Halysaah Page 127 By Khaleesat Haydar
HALYSAAH PAGE 127….Tsabar farin ciki Khaleesat kawai fashewa tayi da kuka don bata taba zaton ganin Aunty Farida a Maryland ba, she thought she was dreaming, ta kara rungumeta muryarta na rawa tace “Wayyo Aunty baki gaya min zaki zo ba ai” Aunty Farida ta dan yi murmushi tace “Ai na zata Junaid ya gaya maki” Ita dai Khaleesat bata ce komai ba tana hawayen farinhankali Khaleesat tace “Alhamdulillah, za mu fara jarabawa sati na sama in sha Allah Aunty” Aunty Farida tace “Maa sha Allah, Allah Ubangiji ya baku nasara” Cike da shagwaba Khaleesat tace “Aunty ina Ummata da Baba har da Nenne?” Aunty Farida tace “Duk suna gaishe ki” Khaleesat ta gyara zama tace “Amma yaushe kika zo? Yau ko jiya? Kuma naga you look dull, ko dai gajiyan hanya ne?” Aunty Farida tace “Daxu da rana ya dauko ni Airport, dama dolw akwai gajiya mana….” Khaleesat ta sauke ajiyar zuciya a hankali tace “Aunty naji dadin ganin ki sosai” Aunty Farida na kallonta tace “Bakya cin abinci ne kika rame” Khaleesat ta marairaice tace “Karatun final exams fa muke yi” Aunty Farida tace “Haka ne, Allah ya baku Sa’a” Sosai taga Khaleesat ta kara kyau, fatar ta sai wani sheki yake amma kuma ta rame, abincin da Ajay ya siyo ma Aunty Farida ta dau daya a ciki ta fara ci, don abinci kala hudu yayi ordering mata daban daban, Aunty Farida dai sai bin ta da kallo take, har aka yi magrib Khaleesat taki barin dakin sai labari take yi ma Aunty Farida, she look so excited don ma dei taga Aunty Farida kamar bata son magana don sama sama take amsa ta, kawai tayi tunanin saboda gajiyan hanya ne, dakinta ta tafi zata dauko extra darduma ta kai dakin da Aunty Farida ta sauka, tana shiga dakin taga wayerta saman gado a ajiye, daukar wayar tayi tana turo baki ta duba ko ya fashe taga ba abinda yayi, number Safiyyah tayi dialing babu bata lokaci ta dana, cike da muma Khaleesat ke sanar tace “Ke haba dai? Da gaske Aunty Farida ta zo??” cike da muma Khaleesat tace “Wallahi in gaya maki” Safiyyah tace “Ai ko gobe da safe ina nan zuwa gidan, Aunty Farida a Maryland?? Lallai mun yi babban bakuwa, zan mata girki kuwa in taho mata da shi gobe” Khaleesat na murmushi tace “To sai kin 20 goben, ki zo da wuri plss” Safiyyah tace “In sha Allahu kuwa” A haka Khaleesat ta katse wayar ta fita daga dakin tana rike da darduma, ido hudu suka yi da Ajay ya taho daga part dinsa, ta hade rai ta wani cinno baki kamar ba ita ke murmushi ba ta juya tayi taifiyarta dakin da Aunty Farida take, ya bi ta da kallo. Karle tara da rabi na dare Aunty Farida ta kalli Khaleesat dake zaune kusa da ita tana danna wayarta tane “Ki tashi ki tafi sai da safe, ni kwanciya zan yi” Khaleesat ta ajiye wayar hannunta tana kallonta da mamaki tace “Aunty in tafi kuma, nan zan kwana ai muyi hira” Aunty Farida ta hade rai tace “Hiran uban me za ki min?” Ganin babu wasa tattare da ita yasa Khaleesat ta mike a sanyaye tayi mata sai da safe tana tafiya a hankali ta nufi kofa ta fita daga dakin, hawaye taji ya cika idonta, tun zuwan Aunty Farida taga ta ki sake mata fuska har tana tunanin ko duk gajiyar hanya ce, magana ma sama sama kawai take yi mata, haka nan Khaleesat ta koma dakinta cikin sanyin jiki ta kwanta tayi lamo kan pillow. Washegari da asuba Khaleesat ta shiga gaida Aunty Farida, Aunty Farida ta amsa gaisuwarta, Khaleesat na wasa da hijab din iikinta tace “Ya gaiivan hanva Auntv?” ilyasazkar, after some minutes Khaleesat ta mike a hankali ta fita daga dakin ta koma dakinta, zaunawa tayi gefen gado ta fara tunanin to ko dai Ajay yace mata tayi masa wani abu ne bayan babu abinda ta taba masa tunda take, hawaye ya cika idonta ta kwanta gefen gado tana goge hawayen, bata koma bacci ba har karfe takwas sannan ta shiga bandaki tayi wanka ta fito ta shirya ta dau hularta ta saka sannan ta sauka downstairs zata shiga kitchen ta dora breakfast, zaune ta tarar da Ajay da Aunty Farida a parlor suna hira, tana hada ido da shi ta wani hararesa fuska daure ta wuce kitchen, shi dai ya ci gaba da maganar da yake yi da Aunty Farida, har aka yi azahar Aunty Farida bata yi wani hira da Khaleesat ba sai ma voice note da take tayi da Umma suna hira, duk jikin Khaleesat yayi sanyi don har ta gama concluding akwai abinda Ajay ya gaya mata, wani azababben haushinsa ta dinga ji a ranta, tana kitchen tana duba abincin da ta dora wajen karfe biyu Safiyyah ta shigo kitchen din da warmers din abinci a hannunta tana washe baki tace “Su Khaleesat yau a kitchen ga kamshi duk ya cika gidan nan, sai fa Aunty Farida tayi zaton cikin lumana ku ke zaune gidan nan ke da Ajay, sai kace girki kika saba yi a gidan” Ita dai Khaleesat bata ce komai ba ta amshi warmer din hannunta daya ta ajiye, Safiyyah na kallonta ganin mood dinta tace “Lafiya? Ya na gan ki haka? Me ya faru” Cikin rawan murya Khaleesat tace “Wallahi ban taba ganin devil kamar mutumin nan ba Sophie gashi nan ban san mekuwa da kyar take amsa min magana idan nayi mata, shi bayan iskanci har da gulma dama ya iya ban sani ba” Safiyyah ta bude baki tace “Kai haba? To ke baki tambayeta me yasa take amsa ki haka ba?” Khaleesat ta fashe da kuka tace “Wallahi taki kula ni mu yi hira tun jiya, alhalin shi sosai take magana da shi har da dariya, wallahi nasan sharri kawai ya laka min a wajenta, dama manipulator ne shi ban sani ba ashe” Safiyyah ta sauke ajiyar zuciya tace “Amma anya kuwa Ajay na da wannan lokacin Khaleesat, yaushe zai je yace masu ai kin hanasa hakkinsa?” Khaleesat ta mata wani kallo ta tsuke fuska, Safiyyah ta rufe bakinta da hannunta da sauri tace “Au, to… cewa zan yi yaushe zai ce masu baku zaune lafiya bayan magana ma sai ya ga dama yake ma mutum, kema kin san ba shi da wannan lokacin sai dai ki masa sharri, mutumin da ko magana ma sai ya so yake yi, ni dai bari in je in sameta, Allah ya sa kar laifin ki ya shafeni, bari in tafi mata da shinkafar sai ki taho da miyan” Daga haka Safiyyah ta fita daga kitchen din sai kuma ta dawo da sauri tace “Dakin ki ta sauka?” Khaleesat ta goge hawayen dake makale idonta ta girgiza mata kai sannan ta mata describing dakin da Aunty Farida ta sauka, Safiyyah ta fita daga kitchen din ta wuce sama, a stairs suka hadu da Ajay ta gaishesa ya amsa sannan ta wuce sama, da fara’a Aunty Farida tayi welcoming din Safiyyah, Safiyyah na murmushi tace “Kin sha hanya Aunty, ya gajiya?”da Nenne?” Aunty Farida tace “Umma suna gaishe ku gaba daya” Safiyyah tace “Ai mun kusa gamawa da Maryland in sha Allah mu koma gida” Aunty Farida tace “Allah ya baku sa’a Safiyyah” Safiyyah tace “Ameen Aunty” Aunty Farida ta sauke ajiyar zuciya tana kallonta tace “Tun da mu ka yi chatting dake few weeks ago Safiyyah hankalina yaki kwanciya har yanxu, dama kuma Junaid yana ta insisting in zo Maryland tun bayan sun dawo babu dadewa amma naki saboda naga kamar yayi wuri ace na zo, wannan abun da kika gaya min yasa nayi accepting na taho yanxu, ashe dama abinda Khaleesat take yi kenan Safiyyah? Me yasa tun da kika yi noticing hakan baki gaya min da wuri ba?” Safiyyah ta dan yi murmushi tace “Aunty ai ina ta kallon ko zata canza ne ammatace “Aunty ai ina ta kallon ko zata canza ne amma sai naga abun nata gaba yake yi, ga kuma chatting da naga tana yi da Jawwad, i tried my best in sa ta a hanya taki, kuma kin san ta da taurin kai” Cike da takaici Aunty Farida tace “Don bata da kunya har fa message ta min bayan mun yi magana dake da kwana daya wai in tura mata number Jawwad zata gaisa da shi ta WhatsApp tayi misplacing number sa, da baki min magana ba bazan kawo komai a rai ba zan tura mata, kuma ko da baki riga kin min magana ba nima zan ga ai Junaid ya kamata ta tambayi number Jawwad ba ni ba, yanxu abun kunya Khaleesat ke son ja mana a idon duniya kamar bamu bata ilimin addini ba? Allah ya rufa mana asiri tananeman tona mana??” Safiyyah Safiyyah tace “Amma dai baki isa ba.damuwa ne sosai” Safiyyah tace “To Allah ya sa komai ya canza a dalilin zuwan ki, amma kam Khaleesat tayi nisa bata jin kira, kuma fa duk da haka Ajay bai fasa yi mata duk abinda ya kamata ba just to make her comfortable in this country” Aunty Farida tace “Tsinuwar Allah take ta kwasar ma kanta kuma idan bata yi hankali ba tun ba aje ko ina ba zata gane kurenta, duka duka shekarunta nawa da ta san salon shaidanci haka? Wato rayuwar da tayi da Abdul bata dau darasin komai ba sai ma dodewa da kwakwalwarta ya kara yi” Safiyyah tace “Yanxu da na shiga kitchen take min kuka wai duk yanda aka yi Ajay ya laka mata sharri a wajenki, wai tun da kika zo kin ki kulata in ta maki magana da kyar kike amsata, ni dai Aunty kawai ki nuna mata kamar ba komai sai ki sa taAunty kawai ki nuna mata kamar ba komai sai ki sa ta a hanya kawai idan ba haka ba zata sake kullatar Ajay ne” Shigowar Khaleesat dakin yasa Safiyyah ta gyara zama tana murmushi tace “Allah sarki, amma dai kina nan har mu gama exams ko Aunty? Nan da kwanaki kadan za mu fara jarabawan” Aunty Farida tace “A’a gaskiya, ina ni ina zama har ku gama exams, few days zan yi in koma in sha Allah” Khaleesat ta ajiye warmer din miya dake hannunta sannan ta juya ta fita daga dakin fuskarta babu walwala, parlor ta sauka suka sake hada ido da Ajay dake zaune parlon yana shan fruit, ta zabga masa wata uwar harara kamar yanda tayi sanda zata wuce sama ta kai coolern miya, mikewa yayi fuskarsa a murtuke tana ganin haka ta juva da qudu ta koma sama. Bavan tafivar Safiyyah dagidan sai sannan an Aunty Farida tayi mata magana, ta tafi kitchen ta dauko mata madaran da Cup ta kawo mata tana kallonta cikin sanyin murya tace “Aunty shayi zaki sha in dauko maki Milo?” ba tare da Aunty Farida ta kalleta ba tace “Haka nace maki” Khaleesat dai na zaune tana kallon abubuwan da Aunty Farida ke cirowa can kasan akwatinta har ta gama fiddo su, kauda kai Khaleesat tayi, can ta mike zata fita daga dakin Aunty Farida tace “Ina za ki?” A hankali Khaleesat tace “A’a dama gyara kaya nake a dakina” Aunty Farida tace “Dawo ki zauna” Ba musu ta dawo ta zauna, daya bayan daya Aunty Farida ke mixing mata magungunan da ta ciro akwatinta tana bata, ita dai sai dai ta amsa ta sha don bata ga alamar wasa fuskar Aunty Farida ba baille har tace A’a, amma a ramita taiksici takke me yasa ba a ga kayan a Airport ba sandia ta shigo kasar, a haka har ta gama shan magungunan maltan ffuskarta babu walwaila ta mike ta fice diaga daikin ta koma nata dakin. Khaleesat na ta Awance dakinita har kasen kerte bakwai tun bayan da ita ga Aurity Farida zaune downstairs da Ajay suna hira wajen karte biyar, beside that gaba daya yanayinita ya canza kamar dai yanda taji shekaranjiya, she was just restless from what she is feeling, har fruits salad taji miyyar hada ma Aunty Farida amma taji baita de strength din zuwa tayi mata, bayan ta idar da magrib tana sanye da hijab dinte her kesa tana talfiya a harikali ta tafi dakin da Aunty Farida take, zaune ta sameta kan darduma ta idar da sallah itamaiki fruit ne?” Aunty Farida tace “A’a, Cup zaki dauko min kitchen” Khaleesat ta mike ta fita daga dakin ta sauka downstairs, tana shiga kitchen din taga Ajay a tsaye yana making cup of coffee, ko kallonsa bata yi ba ta dau cup din da zata dauka ta nufi kofa ya bi ta da kallon gefen ido, tun da Khaleesat taga Aunty Farida wani maganin matan zata bata ta hade rai, sai kuma ta juya zata fita Aunty Farida tace “Gidan uwar wa za ki?” Ta juyo kamar zata yi kuka tace “Ni fa Aunty zuciyata tashi yake yi tun daxu” Aunty Farida tace “Yayi fiftike zuciyar, dalla zo ki amsa gantalalliya kawal Khaleesat ta tafi ta zauna ta amshi cup din hawaye har ya cika idonta, bayan na cup din Aunty Fanda sai da ta kara mata wani daban, tun a nan ta fara in wani iri ilkinta……
