Hausa novels

NIHAAD Chapter 34 By Khaleesat Haiydar Complete Novel

34
Duk a zaton Nihad aljanin daren ne ke tattaba ta cikin Hijab, tunda dama da shi ta kwanta a rai, a rikice take tattaba jikinsa tana kokarin cire hannunsa daga bakinta ta kara kwala wani ihu kamar xata shide, bayan ta gano shine ta fada jikinsa da sauri ta rufe fuskarta a kirjinsa tana kuka sosai tace “Don Allah kace Abba ya canza mana gidan nan ni baxan iya zama ba wallahi, wayyo Allah na shiga uku” Ya rike ta very tight shi ma ya daura fuskarsa saman kanta, tana jin yanda yake sauke numfashi still holding her tightly, kamshin turarensa shi ma ya taimaka wajen kara kwantar mata da hankali, sun fi minti goma a haka, jin ya ki saketa ta dago a hankali har lkcn gabanta na faduwa tana kallonsa cikin duhun, a hankali taji ya saketa ya koma ya kwanta a bit relieved, tana ganin haka tayi saurin kwanciya bayansa tana kuka a hankali, ko minti biyar bai kara ba bacci me nauyi ya daukesa, Nihad kuwa bata sake komawa baccin ba, don duk tunaninta kilan shi ma ya ga aljanin daren ne shine ya ji tsoro ya riketa haka, toh shi ma ya ji tsoro ina ga ita, hakan ya kara daga mata hankali ta dinga shige masa tana shesshekan kuka ta takure cikin hijab dinta, raba daren Nihad tayi tana masu gadi, duk motsin da taji sai ta kara makale masa, sai kusan karfe hudu da rabi bacci barawo ya saceta. A hankali khalil ya bude ido ta dalilin tada sallah da aka yi, ya mike zaune da kyar ya kunna switch din dakin dake bangaren da yake ya juya yana kallonta, baccinta kawai take, ya kalli towel dinta dake can side din sai kuma ya sauka daga kan gadon ya shiga bandaki, Har ya dawo masallaci Nihad bata farka ba, kallo daya yayi mata ya dauke kai da sauri, ya dau karamar wayarsa ya fita daga dakin. Sai karfe bakwai saura Nihad ta bude ido a hankali, bin dakin tayi da kallo sannan ta kalli gefenta towel dinta ta gani a yashe ta zaro ido ta kalli jikinta da sauri ta mike zaune tana gyara hijab dinta, kaddai ya ganta haka? Tunanin hakan yasa ta rufe fuskarta da pillow tana kara rufe jikinta da hijab dinta a kunyace, daga karshe dai ta mike ta shiga bandaki, bayan ta idar da sallah tana ta zaune saman darduma har gari ya waye gaba daya sannan ta mike ta fita ta koma dakinta, wanka tayi ta shirya ta fito parlor, bata gansa a parlon ba sai wayarsa dake saman kujera, ta kalli kofar kitchen din alamar yana kitchen, ringing wayar ya fara yi ta kalli kofar kitchen din da sauri, da ta ga kamar bai ji ba tunda bai fito ba tana tafiya a hankali ta karasa gun wayar ta dauka tana kallon me kiran, Father ta gani a screen din, dai dai nan ya fito daga kitchen din ta mayar masa da wayar ta ajiye, kamar yanda ta ki kallonsa shi ma haka bai yarda ya kalleta ba, ya tafi gun wayar ya dauka, kallon screeen din yake ko kiftawa babu, yana ta kallo har kiran ya katse, ta ga ya zauna without knowing he did so, still kuma idonsa na kan screen din, he looks a bit baffled, sake kiransa aka yi, ya daga kai ya kalleta suka hada ido, sai kuma ya dauke kansa ya mike ya nufi kofar ya fita compound, bayan ya fita still bai daina kallon wayar ba kuma ya ki dagawa, zaunawa yayi a saman dakalin da ya saba zama ya daga kiran tare da sallama, he wasn’t given the space to even greet or say anything, ya dai yi shiru yana sauraronsa har ya gama fadin abinda xai fada ya rufe ido a hankali yace “Gobe in sha Allah” yana fadin haka yaji an katse wayar ya kalli screen din, sai kuma ya jinginar da kansa da bango, and he sat there for more than an hour ya kasa shiga cikin gidan, Nihad dake ta zaune parlor ta mike ta shiga kitchen din taga shayin da ya hada a mug har ya huce. Har Nihad ta iso inda yake bai sani ba, shadow dinta da ya gani ya sa ya daga kai, ta jingina da bango tace “Me yasa ka bar shayin a kitchen a bude kuma?” Bai ce mata komai ba, ta tsaya for almost 2 mins, can ta juya ta koma ciki, dafe kansa yayi, a karo na farko yayi regretting barin wayarsa a kunne, yawanci sai xai yi waya yake kunna wayar yana gamawa kuma zai kashe but for almost 3 months now ya daina kashe wayar. Tashi yayi daga karshe ya shiga cikin gidan, tana zaune saman kujera ta bi sa da kallo kamar ya sani ya juyo ya kalleta, ta dan turo baki ta ci gaba da kallon tv da take, har bayan azahar khalil na daki, Nihad ta ji ana kwankwasa gate, ganin bata ga alamar zai fito ya bude ba ta mike ta tafi dakinsa, murda kofar tayi ta shiga ciki, a rufe taga idonsa, ta karasa inda ya ajiye makullin ta dauka ta fita, tana bude gate din gidan taga Naf da zully a tsaye, ta ɗan buda ido cike da fara’a tace “Lahhh, sannun ku da zuwa” Naf tace “Nihad, yaushe Husnah ta bar gidan ki?” Nihad da gabanta yayi mugun faduwa don suna cewa Husnah aljanun daren da ta manta ne suka fado mata, cike da karfin hali tace “Jiya da safe” Naf ta kalli Zully, sai kuma ta kalli Nihad tace “Toh lafiya qlau ta bar gidan ki?” Nihad ta marairaice tace “Ni dai da safe na ganta jikinta wani iri kamar an zaneta, fuskarta duk ya kumbura haka ma bakinta da idonta shine tace min wai aljanun dare ne suka mata haka” Naf da zully suka kwashe da wani dariya barin Naf da sai da ta kai kasa sbda dariya, Naf ta dago bayan tayi dariyarta me isarta tace “Halan ku biyu kadai ne a gidan?” Nihad ta girgiza kai tace “Aa shi ma yana nan ai” Zully tace “Ke kuma kina ina sanda aljanun daren yayi mata haka?” Nihad tace “Ni dai bacci nake, kuma ai kun san anyi ruwan sama, kawai na tashi da safe na ganta a kitchen duk an zaneta, tace in miko mata jakarta da wayarta” Dariya kawai su Zully suke har da kyakyatawa, Nihad dai sai kallonsu take with confusion, Naf tace “Toh sai ku daure ku zo dubata a asibiti don tana can rai a hannun Allah an bata gado, mu kuma ce mana tayi bata kwana a gidanki ba hatsari tayi xata tafi kaduna jiya da daddare an kirata mamarta ba lafiya” Nihad ta gwalo ido tana kallonsu, Naf tace “Ai kam dai tana asibitin da aka ta6a kwantar da kawar zully nasan kin gane asibitin” A hankali Nihad tace “Na gane” Naf tace “Sai ki gaya masa ya kawo ki ku dubata, don da aiki ma ake da niyyar mata a idonta daya daga baya kuma idon ya ɗan bude kadan” Nihad tace “Toh xan gaya masa” Naf tace “Mu yanzu akwai inda za mu, amma xa mu hade a asibitin anjima in ya kai ki kenan” Nihad tace “Toh” Daga haka suka koma motar Naf ta bi su da kallo, sai da suka bar layin sannan ta juya ta koma cikin gidan, tsaye ta gansa bakin kofar parlor, tana karasawa balcony ya hade rai yace “Wa ye ya Kwankwasa gate din?” Babu yabo babu fallasa Tace “kawayena ne, sun zo su ce min Husnah tana asibiti bata da lafiya wai har xa ayi mata aiki a idonta daya, ni dai wllh ka kai ni in dubata tunda a nan gidan aljanun daren suka mata haka” Kamar xata yi kuka ta kare maganar, ya dinga kallonta, can ya juya ya koma ciki. Bayan la’asar taga ya shirya yana rike da mukullin mota ta mike da sauri kafin tace komai yace “In kin shirya ina jiranki idan kuma baki shirya ba inyi tafiyata” Da sauri ta tafi daki ta dauko hijab din ta ta saka, bayan sun bar gidan taga sun hau saman titi tace “Asibitin xa mu je?” Yace “Ohk” Nan ta gaya masa asibitin, tana ganin sun kusa asibitin tace “Baxa mu siya mata wani abu ba?” Yace “Ohk za ki siya mata wani abu kenan?” Tace “Ehh” Yace “Me zaki siya mata?” Tace “Ga wasu masu fruits can kawai ka tsaya mu siya mata” Parking yayi dai dai wajen ta bude motar ta tafi tace su hada variety of fruits na 10k, suna hadawa ta shigo motar tana kallonsa tace “Dubu goma ne” Yace “Ohk, ki basu” Tace “Toh ina atm card din?” Yace “Atm din wa?” Ta wani kallesa tace “Naka mana?” Yace “Ni nace maki ina da kudin siyan fruits?” Ta marairaice tace “Toh amma ba sai da na tambayeka ba?” Yace “Bani da kudin biyan fruit din kawarki” Kamar zata yi kuka tace “Na shiga uku, bayan kasa nace su hada fruits din, ni yanzu ya zan ce masu?” yace “Ke ina atm card din ki?” Tayi narai narai da ido tace “Bama ni da shi ni, kuma wllh babu ko sisi account dina tunda Abba ya dai a bani kudi” Yace “Sauka kice masu su mayar da fruits dinsu kin fasa siya” Ta gefen ido take kallon alamar atm card din nasa dake aljihun rigarsa, can ta zura hannu da sauri ta cafki atm din, rike aljihun yayi yace “Keee” Ta hade rai tace “Idan baka sake ba zan karya wallahi” sai kuma ya cire hannunsa a hankali, ta turo baki ta zare atm card din ta sauka daga motar ya bi ta da kallo, ta basu suka cire kudinsu ta koma mota da fruits din ta saka atm card din a handbag dinta ta kulle, bayan few seconds kawai ya tada motar suka bar wajen. Suna isa asibitin Nihad bata taba tunanin zai shiga dakin ba, amma sai kawai ta ga ya shiga, Husnah na hada ido da shi sai da ta firgita, Su Naf da Zully da wasu frnds dinsu biyu dake dakin suka mike ganin irin firgitar da tayi, Nihad ta kasa karasawa cikin dakin ta makale jikin kofa ganin yanda kamannin Husnah ya canza, ita tsoronta ma take ji yanzu, shi kam ya karasa can cikin dakin har gun gadon ya kalli su Naf calmly yace “Sannunku” Siyama kawar Naf tana Murmushi ta tashi daga saman kujeran da take zaune ta ajiye masa tana kallonsa keenly, cikin taushin murya tace “Yauwa sannu da zuwa, have a seat pls” Ya dan kalleta yace “Nagode kiyi zamanki” Kallon siyamar kawai Nihad take babu yabo babu fallasa, ai tun da Husnah ta kalli khalil sau daya bata sake yarda ta kallesa ba sai mutsu mutsu take yi a inda take zaune kamar warce cinnaka ke cizo, Naf, Zully, da su siyama sai kallon khalil kawai suke, ya dafa gadon da Husnah ke kai yana kallonta da kyau yayi kasa da murya as if talking to him self yace “How are you feeling?” Naf ta kalli Zully da sauri, Husnah dai kai kawai ta gyada ba bakin magana, ko kadan Nihad bata ji abinda yace ba, Yana gyada kai yace “Quickest recovery dear!! And u are always welcome to our home you Slattern!!” Yana gama fadin haka ya juya ya bar wajen duk suka bi sa da kallo, Zully da Naf sai kallon juna suke da wani expression, Husnah dai bata dago kai ba, Yana isa bakin kofa ya amshi fruits din hannun Nihad ya ajiye masu nan bakin kofar a saman wani table, ya juya ya kullo masu ward din, har suka shiga mota Nihad bata iya ta ce komai ba kamar yanda shi ma babu abinda yace, she still can’t believe Husnah ce ta koma haka…. Tana ganin ya dau hanyar gidansu ta daga kai ta kallesa, a kofar gida yayi parking ta sauka ta shiga gidan ba tare da ta jira sa ba, tana shiga parlor ta kalli Nihal dake zaune parlor tana welcoming dinta da fara’a, Nihad bata wani saurareta ba tace “Umma fa?” Nihal tace “Bata nan” Nihal ta taso tana kallonta tace “Kin ga yanda kika yi wani fresh kika kara haske sis, amma kin rame, mu je ki gaida Mumy” Daga haka ta ja ta zuwa bangaren Mumy, Nihad dai gabanta sai faduwa yake don yau kuma bata san me Mumy xata ce mata ba, ga mamakinta da ta gaida Mumy sai taga ta amsa mata normal normal, cikin sanyin murya tace “Mumy ina su Sudais” Mumy tace “Sun tafi islamiyya ya gida?” Tace “Lafiya lau” Mumy tace “Ina Ibrahim din?” A hankali Nihad tace “Yana kofar gida” Mumy tace “Ohk” Nihad ta daga kai ta kalli Mumy dake kallonta, tace “Mumy su sudais basu ta6a zuwa wurina ba” Mumy tace “Za su je in sha Allah” Nihal dake zaune parlon ta mike ta fita, Mumy na kallon Nihad tace “Kin shiga kin gaida Abbanki ne, yana parlonsa” Nihad ta girgiza kai tace “Aa” Mumy tace “Toh in za ku fita ki shiga ki gaishesa” Nihad dai ta sunkuyar da kanta bata ce komai ba, bayan few seconds a hankali Mumy tace “Ina sake tunatar maki ki rike mijin ki, ki bi sa, ki masa biyayya, ki zauna lafiya da shi, farin cikinsa ya zama naki, bakin cikinsa ma ya zama naki, a yanzu baki da wani gata a duniya sama da shi, shi ne gatanki Nihad, kar ki yarda ki bari baraka ya shiga tsakaninku har a ji kanku, Abbanki ba kallonki zai yi ba, tunda a haka kaddarar ki ta zo sai kiyi hakuri ki rungumi kaddararki sai Allah ya dubeki, in sha Allah ina da yakinin Ibrahim baxai cuceki ba, baxai bari kiyi kuka ba in har kika amshesa a matsayin mijin da Allah ya zaba maki a nan duniya” Nihad ta daga kanta hawaye na sauka idonta tana kallon mahaifiyarta, Mumy tace “Duk wani wanda zai zugaki kar ki zauna lafiya da shi ba sonki yake ba, makiyinki ne shi Nihad” Nihad ta gyada kai da kyar hawaye na bin kuncinta tace “Toh Mumy nagode” ita kanta Mumy daurewa kawai take, cike da karfin hali tace “Idan ma da wani abu zaki iya dinga amsar wayarsa ki kirani har zuwa lokacin da zai yarje maki rike waya, Allah ya maki albarka, Allah ya baku xaman lafiya me dorewa” Nan ma Nihad kai kawai ta gyada ma Mumy hawaye na sauka idonta, Sallama khalil yayi bakin kofar parlon, Mumy ta amsa ya shigo ciki, kallo daya yayi ma Nihad dake goge hawayen idonta ya zauna kasa ya gaida Mumy a hankali, ta amsa da fara’a tana tambayarsa gida, Mikewa Nihad tayi wasu hawayen na sauka idonta ta fita daga parlon ta koma main parlor, Nihal na ganinta ta mike tana kallonta har ta zauna kan kujera, Nihal ta karasa ta zauna kusa da ita a sanyaye ta jawota jikinta tace “Kiyi hakuri sis, nasan duk abinda Mumy ta gaya maki abu ne da zai taimakeki har karshen rayuwaki, i want to see u happy and lively once again as before plss sis” Nihad ta fashe da kuka sosai, Nihal ta rungumeta ita ma tana hawaye, Nihad tayi kukanta me isarta Nihal na rarrashinta, daga jajayen idonta tayi tana kallon Nihal da ita ma idonta yayi ja, cikin rawar murya tace “But kema ai kinsan abinda xanyi da wanda baxan yi ba ko Nihal? U know baxan taba yin wannan video din in bar shi a wayana, ba halina bane yin video haka” Tana fadin haka ta kara fashewa da sabon kuka, Nihal ta rungumeta a sanyaye tace “I know sis, ba halinki bane hakan, but we are hoping one day one time gaskiya zata bayyana, in sha Allah xaki yi dariya wataran, in sha Allah” Kai kawai Nihad ta gyada mata tana share hawayen da yaki tsaya mata, A hankali Nihal tace “Mu je parlon Abba ku gaisa, he is inside” Nihad dai tayi shiru, Nihal ta mike ta kamo hannunta suka nufi parlon Abba, Nihal ce tayi sallama bakin kofar parlon, ya amsa ta shiga ciki tana rike da hannun Nihad, tun da yaga Nihad ya hade rai sosai, Nihad dai ta kasa dago kanta, Nihal ta sa suka zauna kasa daga gefen Abba tana kallon Abban a sanyaye tace “Sister dita ce ta zo za ku gaisa Abba” Sai a sannan Nihad ta daga idanuwanta ta kalli Abba cikin rawan murya tace “Abba ina yini?” Abba ya mike yace “Wa ya kawo ki gidan nan” Cikin kuka tace “Tare muka zo da shi” Abba yace “Ba nace bana son in sake ganin kafarki a gidan nan ba, wato u want to dare me shi yasa kika zo right?” Nihad na kuka tace “Don Allah Abba kayi hakuri” A fusace Abba yace “Toh bari kiji, yau ya zama first and last day da zan sake ganin kafarki a gidana, bana bukatarki, bana bukatar ki kwata kwata, kije can kiyi rayuwarki amma wllh kar in sake ganin kafarki a gidan nan, idan kuwa ba haka ba duk abinda na maki You caused it for ur self, sannan ita ma uwarki xan dau mummunan mataki a kanta in har kika sake shigo min gida” Nihal ta fashe da kuka sosai tace “To nima Abba ka samar min wani wajen daban don in na koma makaranta babu abinda xai sake dawowa da ni gidan nan, why will u be so harsh on her kamar ita ta rubuta ma kanta ƙaddara, why are you doing all this to her Abba, so kake wani abun ya sameta, kar ka manta she neva bargained for all what is happening to her, me yasa baxa mu taya ta rungumar kaddararta ba ko zata samu sassauci a ranta? Me yasa zaka dinga korarta Abba??” da mamaki Abba yace “Ohk rashin kunya za ki min? Ni kike gaya ma wannan maganan??” Nihal ta mike tana kuka sosai ta dago Nihad suka fice daga parlon, Tsaye khalil da ya fito daga part din Mumy yayi yana kallonsu, nan saman kujera suka zauna suna kuka a tare, sai ga Abba ya fito parlon, Yana ganin khalil yace “A kan wani dalili ka kawota gidana? Ba nace maka ko da wasa bana son ganinta a gidana ba, don me zaka karya min umarnina?” Shi dai khalil bai iya yace komai ba sai kallon Abban yake, Strictly Abba yace “Toh yau ya xama rana ta karshe da zaka kawota gidan nan, kai ma ba sai ka zo ba kuyi zamanku a can kawai, wai ma ba cewa kayi zaku koma zaria ba? Me ya zaunar da ku har warhaka? To Gobe ka tattarata ku bar garin nan, bana kuma bukatar duk abinda zai sake dawowa da ita kano, gidan da kace ka samar maku da farko nasan akwai sauran kudin da na tura maka last week a account dinka kayi amfani da shi ka biya hayan gidan, sannan ka ajiye min makullin motata….” Shiru khalil yayi yana kallon Abba babu ko kiftawa, duk wannan abun Umma da dawowarta daga anguwa kenan tayi still bakin kofa ta kasa karasowa, Mumy ma da ta jiyo muryar Abba ta fito tana tsaye kofar parlornta, Abba ya kalli Nihad yana nuna mata kofa cikin tsawa yace “Tashi ki fita” Tashi Nihad tayi da sauri Nihal ta rikota cikin kuka sosai tace “But she have all right to stay Abba, u can’t just send her away because of a mistake she never bargained for her self, ba ita ta rubuto ma kanta kaddarar nan ba ai naga” muryar Umma suka ji tana cewa “Kul Nihal, kul…. Karen hauka ya cije ki ne kike ja’in ja da mahaifinki? Ashe ke mahaukaciya ce dabba ban sani ba? Are you stupid? Kaji min mahaukaciya shashashar yarinya, ko duniyar ce baki son gamawa da lafiya?” Nihal ta sake Nihad tana kuka sosai ta mike da gudu ta wuce dakinta ta dau waya ta kira Yaya farooq, Umma ta nufi Abba tace “Alhaji ka yayyafa ma zuciyarka ruwan sanyi kada wani abu yaje ya sameka don Allah” Cikin tsawa Abba yace “Su fitar min a parlor kawai” Umma ta kalli Nihad da damuwa tace “Tashi ki fita Nihad….” Sai kuma ta kalli khalil tace “Ka ajiye masa makullin motar ibrahim, ku je kawai kun ji” Mikewa Nihad tayi tana kuka sosai ta nufi kofa Khalil ya ajiye makullin motar dake hannunsa saman kujera ya bi bayanta har suka fita daga parlon, Juyawa Mumy tayi tana share hawayen dake ta zuba idonta ta koma bangarenta, Abba ya shige parlonsa a fusace Umma ta bi bayansa da damuwa. Har suka kai gate Nihad ta kasa daina kukan da take, tun da suka fito dama Aminu ke kallonsu, don duk wanda ke compound din nan ranan sai ya jiyo muryan Abba, Aminu dai ya sunkuyar da kai ya kasa cewa komai, a karo na farko ya ji tausayin rayuwar Nihad, xuciyarsa ya karaya sosai, Khalil ya dafa sa a hankali yace “Xa mu yi waya” Daga haka ya fita gate din Aminu dai ya bi su da kallo ya kasa cewa komai, har suka isa titi Nihad bata daina kukan da take ba.

 

Click Here To Read Nihaad Chapter 35 By Khaleesat Haiydar Complete Novel

☝🏻
*Day before yesterday’s update that some people are still waiting for!*

Settled!! so i will keep on updating yanda na saba from tomorrow.

 

Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah.

 

Back to top button