Hausa novels

Karfe A Wuta Chapter 84 By Ayshercool

Fitar ta yi wa mairamu daɗi sosai da sosai, dan ko kiwo zata fita, ba ta yi hanyar barin garin, balle ta fito bakin hanya.Suna zazzaune, shanunta na gefe na kiwo, sai nishaɗi take ji, tana ƙissima ta nan hanyar hammanta yake wucewa, idan zai zo riga, ko kuma ya tafi. Yayi mata alƙawarin komai daɗewa zai zo ya ɗauketa daga riga, ya tafi da ita can in da yake, ita ma ta ga gari, amma ba zata ji daɗin tafiya ta bar baffa da dada ba. Gashi rashin jituwar hamman da baffa baya yi mata daɗi, sai dai tana fatan barin rigar, tana son tayi karatu irin na hammanta, babban abin da yake ƙara burgeta da yi mata daɗi, shi ne idan ya zauna yana koyar da ita karatun addini, yana bata tarihin Annabi Sallallahu alaihi Wasallam, da sahabbansa wanda yake matuƙar ratsata da sanya mata nutsuwa da farinciki.Idan ta tafi birni, wurinsa ta san kullum sai ya bata tarihin Manzon Allah da wasu annabawan. Kuma ta huta da takurar baffa, a kan rashin fitowar manemanta, da an fara magana sai abu ya lalace, ya fara zancen ko iskokai ne suke hana maganar, ya saka ayi ta banka mata hayaƙi, dan an saka hayaƙi kuma sai ta hau suma, hakan ya sanya suke ƙara yadda da hakan. Bayan haka bijirewar jibo na zaman riga da zaɓar boko da barazanar da yake yi, ya ƙara sanya samarin garin nesanta kansu da Chubaɗo.”Chubaɗo, tunanin me ki ke yi ne?” Firgigita ta farka tana murmushi ta ce “Bakomai, daɗi nake ji, yau gani a bakin hanya, ina ta kallon motoci” sauran yan matasan suka din ga yi mata dariya, dan su suna zuwa, ita ce dai baffa baya barinta zuwa ko ina.Wani mutum suka hango yana tunkarosu, hannunsa riƙe da galan, gashi matashi a ƙalla zai shekara ashirin da bakwai, a ganinsu babba ne, amma sanye da ƙananan kaya, wanda hakan baƙo ne a wurin su.Yayi musu sallama suka amsa, ya ce “Yan mata dan Allah ina zan samu ruwa? Motata ta ɗauki zafi, a can baya na bar ta, kuma ina son zan yi salla, ruwan sha ne kawai a mota ta”Dukkaninsu kowa ya ce “Bai sani ba”‘ ban da chubaɗo, da tayi ƙuri da ido tana kallon kayansa, hamma yana saka irin kayan, kenan shi ma bayahude ne?.Ya ja ya tsaya cikin damuwa yana waige-waige, da alama kuma a gajiye yake.Kamar daga sama cikin siriryar muryarta ta ce “Na sani, amma ruwan  rafi ne, kuma a ɗan ciki ne” tayi maganar tana nuna masa hanya, yanayin hausar ya tabattar masa da cikakkiyar bafulatana ce, duk yan matan babu mai mayafi, suna sanye da kayan saƙi da ɗan kwali.Duk suka waiwaya suna kallon chubaɗo.Ya ce “Yauwwa yar albarka, nuna mini wurin”Cikin harshen fulatanci, suke gargaɗin ta a kan meyasa zata bi kaɗo, daga ganin sa yau.Ta ce “A tarihin Annabi da hamma yake bata, Annabi yana taimakon mutane, kuma babu kyau wulaƙanta mutane” ta wuce gaba ya fara bin ta a baya.Tayi gaba ba tare da ta ce masa uffan ba, tana ta kaɗa ‘yar sandarta, tana cilla ƙafarta cikin nishaɗi.Ya ce “Ba a kusa ba, na gaji” ta tsaya ta waiwaya ta ce “To kawo abun ka zauna ka jirani, sai na ɗebo maka”.Ya ce “A’a mu je” suka cigaba da tafiya, sun yi tafiya sosai, sannan suka ƙarasa rafin, ya durƙusa yayi alwala, ya ɗebi ruwa a galan ɗin da ya zo da shi.Yana satar kallonta, gaba ɗaya ba ta da wata damuwa, tana ta wasa da layar da take wuyanta ta sauko har kan ƙirjinta, hannu ɗaya kuma tana wasa da sandarta.Ya gama suka nufi komawa, ya ce “Ya sunanki ne?””Mairamu”Ya ce “Masha Allah, sunana Bashir, ina yawan wucewa ta hanyar nan, ba taɓa zaton akwai mutane ba, ko daga wani wurin ku ke zuwa?”Ta ce “A’a rigarmu na can ciki”Ya ce “Masha Allah, mu je na sai nonon na sha, idan zan wuce na din ga tsayawa mu gaisa, ba zan manta da taimakon da ki ka yi mini ba””Ba ni nake sayar da nonon ba, ni rako su kawai nayi, shanuna nake kiwo””Au har kiwon shanu ki ke yi? Lallai ke jaruma ce” suka yi maganar lokacin da suka dawo in da ya tarar da su, ya sa nono mai yawa sosai, ya basu kuɗin.Ya ce “Mairamu, sai na sake dawowa, ni ɗan garin azaren jihar Bauchi ne, ta nan nake wucewa, sai mu din ga gaisawa na gode sosai Allah ya saka da alkhairi” ta amsa da amin.Suka koma gida, sai da aka gaya wa ramata mariƙiyar chubaɗo, ta bi wani kaɗo ta raka shi rafi, ramata tun daga ranar ta hanata bin su.Bashir ya daɗe yana wucewa, idan ya tambaye su ina mairamu, sai su ce masa an hanata zuwa. Ya ce idan sun je su gaishe ta.Sukan gaya mata, sai da ta ce musu to, amma bata ɗauki hakan da muhimmanci ba.Maitama ya sake zuwa rigarsu, sun fafata da baffa sosai, a kan ya bashi mairamu, amma ya hana shi, ya ce shi aure zai yi wa yarsa, ba za a kaita cikin kafurai ba.Ga surutu ya fara yawa a kan rashin aurar da chubaɗo duk da irin kyau da Allah ya bata.Maitama ya kawo mata ƙatuwar radio da carsets, na wa’azi da tarihin manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam, ya koya mata yadda ake amfani da ita.Da daddare ƙawayenta da maƙwabtansu, zuwa suke su taru ta kunna musu, suyi ta saurara, idan wannan ya ƙare a saka wancan.Wani zuwa maitama ya zo da matarsa da ya aura, har da yara biyu da ta haifa, a wannan karon suka fara zuwa garin tare.Duk da haushin maitama da suke ji, sun karrama matarsa da yaransa sosai da sosai, sai dai a fili ta nuna ƙyamarta ga rigar, da nuna ita ba zata iya zama ba.Mairamu kamar ta haɗiye yaran nan, tayi ta ɗaukar ƙaramar tana goyawa, tamkar ta haɗiye su, da kyar suka yi sati ɗaya.Watanni shida suka shuɗe, mairamu ta sake bin ayari, zuwa bakin hanya wadda ta tasamma zama ƙaramar kasuwa.Ana ta hada-hada, kawai ta yanke jiki ta faɗi, numfashi ya sarƙeta, ya zamana ko motsi bata iya yi.Gaba ɗaya hankalinsu ya tashi, suka rasa yadda za su yi da ita, kamar an yi masa wahayi, sai ga motar Bashir, ya zo wucewa ya tsaya zai sayi nono ya wuce, ya hange su sun yi cincirindo a wuri ɗaya.Ya sauka ya fita, yana zuwa ya tarar da chubaɗo a baje a ƙasa ko motsi bata yi.Cikin tashin hankali yake tambayarsu, meyafaru da ita? Suka gaya masa faɗuwa tayi.Saroro suka yi, ganin ya taɓa ta, ba ta motsa ba, sai wani irin numfashi mai sauti daga ƙirji da take yi.”A garin nan kuna da Asibiti ne?” Suka ce “A’a, sai dai wurin mai magani”Bai yi sanya ba, ya ɗauki mairamu, ya sakata a motarsa, ya ce wasu daga cikin su su bishi, su tafi kaita Asibiti.Hama ce ta ce masa “A’a mufa rigarmu ba a zuwa asibiti” duk aka rasa mai bin sa, kawai ya shige motar ya ja ya tafi da ita.Cikin tashin hankali, suka kwashi kayansu, suka koma riga.A lokacin maitama yana gari, ai kuwa cikin kiɗimewa, aka yi ayari suka taho bakin hanya, amma babu Bashir babu alamarsa.Ramata kuwa tuni ta fara kuka tana salati, tana Allah ya rufa mata asiri ya sanya a ga mairamu, ba ita ta haifeta ba, amma akwai soyayya da shaƙuwa a tsakanin su.Sai dai suka dawo bakin hanya, amma babu Bashir babu chubaɗo, sosai Baffa ya din ga yi wa ramata faɗa, ta din ga kuka kuwa.Maitama ya ce su bari zai je asibitocin hanya ya duba, in dai da gaske kamar yadda sauran suka faɗa, asibiti ya ce zai kaita, to zai ganota.Baffa ya ce lallai sai dai su tafi tare, suka rankaya suka din ga duddubawa, ƙarshe a wani asibiti a nan jalingo suka gano mairamu.Maitama ya fara yi wa mutumin masifa, a kan dan meyasa zai ɗauke ta ya tafi da ita.Bashir ya ce “Ku yi haƙuri dan Allah, na san na ɗaga muku hankali, cikin yaran an rasa wanda zai biyo ni, na tarar da su da ita a gefen hanya, ba ta numfashi shiyasa kawai na ɗauke ta zuwa asibiti, in da muka fara zuwa suka turo mu nan”Baffa ya din ga faɗan shi baya zuwa asibiti, bai yadda da wannan abun ba, a ɗaukko masa ‘yar sa ya tafi da ita.Maitama ya ce “A’a ba za ayi haka ba”. Chubaɗo ta galabaita sosai da sosai, baffa ya cigaba da mitar, sai an bashi ‘yar sa, za a kashe masa ‘ya duk an ɗaura mata wasu kwanuka a fuskarta.Likitoci suka ce, ba zasu bayar da chubaɗo ba, ba ta warware ba, aka din ga kai ruwa rana da baffa, da kyar aka lallaɓa shi, ya ce yar sa ba zata kwana a wurin ba.Yamma sosai, Maitama yana son mayar da baffa gida, amma ba zai yiwu ya bar mairamu a asibiti ba, da mutumin da bai sani ba, ga lokacin babu waya.Ya lallaɓa baffa, ya kai shi tasha ya ce komai dare zai dawo masa da mairamu gida.Sai dai ya ga Bashir ba shi da niyyar tafiya, ya ce “Abokina mun gode da taimakon da kayi mana, zaka iya tafiya fa”Bashir ya ce “Ba zan iya tafiya na bar ta a halin nan ba, zan yi ta wasi-wasi ne. Dan ban manta alkhairin da tayi mini ba watanni baya” ya bashi labari.Nan hira ta ɓarke, yake bawa maitama labari, cewa shi coustom ne, ƙarshen wata yake komawa Bauchi hutu, yanzun ma gida zai tafi ya tsaya sayen nono, ya tarar da chubaɗo babu lafiya.Har yake bashi labarin, ainihi shi ɗan kasuwa ne, ya fi son harkar kasuwancin sa, amma aka turasasa masa wannan aikin, duk a takure yake.Shi ma maitama yake bashi labarin shi soja ne, nan da nan suka saba, suka din ga hira, kasancewar jikin da ɗan sauƙi.Yake gaya masa burinsa a kan mairamu tayi karatu, amma baffansu baya so, soyake lallai sai ya aurar da ita, ga shi bata da cikakkiyar lafiya.Suka kwana tare ta farfaɗo sosai aka bata magani, maitama ya ce ya samu dama, tafiya zai yi da mairamu can garin da yake aiki, a Benue state.Haka aka yi, asubar fari suka hau motar Bashir, ya je tasha in da ake hawa motar garinsu, ya bayar da saƙo a gaya wa Baffa, Bashir ya rage musu hanya, maitama yayi ta yi masa godiya sannan suka rabu.A hanya ya sake jaddadawa mairamu, zai tafi da ita gidansa da yake zaune, taji daɗin hakan, sai dai ta wani fannin ta ji kewar gida, yadda aka rabota da garin babu ko sallama.A cikin barrack gidan sa yake, matarsa kawai sai ganinsa tayi da mairamu, dan hatta kayan sakawa a hanya ya saya mata.Bayan ya huta take tambayarsa, lafiya ta ganshi da ita, ya sanar mata ta dawo nan da zama, nan ta ce bata yarda ba, shi kuma ya ce to ta koma gidansu, shi zai rayu da ƙanwarsa.Ta ɗauki gaba da fushi da shi, shi kuwa ko a jikinsa, chubaɗo bagidajiya ce a birni, ba ta iya komai ba, ta din ga ganin abubuwa kamar ba a duniya ake ba, maitama da kansa ya din ga koya mata abubuwa.Baffa ya rikice kamar yayi hauka, bayan samun saƙon maitama, na ya tafi da mairamu.Mairamu daga ita sai maitama, sai yaran gidan take mu’amala da su, hatta amfani da kayan wanka komai shi ya koya mata.Satinta uku a garin, babu alamar musulmai a in da suke, duk sati maitama yake kaita ganin likita, saboda matsalar ta. kwatsam sai ga Bashir. Abun ya basu mamaki nesa ba kusa ba, wai duba mairamu ya zo.Nisan tafiyar kawai maitama ya din ga hangowa, suka karɓe shi, suka karrama shi sosai da sosai, ya din ga murnar ganin mairamu ta samu lafiya. Sai da ya kwana a garin sannan ya koma.Sai dai bayan wata guda ya sake dawowa, a lokacin maitama ya saka mairamu a makarantar boko, karatun addini kuma, yana koya mata a gida.Duk wani aikin gida, mairamu tana yi wa matar hammanta, amma sam bata gani, kawai ta tsaneta.A wannan karon, maitama ya rutsa Bashir, a kan ya gaya masa dalilin zuwan da yake yi, bai yi ƙwauron baki ba, ya sanar masa son mairamu yake yi.”Kana mutumin birni, tayaya zaka auri bafulatanar daji, yarinya ƙarama?”Ya ce masa shi babu komai zai iya yana son ta a haka, sai dai da magana ta yi magana, ya sanar masa yana da mata biyu.Maitama ya ce yayi haƙuri, ba zai iya aura masa mairamu ba, duk da matashi ne, ko talatin bai yi ba, amma yana da abin hannunsa, ya ce yarinya ce yar ƙauye mara wayo wahala kawai zata sha.Sai dai mairamu, bai gaya mata yana son ta ba, amma maitama ya lura da yadda take murna idan ya zo.Sai dai hakan bai hana shi, sake niƙo gari ya zo Benue ba, saboda mairamu. Maitama ya sake jadda masa, ba zai bashi mairamu ba, ya ce shi in dai zai zo ya ganta shikenan, haka ya cigaba da sintiri.Wani zuwa da yayi, ya bata wasiƙa lokacin da ya zo, ta zauna ta karanta ta kasa, saboda manyan turanci ne, ta kai wa hammanta ta ce ya karanta ya fassara mata, ita ba ta san me aka rubuta ba.”Kalaman soyayya ne” ya bata amsa. Sai tayi shiru tana mamakin wace irin soyayya kuma?.Tana kewar baffa da kuma dada, amma tana jin tsoron gaya wa hamma yayi fushi.Sai da ta shafe watanni biyar, sannan maitama ya je riga, aikuwa ya sha takaici, dan ƙiris ya rage baffa yayi masa baki, ya ce ya dawo masa da ‘ya ya aurar da ita, kar ta lalace.Maitama ya ga idan ya dawo da ita, ba zata cigaba da samun kulawa ba, saboda yadda suka jahilci zamani da cigaban da ya zo da shi.Ya ce “To yanzu akwai mijin da zaka aura mata ɗin?””A’a amma zan samo mata””Ni ina da wanda zan aura mata, idan ka yarda ya zo ya nemi aurenta” ya ce bai yarda ba.Aikuwa maitama ya ce ba zai dawo da ita ba, in dai a garin nan za ayi mata aure, idan ya tafi ba zai dawo ba har abada, kuma ba zai sake ganin mairamu ba.Ba shiri ya amince, ya turo masa mijin da ya samo matan.Yayi tattaki har azare, yayi bincike sosai a kan bashir, ya tarar da familynsu mutanen kirki ne, shi kansa nagartaccen mutum ne, har wurin da yake aiki, sai da ya je duk ya kammala binciken sa, sannan ya koma ya tuntuɓi mairamu idan tana son Bashir, tayi shiru ta sunkuyar da kai, hakan ya sanya ya gane in data dosa.Ya nemo Bashir da kansa, ya gaya masa halin da ake ciki, amma ya ce zai bashi auren mairamu, idan ya amince da zai riƙeta amana, ya kula da lafiyarta da iliminta, a duniya ba shi da kowa sai Allah sai mahaifinsa da mairamu, itakaɗai ce yar uwassa.Bashir ya ce ya amince kuma yayi masa alƙawarin haka.Ya tura shi wurin baffa, nan ma sai da aka yi wani darun, ya ce ba zai bayar ba, da shi aka haɗa baki, jibo ya gudu da maitamu, maitama ya tsaya, tsayin daka, Baffa ya bayar da auren mairamu ga Bashir.Ya dawo da ita aka yi biki da ɗaurin aure, aka kai mairamu gidan Bashir da yake jihar Bauchi.Matan Bashir sai da suka kusa yi masa bore, jin zai auro musu, yarinya ƙarama bafulatanar daji, amma ya ce babu gudu babu ja da baya.Ba wata shaƙuwa suka yi da Bashir ba, dan haka wata irin matsananciyar kukyarsa ta din ga ji. Washegari kaita, ya tara matansa a falonsa, ya gabatar musu da mairamu.Sai dai sun sha jinin jikinsu, ganinta jawur kamar ƙosai, dai-dai gwargwado kyakykyawa ce ta gaske, kuma yarinya sharaf.Shi kansa ba wani babba bane ba, amma ya ajiye mata uku rigis, yayi musu nasiha sosai, ya ja amaryar sa ɗaki.Ita ma yayi ta yi mata nasiha, yana yi yana gaya mata kalaman soyayya, ta ja gefe ta duƙunƙune a mayafi, saboda kunya.Ko riƙe hannunta taƙi yadda ya yi, ya nuna mata yaransa, a lokacin yaransa huɗu, biyu maza biyu mata.A da kan ya auro, mairamu faɗa da kishi a tsakanin su, kamar sun cinye junansu, amma tun da yayi aure suka haɗe masa kai.Mairamu na da tsananin biyayya, da safe sai ta durƙusa ƙasa, zata gaishe shi. Suna da mai aiki, idan aka gama abinci, za ta je ta ɗaukko masa, amma ba zata taɓa cin abinci a gabansa ba, saboda kunya.Ana gobe zai bar ɗakinta, ya cika kwana bakwai, sannan wani abu ya shiga tsakaninsu.Kasancewar kowa ɗakinta ciki da ƙaton falo ne, banɗakuna biyu ne a tsakar gida, sai kuma banɗakin da yake cikin ɗakinsa falle ɗaya.Amma a ɗakinta ya kwana, cikin dare yana ƙoƙarin taimaka mata, ta kintsa, uwar gidan ta dalle su da fitila a tsakar gida, ta din ga zuba habaici da rashin mutunci.Da sassafe ta zo ƙofar ɗakin ta ce ya fito, tun da yau girkinta ne.Sai wajen la’asar, ya samu sukunin sake shiga ɗakin chubaɗo, ya tarar da ita a kwance, abincin ma da aka kawo mata ba ta ci ba.”Fulanina, sannu ya jikin?”Ta ƙunshe fuska ta ƙi magana.”Ba ki ci abinci ba, me zan sayo miki ki ci?” Ta girgiza masa kai alamar babu.Ya kwantar da murya ya ce “Tashi na baki abincin a baki, ai za ki ci ko fulanina”Fafur taƙi sai ma ta saka masa kuka wai gida, ya mayar da ita gida. ya tashi ya fita ya sayo mata tsire fal, da fanta ya kawo mata.Ya din ga rarrashinta, da ƙyar ta daina kukan, ai ba ta saurari nama ba, ta din ga ɗaɗɗakar fanta.Yayi murmushi ya ce “Ka ga bafulatanar Bashir, da ga yanzu na gano lagonki, fanta ce maganinki” sai kuma ta sunkuyar da kai tana murmushi.Sai da ya shafe wata guda a Bauchi, ya kaita can garinsu azare, da yake shi ba a can yake zaune ba, a can ya samu ya ɗan sake da ita sosai, dan sai da suka kwana uku, sosai danginsa da yan uwansa suka karramata.Mamaki take yi yadda yake salihi, a gaban mutane, ake yi masa kallon mutumin kirki, yake sunkuyar da kai, amma ida suka keɓe yayi ta yi mata fitsara da rashin kunya.Wata irin soyayya yake yi mata, wadda bai iya nuna mata a waje ba, dan da gaske yake jin sonta a cikin ransa, chubaɗo akwai haƙuri da biyayya, ya samu har ta ɗan fara sakewa da shi, yayi kamar ya ce zai tafi da ita in da yake aiki, dan dab da za ayi bikin su, aka mayar da shi Naija state.Da ya fara yi mata wani abu dan soyayya da kyautatawa, sai ta ce ya bari, saboda tana son ta shiga aljanna.Ya dubeta ya ce “Waye ya ce idan na yi miki tausa, ko dafa miki ruwan wanka, ba zaki shiga aljanna ba? Jin dadin biyayyar da ki ke yi mini, ya sanya nake yi miki abin da zaki ji daɗi kema””To zan shiga aljanna?””In sha Allah, hannuna a naki zamu shiga”Ta rausayar da kai ta ce “Wataƙila babar saifu ta hanaka, ta ce na ta hannun zaka riƙe ita da amarya, ku tafi ku barni” tayi maganar cikin kishi da yarinta.Yayi dariya ya ce “Kowaccenku, zan riƙe hannunta mu shiga tare in sha Allah”Mairamu bata aikin komai, gidan ma kusan ba wanda yake wani aiki a gidan, saboda suna da masu yi musu aiki.Da fari tana so ta ɗan sake da matan gidan, amma suka nuna mata bata isa ba, hatta masu aikin ma wani gani-gani suke yi mata.Sai dai saifullahi ne mutuminta, shi ne ya kan shigo ɗakinta, har su ci abinci tare da shi.Tun da Bashir ya koma aiki, suka mayar da mairamu tamkar baiwarsu, suka din ga sakata ayyuka na wahala, suka dakatar da mai aikinsu, ita ce wanke-wanke, shara raino wankin yara da kuma girki.Gashi har a lokacin da ƙauyanci da ƙuruciya a kanta. Maƙwabta suka din ga ziga su, wai ƴar aiki kawai aka kawo musu, ban da haka ina wannan bagidajiyar zata iya kula da miji.Ranar da zai dawo, duk sun sha ado da kwalliya, mairamu kuwa futu-futu dan wuni tayi tana aiki.Duk zumuɗin ya zo ya ganta, bai ji daɗin ganinta a haka ba, da ya shiga ɗakinta sai da ya ce mata ƙazama. Haƙuri kawai ta bashi ta yi shiru.Ranar da ya dawo ɗakinta, ta yi kwalliya, hakan yayi masa daɗi sosai da sosai, babban abin da ya basu mamaki, bai wuce jiyo dariyar Bashir da mairamu ba, suna yi mata kallon sokuwa, amma ta saka miji a ɗaki suna ɓaɓɓaka dariya.Tambayarta yake yi “Da a baki fanta, da nagge wanne ki ka fi so?”Ta ce “Kai Nagge mana”Ya ciro check, ya rubuta Naira dubu ashirin irin ta da a jiki, ya ce “Nan dubu ashirin ne, da na baki wannan, da na baki nagge wanne ki ka fi so?”Tayi dariya ta ce “Aradu na fi son nagge” suka tuntsure da dariya ya ce “Baki da wayo, wannan kuɗin sai ya sai miki nagge biyar” “Wannan ɗin, takadda ce fa kawai gaskiya na fi son nagge”Bashir ya ce “To da ni da nagge wanne ki ka zaɓa?” Ta waro ido. Ya ce “Sai kin zaɓa fa”Ta faki idonsa ta ce “Nagge”ya riƙeta yana yi mata cakulkuli ya ce “Me ki ka ce?” “Kai na zaɓa” tayi maganar tana dariya.Mairamu ba ta taɓa kai ƙarar wani wurinsa ba, su kuwa ba sa rasa Sharrin da zasu yi mata, wani ya yadda wani ya rabu da su.Ba ta taɓa cewa ya sai mata wani abu ba, duk da yana jaddada mata, duk abin da take so, ta tambaye shi.Maitama ya zo gidanta bayan auren, sai dai yayi farinciki da yadda ya tarar da mairamu, babu yunwa babu ƙishirwa, akwai kulawa sosai da sosai.Duk da kashedin da Bashir yayi musu a kan mairamu ba ta da cikakkiyar lafiya, bai hana idan baya nan su azabtar da ita ba su tura ta gaban hayaƙi ba.A gidan Bashir ta fara al’ada, shi ma sai da matan suka yi ta ƙanan maganganu, dan sun zata ciki ne da ita.Ana haka Allah ya yi wa baffa rasuwa, babu wanda ya sani, dan sai da yayi watanni uku, sannan maitama ya sani, ya saka aka gaya wa Bashir.Chubaɗo ta sha kuka, kamar babu gobe, ta shiga matsananciyar damuwa da tashin hankali.A haka ta shafe shekara guda cif, dada ta zo mata, ta ji daɗin hakan, sai dai sai da suka kuma yin kukan rashin baffa.Dada ta din ga rarrashin mairamu, dan ta fuskanci yanayin zamanta da abokan zamanta babu daɗi, amma gidan akwai kulawa komai na buƙata akwai.Sai da ta shekara biyu, ko ɓatan wata ba ta taɓa yi ba, ko a jikinsa, ita dai tana ta addu’a, Allah ya sa ita ma ta haihu, dan yar da aka haifa hafsa kamar ta ce a bar mata, duk da idan ta  ɗauka ayi ta yi mata habaici.Aka kuma canzawa Bashir wurin aiki, ya samu ƙarin matsayi, ga aiki ga kaswuanci, ya sai wuri a kano, ya fara gini, saboda yana ƙaunar garin kano, yana son idan ya gama, su koma can, ya nemi transfer ya dawo arewa gaba ɗaya, dan a kano ya auri matarsa ta biyu, kuma garin ya burge shi.Watarana da safe, ana shirin karyawa, jaririya hafsa ta fara rarrafe, mairamu ta ce “Ki kula kar hafsa ta ɓaro kunu a jikinta” aikuwa tana rufe baki, hafsa ta sheƙo kunu a jikinta, ta ƙone, tun a ranar suka laƙaya mata maita.Haka kurum ta fara rashin lafiya, abu yaƙi ci yaƙi cinyewa, ga Bashir ba ya gari, aka rasa mai kaita Asibiti, abu har da suma, ciwonta kuma ya tashi, sai masu aiki ne suka kaita Asibiti, a tsukin lokacin Bashir ya dawo, ya sha baƙin ciki da ɓacin ran abin da suka aikata.Duk ta rame ta yi duhu, ya mayar da ita Asibiti da kansa, aka tabattar masa da tana da juna biyu. Ya din ga murna kamar ba a taɓa yi masa haihuwa ba, sai dai yayi shiru da bakinsa, da ya tashi komawa aiki, ya ce da ita zai tafi.Suka yi surutansu da masifarsu, suka gama.In da aka mayar da shi aiki, can wani gari ne a kudancin Najeriya, a lokacin rabonta da hammanta, kusan shekara duk ta damu tana son zuwa ganin gida, ya ce ta bari idan ta kusa haihuwa, zai mayar da ita gida ta haihu ta yi arba’in.Lokacin maitama shi ma babu zama, daga wannan gari zuwa wancan gari, har ƙasashen da ake yaƙe-yaƙe a Afrika ake tura su aiki, dan haka bai samu sukunin sake zuwa wurin mairamu ba, sai dai kullum tana zuciyarsa.Tana yawan yi wa Bashir zancen makaranta, ya ce zai mayar da ita, yana sane, dama target ɗin sa, ta haihu ko ɗa ɗaya ne, sai ya sakata a makarantar.Ashe matansa sun ƙwafe tafiyar da ya yi da ita a ransu, sun ƙullace su, dama a hakan a rashin wayon nata, da azabar da suke yi mata, gani suke yi ta mallake shi abin da take so kawai yake yi.A can garin kuwa, yana bata kulawa iya yin sa, amma laulayi ya sakata a gaba, ciwonta kuma kusan kullum cikin tashi yake, shi yake yi mata komai yake kula da ita, cike da ƙauna da tausayawa, bai taɓa gajiyawa da ita ba, sosai yake tausayinta, ba ta da wasu dangi, da za ace su zo su kula da ita, ko ya kaita tayi rainon cikin a can, dan har ga Allah ba zai iya kaita rigar nan tayi rainon cikin a can ba.Idan ya samu lokaci, yana zuwa can gidan, ya yi kwanaki ya dawo, cike da addu’a da fatan Allah ya sauketa lafiya.Cikinta na da wata takwas, ya je gida, tun da ya je, gaba ɗaya tamkar an shafe masa duk wani tunani da ya shafi mairamu, yazo da kwanaki biyu, aka turo masa da takardar transfer, an mayar da shi aiki jigawa.Bai ko sake komawa garin da ya baro marainiyar Allah ba, ya je yayi reporting a wurin aikinsa na Jigawa.”Abba, ina ga canza hanya zamu yi, akwai go slow sosai a nan, maganar Nasir ta dawo da Abba daga tunanin da yake yi.

Ayshercool 08081012143

Back to top button