Uncategorized

Kishi Da Aljan Chapter 6 Hausa Novel Complete

 

Sosai Abbah ya turniƙe ɗakin Abdul da hayaƙin habba

Lungu da saƙo ba inda be saka ba, ummie na dai tsaye bakin ta fal cike da tambaya

Sun fi minti talatin a cikin ɗakin, kafin su fita,

Tun ummie na saka ran Abbah ze gaya mata wani abun, har ta haƙura, gaba ɗaya be bata fuska ko kaɗan ba

Haka nan ba dan ranta yaso ba ta rabu da shi, ta ci gaba da aikace aikacen ta.

Tunda Abbah ya shiga ɗaki ya hana kanshi saƙat da tunane-tunane, gaba ɗaya tunanin shi ya koma can ruyawar baya

Ya kai dogen lokaci yana tunanin nan, seda yaji kanshi na sara mishi tukun ya haƙura 

Wayar shi ya ɗauka yai dialing numbar Abdul.

Har ta ƙaraci ringing Abdul be ɗauka ba.

yana a office kwance, tinda Abbah ya fara turara ɗakin nashi, shi kuma daga can ya fara jin duniyar na juya mishi, daga baya kuma bacci yai awon gaba da shi.

Me asibitin da Abdul ɗin kema aiki ya shigo ya iskeshi kwance yana sharar baccin shi hankali kwance, ya jima sosai akan shi yana tashin shi

Da ƙyar, kamar wanda akai ma shegen duka ya farka idon nan nashi jajir ya kalle shi

Wanda suke kira da yallaɓai ɗin yace

“Baka ji dai-dai ba amma kai requesting dawowa Abdul?”

Abdul bece komi ba se kanshi da yake shafawa, 

Yallaɓai ya ɗora da

“Ɗana meke damun ka?, se inga kamar kana abubuwan da ba normal bane”

Murmushin yaƙe Abdul yayi, murya a sanyaye yace

“Lafia lau nake sir, nima ban san time ɗin da baccin ya tafi da ni ba”

Kallon agogon hannun shi yayi yaga har time ɗin da yake tashi ya wuce sosai,

Da mamaki ya ƙara ɗago kanshi ya kalli ogan na shi da ya kafe shi da kallon tambaya, yace

“Ahm,hnm, zanzo na wuce sir,”

Kallon Abdul yake sosan gaske yake jin tausayin shi a ranshi, a cewar shi yaro ƙarami ga hazaƙa,

amma da ka kalle shi zaka gane baya cikin walwala.

Can dai da yaga Abdul ya fara tattara kayan shi yace

“ka tura min numbar Baban ka, salon ka ƙara ce min ka manta kuma”

Murmushi Abdul yayi yace

“bazan manta ba sir, zan tura maka yanzu”

Kafin Abdul ya wuce gida seda ya duba office ɗin muslim yaga baya nan, murmushi yayi yace a bayyane 

“Matsoraci”.

Har Abdul ya gama daidaita parcking ɗin shi Abbah na tsaye ta windo yana kallon shi, yana tuna ranar da murjanatu ta damƙa mishi hannun Abdul a hannun shi, sakin labulen yayi ya koma ya zauna, hannun shi ɗaya dafe da kanshi, murya a sanyaye yace

“Allah ya gafarta miki mace tagari”

Tunda Abdul ya doshi saitin ɗakin shi ya fara jin ƙauri-ƙauri a memakon ƙamshi da ya saba ji a kullum kuma a koda yaushe.

A hankali ya furta “Ta gaji kenan?”

Ta bayan shi yaji tace

“BAZAN TAƁA GAJIYAWA DA HIDIMAR KA BA AZIZ”

Can kuma ya fara jin shashahekar kuka da muryar ta, gaba ɗaya ko ina na lungun ɗakin amsawa yake, nan da nan tsiga jikin Abdul ta tashi gaban shi na wani irin bugawa, tsoro-tsoro na neman ya lulluɓe shi

Buɗe ɗakin yayi da sauri ze shige ta riƙe shi gam

A haka yana jin riƙon nata sosai, ji yake kamar an manna shi da jikin bishiya

Yayi-yayi ya ƙwace da ga riƙon nata amma ya kasa, 

A karon farko da addu’a ta faɗo mishi a rai, amma gaba ɗaya ya kasa ɗaga harshen shi ballanta na ya buɗe bakin ma.

A saitin kunnen shi yaji maganar ta yanzu

“AZIZ, KA TSAYA KA SAURARE NI, A YAU ƊAKIN KA YA FI ƘARFI NA, SHI YASA BAN BARKA KA SHIGA BA, IN KUMA TA LALAMA NA BIKA NA SAN NAN MA BA JI ZAKA YI BA, SHI YASA NA RIƘE KA.”

Abdul bece komi ba, se mutsu mutsun ƙwacewa da yake yi, gaba ɗaya ji yake kamar ƙaya na sokan shi yarda ta rungume shin

Be samu wannan damar ba

Ƙara sunkuyo wa tai saitin kunnen shi tace

“ANA SO A RABAMU DA ƘARFI DA YAJI AZIZ, 

BASU SAN YARDA AKAI HAR MUKA KAWO YANZU BA, AMMA SABODA BUTULCI DA RASHIN SANIN YAKAMATA NA BIL’ADAMA SUKE SON SU RABA NI DA KAI!

DAN ALLAH AZIZ KAR KA BASU WANNAN DAMAR, KA DAURE KA BANI DAMA IN ZAME MAKA KOMI DA KOMI NA RAYUWA”

Kafin Abdul yace komi kira ya shigo wayar shi,

Abbah na, yagani

Ƙin barin shi tai ya amsa call ɗin, tace

“IN KAJE KA GABATAR DANI AZIZ”

Ɗif yaji komi ya saki a jikin shi

Kiran Abbah ne ya sake shigo mishi, ya ɗaga da sauri

Kafin yace komi, Abbahn yace “ka same ni yanzu-yanzu Abdul”

Da “to” Abdul ya amsa, sannan ya ƙarashe shiga ɗakin  na shi dake ta faman ƙaurin abinda be sani ba.

Seda ya bubbuɗe windows sannan ya kunna turaren wuta na tsinke kafin ya cire kayan jikin shi ya shiga toilet.

******

Shiru Abdul yayi kamar baze ce komi ba, 

A nutse ya ɗaga kai ya kalli Abbah da ummie da suke jiran jin ta bakin nashi, yace

“Da gaske nake Abbah, wallahi ba warda muke magana da ita ballanta na har makamancin wannan maganar ta shiga tsakanin mu”

Kafin Abbah ya ce komi, suka ji muryar ta,

 gaba ɗaya palon amsawa yake, 

GabanAbbah ya yanke ya faɗi rass

 ummie da se yanzu tsautsayi ya ritsa da ita ta sanƙame a wajen, ba motsi ba numfashi.

Aziza tace

“TUNDA YAƘI GABATAR DANI A WAJEN KA, TO GASHI NA KAWO KAINA DA KAINA ABBAH, AJI TAUSAYI NA A DUBA MIN”..

wutar Abbah gaba ɗaya ɗaukewa tayi, sadda kanshi ƙasa yayi yana karanta duk addu’ar data zo bakin shi

In ka lura da kyau zaka gane jikin Abbahn rawa yake shima

Tunda Aziza tazo gabatar da kanta a wajen Abbah ta ɗauke hankalin Abdul gaba ɗaya da sarewar data saba mishi

Ummie ta suma, Abdul kuma baya a duniyar, Abbah kaɗai ke cikin masifa

Kaf sarauniya Aziza ta gama kai koken ta a wajen Abbah,

Abbah yai bakam kamar bashi a cikin palon, ba ta inda zufa bata keto mishi, gaba ɗaya hanjin cikin shi motsawa suke.

Har Aziza ta tafi Abbah be san ta tafin ba, tunda dama ba ganin ta yake ba sedai jin muryar ta.

Idon Abbah a rufe bakin shi ne kaɗai ke motsi, gaba ɗaya ya nemi miyan bakin shi ya rasa

A hankali Abdul ya buɗe idon shi bayan sarewar ta kai ƙarshe

Idon shi a kan momi ya fara sauka da gaba ɗaya ta tafi, rabin jikin ta a ƙasa rabi kuma a kan kujera

Abbah ya kalla da shima ya maƙure a waje ɗaya ya cusa hannuwan shi a tsakankanin cinyoyin shi idanun shi a rufe ƙam bakin shi na ta motsi da sauri da sauri.

Tashi Abdul yayi daga inda yake zaune, ya matsa kusa da inda Abbah ke takure

Hannu ya saka ya dafa kafaɗar Abbahn yana  ƙoƙarin fisgo maganar da ya kasa yi tun ɗazu

Abbah najin hannu a kafaɗar shi ya zabura yai baya, ya ƙara mannewa da kujera, ƙanƙanme idanun shi ya sake yi, 

Addu’ar da yake yi ƙasa-ƙasa ya buɗe baki da ƙarfi ya fara karanto Ayatulƙursiyu da iya ƙarfin shi.

“Abbah!, menene?”

Da sauri Abbah ya buɗe idon shi jin muryar Abdul a kusa da shi

Miƙewa tsaye yayi da sauri yai kan ummie da har yanzu ba ta motsi,

Bin shi Abdul yayi, yama rasa me zeyi, tsayawa yayi yana kallon yarda Abbah ke ƙoƙarin ganin ta dawo hayyacin ta, sam Abdul ya kasa taɓuƙa komi, dan bashi da wannan kuzarin, kamar an mishi shegen duka yake ji.

A hanjali cikin sanyi murya yace

“Abbah, kar mu barta a haka, mu daure a kaita hospital, ko kuma ka kira muslim yazo”

Abbah bece mishi komi ba, se ma tallafo ummie da yayi zuwa jikin shi, tofi ya fara mata, 

Duk ayar da tazo kan shi yake karantawa ya tofa mata

Abdul na daga gefe, da ma yaji tsayuwar na neman ta gagare shi ya koma kan kujera yai kwanciyar shi

Kafin wani lokaci bacci me nauyin gaske yai awon gaba da shi

Hankalin Abbah rabuwa biyu yayi, ɗaya akan ummie ɗaya kuma akan Abdul dake kwance

Da ƙyar Abbah ya samu ummie ta farfaɗo, amma ba cikin hayyacin ta ba, surutai take ta zubawa wanda ba lale ka fahimci me take faɗa ba, se kuma lokaci zuwa lokaci ta fara zabura tana neman ƙwacewa daga riƙon da Abbahn yayi mata.

A hakan su fauza suka riske su, hankalin su yay masifar tashi ganin ummien a haka, haɗa baki sukai wajen tambayar Abbahn abin da ya faru

Kallon Amal da tafi kusa da Tv yayi yace

“saka min karatun ƙur’ani maza”

Da sauri Amal ta juya tai abinda Abbahn ya sata

Tunda aka saka karatun ummie ta dena fisge-fisgen da ta ke, 

Abbah da yaran sukai tsuru duk da dai su basu san abunda ke faruwa ba, amma in ka kalla Abbah se ya baka tausayi.

*******

Mama ki ɗaure min kafin wata cutar ta shiga, 

Fitowar mama daga wanka kenan ta jiyo rakin zainab na danƙara mata kira, kama hannun zainab ɗin tayi taga yarda yake ta zubar jini tace

“garin yaya hakan ta faru?”

Zainab da azaba ta ishe ta tace

“ƴar baƙa ce ta tankaɗe hannu na shine wuƙar ta yanke ni”

Mama bata ce komi ba, ta kama ɗaure ma zainab yatsar da ta yanke ɗin

Seda ta gama tace

“kibi a hankali kar ta ƙara saki yankewar”

Da “to” zainab ta amsa sannan tai gaba tana jin yarda raɗaɗin wuƙar ke ratsa ta.

Tunda ta yanke ta ture latus ɗin da take yankawa gefe, takaici kamar yai mata me,

 mamaki take ta yarda ma har ƴar baƙa ta iya ta tankaɗe ta,

Ƙwata ta ja tace

“wallahi yau baki shan madarar nan, tunda har kin iya mugunta kina ƴar ƙaramar ki da ke

In kin ga dama kici abinda naci, banda mugun ta ki rasa wanda zaki cuta se ni da nake ciyar dake na shayar da ke? 

To yau sedai kici shinkafa kema”

Shiru ƴar baƙa tai tana sauraren Zainab kamar tana gane me ake cewa, 

Juyawa zainab tayi ta shige ɗaki ta barta a nan

Can kome ta tuna? ta fito, tana fitowa ta iske ƴar baƙa na ta lashe jinin da ya zuba a ƙasa

Shiru Zainab tayi tana kallon ikon Allah, a ranta tace

“Dama mage na shan jini ne?”

Can ƙasan zuciyar ta taji ance “suna sha mana, kin manta har ɓeraye suna ci? kuma ɓeraye ai suna da jini, so in ta lashe jini ba wani abu bane ai”

Ajiyar zuciya ta sauke sannan tace

“zo ki wuce muje kwaɗayayya”

Kamar tasan me ake cewa, zungwi-zungwi tabi Zainab ɗin, tana kuka “miyauuu, miyauuuh.

A daren ranar wajajen sha ɗaya da rabi, sahu ya ɗauke gidan tsit, Zainab anyi nisa da bacci

Abie na zaune yana shan ruwan da mama ta ɗakko mishi suna ɗan taɓa hira sama-sama,

Tashi mama tayi tace

“Bari in sakayo ɗakin can malam”

Da “to” Abie ya amsa mata yana kwanciya.

Kullum mama a ɗakin Abie take kwana, kafin ta tafi ɗakin shi takan kullo nata ɗakin.

Janyo ɗakin tayi ta saka key,

Juyowar da zatai taga ƴar baƙa bakin ta jina-jina da jini tana ta kokawa da wani danƙareren jan nama da ba za’a iya tantance dabbar ba,

“a’uzubillahi minashshaiɗanirrajim” mama tace, a hankali saɗaf-saɗaf tai maza ta shige ɗakin Abie da har bacci ya fara ɗaukan shi a hankali

Motsin mama da yaji da ƙarfi ne ya farkar da shi yace

“ya akayi ne Binta?”

Murya ƙasa-ƙasa mama tace 

“taso ka ga wani abu malam”

Da sauri Abie ya tashi ya saka jallabiyar shi, gaba yayi mama ta bishi a baya

Suna fita shima idon shi ya sauka akan ƴar baƙa da ta kusa cinye naman

Motsin su da taji ta ɗaga kai ta kalle su, tana ganin malam ta saki naman ta danƙara da gudu ta shige ɗakin zainab da bacci ya ɗauke ta bata rufe ba

Abie da mama suka rufa mata baya suma da sauri

Suna shiga ɗakin suka iske ƴar baƙa kwance a gefen Zainab tana ta kwasar bacci hankali kwance, ba wani alamun jinin da ya yai mata faca-face da suka gani a ɗazun

Ido waje mama ke kallon Abie dake ɗan murmushi

Be ce wa mama komi ba, ya juya ya kalli bangon gabas ya karanta falaki da nasi, se ayatulkursiyu, sannan ya rufe da amanarrasulu, ƙafa uku-uku ya karanta sannan ya tofa a bangon gabas ɗin

Ya juya bangon yamma ya karanta, duka seda ya tofe bangon gabas, arewa, kudu da yamma, sannan yaja hannun mama da ta daskare da mamaki suka fito tsakar gidan, bayan Abie ya janyo ma zainab ɗin ɗakin.

Suna fitowa tsakar gidan ya duba naman da ta gudu ta bari yaga yana motsi kamar wanda akwai rai a jikin shi

Kallon shi mama tayi ganin yayi bisimillah ya ɗauki naman yana jujjuya shi a hannu,

Murmushi taga Abie yayi sannan ya nufi hanyar soro da shi

Da sauri mama ta bishi tace

“malam ba dai fita zaka yi ba?”

Waigowa yayi yace

“zan yarda shi ne, ta ƙarashe abin ta a waje ba dai a gidana ba”

Shiru mama tai bata ƙara cewa komi ba, har Abie ya buɗe ƙofar gida yai bisimillah sannan ya wurgar da naman

Rufe gidan yayi sannan ya karanta “BISMILLAHILLAZI LAA YA DURRU MA’AISMISHI SHAI’UN FIL ARDI WALA FISSAMAI WA HUWASSAMI’UL ALIM!”

Sannan ya tofa ma ƙofar ya ja hannun mama zuwa cikin gidan.

Bayan sun shiga ɗaki mama tace

“Malam, al’amarin magen Zainab na bani mamaki daga jiya zuwa yau, ni sam bana son ta da magen nan wallahi”

Seda Abie ya cire jallabiyar shi ya zauna a gefen maman yace

“bani labarin me da me kika gani game da ita?”

Mama tace

“jiya na aje garin accan da zan maka tuwo nazo na iske ta zubar da rabi, rabin kuma ta cinye shi, abin ya ɗaure min kai malam, ban taɓa ganin inda mage ke cin gari ba.

Sannan ɗazu da safe nagan ta da idona tana cin kashin ta da tayi fa malam, mage da na san tana da tsafta, se ɗazu gab da ayi sallar magariba zainab ta shigo hannun ta duk jini wai in ɗaure mata, da na tambaye ta ya akai ta yanke? se cemin tai wai ƴar baƙa ce ta tankaɗe hannun ta tana cikin yanka latus.

Gaskiya malam akwai alamun tambaya anan”

Shiru Abie yayi yana sauraron mama, seda ta gama maganar ta tas sannan ya jawo ta jikin shi

yace

“Ni ban san matata da tsoro ba gaskiya, abinda kike tunani ba shi bane ba, wata magen ce daban ba ƴar baƙa ba”

Shiru mama tayi ta lafe a jikin ɗan tsohon mijin ta

Abie ya ƙara cewa, “Dani suke magana, kin ga zo mu kwanta dare na yi”.

Gaskiya Abbahn Abdul a nema mishi wata, har yanzu Ruky bata dawo hayyacin ta yarda ya kamata ba, ko sunan gidan nan aka ambata a gaban ta se ka ga tsoro ƙarara a idanun ta.

Shiru Abbah yayi dan gaba ɗaya ya rasa madafar da ze dafa akan lamarin Abdul ɗin

Murya a sanyaye ya ce

“Abdul fa kamar ɗanki yake Asiya, in kika daure aka haɗa su auren se kiga matsalar shi ta kau, ki daure kema ki samu ladan ɗan maraya Asiya”

Kallon Abbah ummie tayi sannan tace

“Aiyukan ladan suna da yawa Abbahn Abdul, 

ita kanta Ruky ai marainiya ce, gaskiya ba zan yarda a saka ta cikin matsala ba, ƙiri-ƙiri nuna min fa kake tazo tayi zaman  KISHI DA ALJANA”

Ƙwarai da gaske maganar Ummie ta ɓata wa Abbah rai, daurewa kawai yake ya samu ya nemar ma ɗan shi mafita akan wannan matsala da ta ke neman fin ƙarfin su.

Abbah be karaya ba yace

“Tunda naƙi samun mafita daga wajen ki ke da kika san matsalar ɗana, zan je in nemi alfarma a wajen ita Ruƙayyar, kinga in ta yarda se inje in samu yayan mahaifin ta in nemi auren ta a wajen shi”

Bata ce mishi uffan ba, dan ta san ko duniya da abinda ke cikin ta za’a ba Ruky ba zata yarda ba, bama kamar a yanzu da take a firgicen nan.

Abbah beyi ƙasa a gwiwa ba, da yammacin ranar ya nemi yayan Baban Ruky inda riƙon ta ya koma wajen shi, 

Bayani sosai Abbahn yayi mishi, gani da la’akari da ita kanta Rukyn a baya ta nuna ra’ayin Abdul ɗin

Yayan baban nata be yanke Abbah ba har ya gama gaya mishi abinda ya kawo shin,

Seda ya gama jin Abbahn tas, sannan yace

“Indai yarinya ta yarda ba abune me matsala ba, yanzu muje mu gabatar da sallar magariba, in yaso se a kirata a tambaye ta a gaban ka, indai ta amince shikenan, itace me zama ba wani ba”

Cike da ƙwarin gwiwa Abbah yace

“Bakomai, muje to”.

Tunda Ruky ta shigo palon tai ido biyu da Abbah gaban ta ya yanke ya faɗi,

Da sauri ta maida kanta ƙasa tana karanto duk addu’ar da tazo bakin ta.

Ita ko a mafarki bata fatan ta ƙara ganin wani me kama da Abdul ballanta na Abdul ɗin kan shi

Kamannin Abbah da Abdul kamar an tsaga kara, sedai banbancin shekaru.

Yanayin ta kawai Abbah ya gani jikin sa yai sanyi

Shiru yai ta kasa magana, se yayan Baban fa ne yai mata bayanin abinda suke shirin yi na haɗa su aure da Abdul

Be ma ƙarasa maganar shi ba Ruky ta miƙe tsaye, ido a waje take kallon yayan Baban nata

Baki na rawa ido na marmar, alamun kuka na gab da ƙwace mata

Ƙiftawa da bisimillah suka nemi Ruky suka rasa

Fellawa da gudu tai ta bar palon

Baki sake Abbah ke kallon hanyar da Ruky tabi,

Ya jima yana kallon hanyar kafin daga bisani ya ce

“kar ku matsa nata, Allah ze kawo mana mafita da ikon sa”

Shi kanshi yayan baban nata, ya amsa mi shi ne kawai, amma maganar da sukai da Asiya(ummie) ɗazu be kamata ka ɗauki ɗanka ka miƙa shi ga halaka ba, kawai dai ba’a daka ta mutum ne.

Cike da girmamawa Abbah yai mishi sallama, sannan ya kama hanyar kmawa gida.

Abbah na tafe yana tunanin ina ze samo ma ɗanshi mafita, gaba ɗaya kanshi ya kulle,

Inda yake tunanin yana da hope, shima yaje ba nasara

Dummmm, haka yaji zuciyar shi ta amsa, jin ta ambaci “ZAINAB”

Dogon shiru Abbah yayi yana ta maimaita sunan a cikin ranshi, daga baya kawar da tunanin yayi, 

yace a bayyane

“Malam ya san komi, shima baze bar ƴarshi ta faɗama halaka ba, ballanta na na hango tsantsar ƙaunar da ya ke mata”

Huci me zafi Abbah ya fesar haɗe da kiran sunan ubangiji.

****

Abie na zaune a ƙaramin palon sa yana hutawa bayan ya gama koyar da karatun bayan isha, anan mama ta iske shi da kayan abinci da ta haɗo mishi

Yana zaune yana ƙara nazarin littafin gaba shi maman ta shigo

Rufe littafin yayi yana amsa sallamar ta, abincin ta aje a gefen shi sannan ta zauna itama, tace

“Sannu da ƙoƙari malam”

Murmushi Abie yayi yace “sannun ki uwar zainaba Amaryar ƴan kwanakin nan”😳

Baki sake Mama ke kallon Abie da ya basar yana janyo tray ɗin abincin gaban shi.

“Malam kamar banji me kace ba fa”

Murmushi Abie ya sake yi be dai ce komi ba, 

Wayar shi dake gefe kira ya shigo, 

Jawo wayar yayi, ya ƙara a kunne haɗe da sallama

Banji abinda aka faɗi daga ɗayan ɓangaren ba, na dai ji Abie yace 

“Allah yayi muku albarka Muslim”.

Haka nan Abbah ya gama shawagin shi ya koma gida rai a jagule.

Sanda ya shiga gidan ko ta kan abinci da ummie ke gabatar mishi be bi ba,

Amal ya ƙwala ma kira 

Amal na tsaka da waya da saurayin ta taji kiran Abbah

Da sauri ta yanke wayar ta tashi ta fito “gani Abbah”

Abbah na daga tsaye ta wajen ƙofar palon shi yace

“ɗan samar min rushi me ɗan yawa”

Da “to” ta amsa, ta wuce kitchen ɗin direct, 

tana shiga ta fito tace

“Babu gawayi a inda ake ajewa Abbah”

Kallon ummie Abbah yayi, yace

“shisha coal ɗin da na siyo ɗazu suna ina?”

Harara ummie ta galla wa Amal tace

“Kin saba wannan halin, baza ki duba abu ba se ki zo kice baki gani ba”  

“Dallah gafara min a hanya” ummie tace tana shiga kitchen ɗin da kanta.

Neman duniyar nan ummie tai ma gawayin da ta aje shi da kanta ɗazu da Abbah ya kawo, amma bata gan shi ba,

Da mamaki ta dawo palon,

 Abbah na nan tsaye a inda ta barshi yana jira tace

“Wallahi Abbahn Abdul ban ganshi ba nima, kuma da hannun nan nawa fa na aje shi ɗazu”    tai maganar tana kallon hannayen ta.

Shiru Abbah yayi, a ranshi yace  “Ta ɗauke shi!”

A hankali, murya can ƙasa yace

“innalillahi wa’inna ilaihirraji’un!”

Ummie ce ta katse shirun tace

“Me zaka yi da shi ne wai?”

Kallon ta Abbah yayi da idanun shi da suka fara kaɗawa zuwa launin ja yace

“Zan turara gidan ne da habba”

Tsit ummie tayi, da ta tuna abunda ya faru da su jiya, ta hau baza idanu

Amal na tsaye bata koma ɗaki ba, 

Suna a haka Abdul yai sallama ya shigo cikin palon shima, 

Gaba ɗayan su ido suka zuba mishi yarda ya shigo yana wani sinne kai kamar wanda ya shigo wajen sirikan shi.

Gaishe su yayi, sannan yace

“Lafia kuka tsaitsaya haka Abbah?”

Numfashi me ɗan huci Abbah ya fesar yace

“Gawayi na siyo ɗazu, amma ƙiri-ƙiri sun rasa a inda suka aje shi wai, gashi ina son inyi amfani da shi”

Shiru Abdul yayi na ɗan lokaci, can yace

“Bari in kawo maka, ina da shi a ɗaki na”

SUN SAN ABDUL MA’ABOCIN SON ƘAMSHI NE, BAYA RABUWA DA IRIN WAƊAN NAN ABUBUWAN.

Da “to” Abbah ya amsa, Abdul kuma ya juya ya fice,

Can ba ɗau wani dogon lokaci can-can ba ya dawo ɗauke da kwali ɗaya na shisha coal babba ya miƙa ma Abbah da har yanzu suke anan tsaye.

Har Abdul ya juya ze tafi Abbah ya kira shi ya dawo

Ledar hannun shi ya buɗe, sannan yace

“Bari in ɗibar maka wannan garin habban, kaje da shi, ka tabbatar ka turarashi yanzu kafin ka kwanta”

Miƙa mishi Abbah yayi, ya amsa yai musu sallama ya juya ya fice

Tun shigowar Abdul na farko Amal ke binshi da kallo, 

Sosai ta kafe shi da idanu tana son ta gane wani abu tattare da shi

Ilai kuwa ta gane, yana fita Amal ta kalli Abbah tace

“Abbah, naga yaya Abdul na ɗingishi, kuma Abbah, yaya Abdul baya sa jallabiya har ta kai ƙasa ballanta na ta rinƙa sharar ƙasa, wallahi kuma naga gefen idon shi ɗaya kamar na wata mujiya da na taɓa gani akan motar yaya Abdul ɗin”

Da gudu ummie tayi kan Amal ta mamutse ta alokaci ɗaya tana damtse mata bakin ta da hannu ɗaya

A dai-dai nan Abbah shima yaji gaban shi ya yanke yai wata mummunar faɗuwa, tsiga jikin shi na tashi gaban shi na dukan wani uku-uku.

Amal dake mutsu-mutsun ƙwacewa daga riƙon da ummie tai mata, tace

“unmie kema abun ya baki mamaki ko?”

Da ƙarfi ummie ta buge bakin Amal tace

“dan ubanki kima mutane shuru kar kija mana wata danƙareriyar lukutar masifar da daren nan”

Shurun kuwa Amal tayi tana kallon ummie da mamaki sosai a fuskar ta

Yarda ummien ke haɗa zufa tana muzurai kamar me jin zawo, dole abun ya ba Amal mamaki.

Abbah kuwa umarnin zuciyar shi yabi, be tsaya ɓata lokaci ba ya doshi hanyar fita daga palon

Da gudu ummie ta saki Amal, tai kan Abbah ta riƙoshi gam,

Fashewa da kuka tayi tace

Dan Allah Abbahn Abdul kar ka fita kazo ka gano mana wata masifar da ba zamu iya shawo kanta a cikin daren nan ba, inda ma dai da rana ne, da se mu fice a gidan wannan mun san ido na ganin ido ne”

Ƙwacewa Abbah yayi daga riƙon da Ummie tai mi shi, yace

“ina zuwa Asiya, akwai abunda nake son gani”

Kuka sosai ummie ta ƙara sakawa, ga Abbahn ya fita gashi ita bazata taɓa iya bin shi ba

Baki sake Amal ke kallon ummie dake ta sharɓan kuka,

Kuma tambayar duniyar nan Amal tai mata amman taƙi cewa uffan

Da sauri Amal tai hanyar waje itama zata bi Abbahn wai

Damƙota ummie tayi ta zabga mata wani bahagon mari da seda wutar kanta ta ɗauke tsabar yarda marin ya shige ta

Ummie batai wata-wata ba taja Amal ƙiii zuwa ɗakin su

Fauza na kwance bacci ya ɗan fara ɗibar ta taji an wullo Amal kanta, da sauri ta miƙe  zaune tana mazurai da idanu itama.

Abbah na fita daga palon yai hanyar ɗakin Abdul dake ɗan baya, addu’o’in da duk yasan ya iya ya rinƙa karantowa, 

Ƙirjin shi na dukan uku-uku amma haka yai ta maza ya zagaya 

Har ƙofar Abdul ɗin yaje, be sha wahalar bugawa ba dan a buɗe yaga ƙofar.

Daga waje ya ƙwala kiran Abdul ɗin, shiru yaji ba amsa

Seda Abbah ya kira shi ya kai sau biyar tukun ya ji muryar Abdul dake cikin maganin bacci ya amsa

Ƙara kiran sunan shi Abbahn yayi, 

A kasalance na irin wanda suka jima da yin baccin nan Abdul ya tashi ya fito daga shi se gajeran wando, ko gani da kyau baya yi saboda baccin da yaci ƙarfin shi

Tun daga sama har ƙasa Abbah ke kallon shi, 

Seda ya ƙare mishi kallo tas tukun ya fizgi hannun shi da sauri yai hanyar cikin gida da shi.

Gaf da Abbah zasu shiga palon yaji an fizge ledar dake hannun shi anyi wurgi da ita, 

Tas garin habbatussaudan dake ciki ya watse yai ɗai-ɗai a wajen.

Be tsaya bi takan wannan ba ya shige, se a sannan Abdul ya dawo nutsuwar shi sosai ya kalli Abbah dake figar shi kamar wani ƙaramin yaro.

Jin motsin shigowar Abbah ya fito da ummie dake ta muzurai

Tana fitowa ta ganshi da Abdul, 

A sukwane ta juya cikin ɗakin tana danno ƙofar da mugun ƙarfi.

Abbah be tsaya ko ina da Abdul ba se ɗakin shi, yace

“Ka kwanta a nan, ina zuwa”

Kamar sakarai Abdul ke kallon Abbahn nashi da ya buɗe cikin walldrop ɗin shi ya ɗakko mishi jallabiyar shi ya bashi

karɓa yayi, sannan yace

“Abbah lafia kuwa?”

Dan Abbah ya ƙara tabbatar da zargin shi yace

“a ina ka aje maganin da na baka ɗazu?”

Shiru yayi yana kallon Abbahn da gaba ɗaya in ka kalle shi zaka san baya cikin nutsuwar shi, yace

“Baka bani komi ba Abbah, ni tun bayan magrib na kwanta bacci ya ɗauke ni, ko isha’i ba samu damar yi ba”

Shiru Abbah yayi yana ƙara maimaita “innalillahi wa’inna ilaihirraji’un.

Katse shirun nasu Abdul yayi yace

“zan iya tafia Abbah?”

Da sauri Abbah yace, “a’a, ka kwanta a nan, ban yarda da ɗakin can naka ba”

Abdul be ƙara cewa komi ba ya shiga toilet ɗin cikin ɗakin.

Abbah na ganin Abdul ya shiga toilet ya fito palon shi ɗauke da waya a hannun shi

Kwata-kwata beyi la’akari da cewa dare yayi ba yai dialing numbar Abie.

gaf da wayar zata tsinke Abie ya ɗaga haɗe da sallama yace

“Allah yasa ba wani problem bane Alhaji Ibrahim?”

Kamar me in ina haka  Abbah ya fara ma Abie bayanin duk wani abu dake faruwa

Shiru Abie yayi yana sauraren Abbah,

Seda ya gama tas tukun Abie yace

“Yanzun nan ta bar nan,”

Ba ƙaramin faɗuwa gaban Abbah yayi ba jin abinda Abie yace

Abie ya ɗora da “babu wani abu da zata iya yi, kai dai kayi abinda nace kayi, sannan kuma ka tofe ko ina na gidan da falaƙi, nasi, ayaturkirsiyu da  amanarrasulu, inshaAllah zakuyi baccin ku cikin salama, sannan kuma zuwa gobe ka turo min Abdul ɗin ina son ganin shi.

Godiya sosai Abbah yayi, sannan sukai sallama.

Ba wani ɓata lokaci Abbah ya tashi, ya tofe lungu da saƙo na gidan nashi, sannan ya ɗan samu nutsuwa a cikin zuciyar shi.

(KUMA ZAKU IYA YI A NAKU GIDAJEN, BA LALE SE KUNA DA MATSALA MAKAMANCIYAR IRIN WANNAN BA, DUK NEMAN TSARI NE, ALLAH YA TSARE MU DA TSAREWAR SA)

A RANAR DA YAMMA.

Tunda Zainab ta fito daga gidan iya ta haɗu da wata mata, ita ba tsohuwa ba, ita ba yarinya ba, ƴar dattijuwa haka dai

Kusan a jere suke tafiya, ba wanda yace ma wani uffan, har suka kawo bakin titi kusan a tare

Suna nan a tsaye me kekenapep yazo ya tsaya, 

Shiga Zainab tayi ta gaya mishi inda ze kaita

Har zasu ɗaga su tafi wannan dattijuwar ta shiga itama.

Murya ƙasa-ƙasa tace, NY jection zan sauka

Me keken yace “ɗari ne kuɗin ki mama”

Bata ce komi ba har suka fara tafiya, gaba ɗaya idon ta na kan zainab da ƴarbaƙa dake kan cinyar ta tana bacci

Sarai Zainab ta lura da kallon da matar nan ke mata, 

So take ta tanka amma zuciyar ta na kwaɓar ta da tai shiru

Sunyi ɗan nisa Zainab ta kasa haƙura sam da kallon ƙurillan da dattijuwar ke mata tace

“Tsohuwa, naci ban biya bane?”

Shiru matar ta yi amma bata ce komi ba se ci gaba da kallon ta da tai

Waigowa sosai Zainab tayi ta kalli matar a ido, 

Suna haɗa ido taji gaban ta yai mummunar faɗuwa, har seda ta ɗan dafe saitin zuciyar ta

Da sauri Zainab ta rumtse idanun ta haɗe da faɗin 

“A’uzubillahi minashshaiɗanirrajim!!”

Da sauri matar ta kawar da idanun ta takoma kallon waje

A hankali Zainab ta buɗe ido tana kallon yarda matar ta juya, ƙare mata kallo tas tayi

Addu’oin neman tsari Zainab ta fara karantawa, dan jikin ta na bata cewa ba mutuniyar kirki bace ba.

Gaba ɗaya jikin dattijuwar nan kyarma ya fara, bata zo inda zata sauka ba tace  “tsaya zan sauka a nan”

Tsayawa me keken yayi, ta sauka, ido cikin ido zainab ta kalle ta tace

“Aniyar ki ta biki ƴar tsohuwa”  Ta ƙyalƙyale da dariya tai mata gwalo,

Har sukai nisa zainab bata dena kallon matar nan tana mata dariya da gwali ba.

ALLAH KASA ANNABI MUHAMMAD YA CECE MU🙏

Back to top button