Hausa novels

Haihuwa Da Hanji Page 18 Hausa Novel

Sai da ya bar gida da motar ya fahimci gas din Ac ɗin shi ya ƙare, hakan ya ɓata mishi rai don baya son buɗe glass na mota yana tuƙi, a haka ya tafi Asibiti yayi abin da zai yi a ranar wuraren sha biyu ya bar asibitin ya nufi gida, a daidai babban titin da zai ɗauki hanyar cikin unguwar su na Barnawa hold up ya riƙe shi, a dole ya sauƙe glass saboda zafin da yake ji. Karon farko da idanunshi suka sauƙa a kanta bai gane ta ba sai da ya ɗan yi focusing na seconds kan ya gane ta, wannan yarinya ce da ya taɓa ceta from poison, wannan yarinya da saleem ke so, sam bai yi tunanin wani abu ne ya tsayar da ita a wurin ba sai a karo na biyu da ya mayar da idanunshi wurin suka sauƙa a kan trolley dake gabanta, idanunta ya sake mayar da ido sai ya fahimci ta yi kuka sossai, horn ake ta danna mishi hakan ya sa ya ja motar yayi gaba wayanshi ya zaro ya shiga neman Layin salim sai dai har 2missed calls ya mishi bai ɗaga ba shi da ya tsani kira sau biyu ya kan ce ai duk uzurin da mutum ke yi in ya zo ya ga na farko zai bi ba sai ka ta jera kira kaman marar aikin yi ba, a kira na uku saleem ya ɗaga sai dai ya kasa magana.”Saleem are you Okay? Whats wrong with ur voice?”Saleem ya kasa magana don shi kaɗai ya san me yake ji, Ryan bai taɓa jin Muryar abokin nashi a haka ba, dole ya nemi wuri yayi parking “Saleem Mommy ce?”Yayi uttering “Uhmm Ryan Mommy ta kori Afeefah ban san wani irin hali za ta faɗa ba, mommy tayi alkawarin tsine min na sake ko da magana da Afeefah ne bare yunkurin taimako aure ko soyayya, she’s too young Ryan she’s too young! Na san tana chan all alone, scared and disturbed idan wani abu ya same ta fa? Its all my fault da na fara son ta Its my fault…”Hawayen da yake yi ne ya sa ya datse lips ɗin shi da ƙarfi sai kawai ya katse wayan.Kunna motar rayann yayi yana jin wani abu a ƙasan ranshi, tausayin Saleem ya rufe shi haɗe da damuwan jin halin da yake ciki bai taɓa jin abokin shin haka ba, saleem da ko haɗe rai baya yi. Fuskarta yake gani a idanunshi ashe kallon taimako take mishi, steering ya ɗan buga da tafin hannunshi yana zagayowa inda ya barta sai dai neman duniya bai ganta ba, har parking yayi ya sauƙa yana takawa da kafa ya zazzaga bata nan. Bakinshi ya ɗan taɓe kaɗan yana shirin juyawa wayanshi yayi ringing.Zarowa yayi sai ya ga Driver ɗin Mamminshi ne, dagawa yayi “Ado ya aka yi?”Ya fitar da maganan yana lumshe ido sam ba zaka san yana da damuwa ba ko hankalinshi ya ɗan tashi don fuskar bai nuna ba ko da wasa.”Oga akwai matsala ne, Hajiya ce!”Tuni ya ware idanun a take suka sauya ya fara nufar motanshi yana ji Ado na mishi bayani wai ya kaita sayayya kuma yayi ta jira bata fito ba ya shiga ciki kuma yayi neman duniya bai sameta ba.”A ina ne?””Galaxy mall”Yana kusa da wurin ƙarasa wa kawai yayi “Ka ƙirata?”Ya jefawa Ado tambayar Ado yayi saurin duƙar da kanshi don ya san fushin Rayyan a take sai ya haukace, idanunshi sun yi mishi kwarjinin da ba zai iya kallon cikinsu ba “Ban fito da waya ba”Wani irin kallo ya watsa mishi lip ɗin shi ma sun yi nauyin buduwa bare su sake furta ko da kalmar A.Wayanshi kawai yake dannawa ya shiga ƙiran layinta sai dai ringing na duniya ba’a ɗaga ba, tracker ya shiga na Find my Iphone tuni ya ga location da take, a maimakon hankalinshi ya kwanta sai hankalinshi ya sake tashi ba za ka sani ba amma in ka ƙura mishi ido zaka ga hannayenshi har rawa suke idan kuma ka taɓa za ka ji sun yi sanyi tamkar ƙanƙara to baya cikin lafiya kenan.Mota kawai ya shiga ya ja tafiyar mintuna goma ya isar da shi asibitin yayi rough parking ya sauƙa ya nufi ciki, a gaban nurses station ya tsaya “An kawo wata elderly woman yanzu! Where is she?”Da ɗan karfi yayi maganan don ya ga mace ɗaya ce kawai ta mayar da hankali kanshi tsawar da yayi ya sa duk suka juyo, kofan emergency kawai ta nuna mishi ya nufi wurin kawai ya tura ya shiga.”Excuse you! Baka san ba’a shiga nan bane?”Id card ɗin shi ya fitar ya nuna musu idanunshi na kan Mammi da suke ta ƙoƙari wurin ganin sun ceceta ya furta a hankali “The patient is experiencing end-stage renal disease(ESRD) nd she’s diabetic i hope ba ku yi kuskuren komai a kanta ba”Ja da baya wanda ke rike da drip yayi don ba ruwan masu sugar bane, Id card ɗinshi kuma ya tabbatar musu da waye shi. A tare da shi aka cigaba da ƙoƙarin ceton Mammin kusan awa ɗaya da wani abu kan suka fara fitowa aka barshi shi kaɗai.A kan kujera ya zauna ya sa hannu ya riƙe nata ɗaya ya gimtse a duka hannunshi biyu ya ɗora goshinshi a kai yana jin jininshi na cigaba da tsitstsinkewa rauni mai girma ne da ba zaka ɗauka irin shi mai dakakkiyar zuciya zai nuna ba bayyane a fuskar shi da ma idanunshi, ƙiran sallah ne ya sa ya ɗago a hankali ya zuba mata idanu sama da mintuna uku kan ya mayar da hannun a hankali ya ajiye mata ya miƙe ya fito Fuskarnan babu ɗigon walwala, a kan trolley idanunshi suka fara sauƙa ya ɗan kalli Ado da ke maƙure gefe kaɗan kaman zai yi magana kuma sai ya fasa yayi gaba, sallah yaje yayi bayan ya idar ya dawo yana shigowa reception ɗin tana ɗagowa suka haɗa idanu, handbag ɗin hannunta ya ɗan kalla kan ya nufeta.Yana matsowa dukar zuciyarta na ƙaruwa gabanta sai dukan uku uku yake tamkar za ta rasa numfashinta take ji don bai daina kallonta ba kuma bai daina nufarta ba kamshinshi ya riga shi isa, ko kan ya iso aka ƙira shi”Sir the patient, ta farka”Numfashi kaɗan ya sauƙe ya juya ya nufi ɗakin, bata san ta kama numfashi ba sai da ya ɓace mata taji tana kokarin mutuwa ta sake shi da ƙarfi tana dafe kirjinta, Allah ya gani tsoron shi take bata sani ba ko tun ihun da yayi mata ne tayi developing wannan tsoro ko yaya amma muddin ya sauƙe ido a kanta sai ta ji wani tension na building inside her.Idanu kawai ya zuba mata ta ɗago ido ta kalleshi cikin ƙarfin hali ta sakar mishi murmushi tare da miƙa mishi hannunta, ya taka a hankali yaje ya kama yana zama “Mammi…”Sai yayi shiru ta sake yin murmushi mai kyau “Saraki na ji sauƙi ka kwantar da hankalinka, sannan am sorry na ji ina son ɗan shan iska ne ya sa na fita not knowing hakan zai faru am sorry na ɗaga maka hankali””Mimmi stop it please, am sorry i wasn’t there to take you out myself da kin faɗa min zan bar duk abin da nake zan zo na kai ki na kula da ke har mu koma, Its my fault da nake emphasizing akan zaman gidan am sorry you get bored”Hannunshi ta ɗan matse tana murmushi har lokacin, ɗago ta yayi ya buɗe ruwa ya bata ta karɓa babu musu ta sha sossai kuwa don masu ciwon su na buƙatar enough ruwa a jiki.Basu wani jima ba suka fito yana riƙe da ita, har lokacin in har ka san shi sosai za ka hangi akwai damuwa a fuskar shi, Afeefah da har lokacin tana zaune a wurin tayi saurin Miƙewa ganin su tare, dama ya san matar? Menene alaƙarsu? Ta ya aka yi ya san tana nan? Su ne tambayar da ta tsaya yi tana daga tsaye tana kallon su.Idanun Mammi ne ya kai kanta, sai ta dakata tana tunani ga jakanta dai hannun stranger a hankali take tuna abin da ya faru yarinyar ce ta taimaketa, ta yi mamaki ƙwarai ganin yarinyar har lokacin kuma riƙe da jakanta da alama ko ajiye shi bata yi ba, tana tuna kalaman yarinyar na ban haƙuri a sadda ta ɗauki ɗari biyar ciki.”Saraki wanchan yarinyar ita ta taimakeni ta kawo ni nan, da ban san me zai faru ba”Kaman bai fahimta ba ya sake kallon Afeefah, chan ƙasan ranshi ya ji daaɗi kuma ta samu wani ƙima a idanunshi saboda duk wadda ya kaunaci Mammi ko da bai kaunaceshi ba shi ya bashi daraja na musamman, sai dai har lokacin fuskar shi bai nuna ba sai nufanta da Mammin ta sa suka yi, ita abin da ya kaɗa ta ma tahowarsu tare, ita dai ta rasa wannan irin razani da take shiga da kwarjinin wannan bawan Allahn, ko da suka tsaya gabanta sai ta ga ya cike wurin gabaɗaya, kuma kallonta yake don Mammi ta sake shi ta kama hannunta.”Ɗiyata yaya Sunanki?””Sunana Afeefah, Aunty ya jikin ina fata komai lafiya?”Tayi maganan kaman mai tsoron wani abu zai kama ta “Alhamdulillah Afeefah, na gode ƙwarai da kyakyawar tunanin ki ba kowa ne zai iya irin taimakon da kika yi min ba, Allah ya saka da alkhairi”Afeefah tayi murmushi “Babu komai Aunty, ga jakarki ki yi haƙuri na cire ɗari biyar a ciki mun hau adaidaita saboda ba ni da ko biyar”Murmushi Mammi ta saki ta ɗan kalli Rayyan da bai ce komai ba ya zuwa yanzu ya kawar da kai daga kallonta sai dai yana sauraren su.”Gaskiya samun irin ki a wannan zamani sai an tona”Idan ta tafi da jakar nan ba karamin abu za ta samu ba don bata tantama har zobunan gwagwalanta suna ciki amma bata ko buɗe ba bare tayi tunanin yi mata sata, hakan ya matuƙar burgeta.”Saraki mu kai ta gida ko? Ina so in ga gidansu in yi ma iyayenta godiya kuma in basu hakurin rashin ganinta kan lokaci”Ta kalleshi shima ita ya kalla bakinshi ne yayi mishi nauyi, kuma ba ya son dogon bayani sai ya kalli Afeefar da kanta ke ƙasa kaman daga sama ta ji ya ce “Kina da gida?”Yayi maganan yana ɗage gira ɗaya.Mammi ta Harare shi”Wani irin tambaya ne wannan akwai wanda ya faɗo daga sama ne?”Ita dai tambayar ya zo mata wani iri sai hawaye suka cika idanunta a lokacin ta tuna ashe bata da inda za ta je, da alamu kuma ya sani don maganar shin ya fi yi mata yanayi da gatse, a hankali ta kalli Mammi”ba sai kun kaini gida ba Aunty, kina bukatar hutu saboda jikinki daga nan zan koma da kaina”Tayi saurin juyawa amma duk da haka ya ga hawayen da ya silalo mata, Ado ya kalla “Ɗauki akwatin nan mu tafi”Yana kai nan ya fara kokarin kama mammin “She has No where to go, for now za mu tafi tare”Cike da tausayi Mammi take kallonta, so take ta ji karin bayani me ya sa bata da inda zata je? Ina dangin ta in bata da iyaye? Amma sanin duk ba yanzu bane lokacin maganar ta saki Rayyan ta riƙo hannun Afeefar galala yayi yana kallonta ko ta tsaya don ta san rigimar shi, haɗe fuska yayi sossai ya biyo bayansu.Sanin halinshi ya sa Mammi ta zauna gaba Afeefah ta shiga baya, ya ja motar a hankali ya fita daga asibitin, Ado ma ya bi bayanshi har yanzu zuciyarshi bai dawo daidai ba yana tantamar ko Rayyan ya barshi ko sai ya ɗauki mataki a kanshi don abin da duk ya shafi Mammi baya wasa da shi sam kaman yadda ita ma bata da kaman Rayyan a duniyarta.Shiru motar yayi don Mammin na buƙatar hutu so ganin ma kaman ta gaji da zaman ya nemi wuri yayi parking, ya ɗan koma baya ta yadda ya sake birkita Afeefah dake zaune saitin kujeran shi ya sa hannu ya kwantar da seat ɗin mammin a hankali, ta buɗe ido ta kalleshi ta ɗan yi murmushi kawai ta sake lumshe ido ya furta “Sannu”Cikin tsantsar kulawa, sai kallonsu Afeefah take yi. A iya zaman nan ta fahimci matar tana da matuƙar muhimmanci a rayuwarshi Dukda bata ga kama ba don matar baƙa ce kaman ita shi kuwa farin shi har ya ɓaci, ba zaka taɓa cewa bai hada dangi da Larabawa ba barin ma kasumba da gemun da ya ajiye ɗan daidai da shi baƙi sidik.Motsin kirki bata iya yi kamshin motar har yana hawa mata kai a haka suka isa wani tsararren unguwa shiru ne unguwar kaman ba titin da suka baro ke ɗauke da hayaniya da jama’a ba, nan ɗin gidajen manya manya ne, sai dai ka hangi su dawisu da su jimina a gidajen da gininsu ma na zamani ne, gaban ko wani gida kuma akwai securities zaune kusan kowanne sanye da uniform ko yellow ko blue, a hankali ya gangara gaban wani golden gate mai girma fuskar sai sheki take horn yayi, sai gashi an leƙo wannan ɗin ma na sanye da blue riga da bakin wando, Gaisuwa ya shiga miƙawa Ogan nasu ya ɗaga mishi hannu kawai don Window na sauƙe saboda rashin Ac. Tamfatsetsen gida ne don yayi na su Saleem sau uku ko biyu da rabi, gidan tamkar ginin sarauta saboda fari ne kal an mishi ado da golden paint har kwanon golden Color ne, harabar na shimfide da interlocks ɗauke da shukoki masu tsananin kyau da ɗaukar ido, Dukda akwai parking lots har uku jere da motocin alfarma bai yi parking a ciki ba sai da ya je dab kofar shiga yayi parking ya sauƙa ya zagaya ya buɗewa Mammin kofa.Ita dai Afeefah na ta mamaki don bata zata akwai wanda wannan mai zafin ran ya dauka da muhimmanci ba haka, bata taɓa zaton zai iya buɗewa wata macen kofa ba kila dai mahaifiyarshi ce, kila kuma kamannin mahaifinshi yayi shiyasa basa kama ko ta wani ɓangare.”Afeefah sauƙo mana kin zauna ciki”Ta faɗa a hankali, buɗe murfin tayi ta sauƙa tana jin kanta dake sara mata na ƙaruwa saboda tsabar kukan da tayi yau, kunyar hijabin jikinta take don onion colour ne kuma duk gaban da ya jike da hawaye ya bushe sai yayi wani jirwaye jirwaye, A baya ta bi su har suka shiga cikin tsararren parlorn mai girman gaske sanyi ne ke ratsa ko ina ga kamshi, parlorn kal kal kaman a zuba maka abinci a ƙasa ka ci komai na parlorn royals ne golden and milk, tana kuranta kyaun gidan su saleem wannan gida ya fi nasu tsaruwa nesa ba kusa ba.A cikin kujera suka samu wata budurwa ganin Mammi ya sa ta tashi da gudu ta nufeta sai dai hararar da Ryan ya sakar mata ya sa ta fasa isa da gudun ta ɗan natsu “Mammi are you Okay? Me ya same ki? Na dawo daga school wai kin fita Mammi jikinki yayi kyaun da za ki fita? M…””Will you shut up and let her rest?”Ya faɗa ba da tsawa ba sai dai ba kuma da wasa ba, mammi ta ɗan yi murmushi “Abeeha ga Afeefah ki kai ta ɗaki na musamman a kai mata abinci tayi wanka ta kwanta ta huta sossai please she’s exhausted daga alamunta”Kallon Afeefah Abeeha tayi sai ta juyo zata fara jero wa Mammi tambayoyin ina ta samo ta sai suka haɗa ido da Ryan tuni ta wuce ta kama akwatin da Ado ya shigo da shi suka yi wani ɓangaren daga cikin parlorn.A hankali suka isa wani matakala uku suka hau zuwa wani corridor da ya ji interior kan suka shiga wani parlor madaidaici kuma tsararre grey ne da Black colour, bai barta nan ba sai da ya sadata da cikin bedroom ɗinta duk ko ina suka bi kalkal yake gidan kaman kullum ake wankewa, a bakin gadon da shima Grey ya ji shimfida White ya ajiye ta ya buɗe wani frigde dake gefe ya fiddo ruwa marar sanyi sossai ya bata ta sha sossai kan ta ɗan kwanta “Sannu Saraki Allah yayi maka albarka”Idanu ya lumshe ya buɗe tuni suka ɗan sauya, a hankali ya amsa da Ameen kan ta ɗan kwanta tana sauƙe numfashi.”Mammi ki huta sossai please, bana so in tafi in barki amma Saleem bashi da lafiya i need to go and see him, ba zan jima ba zan dawo”Tayi murmushi “Su fa Maryama suna nan kar ka damu take your time, kuma ma Abeeha ba ta dawo ba na san tana gamawa da Afeefah zata zo””Ta ishe ki da surutu dai”Yana kai nan ya miƙe tana mishi sai ya dawo ya gaishe mata da saleem ya fice.Wani motar daban ya ɗauka mai Ac ya fice daga gidan bayan ya umurci Ado da ya fita da wanda ya dawo ya kai a saka Gas na Ac, kai tsaye gidan su Saleem ya nausa bayan ya isa ya bi ta baya ya haye saman zuwa ɗakin saleem ɗin komai a kashe ya samu kaman ba mutum, hasken ya kunna ya nufi cikin ɗakin sai ya samu saleem lullube da bargo, kanshi ya nufa ya janye bargon ya sa hannu a goshinshi ya janye “Subhallah! Saleem you are burning up tashi mu tafi hospital””Ryan Afeefah, ban san wani irin hali zata faɗa ba am scared kar Allah ya kama ni da laifi… Please help me find her please”Da kyar yake maganan saboda zazzafar zazzabi dake kassara gaɓoɓinshi.”Za mu same ta, In shaa Allah i will find her lafiyarka First ur temperature is very high”

Back to top button