Halysaah Page 147 By Khaleesat Haydar
HALYSAAH PAGE 147…Da asuba Khaleesat na dakin Mami a kwance tana bacci, wanda sai kusan karfe hudu da rabi na asuba baccin ya dauketa bayan Mami ta bata pain reliever har sau biyu a daren, kana ganinta kasan ba bacci me dadi take ba cause she is restless gashi sai firgita take ita kadai, Ita kanta Mami bata yi bacci ba daren don da ta so ma su je asibiti amma tayi considering ko waje bazata iya fita ba sai dai a zo gida a dubata kuma har Dr dinta sai da ta kira a daren bata sameta a waya ba, duk da tasan Gimbiya Firdausi babban likita ce ita dai bata je ta masu magana ba tunda babu wanda ya zo da sunan duba Khaleesat banda Hajiya Habibah ita ma tasan zuwan kwakwaf ne ba wai don Allah ta zo ba don tana zuwa tambayar da ta fara yi shine wai taji gida ya dauka Halysaah budurwa ce, kuma daga bakin Hajja aka fara jin wannan labarin, sannan banda shiri aka yi ta yaya ihunta zai karade gidan duk girmansa in dai ba waje ta fito tayi ihun ba sannan ta koma ciki, har da cewa su basu ma ji wani ihu ba kuma idonsu biyu a lokacin, Mami dai bata kulata ba, ta karaci maganganunta dake nuni da cewa babu wanda ya yarda da batun a gidan sannan ta fita… Mami na ta zaune kan darduma tayi nisa tunanin da take hannunta rike da carbi Hajja ta shigo dakin da sallama, Mami ta gaidata da ladabi, Hajja tace “Ya ba a kai ta can bangaren nawa ba bayan nace ayi Aseeyah?” Mami tace “Ai ko banda labari Hajja” Hajja tace “Kilishi na gaya ma haka ai, bata gaya maki bane?” Mami tace “Wallahi bata sanar min ba, da yake da wuri ta bar bangaren Junaid din ta bar ni a can, to amma bari in tashi mu je can din Hajja” Mami ta fada haka ne ba wai don Khaleesat zata iya tashi ba, da yaya ma suka zo part din nata don sai da Mami ta tausaya mata sosai, kuma da taimakon Yakumbo suka dawo part din nata, ta rasa wani irin zuwa Junaid yayi mata anya ma yana cikin hankalinsa kuwa yaje mata, kuma tasan dai babu abinda yake sha balle tace, Hajja tayi shiru bata ce komai ba don tunaninta kawai Mami bata yi niyyar kai Khaleesat can bangaren nata bane, dama ga maganganun da ta zo ta tarar kwando kwando a gidan akan irin yanda Mami ta dau karan tsana da tsangwama ta dora ma Hadiyah bata amsa ko gaisuwarta a gidan sannan ta hanata zuwa sashinta, wanda jira take yau ayi zama da Sarki ta ji dalili sai ga kuma issue din Junaid da Khaleesat, dama abu biyu ya kawota masarautar, Dethroning din Ajay da aka yi sai kuma tsangwamar da aka ce mata Mami ta dauka ta dora ma Hadiyah, a takaice Hajja tace “A’a ki bar ta a nan din tunda haka kika so, ya jikin nata?” Mami tace “Hajja Kilishi bata sanar min kince a kai ta can sashin ki ba, kuma ki kirata ki tambayeta ki ji….” Hajja ta dakatar da ita tace “Cewa nayi ya jikin nata?” Mami ta sauke kai tace “Bata samu bacci ba, kuma jikinta yayi zafi sosai yanxu haka duk da nayi ta bata pain reliever so nake idan gari ya waye na kira likita ta dubata ko ba wata matsala, ko kuma mu tati asibitin” Hajja dai tayi shiru don alamu sun nuna ba da hankali Ajay ya je ma yarinyar ba, ko kuma gardama tayi masa, ta juya ta kalli Khaleesat warce kana kallonta zaka san she is in pain duk da bacci take, Hajja ta karasa har kusa da gadon Mami tana kallonta ta kai hannu goshinta taji kamar wuta, numfashi ma da kyar take saukewa, duk da bacci take kana iya ganin yanda idanuwanta suka kumbura saboda kuka and she look pale, lebbenta suka dawo pure pink gaba daya, Hajja ta sauke boyayyen ajiyar zuciya tace “Allah ya bata lafiya, amma naga ai Firdausi na gidan nan, me yasa baki mata magana ta shigo ta dubata ba?” Mami tayi shiru jin abinda Hajja tace, can kuma tace “To Hajja, bari ayi mata magana….” Mikewa tayi ta fita daga dakin, Hajja dai sai kallon Khaleesat take, can ta juya ta fita, bangaren Ajay ta tafi ta samesa kwance a parlonsa, ta karasa ciki tace “Kayi sallah kuwa Ahmad?” Sai da tayi tambayar taga darduma shimfide a parlon alamar yayi sallan, ganin yanayinsa ta cire abinda ya rufa da shi duk da bacci yake bai san ta shigo ba, nan ya fara sambatun da bata ma san me yake cewa ba idonsa a rufe yana kokarin juyawa tayi saurin cewa “Ahmad kar fa ka fado kasa, baka da lafiya ne?” Sai a sannan ya bude ido da kyar amma ya kasa barin idon a bude ya mayar kawai ya rufe, ta kai hannu forehead dinsa taji wani irin zafi don har yafi na Khaleesat zafi, she was quiet for some seconds tana ta kallonsa don ya bata tay sosai, sai kuma a hankali tace “Tashi ka shigaAhmad, me yasa baka kira kace baka da lafiya ba? Haka ka kwana da zazzabin nan me zafi?” Shi dai bai iya ya sake bude idonsa ba yana sauke numfashi a hankali, Hajja ta juya ta fita daga dakin ta tafi part din Jay, kwance ta samesa kan 3 seater shi kadai a parlon, ya juya jin an bude kofa, ganin ita ce ya dauke kansa, ta karaso ciki tace “Nayi tunanin ma ka koma bacci, Sarkin ‘yan bacci” Ya sauke idonsa a hankali ya gaisheta, ta amsa tace “Hadiyar bata tashi ba” Bai ce komai ba, Calmly tace “Jawwad ka tafi ka duba dan uwanka ba shi da lafiya sosai, daga can wajensa nake yanxu” Dai dai nan Hadiyah ta fito daga kitchen rike da cup din tea tana sanye da Kayan bacci, ganin Hajja cike da damuwa tace “Yauwa Hajja gwara kiyi masa magana kilan yaji naki a kira masa Doctor, bai fa yi bacci jiya ba bashi da lafiya kuma yaki barin in kira likita” Hajja tace “Subhanallahi, me ya samesa?” Hadiyah tace “To nima dai ban sani ba, he was running temperature and throwing up all through the night, ko masallaci bai iya yaje ba da aka yi sallah yanxu, he is just lying down here” Hajja dai tayi shiru tana ta kallon Jay, can ta karasa har inda yake kwance ta kai hannu goshinsa taji zafi kamar wuta, shi dai kallonta kawai yake, a hankali Hajja ta zauna kan kujera bata sake cewa komai ba. Da gayya Gimbiya Firdausi ta zo bangaren Mami tare da su Ummi, Hajiya A’isha har da Hajiya Sumayya wajen karfe bakwal da rabi na safe duk a sunan ta zo duba condition din Khaleesat bayan Mami ta a waya don Mami kin zuwa sashin da take tayi, dama tun jiya su Hajiya A’isha ke cewa Gimbiya Firdausi taje kawai tace zata duba Khaleesat don ita kadai ce zata tona asirin Junaid har ma dakomai ba sai plan da aka shirya na rainin wayo a masarautar, don kaf dinsu babu wanda yaji wani ihu, ita tasan inda ta tafi ta tsaya tayi ihun har Mami da Hajja suka jiyota tunda su ne Main target dinta dama, sai da suka jira ranan da Hajja ta sauka masarautar sannan za su aiwatar da shirinsu, Su Hajiya A’isha duk suka zauna parlon Mami ko dakin basu karasa ba, Aunty dake zaune kan kujera a parlon ta amsa gaisuwansu cike da kasaita, ita din ma kiri kiri daxu ta bi Mami har kitchen ta nuna mata wannan abun shiri ne kawai don babu bazawarar da ta taba komawa budurwa in ba raina ma mutane hankali Junaid zai yi ba, Mami dai bata tanka ta ba ta ci gaba da abinda take a lokacin, Gimbiya Firdausi kadai ta karasa har Bedroom din Mami ta shiga da sallama, Khaleesat na kwance don ko zama ta kasa yi, Mami dake zaune dakin tayi nisa tunanin da take, ga breakfast a gabanta ta kasa ci, ita ma duk ta dawo wani iri kamar tare suke jinyar da Khaleesat, Gimbiya Firdausi ta zauna kan kujera bayan sun gaisa da Mami tace “Sai fa an samo hand gloves, in kuma akwai to a bani….” Mami dai bata ce komai ba, don banda Hajja ce tace ayi ma Gimbiya Firdausin magana ita da kawai likitar dake dubata zata kira ta zo ta duba Khaleesat, can Mami tace “Sai a siyo, don bani da Hand gloves tunda ba aikin lafiya nake ba” Gimbiya Firdausi tace “Da aka san babu ai tanadinsa ya kamata ayi kaf a kirani, tunda dubata aka ce za ayi, hakan kuma ba mai yiwuwa bane babu gloves” Mami bata sake tankata ba, after a while ta dau wayarta ta fara kiran Mukhtar yaje ya siyo Hand gloves din…. Bayan Gimbiya Firdausi ta gama duba Khaleesat a dakin Mami ta fita ta koma can sashinta dake cikin gidan, nan ta tarar da su Hajiya A’isha zazzaune a parlor suna jiran dawowarta don tuntuni suka baro part din Mami bayan da Hajja ta shigo, tun da Gimbiya Firdausi ta shigo parlon su Ummi ke ta kallonta suna jiran jin Feedback, Kilishi ta kasa daurewa tace “Duk plan ne ko Aunty Gimbiyah? Naga duk ranki a bace da alama bata maki lokaci kawai aka yi gashi ko Breakfast baki yi ba” Gimbiya Firdausi ta zauna kan/kujera ta sauke wani ajiyar zuciyar takaici tace “To amma menene fa’idar cewa da aka yi yarinyar ta taba aure? Kuma naji an ce daga bakin iyayenta hakan ya fito, to guduwa tayi bayan an daura mata auren amma dai ko?” Duk su Ummi da Hajiya A’isha suka dinga kallon Gimbiya Firdausi babu wanda yace komai, Can Hajiya Habibah tace “Ikon Allah, a takaice dai yarinyar budurwar ce kenan dai Yaya Gimbiyah?” Gimbiya Firdausi tace “To sai ma an hada mata da dinki, yanda ku ka san mara hankali haka yaje mata….” Takaici yasa Kilishi ta kasa cewa komai ta wani rungume hannuwanta tana zaune ta cika one sitter sal sauke numfashi take da kyar tsabar kibarta, da wani expression Ummi tace “Budurwa ce dai kenan?” Hajiya Habibah tace “Kin ji wani zance Maimuna, abu kina ji ance sai an oa mata da stitches, duk yanda aka yi auren farko da aka yi mata shegiyar kin zama tayi ta gudu saboda ta kwallafa rai kan Jawwad, kilan ma shi zal ce ta tace Junaid take so, sai gashi ma za a amshe title din a hannun Jawwad din yau, kowa fa yana son mulkin nan ace ya dawo gidansa ko ta yaya, ita ma A’isha ina lura da take takenta so take ta cuso Iklima, Ita kanta shegiya Maimuna ji murnan da take da aka kwace ma Junaid Yarima aka ba mijin er ta, don haka gaskiya gwara mu canza tsari Aunty Gimbiya, in har Hajja ta birkice ma Sarki fa to dole zai maida ma Junaid Title dinsa” Gimbiyah Firdausi tayi kasa da murya tace “Ke yanxu ya kike ganin za ayi Kilishi?” Kilishi ta dawo kusa da ita cikin rada tace “Ba kince tana can ya farketa ba har dole sai anyi dinki?” Gimbiya tace “Dole kuwa sai anyi dinki” Kilishi tace “To yanxu an tafi siyo maki kayan aikin da zaki dinka ta din ne? Abinda zai faru kawai cusa scissors zaki yi a mahaifar ki katse sa in zai yiwu, wato dai kiyi damage din mahaifarta kawai Aunty Gimbiya yanda da bazai iya zama ciki ba, ko bazai yiwu ayi hakan ba?” Gimbiyah Firdausi ta zaro ido tace “In ma zai yiwu Kilishi a dakin Mamin zan yi wannan aika aikan matar da saboda bata yarda da kanta ba ko ina na bangarenta Cctv ne” Kilishi ta wani kalleta tace “Kai kin ji ki, wallahi ba wani Cctv a dakinta, Parlon ma saboda satan da Walid yayi mata kwanaki na gwala-gwalanta yasa ta saka Cctv din, amma ba komai dakinta, wallahi in wannan damar ta wuce mu shikenan mun shiga uku mun lalace, kinga in aka ga bata haihuy karin aure ya kama Junaid, to a nan za mu Shahuda ko Humaira” Gimbiyah Firdausi tace “To har Aseeyan ta kira likitan da za tayi aikin, yanxu haka can na barosu tare da likitan, balle ni ba mahaukaciya bace da zanyi wannan aika aikan a bangaren Aseeyah” Kilishi ta ciji yatsa tace “Kashhhh” shigowar Hajiya A’isha ne ya sa duk suka yi shiru, Kilishi tayi maza ta canza zancen. Wajen karfe uku na yamma Khaleesat na bangaren Hajja a dakin da Hajjan ta sa aka gyara mata aka shimfida mata lallausan zanin gado tun bayan da likitan Mami ta gama abinda zata yi mata ta tafi da safe, she felt a lot better akan yanda take ji daga daren jiya zuwa safiyan yau, duk da she is still in pain amma tana jin dama dama yanxu, kula na musamman Hajja ke bata making sure she is alright and needs nothing, haka ma Mami da every now and then take zuwa bangaren dubata, sai a yanxu Khaleesat ta fara jin kunyan da bata ji ba daren jiya, don ta kasa dinga hada ido da Mami ko Hajja, sai tayi ta sunkuyar da kai, kaf gidan babu wanda ya shigo side din Hajja da sunan ya zo dubata sai dai in tasa ta shigo da shi sai Hajja tace ya shiga yayi mata sannu a daki, Hajja na parlor Jay ya shigo kansa a kasa, Hajja dai sai kallonsa take ganin har ya fada zazzabin da yayi, ya zauna kusa da ita tayi kasa da murya tace “Ya jikin Jawwad?” Yace “Naji sauki” Tace “Amma ka kara shan magungunan da likitan ya baka kuwa?” Yace “Na sha” Hajja tace “To ka ci abincin da na aika maka?” Yace “Na ci” Hajja sake cewa komai ba tayi shiru tana kallonsa, tun daxu take son zuwa dubasa a side din nasa amma saboda bata son barin Khaleesat ita kadai gashi Mami ta fita vasa bata le bandaren nasa ba. hatta… dazu baki ta tabe as far as ta taba aure har ta fito kafin ta shigo gidan nan babu abinda zal goge wannan tag din Bazawarar a rayuwarta, ko mijinta na farko ya sadu da ita ko akasin haka to bazawara ce dai tunda ya saketa ta fito ta sake wani auren….” a fusace Kilishi tace “Atohh dai Momy, kema dai kya fada, tunda har tayi aure ta fito mu dai har abada a Bazawara za mu dinga kallonta babu ruwan mu da cewar ta zo gidan nan da budurcinta, da bakin iyayenta suka furta cewar Bazawara ce er su tunda su ma sun san gaskiya, in dai kayi aure ka fito to babu zancen wani Budurci ko da mijin bai sanka ba ka fito gidan” Hajiya Habibah ta wani tabe baki tace “Ga dai Hajja sai nanata cewa take jinin budurci ne kan gadon da yake dama babu wanda take so a gidan nan irin Junaid in ma ba gaskiya bane ita tuni ta nemi rufa ma shi da matar tasa asiri tun a daren jiya, sai wani farin ciki take uwa an mata albishir da aljanna, tayi sintiri bangaren Aseeyah yafi a kirga da safen nan, me yasa bata ma Hadiyah haka ba tunda dai ita ma a matsayin budurwa aka aurar da ita, anya kuwa??? ko da yake mu ma mun fi sati a gidan nan bayan tarewar Hadiyan amma bamu ga alamar komai ba wallahi, ko canjin taku…” Hajiya A’isha ta dinga ma Hajiya Habibah alamar tayi shiru ga Ummi zaune a wajen, tuni Hajiya Habibah ta ankare tayi maza ta canza zancen don shafff ta mance Ummi na parlon, Ummi na mata wani kallo tace “Anya me Yaya Habibah? Me kike nufi?” Hajiya Habibah ta buda hannuwa biyu uwa almajira ta langwabe kai tace “Anya kuwa ta dau Hadiyah da Jawwad yanda ta dau Junaid? Jawwad din da ta rasa mahaifinsa tun yana karami wallahi bata nuna masa soyayya yanda take ma Junaid dake da gatansa ba tunda ga Mai martaba a raye, ko zuwan nan da tayi ma na samu labari daga tushe me karfi ta zo ne don ta umarci Sarki da ya mayar ma Junaid Title dinsa na Yarima kar rai ya baci” Ummi dake ta kallon Hajiya Habibah babu ko kiftawa tace “A ina kika ji wannan magana Yaya Habibah?” Hajiya Habibah ta gyara zama tace “Kema dai Maimuna, kin fa san maganar cikin gidan nan bai boyuwa gaba daya barin ni da na jiyo hakan daga majiya me tushe, muna nan dake ba dai anjima ne zaman Meeting ba zaki ce Habibah ta fada, Hajja bata duba cewar idan aka bar ma Jawwad title din nan ba sarauta bazai taba barin lineage dinmu ba tunda Hadiyah dai dole ita zata haifi future king din Emirate din nan, kuma ita din jikar sarki ce uwarta er sarki, amma take so ta karfi da yaji ta mayar ma Junaid ta yanda buzaye za su amshe mana sarauta wataran muna ji muna gani, kan kace me gaba daya masarautar sai dai a ga jajayen buzaye na yawo maimakon Hausa Fulani” Mikewa Kilishi tayi fuuu ta wuce dakin Gimbiyah Firdausi, ta z kan kujera tana kallonta don shayi take bukata zata sha, Gimbiya Firdausi tace “Amma nayi mamaki ainun kasantuwar yarinyar nan budurwa Kilishi” Cikin bacin rai Kilishi tace “Yanxu Aunty….. tace kakar Khaleesat ce… Dai dai nan Nenne ta shigo parlon da sallama tana rataye da jakarta ta sha tsadadden lace da mayafi shi ma me tsada, kai baza kace ita ta haifi Malam Ali ba, bayanta kuma Aunty Murja ce ita ma ta yafa gyalen da Nenne ta ara mata me tsada akan sabuwar atamfar jikinta, Sai Noor da Aunty Murja ke rike da hannunta, da fara’a Hajja ta dinga masu sannu da zuwa tana kallonsu, Nenne ta tafi har gabanta ta zauna sannan ta mika mata hannu biyu cikin ladabi suka gaisa da Fara’a, Aunty Murja da ta zauna kasan carpet ta gaida Hajja cikin ladabi ita ma, Hajja na mata sannu da zuwa, Mami na kallon Noor da ta rakube jikin kujera tana wasa da kujeran bata zauna ba tayi mata murmushi tace “To zauna kan kujeran mana yan mata” Noor ta sunkuyar da kanta ta zauna kasan carpet, Hajja ta mika mata hannu tace “Taho nan ki zauna yarinya, ya sunanki?” Noor ta mike ta tafi kusa da Hajja tace “Ina yini” Hajja ta rungumota tana Kallonta da fara’a tace “Lafiya lau Baby girl, amma ke kanwar Jiddah ce ko, ga kama nan Maa sha Allah, ya sunanki?” Noor na wasa da fingers dinta tace “Sunana Noor” Nenne na murmushi tace “Fatima ce Ranki shi dade, shi ne ake kiranta Noor, tagwaye ne, dayar me suna Islam tana can ita bata iya nisa da uwar, duk kannen Khaleesat ne uwarsu daya ubansu daya” Hajja ta bude ido sosai tana kara kallon Noor da kamar an tsaga kara it Khaleesat tace “Maa sha Allah, takwarata c ashe, sannu da zuwa Noor, Allah Ubangiji ya maki albarka” Sai a sannan Jay ya gaida su Nenne, Nenne ta rike baki tace “Au, ai ban lura kai bane Ahamad, dama kai ne zaune?” Ya dan yi murmushi a hankali yace “Ya hanya Kaka?” Nenne tace “Ai kwananmu uku kenan a Bauchi amma sai yau Allah ya bani ikon zuwa, na zo duba mara lafiya shi ne nace bara dai in zo mu gaggaisa a gurguje in koma, ashe da rabon zan hadu da Hajiya ne tana gari” Tuni masu aikin dake part din Hajja suka taho da ruwa da lemo sai fresh masu yawa aka ajiye ma su Nenne…….




