Hausa novels

Harijin Sarki Page 26 Romantic Hausa Novel

Koda suka je Fes ɗin kai tsaye gidan granny suka isa ta tarɓesu da farin cikinta ganin halin da Samha take ciki ta kaɗu matuƙa ta rinƙa cajeta ita kuma ta kwantar da kanta a jikinta tana hawaye cikin sanyin yanayi tace “Shiyasa naji banason zuwa Casanblaca kuka dage da faɗamin babu komai ashe zuwa zanyi na haɗu da ƙaddarata Granny don Allah dubeni, ki kalli yanda na koma abar tausayi bana iya yiwa kaina komai sai abinda akayimin, yanzu a haka zanci gaba da rayuwa babu farin ciki?”….. Rufe mata baki Granny tayi tace “Insha Allahu da wuri zakibada labari wannan sharrin tsafi ne, muda muke da Allah wanda ya halicci tsafi ya kuma halicci me yin tsafi Samha babu komai matakin nasara juriya kaddararki da wahala amma zata zama abar mamaki ga waɗanda suke burin nakasa rayuwarki ta lalace insha Allahu saidai tasu ta lalace” Sultan bai wani daɗe sosai ba ya fita sai wajen magrib ya dawo ashe surck ya tafi yayo siyayya wa matarsa da babynsa nan ya nemi keɓewa da Granny ya sanar da ita komai game da damuwar Samha sannan ya faɗa mata yanzu haka Samha tanada ciki amma itama batasan dashi ba, an shawarceshi da yayi shiru kada ya sanar da ita ne saboda damuwar dake tattare da ita gashi har yanzu tanajin ita batakai zama uwa ba, sosai Granny tayi farin ciki da jin jikanyar tata nada ciki kuma tayi masa alƙawarin kulawa da ita domin ta fuskanci duk a rikice yake kamar an raba shi da wani sashi na rayuwarsa haka yakeji, da wannan yayi musu sallama ya tafi itama Samha taji babu daɗi ganin ya tafin ne yasa tun a daren Granny ta fara haɗa mata magunguna wanda ta karanto a Ɗubbu Nabiy (Likitancin Annabi) ta fara yi mata amfani dasu, cikin ikon Allah a cikin wata guda sai gashi ta fara motsa jikinta har tana iya tashi daga kwance tana iya kai hannunta ta ɗauki abinda takeso.Duk sati Sultan yake zuwa sosai Granny ta fahimci rashin kunyarsa da jarabarsa don haka da yazo take shigewa ɗakinta ta barshi da matarsa haka zai yini babu inda zashi yana lalube Samha idan yaga babu idanun mutane ya ɗauketa zuwa ɗakinta ya baza mata wutsiya son ransa sannan ya tafi wani lokacin ma idan yaso iskanci haka zai ce kwana zaiyi ko kuma yace zai fita da ita unguwa to ita take ƙin zuwa unguwa don tsarin maganin babu yawo har sai angama, haka zai ji haushi ta ita kuwa tayi masa kamar bata fahimta ba haka zai gama fushinsa ya ware in kuma ya tafi da fushin bazai hana in yaji jarabarsa ta kasa sauka ya dawo ba, to a can gidan nasa ma rigima taƙi mutuwa domin ko yanzun da Samha batanan yaƙi yarda da dukkan matansa biyu har gara Jalila tana samun arziƙin yana amsa maganar ta amma tunda Aqsam ya bayyana masa ya tuhumi cikin matansa akwai waɗanda suke shirya wani mugun abu a kansa da Amaryarsa, daganan ya ƙara sanyawa takunta idanu yake kallon duk motsinsu batare da sun sani ba inda ya ƙara cika da mamakin yanda suke ta shirya mugun abu cikin sirri su a tunaninsu sunata murnar Samha ta tafi kenan domin kuwa daga can mutuwa zatayi inda suke haƙon suna gamawa da Samha zasu koma kan Jalila da NahNah suyi ƙoƙarin haihuwar Sultan ƙarami kuma a tsakaninsu.Jikinsa yayi sanyi duk yaga ta kowa ita kuwa Jalila itama tsaf ya kalleta duk ƙulle ƙullenta na ta samu ta ya ƙulata ne ko sau ɗaya ita kuma tasan yanda zatayi ta samo cikin da zatazo ta haifa matsayin nasa, sosai jikinsa yayi sanyi sai a wannan lokacin ne ya gano ashe Najjisa da Amrusha duk da sanya hannun Najjisa itace tayi tsafin da ya zama ajalinsu ake kallonsa da abin har yanzu akwai masu masa kallon wani gawurtaccen matsafi me amfani da wani sashi na jikin ɗan adam matuƙa an zargeshi da kisan Nataj da Amrusha yanaji yana gani bashi da hanyar kare kansa.Duk da yasan komai suke shiryawa bai taɓa nuna musu ya sani ba kawai dai kwanciyar aure yaƙi aminta yayi da kowacce akwai ranar da Jalila taci alwashin ko a rashin hayyaci sai ya sadu da ita itadai burinta tayi ciki, ta haɗa kayan ciye²nta tasa aka kawo masa yana zaune a lambunsa ta caɓa ado irin na haɗaɗɗun matan, Morocco ta nufo lambun cikin isa sai zuba ƙamshi takeyi. Tana zuwa ta zauna kusa dashi tana wani yauƙi tana masa kwarkwasar da tasan zata ɗauki hankalinsa ya kalleta kawai yayi murmushi tare da cewa da Samha zan kira da dare karki kashemin waya yau”Juyawa yayi ga Jalila ta kalleshi tana karyar dakai tace “Ranka ya daɗe nazo ɗebe maka kewa ne” murmushi yayi yace “Kin kyauta sosai me kika kawo min dama yunwa nake ji” lumshe idanunta tayi tace “Abinds nasan kana so lokacin kana sona” buɗewa ta fara yi ya kalleta ya jinjina mata kai yace “Yayi kyau fara ci sai naci nima” batayi masa musu ba ta zuba abinda tazo dashi tanaci tana kallonsa ya ɗauki ruwa zai sha ta maza ta tsiyaya masa lemon data haɗa yaja fasali ya karɓa ya kurɓa kaɗan ya ɗago kanta yakai mata bakinta ta ɗauka ɗan na soyayyar nan zai bata, yana ganin ta kafa kai ya danna mata cup ɗin saida ta shanye tsaf sannan ya cire yayi cilli da cup ɗin ya tashi yana mata murmushi ya nufi part ɗinsa ta Mike ta bisa da sauri tana ayyana wannan wanne irin abune ta haɗa masa magani don yasha ya ci ta ƙarshe ya ɗaɗaka mata shi a cikinta ta shanye aikuwa bisa zatayi dole sai ya san yanda zaiyi da ita, kafin ta gama shiga shi kuma ya fice ya shiga mota ya fice tana kallonsa cike da baƙin ciki hawayen takaici suka zubo mata tabbas Sultan ya raina mata hankali yanzu duk wannan shirin da tayi ya tashi a banza kenan????………….

Back to top button