Uncategorized

Wasu manyan litattafan ilimi da ya kamata ku mallake su.

Wasu manyan litattafan ilimi da ya kamata ku mallake su, Quran app download, arba’una Hadith, Hisnul Muslim Apps,

Assalamu alaikum yan uwa barkanmu da wannan lokacin ya kuke ya hakurin kasancewa tare damu..

Ganin yadda manyan wayoyin hannu na Smartphone suka yawaita a hannun mutane yasa na yanke shawarar kawo wa mutane wasu Application da zasu taimakemu duniya da lahira domin wannan wayoyin da suke hannun mu idan mun so ta sanadiyyar ta zamu iya yin aikin alhairi wanda Allah zai saka mu a Aljanna, sannan zamu iya yin aikin assha wanda sanadiyyar haka Allah Ya azabtar da mu muna rokon Allah Ya kiyashemu da bin wannan tafarki. Kada na tsawaitaku da zance ga dai Application ɗin da naso maku wanda ina da yakinin insha Allahu zamu Amfana da su duniya da lahira.

Na daya

                 Quran Application Download! 

Alqura’ani littafi ne mai tsarki daya kamata kowanne musulmi ace ya mallake shi koda a cikin wayarsa ne wanda zai dinga karantawa koda sau daya ne a rana, a matsayimu na musulmi bai kamata ace rana ta fito har ta fadi ba kuma ba tare da mun ware wani lokaci domin karatu ba.

Domin sauke shi cikin wayoyinku sai ku taɓa alamar Download!

Na biyu 

    Hisnul Muslim App,  Download! 

Hisnul Muslim shima wani littafi ne na addu’a da aka mayar dashi ya zama Application domin musulmai su mallaka kuma suji saukin amfani dashi, a ciki akwai dukkan addu’o’i da Annabi Sallallahu Alaihi Wassalam ya koyar sannan ya umarcemu da dinga yi a ko wane lokaci.

Domin sauke Application ɗin cikin wayar ko sai ku taɓa Download!


Na Uku

          Tajweed Quran App,  Download!

Shima wannan littafi ne da aka mayar dashi Application, wanda zai baku damar karanta AlQura’ani daidai da kuma sanin ka’idoji na karatun Alqura’ani mai girma.

Domin Sauke shi sai ku danna inda aka saka Download!

Na Hudu

   

         Arba’una Hadith App, Download! 

Ga duk wani musulmi yasan wannan littafi na Arba’una Hadith domin kuwa ya shahara. Shima an mayar da shi Application domin saukaka wa yan uwa musulmai.

Domin sauke Application din zuwa wayoyinku na hannu sai ku danna inda aka saka Download!

Wadannan litattafan zasu taimaka sosai a rayuwarmu dama gobe kiyama.

Back to top button