Uncategorized

Alamomin gane Masoyiya ta gaskiya

 ALAMOMIN GANE MASOYIYA TA GASKIYA

A lokacin da ka ke ƙoƙarin gano matsayinka a zuciyar budurwarka shin tana son ka ko akasin haka? da akwai buƙatar ka nazarci wasu abubuwa waɗanda wasu sun kasance waiwaye ne wasu kuma suna kan faruwa.

  • Farkon haɗuwarku
  • Halayyarta

FARKON HAƊUWAR KU

A yayin gabatar da soyayyarka gare ta, yana da kyau ka yi amfani da salo mai karsashi wato sai da ka gama jan hankalinta da ra’ayinta a kan ka sannan ka bayyana a gareta da lamari na soyayya?

Furta kalaman amince wa na soyayya ga wanda suke so abu ne da mata suke jin kunyar furta wa a karon farko ga samarin na su, sai dai duk da haka zata dinga nuna maka alamun tana son ka kuma zata ke nuna maka wasu alamomi da suke nuni da SO.

Salon da kake bi wajen gudanar da soyayyar ta ku shi ne sikelin auna ci-gaba ko ci-bayan soyayyar ta ku, misali a lokacin da kuke tsaka da soyayya sai ta samu wani da ya fika iya kalaman soyayya da barkwanci da rashin yawan mita da dai duk wani salo mai burge wa to babu shakka ko kafi ƙaruna dukiya zai iya ɗauke hankalinta da ga kan ka, sai dai ta tsaya da kai dan kuɗinka. A saboda haka akwai buƙatar ka kasance mai sabunta salonka na soyayya tun daga kan kalamai da yanayin yadda kake bata kulawa da sauran su lokaci bayan lokaci.

A dukkan lokacin da ka buƙaci mace ta baka amsar amincewa tana son ka, sai ka ga ta yi murmushi ko ta kasa furta hakan a karo na farko to hakan yana daga cikin alamu na SO domin kuwa wanda ake so ake jin kunya.

Ka da ka damu da sai ta furta maka kalmar tana son ka kai dai kawai ka lura da waɗannan abubuwa kamar haka;

  • Sau nawa kake kira kafin ta amsa? Idan har da so zata amsa a kira na farko idan kuma bata amsa ba zata amsa a kira na biyu har ta baka uzurin da zaka gamsu na dalilin rashin amsa kiran, idan har bata amsa a kira na biyu ba sai ka bar kiranta haka idan har da so zata kira ka da zarar ta ga kiranka da ta rasa har ta baka uzurin kare kai.
  • Matuƙar tana son ka za ta kasance mai karɓar shawarar da ka bata.

Zan dakata anan amman zan ci gaba da izinin Ubangiji.

Back to top button