*🌈MIJIN MALAMA🌈*
Nimcyluv Sarauta
*9……*
Yadda suka ɗaure Abraham a jikin sarƙa zaka ɗauka wani tantirin ɗan fashi ne ko kidnaper, ko irin mutanen nan masu muyagon harƙalloli. Suna zuwa suka cilla shi a mota tare da yiwa motar key.
“Ku daka ta” P.a Hammad ya faÉ—a yana Æ™ara sawa inda suke ya dubi Abraham wanda kansa yake sunkuye jini ya É“ata masa fuska.
“Mene matsayina?” Kai tsaye Captain ya ce “Kai P.a ne a wajan His Excellency” Hammad ya jinjina kai ya ce “Good, kamar matsayin P.a ya fi na mataimakin Gwamna, idan ya tabbata haka ne la shakka zaku bi nawa umarnin” suka kalli juna
cikin kuma rashin fahimta Captain ya ce
“Me kake buÆ™ata?”
Ya ce “Ku kai Abraham gidana, ya zama sirri ni da ku kada ku kuskura akai shi Prison idan ba haka ba, ku ne zaku tabbata a can har Æ™arshen rayuwa”
“Cin amana?” “Shi ma ita ya yi” cewar Hammad. Captain ya ce “I can’t, dole mu kaisa prison kamar yadda ya umarta”
“Nawa ya baku?”
“Mu ai ma’aikatan gwamnati ne, wannan shi ne aikinmu” Hammad ya yi murmushi mai kyau kafin ya ce “Mu ne Gwamnati ai, baka san inda rana zata faÉ—i ba gobe” “Kowa ya san ta yamma take faÉ—uwa” Captain ya tari numfashin Hammad da faÉ—in hakan.
“Zan baka 10Ms, zan faÉ—a maka yadda za kayi” ya yi shiru alamar tunani kafin ya ce “Sauran securities É—in fa?” Hammad ya watsa hannu ya ce “ÆŠauke shi, lokacin ya fara” Captain ya dubi abokan aikin nasa, ganin sun yi nesa da su hakan ya tabbatar ba su ji abinda suke tattaunawa ba. Tunaninsa ya rabo gida biyu shin ya amshi kuÉ—in? Idan ya amsa kuma ya ci amanar Gwamnansa, da Æ™asar shi da kuma aikinsa. Amma miliyan Goma ai ba nan ba ce, babu wanda kuma zai sani.
Ya shiga motar, sauran securities ɗin ma haka kai tsaye suka fita daga cikin keɓantaccen gidan na His Excellency Abu-turab.
Also Download Banana Island Book 1 Hot Romantic Hausa Novel Complete Document
Hammad ya yi murmushi a fili ya ce “Kaci amnar maci amana kamar babu laifi? Ba zan jure ganin hakan ba, am sorry Best friend”
Abu-turab ya na tsaye da hannunsa wanda aka karya ya dubi Majeederh dake zaune tayi shiru ta sanya hannunta tsakanin cinyoyinta hakan na nufin tunaninta ya girmama har ya kasa É—aukan Æ™waÆ™walwarta. Abu biyu ya fi tsaya mata, kalaman mahaifinta Abbu, da kuma kalmar Abraham “I am the who raped her” hakan na nufin Abraham yaga surarta na É—iya mace? Ya gama kallonta. Ta rutse idanu tana kiran sunan ALLAH. Yaron cikinta? ÆŠan data raina? Ya yi mata FyaÉ—e? Ya samar da cikin Khalil, ta ya ya hakan ya faru? Rabonta da shi shekara biyu, shin ciki yana shekara biyu ne? Ya akai har ya yi mata FyaÉ—e bata sani ba? Yaushe hakan ta faru.
“Jiddo” Abu-turab ya kirata a ruÉ—e ganin yadda jikinta ke rawa kamar wacce take shirin yin jijjiga. “Ka da ki sawa kan ki damuwa wani ciwon ya kama ki, don Allah Jiddo listen to me ki bani dama, ki bani dama just one chance, please Jiddo Give me one chance”
Ta É—ago kai a nutse ta faÉ—aÉ—a kyakkyawar fuskarta speaking calmly ta ce “Your Excellency”
“Yes, Jiddo”
“Don Allah ka bani waje” ta faÉ—a murya can Æ™asa idanunta na lumshewa.
Ya jinjina kai ya ce
“Zan fita,idan zaki farin ciki” yana faÉ—in haka ya yi waje yana zuwa wajan Æ™ofa ya juya ya kalleta sai kawai ya fice yana rufe Æ™ofar bedroom É—in. Yana fita ta zame Æ™asan lallausan carpet na É—akin, zuciyarta tayi mata zafi Æ™irjinta na É—agawa sama. Tsoron t É—aya kada bakin mahaifinta ya kamata ya sanya ta lalace kum ta bi duniya kamar yadda kalamansa suka bayyana haka, mene ya sa ya kasa yarda da ita ya kasa fahimtar ba zata taÉ“a aikata zina ba, ya kasa amincewa Æ™addara ce ta faÉ—a mata.
Kuka take son yi ku zuciyarta za tayi mata sanyi amma ta kasa sai ma wani abu daya tsaya mata a ƙasan maƙoshi da ƙyar take jan numfashi. A raunace ta ɗaga kai sama ta ce
Also Download Dr Eeshatt Romantic Hausa Novel Complete Document
“Allah na gode maka, Allah na gode maka da wannan jarrabawa, yadda kayo ni a Musulma mai yadda da Æ™addara Ubangiji ka sanya na cinye wannan Æ™addarar, zuciyata ta kasa jurewa Allah kai kasan abinda yake É“oye Ubangiji idan rayuwata a wannan duniyar shi ne alheri ka tabbatar dani a raye ka bani haÆ™urin jure Æ™alubalen cikinta, idan mutuwata ita ce hutu a gareni Ya Allah ka É—auki raina a wannan lokacin, ka yafe mini kurakuraina ka kula mini da abinda na haifa” Ta rufe idanu tana Æ™anÆ™ame jikinta tana jan numfashi da Æ™yar ta ce
“Asstagafirullah Ya Allah, Asstagafirullah, Asstagafirullah Ubangiji kana kallo,kana ji, kana gani albarkacin imanin da nayi da kai, albarkacin kare addininka da nayi, Ya Allah ka bani haÆ™uri kwatankwacin haÆ™urin da Annabi LuÉ— ya yi da mutanensa, ka bani ikon jure yanayin rayuwa kwatankwacin juriyar da Annabi Yusuf ya yi, Allah ka bani Æ™arfin zuciya wacce zan fuskanci ko wanne Æ™alubale, kwatankwacin Yadda ka bawa Annabi Sulaiman Æ™arfi ikon, Allah ka kula dani kwatankwacin kulawar daka bawa Annabi Musa a cikin gidan Fir’auna… Ya Allah Asstagafirullah!”
Jira take taga ta inda mutuwarta zata fara, amma shiru hakan na nufin rayuwata ita ce alheri a gareta.
Abu-turab na zaune Æ™asan carpet ya sanya Mama a gaba hannunsa naÉ—e da bandeji cikin kulawa ta ce “Abu-turab me ka ke so?”
“Majeederh nake so Mama” ta ce “Nemi Soyayyarta idan ta amince ba zan hana ba”
Ya yi shiru ta ce “Idan baka da abun faÉ—a jeka, ka sani a gaba” ya kalleta ya ce “Kamar ba zata amince ba” Mama ta dube shi sosai tana duba yanayinsa ta ce
“Idan har baka sanya son zuciya cikin lamarinka ba babu shakka zata amince, ka yarda da kan ka shi ne kawai” tana kallon T.v ta ce
Karanta>>>Â Matsi Ga Sabbin Amare Kafin Kije Gidan Miji.
“fight for the truth, fight for your love, idan har ka faÉ—a mata wahalar daka sha akanta Majeederh zata ji tausayinka, sai dai bana son ta aureka don jin tausayi sai don cewa tana Son ka”
“Tausayi yana zama so”
“Inji ku Hausa ba, babban kuskuren da kuke kenan, gurbin tausayi daban na So daban go and search”
“Mama please ki….,”
Cikin faÉ—a ta ce “Abu-turab ba zan tilasta Æ´ar mutane ba, fita ka bani waje” ya miÆ™e jiki a sanyaye yabar bedroom É—in, Jidda na nufar inda yake ya daka mata tsawa. Mama ta ce “Na gode Allah tunda Æ´arka ce” yarinyar ta fashe da kuka sosai da gudu kuma ta nufi bedroom É—in Majeederh ta sameta zaune inda take..
“Mami” Majeederh ta zubawa yarinyar idanu sai ta É—an saki fuska ta ce “Call me Jidda”
“Dady ya ce Mami” Majeederh ta jingina da bed ta kallon yarinyar sosai tayi kama da mahaifinta. Jidda ta ce
“Ina son Daddy, kema kina son shi?” Majeederh shiru ba amsa ta Æ™ara cewa “Zaki zama Mamina?” Sai a lokacin ta ce “Ai ni Mamin kowa ce come here”
Barrister na zaune looking so worries ya Æ™ara ramewa ya yi baÆ™i kamar ba kyakkyawan matashin nan ba mai jini a jika. “Aliyu Meke damunka?” Ya dubi Hajia ya ce “Me kika gani Hajia?” Ta haÉ—e rai sosai ta ce “Why are you asking my question with a question?”
“ÆŠan Najeriya ne fa?” Almustapha ya bada amsa yana hararar Bar Aliyu Sufyan Alhassan. “Lafiya nake” “Æ™arya ka ke, na san halinka dole da abinda yake damunka” Aliyu ya rasa me zai ce, ya faÉ—awa mahaifiyarsa damuwarsa tamkar ya tona sirrin aurensa ne, kuma zata tsani Matarsa Latifa Omar, amma seriously yana cikin damuwa ya mance when last da ya yi mu’amalar aure da Latifa, ya manta rabon da ya ji Æ™amshin girkinta kullum abinci da Æ™auri ya manta rabon da yag kitso a kanta, ya mance rabon da ya ji kalmar adawo lafiya daga bakinta. Yana buÆ™atar kasance da matarsa haÆ™urinsa ya fara gazawa.
Ya riƙe kansa, da mutuncinsa sbd gudun faɗawa halaka, amma irin su Latifa sune suke sanya maza neman mata da aikata zina.
“Ni banga abinda ka rasa a gidanka ba, amma ka sanya wa kanka damuwa akan wata Æ´ar iska haba Aliyu” Barrister ya kalli Almustapha ya ce
“Mai É—aki ai shi yasan inda yake masa yoyo, ba zan hana ka aibata Majeederh ba amma ba kowa ake halinsa ba” Almustapha ya kalli Aliyu sai kawai ya miÆ™e tsaye. A tare suka fice daga cikin gidan nasu, Bar Aliyu ya yi Lodge Road wanda dalilin Majeederh ya kama haya a unhwhaty, shi ma Almustapha ya nufi hanyar gidansa. Maimoon na zaune ita da Æ™awarta wacce suke neighbor da ita.
Karanta>>>Â Ga Masu Neman Karin Kiba Ga Hanyar Da Zaku Bi
“Maimoon kin ji daÉ—i, Allah ya baki miji wanda yake wada taki da komai na rayuwa” Maimoon tayi dry sosai ta ce “Allah sarki, wallahi bani da matsala da mijina saÉ“ani bai taÉ“a haÉ—ani da shi ba, yana da haÆ™uri sauÆ™in kai, sometimes na fisa rikici ma, gaskiya samun miji kamar Almustapha da wahala, yana da kare hakÆ™in aure da nasa, kullum cikin kyautatawa iyalansa yake” Maryam tayi murmushi ta ce
“To Allah ya bamu irin taki” “Haba ya bawa Æ´an gaba dai, ke kina É—akin mijinki ai ki ce kawai Allahamdulillah,kin san duk wani kwanciyar hankalin aure shi samun daidaito tsakanin ma’aurata, yarda da juna, haÆ™uri, tausayi. Ni kam i trust my husband” Shira suka ci gaba da yi. Suna zaune Maimoon ta ji anyi horn ta miÆ™e da sauri ta ce “To ga É—an halak nan” Maryam ta ce “A’a zama bai ganni ba, lemme have my way” sukai dry kana sukai sallama.
Maryam na fita compound na gidan Almustapha na fitowa ya dinga kallonta domin bai taÉ“a ganinta ba. Ya shafa kai lokacin da take cewa “Sannu da zuwa”
“Thank you, can i know you?” Ta ce “Matar maÆ™ocinka ce Habib”
“Oh, you’re too beautiful” Mamaki ya kama Maryam sai tayi É—an murmushi ta ce “Harna kai Matarka Maimoon?” Ya yi murmushi yana kashe mata idanu guda ya ce “Haba waccar Dabbar?” Maryam ta zare ido ta ce “Innalillahi wa’inna ilahir raji’un Matarka ka ke kira da Dabba?” Ya watsa hannu ya ce “Yes, Kinga bani number ki please” Number ta bashi ta shige tana KaÉ—a masa jiki, ji ya yi kamar ya bi bayanta domin ya tabbatar mijinta baya gari.
Cikin dare Abu-turab na zaune ya samu sanarwar gaggawa an samu motar jami’an tsaron shi a wani gefen hanya, gabaÉ—aya jami’an sun mutu guda É—aya ya yi saura Captain shi ma yana gadon asibiti. Misalin 2 na dare Uncle Isma’il na harabar gidansa yana duba jaridar ranar inda yake ganin cewa Governor yana asibitin Cameron domin duba lafiyar shi, kamar yadda aka samu sanarwar ta bakin mai kula da lafiyarsa. Ji ya yi an tsaya gabansa ya miÆ™e da sauri da Æ™arfi ya ce “Abraham innalillahi,mene ya sameka…
MIJIN MALAMA
Book1 500
Book2 500
Mutum zai iya biyan book1 kafin a fara book2… Idan kuma yana da hali zai iya biyan 1k É—in bakiÉ—aya. 08119237616 kuyi magana ta nan.