya faɗa min,hankalinta yayi mugun tashi sosai,nan take ta tashi ta nufi gurin nazli cikin ɓacin rai, tana zuwa ta labarta mata komai ,sannan ta kara da cewa idan muka zuba ido fa zata lalata mana yara ,tayi musu asiri su rabu damu, dan haka ya zama dole mu taka mata burki”alokacin hankalin Nazli ya tashi,dan tasan amma bazata mata karya ba,kuma itama ta fuskanci sauyi daga gurin Adeeb ɗin,dan haka saitace zata dauki mataki akan abin muyi hakuri abi komai ahankali.

Download>>> Goje Sadauki Omar Return Complete Document

Aikuwa Nazli da kanta ta je gurin ammi dan suyi magana akan yaran ,kuma tajene akan zata yi mata magana cikin hikima ta yadda tsoron Allah zai shigeta,abinda bata sani ba ,tuni ammi tayi nisan da bata jin kira.

Tana zuwa  dakin zata shiga ,tajiyo Muryar ammi tana waya ,

“Kun tabbata dai kun dauke yarinyar nan?kuma kun fitar da ita can wata kasar daban?bana son asami matsala ,so nake tayi nisa,nisa na har abada ,ta yadda bazata ƙara ganin yar ba,ai wllh dama na faɗa duk wanda yaci tuwo dani miya yasha.

Shikenan ,zakaji alart.

Tana gama faɗin haka ta ajiye wayar tana murmushi.

“Suhaimat ,kinyi kuskuren auren wanda nake da burin aure,wllh nayi ta sanya rayuwarki cikin bakin ciki da tashin hankali,nasa an dauke ƴarki,an jefar da ita ,can wata kasar,ta yadda ko gawarta bazaki gani ba,na Tsaneki suhaimat,na tsani ganinki,kin auremin wanda nake so ,sannan kin haihu Ni ban haihuba, wllh sainayi ta shuka miki bakin cikin da zaiyi silar mutuwarki,bana ƙaunarki sam cikin raina.kuma keda ƴarki har abada”ammi ta fada cikin muryar azzalumai tana wani murmushi na mugunta.

Jikin Nazli banda rawa ba abinda yake ,tashin hankali ya baibaye dukkan ilahirin jikinta.

Yanzu zalumcin ammi harya kai kan yar uwarta?yar uwarta take cutarwa haka,ta sanya an sace Mata yarta an jefar,wannan wane irin rashin imani ne,? innalillahi.

Cikin mugun ɓacin rai sarauniya Nazli ta buga kofar falon ammi da karfi ta shigo ciki,idanunta na zubda hawaye,

Azabure ammi ta mike tsaye tana kallon momma,koba’a faɗa mata ba ,tasan cewar amma taji duk abinda take faɗi,dan haka kura mata ido tayi cikin yanayi na rashin gaskiya .

Momma kuwa wato Nazli,cikin muryar kuka take magana da cewa”wllh ammi kiji tsoron Allah,ki sani zaki mutu ,kuma ,zaki koma gareshi,duk abinda kikeyi yana kallon ki,wacce irin zuciya gareki?da har yar uwarki ma bata tsallake sharri ki ba?to kisani tabbas sai naje na sanar da iyayenku abinda kika aikata azzaluma marar imani,sannan kisani,duk abinda kike aikatawa akan yayanmu to yazo kunnenmu ,kuma in sha Allah asirinki bazaiyi tasiri akan yaran mu ba,baki isa ki rabamu da suba.turrr da hali irin naki makira”momma na gama faɗin haka ta fice daga ɗakin cikin tashin hankali,har bata san inda take sanya ƙafartaba.

Download>>> Tubabbiya Complete Document

Ammi kuwa tuni zuciyarta ta tsinke tsoro da fargaba sun gama baibaye zuciyarta,yanzu idan Nazli ta tona mata asirifa?me yakama tayi ,dole ta dauki mataki tun kafin maganar taje kunnen wanda bataso suji,wayyo Allah me Yakamata nayi”ammi ta fada cikin tashin hankali tana mai Safa da marwa.

Kuka sosai Nazli keyi cikin dakinta tana mamakin zalunci irin na ammi,yanzu ashe mutum zai iya cutar da ɗan uwansa akan abin duniya?wannan wane irin rayuwane?turrrr da halin ammi Allah ya shiga tsakaninsu da ita .

Tana cikin wannan halin ne, na isketa,dan haka cikin damuwa na tambayeta meke faruwa.nan take sanar dani abinda kunnenta yaji,hankalina yayi matuƙar tashi lokacin dan banyi tunanin rashin imaninta yayi nisa har haka ba.

Nan sarauniya Nazli ke sanar dani gobe gobe zata je har gidansu ammi ta fadi abinda ammin tayi .naso in hanata Amma tace sam bazata iya zama da wannan abin cikin ranta ba ,dan kuwa har ta sanar da mai martaba tana son zuwa anguwa.

Washe gari kuwa mijina ya dauki ammi da yaranta ,suka tafi,amma banda Adeeb ɗan lokacin ma suna makaranta .ko minti goma ba’ayin da fitarsu ba aka aiko cewar motar su ta kama da wuta sun kone kurmus…

Kuka ne yaci karfin nanny ta kasa magana sai kuka da takeyi,haka ma amma banda kuka ba abinda takeyi, tareeƙ kuwa idanunsa sunyi jajur dasu,fuskarsa har wani karkarwa take.

Fattu kuwa tsabar kuka har neman shiɗewa take,abubuwa sun taru sunyi mata yawa,ga tsantsar tausayin Adeeb ,ga kuma mamaki da al’ajabi cewar ammi yar uwar mahaifiyarta ce .sannan itace silar rabata da iyayenta…sosai take kuka ta ƙanƙame jikinta akan kujera,wani irin zafi take ji cikin zuciyarta ,duniya ba tabbas,yanzu dan uwa shine zai cutar da ɗan uwansa,ashe shiyasa ta dauke sarƙar nan yawa?dan bata yi tsammanin ina raye ba ,kuma saigashi Allah ya kawoni har mazaunin ta,shin wacece mahaifiyar tawa? Acikin yan uwan ammi.wayyo Allah na gode maka ya Allah ka sadani da ahalinsa cikin aminci.allah sarki baffana.

Duk fattu ke wannan zancen cikin zuciyarta,tana jin kamar ba ita bace.

Cikin kuka da muryarta wacce ke rarrabewa tace”wa…c..e..cc…ee ma…ha…I…fiya …..ta 

Kuma …..ina….za…..n…ga..nta.”

Download>>> Raɗaɗi By JUT Complete Document

Muje zuwa ɗan jin ya zata kaya.

Sorry jiya kuna ta jirana na ƙunƙuni shiru, bankin daɗi ne wllh.

Mrs babi ce💘💘

Share and comment fisabilillah.

More comment

More typing.

Back to top button