Tun bayan ficewar jarumi Nuhu Abdullahi da yake amsa sunan Mahmud a cikin shirin, to sai fa shirin ya fara walan keluwa.
Shirin na labarina yana cikin wannan walankeluwarne kuma kwatsam sai itama mai gayya mai aiki wato jaruma Nafisat Abdullahi da take amsa sunan Sumayya a shirin ta bayyana ficewarta daga cikin shirin.
Bidiyon Sadiya Haruna Tana Taki Rawa Tabar Kasida Ta Koma Bin Safara’u Da 442
Matsayin da Na ba Mahaifina na Gida, Shi na bai Wa Adam Zango – Jaruma Tumba Gwaska
Kalli video Yadda Jarumin Adam A Zango Yake koyawa ‘Yarsa Waka
Yadda Rayuwar Jaruman Hauwa Waraka Ta Koma Bayan Daina Saka Ta Film
Masha Allah: Bidiyon Hafsat Idris (Barauniya) A Gidan Aureta
Haƙika ficewar Nafisat Abdullahi ba karamin nakasta fim ɗin yayi ba domin itace asali kuma gundarin labarin wanda dole sai da ita sannan fim ɗin zai ta fi yadda ake so.
Ga Cikakken Bidiyon dalilin da ya sa👇👇
Duk da cewa director Malam Aminu Saira da kuma marubucin shirin Nura Ngwangwazo sunyi ƙoƙarin riƙe masu kallo amman hakan bai hana jama’a fahimtar cewa Mashiryin shirin na labarina sun samu matsala da jaruman shirin ba.
Bayan sun samu da kyar an kammala shirin na labarina kashi Na 4 da kyar wanda gaba ɗaya bai yi wani armashi ba saboda tsaya a waje ɗaya da aka yi, duk a dalilin saɓanin da Mashiryin hirin ya samu da jaruman.
To kwatsam kuma bayan share kusan wata biyar ba tare da jin ɗuriyar shirin ba, sai kuma akaga wata sanarwa daga daraktan hirin wato Malam Aminu Saira inda ya wallafa kamar haka:
SANARWA! SANARWA!ASSALAMU ALAIKUM WA RAHMATULLAH 🙏Muna Sanar da Ma’abota Kallon Wannan Shirin #LABARINA series cewa In sha Allah Zamu cigaba da daukar Season 5&6 . Muna kuma Sa ran Fara Haska muku shi a wata mai kamawa (JULY 2022) in sha Allah. Muna baku hakurin akan dogon Jira da kukai, muna Godiya ga ƙyaunar ku Gare mu 🙏 Allah yabar Zumunci 🙌❤️🌎 @sairamoviestv #LABARINA 5&6