Hausa novels

Mejo Najeeb Page 30 By Autar Alheri

“Ido general aliyu yazaro jin wannan kalaman na aminin nashi wanda yanada tabbacin bagaskiya bane, to miyasa yafiɗi Hakan? Kuma agaban duka iyayensu, kenan Hakan nanufin yakamuda soyayyar yarinyar ne? Yayiwa kasanshi tambayar da amsarta abayyane take…shi kuwa dady mutuwar zaune yayi babu abinda yake tunani Aranshi illa yoshe najeeb Yakoma marar kunya Hakan ? Ashe ze iya faɗar Hakan agabanshi? Su Hajiya mama mahakan abin yake agaresu domin gabaki ɗaya kalaman mejo sunsakasu shuck…fannin General faruk kam ba’amagana domin kafe mejo kawai yayi da ido yana kallo ko kiftawa babu, lallai tabbas labarin najeeb yakeji haryanzu begama saninshiba.Gabaki ɗaya kowa awurin yayi tsit bakajin motsin komai illa na’urorin lantarki dake aiki a perlor….Alhaji Abubakar ne kawai yasamu zarafin buɗe baki Shima cikin mamakin dabegama sakinshiba yace “shikenan zance yaƙare kutashi kuje zamu nemeku…ai yana rufe bakinshi mejo yamike tareda riƙo hannun maryama ze mikarda ita…da mamaki dady ke kallonshi kafin yace “inakuma zakaje da ita?? “Gida zan maidata, yafaɗa lokacinda yagama miƙarda ita tsaye. “Humm dady yasauke ajiyar zuciya kafin yace “ba’inda zakaje da ita anan gidan zata zauna harse iyayenta sunbaka ita dakansu tukunnah….ido mejo yaɗan zaro kamin yabuɗe baki zeyi magana kenan Alhaji Abubakar yace “kaga najeeb zancen alhaji Khamis gaskiya ne doline se iyayenta sunsan tana hannunka sa’annan zamu baka ita tunda kaga yanzu ai yayarta nagidan doline semunje can garinsu angaya musu abinda kefaruwa dakuma wadda kai kazaɓa kaga daganan seka saki waccan tukunnah kazo da wannan ɗin amma bazeyu kucigaba dazama atareba bayan dukkansu Aurensu nakanka…Hakane kam. Cewar dady.Ɗan cije lips ɗinshi naƙasa yayi kana yajuya kawai yahaura pert ɗinshi, general aliyu yatashi jiki asanyaye yabi bayanshi hakama general faruk…itakam mufeedah data dasƙare tinɗazu haryanzu bata motsaba.Hajiya mama ce tasauke ajiyar zuciya kana tamiƙe tare da riƙo hannun Isseta tace muje ƴata, suka kama hanyar pert ɗinta…Hajiya Umma ma nata ɗakin tanufa dukkansu zuciyoyinsu adagule da wannan mirɗaɗɗen al’amarin.Sukuwa su anty hawwa amarya sunacan pert ɗin da’aka ware musu sunashan kallo sam basusan wainarda ake toyawaba agidan…Mejo kuwa yanashiga perlor shi yazube akan kujera tare dafe kanshi dake tsananin sara mishi Yanajin wani irin kuna Aranshi, wai ace Kamarshi da girmanshi dawayonshi dakomai Dady zerika tallarshi sekace wani mace? Wai miyayiwa majaifin nashi dake mishi arin wannan abubuwanne? Kodai bashine yahaifeshiba? Yana cikin wannan tunanin yaji andafashi tabaya koda yaɗago yaga general aliyu akanshi, mayarda idonshi yayi yalumshe….zama general aliyu yayi adede lokacinda general faruk ma yashigo perlor.Cikin tausayi yake kallon aminin nashi domin yasan tabbas wannan abin da Dady yayi mishi ba daɗi kokaɗan, taya zakiyawa yaronka aure amma besaniba seda aka kawo matar gida tukunnah? Ko maryam inda ƙaddara bata haɗasu da Maah ba kenan bazesanda auren ba se ayau? Za’ace yasaki ɗaya yazauna da ɗaya sekace zamanin gaba’gaba suke ayanzu..ajiyar zuciya yasauke bayan yagama zancen zucin nashi yakwantarda murya kana yace “Najeeb I’m very sorry for that please 👏 nasan badaɗi sam amma karka saka wannan abin aranka inaso kaɗauka kalar taka ƙaddarar kenan, sa’annan kasani cewa iyayenmu sunwuce komai agaremu doline muyi musu biyayya akan duk wani hukunci dazasu zartar akanmu sekaga munsamu nasara arayuwarmu dan Allah karka ɗauki wannan al’amarin dazafi please.. “wannan gaskiya ne general aliyu yafaɗa mejo kayi haƙuri Kamaida komi ba komiba kaji friend, general faruk yafaɗa Shima cikin tausayin abokin nasu domin kobesan komaiba arayuwar mejo wannan abin kawai dayagani ayau yasan cewar akwai matsala.Ajiyar zuciya mejo najeeb yasauke kamin yabuɗe blue eyes ɗinshi yana kallonsu, abin mamaki kuma seyayi wani ɗan murmushin takaici kana yace “it’s okay dama ba abinda nasaka araina Aliyu domin gata dady yayimun na ɗaura min aure da kyakkyawar mace kuma metausayina tun batasan wayeniba koda dady be auramin itaba dakaina zan nemeta na aura domin idan baka mantaba Aliyu aranarda mukaje Delta state Maryam tasadaukarda tata rayuwar taceci tawa, awannan lokaci ko namiji bakowanne ze iyayin abinda tayiba tindaga wannan lokaci nasakata acikin matanda nakeda burin aura..shiru yayi yana taune lips ɗinshi naƙasa ga dukkan alamu akwai abinda yake tunani. Muryar General aliyu ce takatse mishi tunin inda yake faɗar kamarya cikin matan dakakeda burin aura har mace nawa zaka aura mejo? Yajeho mishi wannan tambayar…..ɗan kallonshi yayi dagefen ido kafin yace “ɗaya kafin na haɗu da Maryam bayan na haɗu da ita kuma suka koma biyu.. “iKon Allah to wacece tabiyun? “Nima bansantaba amma inaso nasanta domin itace yarinyar data fara temakona amafalkin daya kasance gaskiya ne ba mafalkiba idan kaduba bayyanar Maah agareni hakan nanufin cewar Itama tabbas zata bayyana kuma zan aureta in sha Allah…”iKon Allah wannan gaskiya ne najeeb amma kuma inaso kasani abune wanda yake aɓoye Allah ya bayyanama amafalki kamar yadda Maah tafaɗa amma kasaka aranka balallaine dan maahh ta bayyana agareka ba ya kasance Itama wannan yarinyar tabayyana agareka kawai kayita addu’ar zaɓin Allah kuma zamu tayaka in sha Allah.”In sha Allah I’ll do it, kafin kuma yace “please minene shawararku? banasan zaman Maryam agidannan koda kwana ɗaya ne kuma banason jayayya da dady akan zancen, yakasara zancen cikin damuwa. “To miyasa bakaso tazauna mejo? Inagafa kowanne irin zamane zatayi baze ɗauki lokaciba, sekuma yasaka dariya yace dan iska kodai abinda kagayawa su Dady ne kakeson maidawa gaskiya domin wlh Allah nasan ƙarya kikeyi ba abinda yataɓa shiga tsakaninku, kai kardai nayi ƙaryar nima namantada nakusa mugun gani last time maybe aranarne kayi ɓarnar, yakarasa zancen yana sheƙewa da dariya..wata muguwar harara mejo yabanka mishi kafin yace munafikin banza ina ruwanka…”ahh meda wuƙar yanzu miyasa bakaso tazauna anan ɗin?.. “Humm bazaku gane bane akwai matsala agidannan wadda bansan daga ina take faruwaba..”wacce irin matsala kuma? Cewar general aliyu..”Humm kaide bari abunma badaɗi wlh “nan mejo yabasu labarin matar dake leƙenshi Aban ɗaki dakuma kwartancin datayi mishi yana bacci, yaƙarasa maganar zuciyarshi na kuna cikin ɓacin rai ninafi tunanin bamutun bace ayanzu duba da yadda take ɓacewa lokaci ɗaya.. “Humm gaskiya kam da matsala indai Hakane mejo domin ko aljana ce haduwarsu da Maryam akwai haɗari acikinshi sabida naga abinda nagani da idona wanda kai baka ganshiba..nan general aliyu yabasu labarin tashin ciwon mejo agidan da Isseta take dakuma abinda yafaru na zuwan gimbiya mardiya….wani irin zaro ido general faruk yayi cikin mugun tashin hankali da mamaki yace “agabanka friend ? Kuma katashi daranka? Lallai Kanada ƙarfin zuciya wlh danine awurin sedai afitodani, yakarasa zancen yana share guminda yawanke mishi fuska.Shi kuwa mejo ko ajikinshi wani miskilin murmushi Mayayi Aranshi yace “that’s good aikuwa yanzu ma nasamu damar barinta agidan kuma wlh koda bala’i a pert na zata riƙa kwanciya….shidai general aliyu yanacan yana dariyar general faruk yayinda mejo kezancen zucinshi har aka kira magarib sukashiga anan bathroom ɗin dake perlor mejo sukayo alwala kana sukafito tare da nufar masallaci..Isseta na bedroom ɗin Hajiya mama zaune bayan ta gama sallar magarib tana tunanin wannan abubuwan dasuke faruwa da ita daga wannan se wancan Allah sarki amminta kotana ina ayanzu? Kotasamu lafiya? Allah dai yasa halima naziyartata kamar yadda umaima tagaya mata…tana cikin wannan tunanine tajiyo ana magana a Perlor, cikin mamaki take sauraren muryar juwaira domin kab ƴan gidansu bawanda bazata gane muryarshiba, batagama mamakin miyakawo juwaira garinba taji tana faɗar “Ummi wai dagaske ne wannan zancen da’ake faɗa agidannan? Dagaske ne yah najeeb aka aurawa mata har biyu kuma ciki hadda yayata? Innalillahi wa’inna ilaihiraji’un nashiga ukku ni juwaira taƙarasa zancen tana fashewa da kuka. “Cikin lallashi Ummi tace “haba juwaira mikikeyi Hakan please kiyi hakuri mana dama tunfarko dakika ɗauko soyayyar yah najeeb seda nahaneki badan komai ba sedan sanin waye yah najeeb yayanane nafiki sanin halayyarshi ciki da waje shiba irin sanarin dake kula mata bane sam yah najeeb mace bata gabanshi, amma baki yaddaba anan gidan ina gaya Miki mansura nashige mishi bako cewa tayi tana sonshiba shige mishin kawai datakeyi amma sekinga yadda yayi mata shegen dukan mutuwa kuma wlh cousin sister ɗinshi ce niba abinda zance Miki anan illa kiyi haƙuri.. “haƙuri Ummi wlh bazan haƙura ba bashegiyar yarinyar dazan barwa yah najeeb koda kuwa wannan yayarce tawa wlh bazan bar matashiba sabidashifa nabaro garinmu nazonan atunanin mutanen gidanmu duka gun dangin mamarmu naje domin mamar kawai nagayawa gaskiyar inda zanje Seyanzu kuma bayan sunzo sunganni nakoma a tutar babu?? Wlh sam bazeyuba.. “to shikenan tunda Hakan kika zaɓa nidai baruwana domin wlh bazaki jamun dukan banzaba agun yah najeeb..sunacikin wannan surutun Isseta taji sunyi shiru..Ashe Hajiya mama ce tashigo Perlor shiyasa sukabar zancen…….shigowa tayi ɗakin tasamu Isseta zaune inda tabarta murmushi tayi mata kana tace “Maryam kingama sallar? Eh nagama, Isseta tafaɗa kanta aƙasa…to shikenan zokiyi wanka sekici abinci kinji..to kawai Isseta tace tare da Miƙewa tabi bayan Hajiya mama takaita har bathroom tahaɗa mata ruwan wanka dakanta tare da zuba mata turarukan wanka masu gyaran jiki da daɗin ƙamshi kana tafice daga bathroom ɗin…sosai Isseta taji daɗin yadda matar kemata Hakan yasa tayi wankanta hankali kwance amma zuciyarta fall tunanin zantukan juwaira..bayan tafito tasamu wata abaya milk color ajiye akan gado tare da pant da bra duka sababbi ga dukkan alamu na ummi ne Hajiya mama taɗauko mata.Wurin mirror tanufa tagyara jikinta kana tasaka abayar kawai tare da zura hijabin datayi sallah domin pant da bra ɗin Ummi kam bazasu yimataba, ahakan tazauna bakin bed ɗin tana tunanuka dayawa gefe ɗaya tunanin juwaira takeyi gefe ɗaya kuma tunanin mejo Najeeb takeyi ko awanni hali yake domin tafahimci yanayinshi kamar ranshi amugun ɓace yake..ahakandai Hajiya mama tasake dawowa takawo mata abinci tafita, itako Isseta data buɗe kayan abincin sekawai ranta beyadda dataci abincinba kumadai dama batajin yunwa Hakan yasa taɗauki fruit ɗin dake kai kawai tasha..Gombe Misalin ƙarfe 8:00pm Hajiya Hannah ce zaune tana wayada megidanta Alhaji Abdussalam cikin kunar Rai take bashi labarin duka da mama bintu tabata gameda zaman Isseta agidan babban abinda yafi tada mata hankali anan shine aurenda akace mlm Musa yaɗaurawa maryama kuma wai basusan angonba sabida yamaidata ƙasƙantaciya marar asali….tunda suka fara wayar alhaji Abdussalam ke sauraren ta yana jinjina girman uban giji daya ƙadartawa ƴar cikinshi irin wannan rayuwar kuma duk acikin kalaman Hajiya Hannah zancen wannan Auren ne yafi tsaya mishi arai, nisawa yayi kana yace “Hannah wannan matar dakikasa aka tsare adawo da ita cikin iyalanta kuma zankira general faruk ingaya mishi ɓatan maryama domin yanemi temakon jami’an tsaron ƙasar Nigeria wurinnemanta, kisani duk abinda yasamu maryama karmu zargi kowa sekamu mundaukota munkawo ƙasar da batada kowa se Allah kuma munkasa waiwayarta dudda Cewar ba’asan ranmu Hakan takasanceba muma kuwa bedace muɗora wani laifinba. dan shiru yayi Yanajin yadda zuciyarshi keƙuna akan wannan lamarin kafin yacigabada faɗar “abu ɗaya ne bemin daɗi ba shine aurarda maryama Hannah domin kuwa maryama nada mijinta tunzuwanta duniya aurene kawai ban ɗaura musuba kuma inda tabbacin kinsan Hakan sabida Hakan zanshigo Nigeria in sha Allah domin munemi kowaye aka ɗaurawa mata aure dashi yasakarmin ƴata, yana gama faɗar Hakan yayanke wayar yaname dafe zuciyarshi dayakejin kamar zata fashe sabida ƙunci…..da kallo Hajiya Hannah tabi wayar hannunta kamin ta’ajiye tana tunanin zantukan megidan nata tabbas yanada gaskiya acikin kalamanshi amma Hajiya tabawa itace selar komai Allah yasaka mata akan wannan matar..Gidansu IssetaAbba kuwa tun da yafita bayan tafiyarsu Hajiya Hannah bekoma gidanshiba se cikin salamainin dare yayi biɗir biɗir dashi kamar wanda akatuno daga kabari sabida tashin hankali gabaki ɗaya ya hargitsa kanshi domin ya shiga firgici marar misaltuwa haƙiƙa yayi nadama yayi danasa nin korar maryama babu adadi…koda yashigo gidan mama bintu nazaune tsakiyar gidan Ita kaɗai tana lazimi, dagashi har ita bawanda yacewa kowa komai yashige ɗakinshi.LagosBayan sundawo daga masallacine general aliyu da general faruk sukatafi shikuwa yashigo domin basu baro masallacin ba seda aka yi sallar isha’i yana shigowa yawuce part ɗinshi domin besamu kowa a general parlor ba, cire kayan shi yayi zeshiga wanka kawai gabanshi yafaɗi Hakan kawai yashiga fargabar shiga wankan agidannan, shiru yayi yana tunanin abunyi har kusan ƙarfe 10:00pm yana zaune har Hajiya umma tashigo takawo mishi abincinshi tafita,,yana zaune yarasa tinanin ma dazeyi can Isseta tafaɗo mishi arai yafara tunanin yaza’ayi tazo part ɗinshi domin ya san idan tana ciki bawanda ze leƙashi Aban ɗaki to Amma Tayaya? Domin yanada tabbacin Hajiya mama bazata bari tazoba,,yana cikin wannan tunanin ne wata dubarar tazo mishi cikin Sauri yaɗauki wayarshi tare da Kiran Ummi tana ɗagawa yace tagayawa Maryam tazo takarɓi kayanta na sakawa daya ɗauko mata amma suzo tare daga Hakan ya kashe wayar.Miƙewa Ummi tayi tacewa juwaira ina zuwa daga Hakan tanufi bedroom ɗin Hajiya mama koda tashiga Isseta na kwance akan gado hajiya mama nagefenta tana lazimi, sallama tayi tukunnah ta isarwa da Hajiya mama saƙon yah najeeb. Hajiya mama batakawo komai arantaba tacewa Isseta tatashi suje…..itako kamar Jira takeyi tamiƙe sanyeda hijab ɗinta tabiyo Ummi suna fitowa perlor sukayi ido huɗu itada juwaira dake zaune…wani irin miƙewa juwaira tayi tare da zaro duka idanunta tace Isseta….!

Back to top button