Uncategorized

Abban Sojoji Chapter 8 Complete Hausa Novel

 

“`The father Of Soldiers“`

        

Story 

     &  

       Written 

       By 

      Hafsat Bature

          (Boss Lady)

“Yeah but we are not sure, ba tabbacin cewa gobe zasu dawo, muna zuba ido dai,’ kanal yusif ne ya bashi amsa,

Jinjina kai captain najeeb yayi tare da cewa “aiko bazan kwana ba, yau zan koma lagos, ba dani ba

dariya su kayi hajiya azeema tace “ashe muna da manyan baƙi, lion da tiger zasu dawo kenan, wannan karan bansan da wata rigima zai zo ba, Allah kaɗai yasan jinin da za’a zubar,’ 

    Hankalisu twins ba ƙaramin tashi yayi ba dama suna zaune matse da juna, sunyi zuru zuru, zuciyoyi na bugawa,

 Basu kaɗai ba hada fawan da su jabeer da irfan da sauran atakure suke jin kansu, a wurinsu zuwan Babban yayansu ba alheri bane, bawai don basu son shi ba, sai don tsoran abunda zai faru zuwansa, 

“ae na jima ina bama ishaq shawara akan ya tunzura Abba, ya aurar dasu, wlh indai su kaji mace atare dasu zasu samu weakness ajikinsu su daina jin kansu tamkar dodonni,’ sakin baki su kayi jin abunda aunty babba tace,

Azeema tace “da alama bakisan wanene RAFAYET ba, ai rafayet zuciyarsa tamkar dutse take ! ban ta6a ganin mutumin da mace sam bata gabansa ba irinsa, sam bai da shauqi akan mata, ke shi fa hasalima yadda yake kallon jinsin sa namiji haka yake kallon mace,’ 😧

ta ƙarasa maganar tana kurbar lemun hannunta, general ishaq yace “kwara ki faɗa mata da kanki may be she will understand it now, i had been explaining to her about rafayet but taƙi fahimta,’ ya ƙare maganar yana kallonta,

Murmshi azeema tayi tare da gyara zama tace “Anzo inda nafi auki, anzo dai dai wurin ba mai sauka, rafayet da kike gani ba mutun bane …….. 

dariya ce ta kubce mata su kansu dariyar suke ba don komai ba sai don maganarta takarshe da tace rafayet ba mutun bane, 

Download>>> Aziza Da Azima Macizai Ne Complete Document

dakyar ta saita dariyar ta ci gaba da cewa, ” Ai dashi da mahaifiyarsa halinsu kusan ɗaya ne, kaifi ɗaya ne wasu irin bauɗaɗɗun mutanene, koda yake in mukayi la’akayi da cewa mahaifiyarsa baturiya ce, sannan kuma ba musulma ba, yanayin rayuwarmu da tasu ba ɗaya bace, amma gasky munsha Wahalar fatima fiye da tunanin mai tunani, ta azabtar damu saboda muna kwakwar ƴa’ƴanta, har yau fa ita bata yarda cewa Allah ɗaya bane, taƙi karbar musulunci, kuma bata yarda cewa ƴa’ƴanta sun musulunta ba, in har zasu taka suje wurinta to fa basu ba yin sallah ko karatun qur’ani sai dai in ba dasaninta ba, dakyar fa aka samu rafayet ya musulunta har yakai shekara 20 aduniya ba shi ba musulmi bane, 

ta tsagaita da maganar tana sauke ajiyar zuciya, gaba ɗaya sauraronta sukeyi, musamman Aunty babba da Amani su da basu son komai ba game da su rafayrt ba, 

Su twins kuwa da fawan jikinsu yayi sanyi domin ana magana ne akan mahaifiyarsu, 

Aunty babba tace “nikam inaso nason wacece fatiman nan, ya akai abba ya aure ta ba tare data karbi addinin musulunci ba, Kuma har akayi gangancin barin ya’yanta suyi koyi da addininta ina nufin rafayet da ki kace yakai 20 yrs batare da yakarbi addinin musulunci ba, sannan ina fatiman take a yanzu, don ni ban ta6a ganin ta ba,’ 

Anzo dai dai wurin, ina fata kowa zai kasa kunnansa ya saurara muda akayi agaban mu, acewar aunty azeema

 

 …….  ………….Bismillah……… ………….

Asalin family ɗinmu Hausa fulani ne, mahaifin.mu bahaushe ne haifaffen garin zariya, mahaifiyarmu kuwa bafullata ce yar jihar damaturu, Haɗuwarsu tafarko a barikin sojoji na kaduna state Allah ya haɗa jininsu har takai su gayin aure ❤

Mu uku ne a wurin iyayenmu banban cikinmu Shine hussain wato (Abban sojoji) tagwaye ne su Allah yayiwa hassan ɗin rasuwa tun kafin su mallaki hankalinsu, Akwai tazarar shekaru a tsakanin mu sosai dashi, shi ne nafarko sai kuma ni azeema daga ni kuma sai ƙanin mu gaba ɗaya, wanda shine autanmu mun girme shi sosai, wato ABUSUFYAN wanda ynx yake zaune a Ƙasar turkey,’

 tun yana 20years a duniya, wan mahaifiyarmu ya bashi auren ƴarsa maryam, yarinyace mai ilmin addini sosai ga hankali da natsuwa, maca ce mai saukin kai, bata ɗauki duniya da zafi ba,

Itace matarsa ta farko, sun sha sosai kamar laila da majnun, domin mu kanmu shaida ne akan hakan, duk in yana gari tashiga tarairayarsa kenan, idan aka turasa aiki kuwa nesa ba ƙaramain shiga damuwa take yi ba, duk tabi ta susu ce, 

Abban mutunne mai son ƴa’ƴa koda yake bashi kaɗai ba, mu dukkan mu haka muke da son ƴa’ƴa zumuncin family ɗinmu yana da ƙarfi sosai, bama wasa da sada zumunci, 

Cikin ikon Allah maryam ta samu ciki, kowa ya hau murna musamman ammin mu grandma ɗinmu, dayake maryam mutuniyarta ce tana sonta sosai kasancewarta yar yayanta modibbo,

Haihuwa tafarko maryam ta haifo kyakkyawan ɗanta, santalelen yaro yaci sunansa Ishaq (wato general ishaq) daga shi kuma sai Abbas wanda ynx yake rike da mukamin colonel general, daga Abbas sai brigadier general Abuhaisam gashi nan zaune kuna ganinsa,  daga shi kuma  sai major genaral Osman dukansu tazarar 2 years ne a tsakaninsu su duka, daga shine maryam ta ɗan huta, 

Bayan nan ne tafiya ta kama su Abba izuwa ƙasar america, an tura su zuwa halartar wani special training na sojoji da za’a gudanar, da courses na dabarun aiki, 

Hankalin maryam ba ƙaramin tashi yayi ba, jin za’a tura mijinta ƙasar turai, tsoranta kada wata tagansa ta liƙe masa Acan, saboda yana da farin jini sosai, 😇

Aiko hakance ta faru domin kuwa da zuwan su Abba u.s wata zankaɗeɗiyar budurwa kyakkyawar gaske ta ƙella ido tagansa taji cewa duk duniya bawan da take so sai shi, 

baturiyar ƙasar amurika sunanta Alexandra ita ƴa’ce ga commender in chief na armed forces, 😯 

Mace mai tsananin ji da kanta, ita a tsarin rayuwarta, Namiji baya gabanta, idan akayi mata maganar aure sai tace, ita jin kanta take yi tamkar namiji don haka ba abunda zaisa ta yin aure don tafi ƙarfin ta zauna a ƙarƙashin wani, idan akayi mata maganar ɗa kuwa, sai tace ita karenta tony ya ishe ta, wani jibgegen kare ne Wanda ta raine shi tun yana jinjiri har ya fara tsufa, 

Download>>> Dan Daba Complete Document

Abba shine namiji na Farko daya karya wannan kudurin nata, At first sight taji duk duniya ba wanda yai mata sai shi~

Kuma gadan gadan taji tana son aurenshi, Iyayenta sun so su dakatar da ita, amma dayake su in yaro ya wuce 18yrs yana da ƴanci ba wanda ya isa ya takamasa burki, har shari’a zai iya yi da iyayensa insun takura masa,

Hakan yasa suka ƙyale Alexandra ta auri Abba, ba tare da sanin family ɗinsa ba, shi kuma soyayya ta rufe masa ido baya ganin kowa in ba ita ba, dama fa su akwai iya tarairaya ga ɗaukar wanka da jan hankali, 

A nan los angels california  suke da zama a katafaren gidanta, nata na kanta dayake itama ta tara kuma ta fito daga babban gida, kuma ita ma soja ce tana riƙe da muƙamin major genaral,

Sunsha soyayya kamar romeo da juliet, acan kuwa 9ja sunyi mamakin jimawar abba, ganin sauran da aka tura Us tare dashi duk sun dawo sai shi kaɗai,

Ga maryam da ƙaramin ciki, kullum cikin zullumi take akan mijin nata, 

time ɗin daya shirya dawowa 9ja yasha wahala kafin Alexandra ta amince cewa zata biyo shi na wucen gadi,

Aiko lokacin sun ga tashin hankali, ganin abba ya dawo da mata jinsin turawa, ran mahaifiyarmu baƙaramin 6aci yayi ba, saboda ta tsani jinsin turawa, sbd tasancewa basu da kunya fitsararru ne, an tada tarzoma a lokacin, gaba ɗaya danginmu sukayi masa caaa akan alexandra,

Amma abun mamaki mahaifinmu Salahudeen ya amince masa, kuma ya tsawatar da kowa akanta, ya hana kowa ya sa baki akan alexandra, haka yayan mahaifiyarmu modibbo ya tsawatar mata akan taja bakinta tayi shiru, haka kowa ya zubama sarautar Allah ido 👀

A katafaren gidansa dake abuja suke zaune ya ware mata part ɗinta daban, na maryam ma da ya’yanta daban, kowa baya shiga harkar kowa, 

Sam maryam bata kishi da alexandra, tafison su samu zaman lafia a tsakaninsu,amma ita alexandra kishin maryam take ji, bakomai yaja hakan ba face sanin cewa su ba’ayi musu kishiya, basa zama da kishiya, 

Cikin rashin sani sai ga ciki a jikin alexandra wanda ya tayar mata da hankali saboda tana shan maganin hana ɗaukar ciki don ita bata buƙatar ƴa’ƴa arayuwarta, 

Download>>> Layla Maleek Complete Document

taita faman kiciniyar cire cikin hankalin abba ya tashi, faɗa sosai sukayi a lkcn, yasha wahalarta sbd sai da takai ga har zuƙunna mata yake akan guiwarsa yana roƙonta akan karta cire masa ciki yana so, 

dakyar ta amince bisa sharaɗin inta haihu, ba ita zata shayar da yaron ba, kuma ba a nigeria zata haifesa ba, tafi so taje can ƙasarsu saboda tafi yarda da likitocinsu, kada a kashe  ta tsoran mutuwa gare ta, 😂

haka ta maida Abba kamar ɗan aikinta da matsayinsa da komai haka zai zauna, yana mata aiki komai takeso shi zatayi, ita dai maryam bata cewa komai binsu kawai take da ido 👀

Hankalinta kwance saboda haryanzu Abba yana tsananin sonta bai wulaƙanta taba, bai kuma canza mata ba, sa6anin wasu mazan da zaka gani daga inda suka yi sabuwar amarya tofa ita waccen tazama expire product, 😥

wata rana yana zaune ɗakinsa saiga alexandra ta shigo da ƙaton cikinta, hannunta ɗauke da farar takarda da wani rubutu ajiki wanda aka rubuta da harshen spanish, ta miƙa masa takardar da biro tace yasa hannu, 

_Gudun rigima yasa bai tambaye ta takardar mecece ba kawai ya raftaka signature ɗinsa, ajiki tare da miƙa mata , tayi murmushi ta kar6a…

a na nan lokacin haihuwarta yayi, abba dakansa yakai ta Airport kamar yadda yayi mata alƙawari,

kuma ya cika, 

Cikin sa’a Alexandra ta haifi santalelan yaronta na farko, wanda ya gigita kowa, kyakkyawan gaske mai matuƙar ɗaukar ido, komai nasa na mahaifiyarsa ne ya ɗauko, hatta launin idonta blue eyes,

Ta jima a us kafin ta zo nigeria, domin ta gwada musu babynta, aikuwa nan fa dangi suka susuce akansa, amma ta hana kowa ya ta6a mata yaronta, iya kallo daga nesa, jinsa take tamkar gold koda yake darajarsa tafi darajar zinari, 

Abba yayi mamakin ganinta tana shayar da yaron, bayan ita da kanta tace anemi mai raino don baxata shayar dashi nono ba inyazo duniya, da alama soyayyar yaronce ta kamata, 

A lokacin itama maryam ta haifi nata yaron kyakkyawan gaske wanda duk cikin ya’yanta bamai kyansa, farinciki a wurin abba ba’a magana a lokacin yama rasa ina zai tsoma kansa, saboda ƙaunar yaran nasa da aka haifa masa, 

Babban tashin hankalin shine, Alexandra ta tada 6alli akan cewa yaronta addininta zai biyo kuma tasanya masa suna Alex, nan fa hankalinmu ya tashi, kowa ya harzuƙa akan lamarin, 

Ran abba ya 6aci sosai kamar yayi ihu, a ƙarshe daya takura mata akan cewa shifa yaronsa addininsa zai biyo, sai ta ɗauko masa wannan takardar daya sa hannu ajiki wadda akayi rubutu ajikinta da harshen spanish ta nuna masa,

Cikin rashin sanin ma’anar hakan yace “me wannan ke nufi”?

Dariya tayi masa tare da cewa ” wannan takarda dace, ta yarjejeniya dake nuna cewa ka amince ƴa’ƴana su bi addini na! in har ka matsamin zamu shiga court ne ayi shari’a, kuma kada kayi tunanin zaka iya ɗauke takardarnan domin akwai copy ɗinta awurina ba ɗaya ba, signature ɗinka ne ajiki, 🙆

Download>>> Bazata Complete Document

Hankalin abba fa ya tashi, bai ta6a dana sanin auren Alexandra ba sai alokacin domin takaisa ƙarshe, Ashe wayau tayi masa, tasan hakan zai faru shiyasa tayi rubutun da harshen spanish, shi kuma gudun rigima ya sa bai tambayi menene fassarar abunda aka rubuta ajiki ba kawai yasa hannu, 😥

yaso ya tada 6alli akan koma mai zai faru sai dai ya faru , amma maryam ta dakatar dashi takwantar mashi da hankali ta nuna masa cewa, inya bi komai asannu wata rana ita da kanta zata canza, canjin da har yau muke jira amma Alhamdllh an samu ci gaba,

Bakowa bane wannan yaron  da ake tada jijiyoyin wuya akansa ba face Surgeon general Rafayet wato BABBAN YAYA,

tun yana jariri bai ta6a kuka da hawaye ba, kuma likitoci sun tabbatar da cewa lafiyarsa garas, amma momynsa har ƙasar waje ta fiddasa aka ƙara dubasa aka tabbatar mata da lafiyarsa, sannan ta yarda, 

A lokacin da yana yaro yayi tashen ƙiwuya, ya tsani bakar fata indai launin fatarka ba fara bace irinta mahaifiyarsa tofa kun raba jaha, 

Duk bala’inka baka ɗaukarsa, hatta mahaifinsa dake mutuwar son shi, bai yarda da shi duk da hasken fatar abban nasa, tsakaninsu sai dai kallo daga nesa , sai kuma in yana bacci uban ya lalla6a yaje ya zuba mishi ido yana kallonsa, 

Shi kuma yaron da maryam ta haifa, ba kowa bane fa ce Marshal omer tazarar satittika ne a tsakaninsa da Rafayet, 

Tun suna yara omar ke son wasa da rafayet, amma bai yarda dashi ba duk da kasancewar omar fari ne sosai  kamar balarabe, yabiyo mahaifiyarsa Maryam bafullatana, 

Gashi shima rafayet ɗin yana son Omar amma tsakaninsu sai dai daga nesa a rinka jefawa juna murmushi 😊

daya ƙara wayau hankali ya fara shigarsa, wata irin shaquwa ce ta shiga tsakaninsa da omar, duk da momyn shi bataso yana hulɗa dasu,

kai har takaiga idan dare yayi sai ya saci hanya daga bedroom ɗinsa izuwa nasu, ya haye saman gadonsu wurin omar ya kwanta kusa da shi, 

Shima omar ɗin harya gane idan dare yayi, yazauna yaƙi bacci yayi ta zaman jiran rafayet, har sai yazo sannan su kwanta tare suyi bacci,

Maryam kaɗai ce ta lura da hakan, ita dai ba ruwanta, tana son rafayet tanajinsa kamar ɗan cikinta, haka zata je tayi musu addu’a tashafa musu kawunansu, 

Ranar da alexandra ta gane hakan akan idonta, taga rafayet ya shiga ɗakinsu omar tsakar dare , aiko washe garin ranar tarinƙa zabga masifa har sai da kowa ya gaji,

Bayan wannan lokacin maryam taci gaba da haihuwa a inda ta sake haihuwar namiji again wanda yaci sunan shi najeeb, gaya nan kuna kallonsa, wato captain najeeb,

daga shi kuma sai Kanal yusif shima gashi nan zaune, daga yusif kuwa sai commender haroon, daga haroon sai Captain adams,

daga adams sai khaleed daga shi kuma sai jabeer da irfan, haka ta haifesu, daga nan ne ta dakata, 

A bangaren Alexandra kuwa shiru sbd tace ta kammala nata, abba najin baƙin cikin musamman inyaga Ya’yansa zasu masallaci sun haɗu su duka amma babu rafayet acikinsu, 

Ya so ya sake tada 6alli akan yaron, saboda yana da hanyar da zai kwaci kayansa daga faɗawa daga halaka, amma mahaifiyarsa tayi masa tatass akan cewa lokacin da ya aurota dawa yayi shawara, taja masa kunne akan cewa kada ya kuskura ya ƙara tankawa akan alexandra, 

A dolensa yaja bakinsa yayi shiru bisa umarnin mahaifiyarsa, 

A karshe ya koma yana nuna mata soyayya don yaja hankalinta, y rinƙa binta sau da ƙafa, 

dalilin komawar Rafayet us da zama ba kowa bane face wan mahaifiyarsa mr donald, mugun son rafayet yake kamar hauka, duk weekends sai yazo nigeria don kawai ya gansa, kai daga baya ma sai ya kai sau 3 yake zuwa a week sam baya gajiya da zarya daga us zuwa 9ja, ran abba yayi matuƙar 6aci, har dai wata rana ya tambayi donald yace masa wai shi bai da ƴa’ƴa ne? da buɗen bakinsa sai cewa yayi, shiya riga da yayi plan ƴa’ƴa biyu yake so arayuwarsa, yanzu ya samu ya’yan kuma dukkansu mata ne, guda biyun , 

abba tamkar ya shaƙe shi haka yaji, wato tunda yasamu biyun duk mata, shiyasa ya dakata  bayan yasan cewa yana son ɗa namiji, 

Ba yadda abba ya iya haka ya zuba ma sarautar Allah ido 👀 haka donald zaizo yaita kashe ma rafayet kuɗi shida omar, kamar hauka bai gajiya, 

bayan wannan kuma abba yaji yana son ya sake samun ƙaruwa da Alexadra, yaje cikin lalama yayi mata magana, sai yaga tana dariya abun ya ɗaure masa kai ,

gyara murya tayi tare da cewa ” na amince zan sake haifa maka ƴa’ƴa har 3 amma bisa sharaɗin cewa zaka amince Alex ya koma wurin ɗan uwana Donald da zama gaba ɗaya, don na fi yarda da ya zauna can sbd zai fi samun tarbiya, zai wataya ya samu rayuwar ƴanci, 

.(wai tarbiya a us 😂)

Download>>>  Saran Boye Complete Document

Kai tsaye Abba yace ya amince dalili kuwa shine ya gaji daganin rafayet ba sallah ba salati ba karatun ƙur’ani, kwara ma yayi nesa dashi zaifi samun salama, 

Amma shima yace yana da sharaɗi guda ɗaya, tace tana sauraronshi,

Abba yace “yaran da zata haifa mashi dole su bi addininsa wannan karan,’ 

Batayi masa gardama ba tace ta amince, a wannan lkcn ALexandra ta ajiye aikinta gaba ɗaya, sbd ta mallaki komai takeso a ynx, tayi mai isarta ynx lokacin hutun rayuwarta ne acewarta, 

A nan ne kuma cikin ikon Allah ta samu ciki, a inda ta haifi twins tagwaye wato Ayaan da jahan, kyawawan gaske Allah ya zuba musu kyau, abba yayi farin ciki sosai, da aka tashi sa masu suna akexandra tace Za6i na wurinta, sbd a yarjejeniyarsu bai ce zaisa ma yara suna ba, don haka tasanwa Ayaan (John) Jahan kuma (James) kowa ya zuba mata ido 👀

daga su kuma ta ƙara samun ciki inda ta haifi fawan shima tamkar sauran wurin kyau, kyakkyawan gaske Fari sol, a inda tasanya mishi suna (Michael) nan Ma kowa ya zuba mata ido 👀

Bayan shine ta dakata da haihuwar gaba ɗaya, nan fa abba yasa rigimar cewa haihuwa uku tace zata yi masa, ita kuma tace ae inya lissafa da twins da fawan ƴa’ƴa uku kenan, ba dole sai ta yi ciki uku ba, Allah ya kawo mata cikin sauƙi, 

Rigima ta 6alle a tsakaninsu daga ƙarshe da Abba yaga ba riba sai ya koma yana lallashinta akan ta taimaka masa ta haifa masa last born, uhmmmmm

A lokacin maryam tana ɗauke da cikin autanta na ƙarshe wanda a wurin haihuwarsa ne ta rasa rayuwarta, bakowa bane fa ce Talal,

Aunty azeema ta faɗi tana nuna sa, jikinsa yayi mugun sanyi, tuni hawaye sun zubo masa, haka sauran ma duk jikinsu ya mutu, 

Ita kuwa alexandra dakyar abba ya samu ta haifa masa last born ɗinsa, 

Wanda ya tafi da zuciyar kowa, da irin kyawunsa, shi na musamman ne, kowa rububinsa yake tun yana yaro yake fama da athma, ko ban faɗa ba kunsan ko wanene, mahaifiyarsa tasa mashi suna ROMEO, a inda mukuma muke kiransa Junaid, 

Ansha wahala sosai kafin alexandra ta kar6i musulunci, a inda sunanta ya canza daga Alexandra zuwa FATIMA, kowa yayi tunanin cewa tayi imani da Allah ne, ashe ita bada son rantaba takar6i addinin,

Takurawar abbace, 

dalilin barin alexandra nigeria tsakaninta da mahaifiyarmu ne basu shiri, hajiyarmu ta tsane ta ba don komai ba sai don yadda take wahalar mata da ɗanta, 

Duk in tazo abuja gidan abba sai sunyi cece ku ce, tun daga ranar da hajiyarmu ta buɗe baki tace ma Alexandra musuluncin ta ba kar6a66e bane, ta musulunta a banza domin kota mutu wuta zata shiga,

Ran Fatima ya 6aci sosai jin wannan maganar hakan yasa, ta koma addininta kai tsaye,

shiyasa ba a so in mutun ya shiryu arinƙa ƙyamatarsa ko kuma ana goranta masa, sbd gudun irin hakan ynx gashi ta koma yar gidan jiya, a ƙarshe da hajiyarmu ta Tsananta mata da baƙaƙen maganganu, ranta ya 6aci sosai 

Wannan shine silar da fatima ta koma ƙasar Australlia  da zama wurin danganin mahaifiyarta can sydney, babban tashin hankalin ma tabar masa jinjirin yaro batare da idasa shayar dashi ba, 

Junaid yaga rayuwa, naso na ɗauke shi,amma azmee ta nuna cewa tana so ta shayar dashi, shiyasa nabarmata sbd nima ina shayar da talal da mahaifiyarsa ta bari,

Rafayet ya musulunta ne a sanadin omar, saboda duk ƙarshen wata donald yana kawosa su gaisa da mahaifinsa, a haka ahaka har suka ja ra’ayinsa duk da ansha wuya kafin asamu ya kar6a, abba yaji daɗi sosai a lokacin, shima kuma donald yayiwa abba alƙawarin cewa bazai ta6a takurawa rafayet akan addininsa ba, zai bashi ƙwarin guiwa duk da kasancewar shi mabiyin addinin catholic,

A lokacin abba ya haɗa rafayet da omar tare ya damƙawa donald ba don komai ba, sai don kukan da yake yi mashi akan yana son ya zauna kusa da ɗan uwansa, sun shaƙu sosai, duk in zasu rabu sai sunyi zazza6in rashin junansu, 

Sannan kuma haɗa omar da rafayet ba ƙaramin ci gaba muka gani ba , domin shike juya rafayet, ya ja ra’ayinsa sosai akan musulunci yana ƙara nutsar dashi, yana tunasar dashi akan ibadarsa da kuma addininsa, da haka aka samu rafayet har ya sauke al’qur’ani mai girma, A shekarar daya musulunta kowa yayi mamakin hakan, duk da munsan  cewa shi na musamman ne lu’u lu’u  ne , mr donald yayi bajinta domin har yau muna ƙara jinjina masa kuma muna yi masa addu’ar Allah yasa ya musulunta dashi da yar uwarsa fatima, 

Domin shi yayi ɗawainiyar su rafayet da marshal omar har suka kai wannan matsayin da suke a yanzu wanda duniya tasan dasu , 

Kuma shi da kansa yasama musu malamin addini wanda ke koyar dasu littattafan addini tun suna yaransu, 

Tun wannan lokacin fatima bata ƙara taka nigeria ba, sai dai duk mai son ganinta yaje inda take, 

Wannan shine takaitaccen labarin gidan Abban sojoji, Allah yasa an fahimta,

Jinjina kai aunty babba tayi tare da cewa “Allah ya jiƙan surukata, ya haskaka ƙabarinta,yasa Aljanna ce makomarta, da dukkan waɗanda su ka rasu Allah ya gafarta musu, Alfarmar annabi muhammad (SAW) ❤

gaba ɗayansu suka amsa da amin ,sannan ta ƙara da cewa “sannan muna yi ma fatima addu’ar Allah ya shirye ta, yasa ta gane gaskiya ɗaya ce, ya bata ikon musulunta, da ita da ɗan uwa Donald,’ 

Jikinsu twins da fawan yayi mugun sanyi, ta shi su kayi cikin wani irin yana yi zasu shige ciki…………………😔

general ishaq yace “kai ina zuwa? Maza ku dawo ku zauna, ku ka yana magani ne? ynx tsakanin ku da mahaifiyarku addu’ace kawai, that’s the only solution, in Allah yasa fatima zata musulunta ae ba wanda ya isa ya hana hakan,’ 

Cikin shesshekar kuka fawan yace”idan ta mutu fa ba tare da ta karbi addinin musulunci ba, azabar Allah zata tabbata akanta ne, kuma wuta zata shiga, aduk lokacin dana tuna wannan ina jin ƙunci araina…’ 

Ayaan ma yace “abba bai kyauta mana ba, kullum cikin zullumin makomar mahaifiyarmu muke,’ 

Download>>> Auren Fansa Complete Document

Jahan yace “kuma bata son mu, ta kama hanya tayi tafiyarta, ko waiwayan mu bata yi, ita wata irin uwace? cikin rashin tausayi ta tafi ta6ar ƙaninmu shi da bai mallaki hankalinsa ba, da tun farko Abba ya za6a mana uwa tagari munyi rayuwarmu cikin salama, da ynx labarin ba haka zai kasance ba, 

“Kada na sake jin wani daga cikinku yayi magana, ku koma ku zauna, koba komai ae kuna da mu, wani irin gatane bamu nuna muku ba, mu fa jini ɗaya ne, babu wani banbanci a tsakanin mu ! ku kun kasance jinin dake yawo ajikinmu, kasancewarku farar fata ba hakan yana nufin kun fita daban acikin mu ba, kuma don mahaifiyarku ta tafi ta barku ba hakan yana nufin kun rasa wani sashe na jin daɗin rayuwarku ba, 

Da ran mu da lafiyarmu bazamu ta6a bari hawayen ɗaya daga cikin ku ya zuba ba, Allah ya riga ya haɗa kuma ba wanda ya isa ya raba, nasan cewa abunda Ammy take yi muku bakwa jin daɗinsa, shine abunda yasa ku ke jin kan ku daban, to inaso kusancewa zumunci a tsakaninmu yanzu ya SOMA,

Wannan maganar ta yayansu Ishaq yasa su jin wani sanyi a ransu, har suka samu ƙwarin guiwar koma wa suka samu wuri suka zauna, 

Suna cikin wannan zaman motoci suka soma antayowa cikin gidan da gudun gaske da wata irin jiniya, wannan alamu ne dake nuna cewa Salahuddeen hussein ya dawo wato chief of army staffs, 

Farin ciki a wurinsu ba’a magana, Abbansu jigon rayuwarsu, backbone ɗinsu ya dawo cikin ƙoshin lafia,

Lokaci guda hayaniya ta kacame agidan manyan mutanen da suka zo tar6arsa ba adadi, sai faman marhaban lale ake yi, gidan ya cika fam da manyan mutane ko’ina ya ɗauka, su azmee da chef ummu da momina sai faman kai komo suke wurin rarraba musu abunsha, 

Abban nasu ba ƙaramin daɗi yaji ba lokacin da yaga warriors soldiers ɗinsa cikin ƙoshin lafiya, murna a gunsa ba’a magana, sai dai har yanzu baiga Sanyin idaniyarsa ba, gashi ya matsu daya gansa, duk da ɗumbin mutanen dake kansa hakan bai hanasa ambaton sunan JUNAID ba, ❤

dakyar fa mutune suka lafa har abban yasamu damar shiga haɗaɗɗen bedroom ɗinsa, wanka ya shiga bayan ya fito ya kimtsa cikin jallabiya fara, kallon kansa yayi a cikin dressing mirror murmushi ya sakarwa kansa tare da cewa “ABBAN SOJOJI” a fili ya yi maganar, 

Abba mutunne mai matuƙar daraja da cikar kamala, mutunne da kowa yake kwaɗayin haɗa iri dashi ba don komai ba sai don sanin kyawawan ɗabi’unsu, mutun ne dayasan darajar ɗan adam, yana da sauƙin kai sosai, hakan yasa naƙasa dashi ke prouding dashi a matsayinsu na shugabansu ❤

Mutunne mai matukar tausayi, hannunsa a buɗe suke indai wurin taimako ne baya gajiya, irin waɗanɗan mutanen na musamman ne su, domin suna da kishin ƙasarsu, shiyasa suke sadaukarwa kansu ga ƙasarsu, kowa zaiyi burin ya mallaki uba irinsa 💕

Kwanciya yayi a saman katafaren king size bed ɗinsa, domin ya samu relief kafin ya wartsake ya gana da ƴa’ƴansa, 

A can ciki kuwa kowa ya hallara a saman dining table domin gudanar da ɗa’amin, su azmee sun kammala jera komai, saving ɗinsu kawai suke kowa na faɗin abunda yake son ci, su kuma suna zuba masa,: 

Cikin natsuwa kowa ke zubawa cikinsa, suna cikin cin abincin aunty azeema tace “wai ina baby junaid nifa na ƙosa na gansa, i really missed him so much,’ ta idasa maganar tana tura dambun naman da ta dumbuzo a hannunta, sam bata wasa da abinci,

  Fawan yace “hmmm indai junaid ne ynx zaku gansa, yunwa ta koro sa, nasan yana cen rungume da pillow kamar jinjiri yana sharar bacci,’ 

  gyaran murya Abbas yayi “idan ana cin abinci ba’a magana,’ ya faɗi cikin zolaya, 

Amani tace “amma agida fa muna yi,” dariya su kayi gaba ɗayansu jin abunda tace, 

….,……….SEHRISH…………………….

A 6angaren sehrish kuwa, baiwar Allah jiki fa yayi rau, ido a kumbure ta farka daga bacci, duk ta tsorata da mafarkin da tayi akansu Husanna, tayi wani mummunan mafarki akansu, cikin mawuyacin hali, jikinta ya gama mutuwa, hawaye ne kawai ke rolling down on her cheeks, tana jin zuciyarta babu dɗi, tana kewar siblings ɗin nata, tana jin cewa bata kyauta ba, da tayi nesa da su amma ya zata yi? the hard way is the only way 👌

Cikin sauri ta shiga toilet, wanka tayi sannan ta fito, jikinta na ta faman rawa, kayan nan da tafara zuwa aiki dasu gidan at her first day, su ta ɗauko, wato burgujejan wandon nan Falazu, 

Wanda ƙafar mutun 5 sai ta shiga ciki ba tare da ya matse su ba, pink colour sai riga ta maza launin ruwan madara (milk) mai ma6allai dayawa ajikinsu da aljihuna, ta gyara gashin bakinta ya zauna raɗau, sannan ta nannaɗe sumar kanta kamar yadda ta saba, 

ta aza hukar nan, yar tashi da kwakwa sannan ta aza kuma mayafinta launin wandon daga saman hular ta naɗe shi,

sai da tatabbatar da komai ya zauna raɗau,

Sannan ta fito gabanta na faɗuwa saboda taji alamun bakin nan fa sun iso, suna cikin gidan batasan ya zasu kalleta ba, ko’ina na jikint rawa yake yi saboda zazza6in da take ji, 

  tun daga inda take ta hango su a zungureran table din, binsu da kallo tayi, musamman aunty babba da Amani da tagansu ƴan larabawa, ga kuma su ishaq da abbas da abuhaisam da sauran duk batasan su ba, amma kamanninsu ya tabbatar mata da cewa yayyansu Kanal yusif ne,

Download>>> Yaro Ne Complete Document

“To fa wanene wannan kuma, baƙon saurayi ku ka yi ne:? .

Sai da sehrish ta firgita jin maganar aunty azeema, lokaci guda kowa ya ɗago yana kallonta 👀

Cikin sauri azmi dake tsaye akansu suna saving ɗinsu dasu chef ummu tace “he’s our new house boy, tukur yana taimaka mun wurin aiki sosai,” 

Jinjina kai azeema tayi tare da cewa “that’s gud” 

ƙarasawa azmi tayi ta ruƙo hannun sehrish tare da janta izuwa kitchen suka tsaya, sannan ta kalle ta tace “meke damunki ƙanwata na shiga na Same ki jikinki zafi baki lafia ne,” 

Hawaye ne suka soma zubo ma Sehrish cikin nuna tsananin damuwa tace “aunty azmi dan Allah ki taimake ni, ke kaɗai ce zaki iya taimako na a halin yanzu, ina cikin tashin hankali…’

“tell me whats happening wit u? Azmi ta tambaya,

“Aunty azmee ina ji araina cewa ƴan uwana suna cikin mawuyacin hali, inaso naje nagansu, dan Allah ki taimakamin naje katsina na duba su koda kwana ɗayane ina tsoran na rasa su bani da kowa sai su….. …..’  

   kuka ne yaci ƙarfinta ta gaza ƙarasa maganar, azmi ta janyota jikinta tare da hugginta ɗinta tightly a jikinta tace….    

    “I feel your pain sehrish,ina mai takaicin sanar dake cewa bazai yiyu ba hakan!

   ɗagowa sehrish tayi daga jikinta tana kallonta ido jawur, cikin muryar kuka tace “meyasa aunty azmi”?

     “Banso na sanar dake ba amma ynx dole ne kiji, sehrish kuɗin da na baki na aikin ƴan uwanki, bana salary ɗinki bane kawai, hada kuɗaɗen dana jima ina tarawa domin na yi amfani dasu, na haɗa miki duka sbd na tausayawa halin da ki ke ciki sosai, salary ɗinki bazasu isa ba dole saina cika miki, a yanzu haka da nake miki magana nikaina banda kosisi domin duka na tattara miki su….” 

Shiru ta ɗanyi tana wani tunani idonta akan sehrish, ita kuwa jikinta yayi sanyi ba don komai ba sai don jin cewa Azmee hada kuɗinta ta haɗa mata don ta biya kuɗin aikinsu husna, sai taji ta ƙara ƙaunar azmi sosai, tana da matuƙar tausayi, ga kyan hali 

    “ki daina kuka sehrish, duk kan tsanani yana tare da sauƙi, ki daina sa damuwa aranki, insha Allah ba abunda zai sami ƴan uwanki, Allah yana tare dasu, maganar zuwanki wurinsu zanyi ƙoƙari akan hakan amma ba yanzu ba,’

   cike da rashin kuzari sehrish tace “shikenan aunty azmee, nagode sosai bansan da wasu irin kalmomi zan gode miki ba, narasa mahaifiyata amma gashi Allah ya bani ke alokacin da nake cike da jimamin rashin wani nawa akusa dani mai sharemun hawaye na,

   Murmushi azmee tayi kafin tace “samu wuri kizauna, me kike so na kawo miki ki ci? tun da safe baki ci komai ba,’ tayi mgnr cikin nuna damuwarta,

    “Aunty azmee i cant eat anything now, zuciya ta tashi take yi bani da kwanciyar hankali,’ 

     dafa shoulder ɗinta tayi tace “Calm down your mind reeshi na, just ave a seat, bari na haɗa miki abu mai daɗi mana ki ci, zaki ji daɗi,’ 

  Ajiyar zuciya sehrish ta saki, wuri ta samu a saman dinner table ɗin dake a kitchen ɗin ta zauna, tana jiran azmi,

a tray ta shirya mata abun tattaunawa, ta ƙaraso da murmushi ta ajiye mata tana faɗin”Ina mai tabbatar maki cewa indai ki kasa wannan Cheese burger ɗin abakin ki sai kin manta da duk wata damuwa da ki ke ciki, musamman in ki ka haɗa da  Cornflakes ɗin Zan haɗa miki ynx da madara haɗi na musamman ,’ 

Wani irin sanyi ne ya ratsa reeshi haƙi ka azmi ta musamman ce acikin na musamman, cikin sanyi murya ta furta “thank u aunty azmee kina ji dani sosai, only God can rewards you,’ 

“Don’t worry your self reeshi i just wanna see you always in happy mood, bana so naganki cikin yanayi na damuwa,’ ta faɗi hakan a yayin da take ƙoƙarin juyawa,

Murmushi sehrish tayi ta zuba wa tray ɗin ido, Cheese burger ce aciki tare da hot dog ga sandwhich, lumshe idanunta tayi aranta tana tunanin me ƴan uwanta suka ci su 😥

ruwa azmi ta ɗebo a Dispenser mai zafi cikin tea cup, ta haɗa wa sehrish cornflakes yaji madara da sugar, tasan cewa sehrish akwai son zaƙi shiyasa ta zuƙa mata shi, 

Ƙaraso wa tayi ta jiye mata shi a gefen tray ɗin, sannan tace “ko kina buƙatar wani abu ne?akwai sauran abubuwa da muka haɗa masu daɗin gaske, 

yar dariya sehrish tayi ganin yadda azmi ke treating ɗinta sai kace ƴar masu gida,

“oh dariya na baki?dama dariyarki nakeson gani kuma gashi naki har dimple ɗin nan naki ya lotsa,’

azmi tayi maganar tana kallonta, cikin jin daɗi sehrish tace “daga ynx zan rinƙa yin dariya aunty azmee tunda kina so insha Allah,’ 

hannu azmee tasa tare da jan kumatunta tace “yawwa haka nake so my daughter, bari na shiga ciki, keep enjoying ur meal banda loma,’ .

ta faɗi hakan cikin zolaya kafin ta fice daga kitchen ɗin,

 tana fita sehrish ta fashe da wani irin matsanancin kuka ba don komai ba sai don, tunawa da ƴan uwanta, kuka take bil haƙƙi da gaske hawaye na sintiri a face ɗinta, Allah sarki baiwar Allah, aduk lokacin da taga abu mai daɗi agabanta zata ci sai ta tuna da ƴan uwanta, wane hali suke ciki? shin sun samu abunda zasu ci kuwa, in ta tuna hakan sai taji ɗaci aranta, maganar oummansu ta tuna a inda take cewa 

  

Domin Sauke Cikakken Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

_sehrish ke ce mai wayau acikin ku, dan Allah duk runtsi duk wuya kada ku rabu ko bayan raina, ku haɗa kanku ina son ku sosai ƴa’ƴana rabin raina_ 😭

Back to top button