Mijin Marigayiya Page 31 Hausa Novel
Yayi ‘yar dariya yace ‘Na zata zaki fi son wadannan dakunan na kasa ai, kin ga sun fi girma. Kuma ai ina ga zai fi min privacy ace dakinki yana nan kasa a madadin yana kusa da nawa idan kin yi baki ina jiyoku.’Tayi dariya tace ‘Haba dai, kuma don nice duk fadin gidan nan sai na rasa wajen sauke baki sai bedroom? Ai dama sama ba wajen saukan baki bane tunda nan kasan ma da parlor. Amma dai can ne dakina, in ya so idan ma baka so yaran su hau sama za a iya barinsu a kasa.’Shukra tace ‘Gaskiya Abba mune a sama mu da Anti, in ya so ita Anti N…’Kafin ta karasa Afaf ta katseta cikin daga murya tana cewa ‘To baki ji me Abban yace ba, kasan ya fi girma ne da space.’Khadeeja tace ‘To mu dai ba ma son kasa, muna sama abin mu.’ Ta ja hannun Shukra suka haye saman.Habib wanda yake tsaye a kusa da Abban nasu ya dubeshi yace ‘Haba Abba, dama ai sama na Anti Khadija ne.’ Kallon da Abban yayi masa ya sa ya kawar da idonsa da sauri ya waske yana cewa ‘Bari naje na tayasu zabn dakin.’Haka ya hakura shima ya bisu saman inda khadeeja ta nuna masa dakin da yake jikin nasa tace shi take so, dayan kuma wanda yake gefe daya sai a barwa yara. Bashi da wata hujja da zai bata a kan hanata daukan dakin sama, kuma har yanzu baya jin ya shirya gaya mata cewa zai kara aure, ya fi so sai ta haihu tukunna saboda kada ma yaji tausayinta idan tace zata tayar masa da hankali. Haka suka gama zagayensu a cikin gidan sannan suka shiga mota suka nufi BUK don su kaita.Har suka isa makarantar bata daina mamakin Mustapha ba; ta kasa gane sai yaushe zai daina yi mata wannan karyar. Kuma ta kasa gane dalilin da yasa yake fifita bukatar Naja da son zuciyarta a kan tata, amma dai haka zata cigaba da biye masa ta ga gudun ruwansa.………Kwanansu biyu da gama jarrabawa Khadeeja ta haifi yaronta, don haka ko kwana bata yi a asibiti ba aka wuce da ita gidanta. Sai daga baya aka kawo mata Anti Binta wadda kanwa ce a wajen Mommy. Tun a asibiti Mustapha ya sanar da su ya sakawa yaro suna Muhammad; sunan Baffan Khadeeja. Daga baya Nabila tayi masa lakabi da Hammad.Nan da nan aka shiga hada-hadar shirya bikin suna; kuma alokacin Mustapha ya sanar da ita idan an yi suna da sati biyu zasu koma sabon gida.Ranar kwana biyu da haihuwa Mustapha ya sameta a dakinta da daddare, tana zaune a gefen gado da baby a cinyarta tana kallosa tana murmushi. Ya ajiye shopping bag din dake hannunsa sannan ya zauna akusa da ita ya shafa kan baby yace ‘Shikenan kuma kin mayar min da yaro abun kallo kamar wata TV ko?’Tayi ‘yar dariya tace ‘To ina laifi, ina yaba halittar Allah ne.’Ya matsar da ledar kusa da ita yana cewa ‘Ga wannan ‘yan office dinmu ne suka bayar a kawowa Baby.’Ta karba ta dan buda ta leka sannan ta mayar ta ajiye tana cewa ‘Mun gode, Allah ya saka da alkhairi. Ai dole Muhammad ya kawo tukuici tunda an yi masa takwara.’Yayi dariya. ‘Wannan ma ba na Muhammad bane, sauran ma’aikatna ne dai. Shi yace sai gobe zasu zo da matarsa.’‘Allah sarki mun gode, Allah ya bar zumunci.’Suka dan taba hira sannan ya fita.Yana fita ta dauki ledar ta zazzage kayan; rigunan Baby ne masu kyau da tsada guda biyu, sai set din kayan sanyi guda daya, set din huluna da kuma sar din kayan wasa. Ta tabe baki ta mayar da kayan cikin ledar, jikinta ya bata wannan kayan Naja ce ta bayar don haka ko burgeta basu yi ba. Rawar kan da yake yi da ya shigo da kayan kadai ta isa ta sa ta san cewa daga wajen Naja kayan suka fito. Ta tsani yarinyar gaba daya ta tsani ta tuna ta, bata ko son jin sunanta. Haka ta ajiye kayan da niyyar da zarar an gaya mata haihuwa itama zata yi barka da su.Lafiya kalau aka gama taron suna; musamman da yake Khadeeja ta kawar da kanta daga abubuwa da yawa. Domin hatta abincin sunan Yaya Jidda cewa tayi ya basu zasu yiwo su zo dashi, shi kuma ya hau kai ya zauna. Tunda taga haka ta gayawa Mommy kada su yiwo gayya da yawa, sannan baffa ya basu kudi suka shirya nasu abincin wanda suka taho da shi. Ko da Yaya Jidda ta gansu da kulolin abincinsu sai ta soke duk wani wulakanci da ta shirya yi musu, haka aka gama taro kowa ya watse lafiya.Bayan kwana biyu tana kwance a dakinta tana hutawa da daddare wayar Mustaphe ta shigo; ta riga ta san yana cikin gidan don haka ta san kiranta yake yi. Haka yake yi tunda Anti Binta tazo; baya shiga dakinta sai dai yayi mata waya ita ta sameshi a dakinsa. Ba tare da bata lokaci ba ta mike ta nufi dakin.Ta karasa ta zauna a gefen guda kusa da shi tace ‘Gani.’‘To sannunki da zuwa.’ Ya fada yana bin idonta da kallo yana kokarin karanto yanayinta.Tayi murmushi tace ‘Godiya nake, a bani abinda aka kawo min.’Suka hada ido na dan lokaci, ya dauke nashi idon ya dan cije lebe sannan yace ‘Ya shirin tashi, saura kwana biyar fa.’‘Ai ni na gama shiri, makota ma duk na gama sallama da su. Sai mun tare zan yi musu kwatance su zo ganin gida.’‘To da kyau.’Suka yi shiru na dan lokaci; ita tana sauraronsa don ta kula da magana a bakinsa yayinda shi kuma yake ta sake tauna maganar bakin nasa yana tunanin ta inda zai fara. Ya kalleta suka hada ido yayi gajeran murmushi, itama ta mayar masa da murmushin. Cikin sanyin murya yace ‘Um ki yi hakuri ki saurareni kuma ki fahimci maganar da zan gaya miki.’Ta kalleshi na dan lokaci da mamaki a fuskarta tace ‘In sha Allah.’Ya sake gyaran murya sannan yace ‘Um Khadeeja aure zanyi, don maganar da nake miki ma saura sati biyu a daura auren. Idan mun tare a sabon gida da sati daya itama zata tare.’Suka hada ido, tayi murmushi sosai sannan ta zare hannunta daga nashi tana cewa ‘Allah sarki, abun ya zo kenan. Toh Allah ya sanya alkhairi.Bude baki yayi yana kallonta saboda tsabar mamakin yanda ta nuna halin ko in kula da maganr tasa kamar dai wadda yake cewa gobe litinin a ranar lahadi. Ta mike zata fice ya rike hannunta yana cewa ‘Um wani abun kike yi ne kike saurin tashi.’Ta koma ta zauna tana cewa ‘A’a, na zata ka gama maganar da zaka fada din.’Ya dan sunkuyar da kai saboda gaba daya ya kasa hada ido da ita, wannan halin ko in kula din da ta nuna yasa duk ya firgice; gaba daya ta goge masa haddar kalaman da ya tsaro don ya bata hakuri. Cikin sanyin murya yace ‘Um baki ma tambayi wacece wadda zan aura ba.’Ta dan yi dariya tace ‘Oh, Naja ce mana. Ko ka fasa auren nata ne?’A jigace ya amsa ‘Itace.’Ta daga gira cikin halin ko in kula tana shirin mikewa tace ‘Allah ya sanya alkhairi.’‘Um, wai dama kin san zan yi auren ne ko naga kamar kin sani tun tuni.’Tayi ‘yar dariya ta koma ta zauna tace ‘Na sani mana, ko bai kamata na sani ba?’Ya jiijiga kai ‘No, ina dai mamaki ne.’Suka yi shiru na dan lokaci.‘To don Allah wa ya gaya miki?’ Muryarsa ta katse mata tunani yana tambaya. Tayi ‘yar dariya tace ‘Oh, ka san fa na dauka kai ka gaya min; ashe ba kai bane. Ina jin dai a cikin wadanda ka gayawa ne kace kada su gaya min aka sami wani ya gaya min.’ Ya sunkuyar da kai domin ya kasa hada ido da ita; wato duk wannan tsawon lokacin ashe kallonshi kawai takeyi duk abinda yake boyewa ta sani. Ba karamin mamaki yayi ba. Kafin yace wani abu suka jiyo kukan Hammad daga cikin gidan, don haka ta dubeshi tace ‘ka ji yarona can yana kuka, bari naje na gani…
