Hausa novels

Harijin Sarki Page 2 Romantic Hausa Novel

Ɗagowa tayi da sauri tace “Amma Yallaɓai….” Ɗaga mata hannu yayi yace “Amma me Dr Samha?” Bai jira amsar ta ba yace “Duk wani ma’aikaci burinsa samun ci gaba da ƙarin ɗaukaka, babban asibitin ƙasa kika koma wanda duk wani isasshe a kasar Morocco burinsa zuwa wannan asibitin don a duba lafiyarsa Sannan akwai wani matsayi mai girma da nake Miki fatan amsawa saidai zan jira lokaci kaɗan kafin bayyana Miki, inada tabbacin zakiyi farin ciki da wannan Mataki kuma zai baki damar ci gaba da bincikenki cikin aminci, yanzu ga gift ɗinki kije ki fara shiri ki sanar da duk wanda zaki sanarwa gobe idan Allah ya kaimu zamu tafi Rabat ki shiga office ɗinki Ni kuma zanyi wani aiki a gidan *SULTAN RASHID IBN FAYAD AL ZIRKAN* akwai yiwuwar kece zaki karɓi aikin domin yanzu kece ludayinki ke kan dawo mu girma ya fara riskarmu kuma ina Miki fatan nasara” Cike da sanyin jiki ta miƙe tace “Na gode Yallaɓai” daga haka ta juya ta fice Zuciyarta cunkushe da damuwa take driving ɗin bata taɓa riskar kanta a yanayin da ruhinta yaƙi amincewa dashi irin yanayin yau ba, koda taje gida bata saurari kowa ba ta shige ɗakinta, wanka tayi tayi sallar Azahar ta kwanta Zuciyarta tana ƙunci, shigowar Jadda ne ya tasheta ta zauna suna fuskantar juna, Jadda ta kama hannunta tace “Bakiyi tunanin yau ɗin zatazo miki da wannan yanayin ba ko jikata tun shekarunki suna kaɗan nake mafarkin ɗaukaka Me cike da ƙalubale gashi a hankali lokacin yazo, tun kafin kije nasan abinda zai faru na faɗawa Abih ɗinki yace a’a basuyi haka da mahaifinki ba, to dai nayi nasarar shawo kansa yanzu ya rage kije ki sanar da mahaifiyarki” wasu siraran hawaye ta share tace “Amma Granny banji ina farin ciki da wannan aikin ba kamar yanda nayi farin ciki da samun Aikina a Fes hospital Meyesa ruhina da zuciyata suka kasa karɓar abin har suke wahalar da gangar jikina?” Dafa kafaɗarta Granny tayi tace “suna faɗa ne da ƙaddararki kuma tafi ƙarfin su sai abinda yake rubutacce ya faru” tashi tayi ta ɗauko mata Tagine ta fara bata a baki tans rera mata wakar da take yi mata lokacin tana ƙarama tana dariya, a hankali ta gusarwa da jikar tata damuwa suka fita suka nufi Souks sukayo siyayya tare suka je gidan Ummuh wacce take itane mahaifiyar Samha tun bayan rasuwar Shaikh Idrees El Fahreey bata kuma aure ba tana zaune ne ita kaɗai sun raba gari da Samha ne don kasancewar Ruƙa’ah Christian ita kuma Samha tabi addinin mahaifinta wato musulunci, daɗi kan haka mahaifiyarta ta wani sashin bokanya ce ita kuma Samha tun tasowarta bata aminta da harkar bokanci da tsafi ba kullum kallonsu takeyi matsayin ƙarya da ɓata wannan ya sanyawa Ruƙa’a ƙiyayyar ɗiyar tata ƙwaya ɗaya tak a duniya har tayi wani furuci da yake bibiyar Samha inda tayi rantsuwa da dogon tsafinta indai Samha batayi amanna da Tsafi da kuma addinin gargajiya ba to babu wani namiji abin halitta da zata burge har yayi mararin kaita gidansa matsayin mata. Tunda Ruƙa’a tayi wannan furucin ga ɗiyarta kuwa ya zamana duk wata dama da Samha take da ita a baya ta ƙwace mata ta rasa masoyin gaskiya, duk wanda zaice yana sonta sai taji bata sonsa, duk kuma wanda taso sai yaji bai sonta haka taketa rayuwa tsayin shekara goma kenan gashi a lokacin sai Allah ya jarabceta da tsananin soyuwar kaɗaici da namiji a babu wands zai kulata babu wanda take burgewa bare ko saɓon ne su aikata ta rage zafi da wannan lokacin da ta gama karatu ta samu aiki sai ta duƙufa wajen binciken hanyoyin kashe sha’awa, bayan tayi nasarar kashewa kanta sha’awane sai ta koma binciken alaƙar jini da sha’awa wanda har yanzu take kansa bata fasa ba kuma bata cimma gaci ba kullum abinda bincikenta yake bayyana mata samun kusanci da me irin wannan damuwar ta sex abuse shine kawai zai bata damar kammala bincikenta, gashi iyakar petiant ɗin da take gani a ɓangarenta bata taɓa katarin haɗuwa dame irin gigitacciyar sha’awar da zata ce irinsa ne zatayi bincike akansa ba, da wannan ta tattara ta aje binciken har Saida Dr Junaid ya nemeta da bincike makamancin wannan sannan ne ta kuma fadaɗa research ɗinta still dai yanzun ma kulleta yayi da cewa sai ta samu namijin da ya kasance cikakken HARIJIN da ya kasance a yini yana iya kwanciya da mace sau goma tsayin dare baiyin bacci, da irin wannan jinin ne zatayi bincikenta ya bata result ɗin da take nema. Kamar yanda suka saba yau ma basu samu wata karɓa gurin Ruƙa’a ba haka suka gaggaisa a daddafe suka sanar da ita abinda ke tafe dasu tayi musu biris ba tace komai ba har Saida Jadda ta tashi ta fice Samha ta matsa gabanta cikin tsananin tausayin kanta da irin mugun fushin da mahaifiyarta takeyi da ita akan ta bi tafarkin da ta amince shine tafarkin gaskiya, kama ƙafar Mom ɗinta tayi tace “Idan zan rinƙa yin komai babu albarkarki Mom bazan taɓa ganin daidai a rayuwata ba, na roƙeki ki daina fushi dani ki rayu dani kamar yanda kika rayu da mahaifina, Meyesa shi kika yarda dashi kika soshi kuma kika zauna a ƙasansa matsayin mata har kuka samar dani, Meyesa Ni zaki kasa yafemin kuskuren dana aikata Miki zaman ƙuruciya”…… Tureta tayi cikin hargowar bala’i tace kar ki kuma zuwa inda nake Ruth matuƙar baki koma bin addinin da nakebi ba, matuƙar baki koma addinin gargajiya ba to babuni babu ke har abada, Meyesa kowa ɗiyansa na gadonsa amma ke kina bin tafarkin son zuciya, me kike samu a Musulunci shima Abie ɗin naki me ya samu a cikinsa banda mutuwa babu kwarjini…..” Miƙewa Samha tayi cikin tsananin zafin zuciya idanunta na zubda hawaye tace “Ko zaki daina amsa sunan Mahaifiyata bazan taɓa yin shirka ba ba kuma zan taɓa bin addinin gargajiya ba” tana faɗin haka ta fice a fusace Ruƙa’a ta biyota tana cewa “Eh naji Nima daga yau Ruth karki ƙara zuwa inda nake kuma karki kuma kallona a matsayin uwar data haifeki kuma a wannan tafiyar da zakiyi Rabat zaki haɗu da ƙaddarar da zata addabi rayuwarki sai kin rayu cikin rashin yanci a matsayin me iko sai kin gwammace ki rayu a yanda nakeso da ki rayu a yanda kika zaɓa”…. Sudai basu kulata ba domin sun fuskanci Ruƙa’a kullum ƙara dulmiya takeyi, haka suka shiga motarsu suka nufi gida, babu abinda yake cin zuciyar Samha kamar sunan Ruth da mahaifiyarta take kiranta dashi, koda sukaje gidan bata da wata walwala duk sanda ta kaɗaice kalaman mahaifiyarta na dawo mata, tunda dake da Mom bata taɓa ma rayuwarta kyakkyawan fata ba. Idan ya tuna wannan abin sai kuka ya ƙwace mata haka zata tottoshe bakinta don kada kakarta me sonta tajiyota haka a daddafe ta wayi gari da safen juyi tayitayi a gadon tunani da dama suna zuwar mata wasu suna ce mata ta haƙura da wannan tafiyar bakin da Mahaifiyarta tayi wannan tafiya tata mai girma ne wata kuma tana faɗa mata kar ta soma komai yana faruwa ne cikin rubutun Allah, idan Allah bai hukunta mata abinda Mom ta furta ba bazai Sameta ba domin ba zunubi ta aikata ba……….

Back to top button