Asanadin Makwabtaka
Book 2
007*
_Destiny may be delayed but cannot be changed…._
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
…..Fanan jikar Hajiyace wato d’iyar Hajiya Maryam ta lagos kuma itace babbar diyarta, acan baya lokacin da mijin Hajiya wato General Adamu zakee yay ritaya a Lagos suka fara zama acan ne kuma ita Hajiya Maryam ta had’u da mijinta Wato Dr Mohammed Abraham wanda babban likita ne da ya kware a aikinshi lokacin tana karatu a Jami’ar Lagos, shi kuma Senator Alee yana Katsina yana kula da harkokin kasuwancinsu, tun lokacin da aka haifi Haisam Hajiya ta kwallafa rai akanshi k’arshe dae har tay nasarar rabasu dashi duk da suma suna matuk’ar kaunarshi don yaro ne mai tsananin farin jini ga kyau da Allah ya yi mashi duk wanda ya kalleshi sai ya tanka hakan yasa kullum cikin yi mashi Addu’oi suke, sosae Senator Alee ya rarrashi matarshi Fateema ya nuna mata Mahaifiyarshi ce bazata ta6a cuta mashi ba kuma tunda Allah yasa tana haihuwar ko shekara mai zuwa sai ta k’ara haiho wani d’an ba matsala bane, da k’yar ya shawo kanta ta hak’ura yana shekara hud’u aka ba Hajiya shi ta saka shi a Makaranta, gatan duniya Hajiya tayi ma Haisam saidae bata bashi gatan da zai sangarce ba duk da dama shi ba mai suffar sangartattun bane a tsayenshi yake tun yana yaro gashi ko dariya bai cika yi ba in kaga dariyarshi to wanda ya sani ne sosae, yana shekara bakwae lokacin yana primary 1 don saida yay nurserys Hajiya Maryam ta haifi d’iyarta ta fari wato Fanan itama dae Tubarkallah badae kyau ba don jinin Mahaifinta ta biyo harma ta fi shi kyau sosae, Fanan irin rigimammun yaran nan ne ga kukan banza da wofi abu kad’an ta 6are baki gashi kuma bata son bak’in mutum hakan yasa bata cika sakin jiki da mahaifiyarta ba ko yaushe tana manne da Mahaifinta shi kuma gashi ba mazaunin gida bane sosae saboda yanayin aikinsa yana aiki a asibitin gwamnati kuma yana da babban private Hospital hakan yasa kullum cikin yi mashi rigima take gashi tayi k’ank’anta bare yace ya tafi da ita koma ya tafi da ita baida lokacin kulawa da ita saidae in barin aikin zaiyi, hakan yasa in ya barta gida tay ta yi ma Hajiya Maryam rigima data yi mata fad’a kuma ta idasa rikice mata, duk wannan abun Mutum d’aya ne ke controlling d’inta wato Haisam duk da shima lokacin yaro ne,duk rigimar da take da sunzo gidan tay arba dashi baka k’ara jin kukanta tana sonshi taita shishshige mashi gashi shi ba son yara yake ba wani lokacin sai Hajiya tay mashi Magana yake d’an sakar mata fuska har ya d’auketa kowa yasan tana shakkar Haisam hakan yasa Hajiya Maryam watarana taje gidan Hajiya ta rok’eta ta bari Haisam ya dawo gidansu, fir ta k’i amincewa tace itama ai don tana son zama dashi ta rabo shi da iyayenshi, wai ance tsakanin d’a da Mahaifi sai Allah K’arshe dae saida Hajiya Maryam tay nasarar raba Hajiya da Haisam da sharad’in duk Weekend nan wurinta zaiyi shi tace su duka ma zasu rink’a zuwa,sosae suka samu sauk’in rikicin Fanan bayan dawowar Haisam gidan duk in zaije Makaranta sai yabar sak’on in tayi rigima daya dawo a fad’a mashi aikuwa har ya dawo bata yin rigimar data yi niyyar farawa Hajiya Maryam zata ce daya dawo sai ta fad’a mashi sai tace ta bari, a lokacin komae na Fanan ya dawo kan Haisam shine yi mata wanka bata Abinci data ga yayi fushi duk sai ta rud’e ta fara bashi hakuri har sai yace mata yayi sannan zata warware da yake lokacin girmanta yafi shekarunta tana da wayo sosae ga baki, Haisam na primary 3 lokacin shekararshi tara da wani abu ita kuma Fanan ta kusa shekara ukku aka ba mijin Hajiya wato Adamu zakee Ministan tsaro bayan wani lokaci suka shirya komawa Abuja dama ba wani son zama Lagos d’in yake ba yafi son ya koma gida Arewa, Hajiya Maryam ta nuna abar Haisam nan ya k’arasa karatunshi Hajiya kuwa tace bai yuwuwa ai iyayenshi ma sai suce wani abu don haka k’afarta k’afarshi aikuwa Fanan ta sa rikicin sai ta bi bro haka take kiranshi sam Hajiya Maryam bata son d’iyarta tai mata nisa saida Dr Mohammed ya nuna mata ta barta su tafi da ita kawae in ba haka ba wani sabon rikicin ne tunda ta saba dashi in ta k’ara wayo sai ta dawo kuma in d’a take so zata iya daina planning d’in da take sai ta haihu dama so take sai Fanan d’in tayi wayo sannan ta k’ara haihuwa, ba yarda ta iya dole ta hak’ura aka tafi da ita Abuja aka saka su Makaranta tare da Haisam sam bata son zama class d’insu kullum tana zarya class d’insu Haisam sai ya kamata ya maidata, da yan class d’insu sun ganta tazo sai suce Zakee ga d’iyarka nan aita dariya shidae sai dae yay d’an Murmushi kawae, har lokacin shi ke mata wanka da sun koma gida ya bata Abinci kullum tana lik’e dashi tun yana jin ya takura harma ya saba, bayan tafiyarta da shekara d’aya Hajiya Maryam ta haifi Farha shima Haisam lokacin Mahaifiyarshi ta k’ara haihuwar yara biyu Laila da Nameer, Haisam na Junior Secondary Mijin Hajiya wato Gen Adamu zakee yay Accident ya rasu lokacin ba k’aramin tashin hankali iyalin suka shiga ba lokacin Fanan na primary 4, rasuwar mijin Hajiya yasa ta kasa cigaba da zama a Abuja ta yanke dawowa Katsina lokacin kuma Hajiya Maryam ta buk’aci Fanan ta dawo gida da taso ta turje aikuwa ta bude mata wuta dole ta koma Lagos shi kuma suka dawo Katsina yaci gaba da yin Senior Secondary lokacin kuma Mahaifinshi ya zama Senator, bayan ya gama secondary ya tafi kasar waje yin degree d’inshi na farko,akwae wani zuwa da yay Lagos lokacin yazo k’asar Fanan na Secondary skul tana ganinshi ta rungumeshi cike da farinciki suka ci Abinci tare da daddare bayan sun gama fira zai je ya kwanta tace mashi wai yayi mata wanka kaman yadda yake mata da d’an murmushi yay mata yace mata ai ta girma yanzu bai kamata yay mata wanka ba tace amman ai shi yayanta ne ba wani abu bane ganin ta turje kan hakan yasa ya zaunar da ita ya fahimtar da ita game da tsakaninsu na shi yayanta ne amman ba muharraminta bane kuma koda ma shi muharraminta ne yanzu takai wani mataki da bazai mata wanka ba tunda shi Namiji ne ganin ta zuba mashi ido yasa ya tambayeta ko bata san miye muharrami ba tace ta sani wanda bazai iya auren Mutum ba yace mata hakane, da bud’ar bakinta sai cewa tay yanzu shi zai iya aurenta kenan yana d’an Murmushi yace mata eh ai shi cousin d’inta ne ba ta sani ba tace eh ta sani,Washe gari bayan sun gama breakfast da yake Weekend ne taje part d’in da ya sauka ta iske shi yana kallo ta zauna kusa dashi itama tana kallon American film d’in da yake kallo, can aka nuno jarumin film din ya duk’a kan knee d’inshi yana rok’on jarumar zata aure shi ya mik’a mata zobe can ta amsa mashi da Yes ta mik’a mashi yatsanta yasa mata zoben ya mik’e suka rungume juna, juyawa Fanan tay ta kalli Haisam da idonshi ke kan tv ba zato ba tsammani kawae ta duk’a a gabanshi ya maido idonshi kanta yana kallon abunda tay murya kaman zatai kuka tace “Ya Haisam will u marry me pls?” dan bud’a mata ido yay alamar mamaki sai kuma yay Murmushi kawae ganin haka yasa ta fara yamutsa fuska kaman zatayi kuka tace mashi”plss answer me,will u marry me?” d’an lumshe ido yay ya jinjina kanshi, wata k’arar murna tasa ta fita daga falon da gudu ya bita da ido kafin ya maido kan tv yaci gaba da kallonshi, wurin Mommynta ta nufa lokacin tana d’akin Dad d’insu saida tay masu sallama sannan tasa kai tana ta dariya ganin haka yasa Hajiya Maryam tambayarta lafiya cike da farinciki tace Ya Haisam ne yace zai aureta yanzun nan, gaba d’aya suka bud’a idanu kafin sukai dariya suka ce suna tayata murna ta dace miji ta juya da gudu tana dariya, bayan fitarta Hajiya Maryam ta kira Hajiya ta sanar mata sosae tay farinciki tace ita dama tasan wannan shak’uwar inda zata kaisu kenan, tun daga wannan ranar Fanan ta koma yima Haisam kallon wanda zata aura, Bayan ya gama degree ya dawo Abuja ya fara aiki ita kuma Fanan ta gama Secondary tace ma Mommynta taji ana Maganar tafiyarta karatu ita dae aure take so tunda tana da wanda zata aura in sunyi auren tayi karatun, jin wannan Maganar yasa Hajiya Maryam ta kira Hajiya ta sanar mata game da zancen Fanan d’in ita kuma ta kira Mahaifinshi Senator Alee, Lokacin da ya kira Haisam d’in yay mashi Maganar auren da mamaki yace ai shi wannan lokacin wasa ne yake mata don baiyi tunanin da gaske take ba ganin ita yarinya ce kuma ya za’ai ai mata aure ma yanzu tayi k’arama, Senator yace yanzu dae bazai aureta ba kenan yace shidae yana mata son yan’uwantaka ne amman bana aure ba,sosae ya fahimceshi ya kira Hajiya ya gaya mata duk da bata ji dad’i ba amman tasan bazasu yi mashi dole ba lokacin ta kira Hajiya Maryam don ta sanar mata duk suna zaune a parlor bayan sun gaisa ne ta fara mata bayanin abunda Haisam yace sam Hajiya Maryam ta manta ma tana tare dasu Fanan d’in take wayar saida taji su Farha sun saka k’ara suna fad’in Sis Fanan ta fad’i sannan ta kai idonta kan Fanan dake baje k’asa kan carpet ashe tana jin abunda suke magana ta mik’e shine ta yanke jiki ta sume wata zabura Hajiya Maryam tay ta cillar da wayar tay kan Fanan, Hajiya nata hello hello sai Abraham ne mai sunan kakansu ya d’auka ta tambayeshi miya faru yace sis Fanan ce ta sume data ji suna waya da Mommy d’insu, rushing dinta sukai Hospital din Dad d’insu anan yasan abunda ke faruwa suka shiga bata agajin gaggawa koda ta farfad’o ta ganta a Asibiti ga iyayenta akanta sai ta fashe masu da matsanancin kuka tana Fad’in”Ya Haisam will not marry me why, why mom, Dad why? Am i ugly?…..” haka ta dingi sambatu Hajiya Maryam harda kuka sai lokacin ta amshi wayarta ta kira Hajiya dama tana ta kira ba’a d’agawa cikin muryar kuka take sanar da ita halin da Fanan take ciki tace tana tunanin ta samu heartbreak ne gashi dama raunannar zuciya gareta, Hajiya na jin hakan washe gari sai Abuja ta zauna da Haisam da iyayenshi tace mashi miye aibun Fanan da bazai aureta ba ko yana da wadda yake so ne yace mata a’a shidae kawae bai mata son aure, tace to yayi hak’uri tunda ita tana sonshi ya daure ya aureta ko don a ceci rayuwarta kar a rasata saboda abunda bai fi k’arfin suyi mata ba yace shikenan zai aureta amman ba yanzu ba sai ya gama Masters degree d’inshi da zai tafi bada jimawa ba Hajiya tace wannan ai ba matsala bane tunda dae ya amince itama sai ta fara karatunta duk in suka gama sai ayi bikin in Allah ya kaimu,Washe gari Hajiya da Haisam harda Senator suka tafi Lagos duba Fanan d’in har lokacin tana cikin mawuyacin hali a Asibiti sai faman koke koke take, koda suka ganta gaba d’aya ta basu tausayi ba kaman Haisam da shi Mutum ne mai tsananin tausayi hakanne ma yasa ya amince da auren nata ba tare da an kai ruwa rana ba, gaishe da ita sukae sukai ma iyayenta ya mai jiki cike da zolaya Hajiya tace “ashe mu Laila muka haifa ba Fanan ba to ai sai ki share hawayenki ga Majnun d’in nan na kawo maki” duk aka d’anyi Murmushi daga baya d’akin ya rage daga ita sai Haisam dake tsaye ya goya hannuwanshi a chest d’inshi ita kuma sai kallonshi take tana sheshsheka, can ya nufi gadon da take kwance ya zauna kan kujera tana ta6e baki tace mashi “Ya Haisam u don’t luv me, u will not marry me why?” fuskarshi a sake yakai hannu ya kamo hannunta ya d’an matse shi Calmly yace “How can i reject a precious gift of a beautiful young lady like u” waro ido tay da sauri tace “u accepted me to be ur wife?” lumshe mata ido yay nan take ta gane mi yake nufi ta tashi da sauri sai kace ba mai jinya ba tanata mashi dariya tana rufe bakinta shima Murmushi yake mata, can kuma sai yaga ta daina dariyar ta kwa6e fuska idanunta sun ciko da kwalla da sauri ya tambayi miya faru kaman zatai kuka tace mashi tasan tausayinta ne yasa yay accepting aurenta ba don yana sonta ba tunda da yace bazai aureta ba, mik’ewa yay ya koma gefen gadon ya k’ara kama hannunta yace mata yana sonta sosae shiyasa ma ya yarda zai aureta kawai lokacin da sukai Maganar da farko ya d’auka tana wasa ne amman yanzu tunda ya tabbatar tana sonshi da aure shima yaji yana sonta sosae, jin haka yasa ta fad’a jikinshi tana dariyar farinciki, a takaice dae tun daga Wannan ranar yasa zuciyarshi ta amince da ita matsayin wadda zai aura dama shi ba Soyayya yake ba duk da akwae mata da yawa dake mashi tayin Soyayya anan gida Nigeria har ma da k’asar waje inda yay karatu, saida Haisam yay da gaske sannan Fanan ta rage had’a jikinta da nashi don ta riga ta saba wata irin zazzafar soyayya take mashi, lokacin da akai Maganar tafiyarta karatu k’asar india cewa tay Haisam zata bi inda zaije yin Masters degree tay karatun acan Dad d’inta ya nuna yafi son taje k’asar India don shima acan yay karatunshi kuma akwae dan’uwanshi shima likita ne acan zai taimaka mata sosae,Lokacin data kira Haisam ta gaya mashi ce mata yay karta damu taje can d’in tace ai ita tsoro take ji yaje can shi kadae wata ta k’wace mata shi har saida yay yar dariya dama yasan kishi ne yasa take son binshi hakan yasa ya tabbatar mata da they’re meant for each other karta damu wannan dalilin ne yasa ta tafi k’asar India karatu, da anso ay auransu bayan ya gama karatun Dad d’inta ya nuna a bari ta gama karatun tunda Haisam d’in zai koma aiki Us ne sai su tafi tare akwae Asibitin da zai sama mata aiki acan itama tayi, lokacin ne kuma Senator ya nuna sai ya fara aiki anan kafin ya koma US d’in shine ya dawo wurin Sweetheart d’inshi K Hajiya, Wannan kenan game da Soyayyar Haisam da Fanan………….
Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 400 ne za’a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za’a turo shedar biya ta wad’annan nos din 09013804524 ko 08169856268._
Some Of Related Hausa Novels
Be With Us
-
- Follow our Facebook Page : Ai Hausa Novels
- Follow our Twitter Page : @ Ai Hausa Novels
- Follow our Youtube Channel: Ai Hausa Novels
DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.