Hausa novels

Mijin Marigayiya Page 16 Hausa Novel

Tun bayan dawowar Khadeeja gidan sau daya Baffanta ya shiga dakin Mommy ya sameta yayi mata sannu.Yana zaune a parlor bayan ya dawo daga sallar tarawih Mommy ta shiga ta sameshi, ta zauna a gefensa suna kallon labarai a tashar Aljazeera tare. Bayan sun dan taba hira yace ‘Dazu Mustapha ya kirawoni yana duba Khadeeja, ya ma ce min idan an bude gari ranar asabar zai zo su tafi.’Ta dan gyara zama ‘Ranar asabar fa kwana uku kenan, haba ai sai ta kwana arba’in.’‘A’ah to ai ni na zata sun gama magana da ita ne a kan hakan.’Ta jijjiga kai tace ‘Gaskiya dai basu yi wata magana ba don da kanta tace min tana so tayi arba’in din. Suna zuwa da na sa ruwan zafi nayi mata wanka ta ji dadin jikinta da kanta tace a barta tayi arba’in din. Haba, kuma haka za a mayar da ita haihuwar fari babu wani gyara? Sai kace ‘yar tsana.’‘To ai naga bari ne ba haihuwa ba.’‘To ai Baffan Nabila bari ya fi haihuwa wahala sosai ma, sannan kuma na fari ne haka za a bashi matar ya ma kasa daga mata a kwana arba’in din.’‘To naga dai ai matarsa ce ko? Ina laifi, kuma ma ai shima ba zai ce bai san wadannan hukunce-hukuncen ba tunda ga yara nan har hudu an haifa masa.’Ta sake gyara zama ‘Ku dai yi hakuri Baffa a barta tayi kwana arba’in ko akalla talatin, kafin nan ta ji daidai a jikinta sai ta koma.’Ya daga wayarsa ya cigaba da dubawa yana cew a’To ai shikenan idan ya zo sai kuyi masa bayani, ni bani da matsala da hakan.’‘Yauwa, ai lalacewar zamanin ba ta kai an daina wanka da gyara a haihuwar fari ba. Amma dai idan ya zo sai kayi masa bayanin idana kana nan tunda ka ga kai ya nema, gara ku cigaba da magana man to man.’Yayi dariya yace ‘To babu laifi.’Ya san halin matarsa da kishi, yanzu haka haushi taji shi Mustaphan bai kirawota ya duba Khadeejan ba ko akalla ya gaya mata zai tafi da Khadeeja ranar asabar tunda ya san iatace zata shirya Khadeejan amman ya kirawo Baffa. Jimawa kadan kuma fice ta bashi waje.______Shi da yara suka zauna suka gama shan ruwan sanna ya sa Afaf ta kwashe kwanukan, nan suka zauna suka cigaba da kallo suna wasannisu.Har lokacin kwanciyar bacci babu wanda ya bashi matsala a yaran.Ya tasa su a gaba ya raka su dakinsu domin suyi shirin bacci; yana shiga dakin zarni ya doki hancinsa. Ya dubi Afaf yace ‘Ba naga Ummi ta fitar da katifun nan ba? Me yasa suke zarni?’‘Ta fitar Abba, sai da yamma sannan ta shigo da su gaba daya. Ban sani ba ko katifar Habib ce bata bushe ba don bamu san anyi fitsari ba sai wajen la’asar sanna ya gaya mata Shukra tayi masa fitsari bayan asuba da ka kwantar da ita. Shine aka shanya, to ina jin itace bata gama bushewa ba.’Ya karewa dakin kallo, ko shimfida ba ayi ba a kan gadon don haka ya sa Afaf ta yi musu shimfida yayinda shi kuma ya wuce dasu bandaki don suyi brush. Nan da nan kowa ya shirya bayan sun fito sun kwanta ya cewa Afaf ‘Wai sai yaushe katifun nan zasu daina zarni ne?’‘Nima ban sani ba Abba, kuma fa idan baka saka su sunyi fitsari da daddare ba haka gobe ma zasu sake yin fitsarin nan fa. Dama Anti ce kullum take tashinsu, Nasreen sau daya ita kuma Shukra sau biyu shi yasa basa yi a kwancen.’‘To karfe nawa take tashinsu?’‘Wallahi Abba nima ban sani ba, kawai dai tana tashinsu.’Ya amsa sannan ya fito ya dawo parlo ya zauna; to shi yanzu ya za ayi ya san karef nawa zai saka su wani fitsari, gashi kuma ga dukkan alamu idan ya barsu suka cigaba da fitsarin nan a kwance to lallai gidan zai daina zaunuwa. To amma karfe nawa zai saka su? Watakila sai dai kawai idan ya tashi kwanciya bacci ya saka su shikenan.Nan ya zauna a parlor din ya cigaba da kallonsa yana chatting, har ya sami Khadeejan ma online suka dan yi hira.Basu fi awa daya da kwanciya ba ya jiyo kukan Shukra daga dakin, da sauri ya dire wayar da take hannunsa ya nufi dakin. Tana zaune a kan gadon tana ta faman kuka harda hawaye. Ya karasa ya zauna a kusa da ita yana cewa ‘Menene Shukra?‘Kashi zan yi.’‘To ai ba sai kinyi kuka ba Shukra, sauko muje na saka ki a toilet.’Ya sauketa daga kan gadon ya ja hannunta suka wuce bandaki, suna shiga ya cire mata wando ya fara kokarin daurata a kan toilet ta dafe duwawu tana juyi tana cewa ‘Ina Fo na Abba a shi zanyi.’Cikin muryar lallashi yace ‘To ai ba ganshi ba ki yi hakuri ki hau toilet.’ ‘Muje ka duba bandakin Anti fo dina yana nan Abba a shi zan yi kashin.’Ya dauketa gaba daya ya dora a kan toilet yana cewa ‘To ki gama kashin kada ya fito in ya so idan kika gama sai muje mu dubo fo din.’Kafin ya rufe bakinsa ta zame ta sauka daga kan fo din, tana kuka. Ta cigaba da bubbuga duwawunta tana shirin ficewa daga bandkin tana cewa ‘Fo na yana bandakin Anti bari na daukoa shi zan yi kashin.’Cike da tsananin mamaki da takaici yake kallonta, ga dukkan alamu kashin ya matseta amma ita bata da niyyar zama a toilet din nan so take dole sai ya dauko mata fo; fo din da ya riga ya jefar ba tare da kowa ya sani ba. Ya kai hannu ya damkota tana shirin ficewa daga bandakin, ya mayar da ita kan toilet din ya zaunar da ita yana cewa ‘Anti ta kulle dakinta ta tafi da mukullinta sai ta dawo zata bude mana, kiyi kashin a nan.’Ta sake direwa ta sauka daga kan toilet din tana buga duwawu harda juyi saboda yanda kashin ya matseta tana cewa ‘Ka zo na nuna maka Abba bata rufe ba, a bude dakin yake dazu nma na shiga.’Kafin yayi wani abu kashin ya kwace mata, dan kadan ya fado ya zame daga duwawunta ya bata tsawon kafarta sanna ya dire a kasan toilet din. Yayi wuf ya dauketa ya daka mata tsawa yana cewa ‘Ki zauna a nan kiyi kashin nace, kalli yanda kika bata jikinki kika bata toilet din da kashi.’Ta sake fashewa da kuka tana yi tana shessheka, takaici ya sa ko magana ba zai iya yi mata ba don haka ya kyaleta kawai yana tsaye tana rungume da kafarsa yana jira ta gama. Ko minti daya bata yi ba tace masa ta gama kashin, ya leka toilet din shi bai ga komai ba. Yace ‘Idan fa kika yi min kashi a wando zaneki zan yi Shukra gara ki gama kashin nan a nan.’‘Na gama.’Ya dauketa cak ya ajiyeta a wajen wanka, ya dauki sprayer din yin tsarki ya fesa mata ruwan da karfi ta yanda ruwan ya wanke kashin jikinta, sannan ya sabi sabulu ya wanke mata da hannunsa. Ya dauketa ya fitar da ita ya shiryata ya kwantar da ita sannan ya koma bandakin; ya tsaya daga bakin kofa ya karewa bandakin kallo. Ga guntun kashin da ta jefar a kasa sannan gashi duk ta shafe na jikinta a jikin toilet din bandakin har ya fara wari. Ya yi tsaki ya juya ya fice, jimaw kadan ya dawo dauke da tissue paper, ya warware kusan rabinta sannan yayi amfani da ita ya dauke guntun kashin jefe a toilet din. Sannan ya sake warwarowa ya goge toilet din yayi flushin sannan ya fito ya dawo parlor ya zauna cike da takaici da gajiya.A nan a parlor din bacci ya kwasheshi, watakila saboda tsabar gajiya domin bacci yayi mai nauyi sosai. Maganar Shukra ce ta farkar da shi wadda taje tashinsa tana sanar da shi zata sha shayi. Ya tashi zaune yana mittsike ido, ya lalubi waya ya duba lokaci; karfe ukun dare saura. Haka ya tashi ya hado mata shayin ya zo ya bata ta shanye sannan ya ja hannunta suka koma dakin. A nan ya tarar ita da Nasreen duk sun riga sun yi fitsarinsu a kwance; ya canzawa Shukra kaya ya lallaba ya kwantar da ita a gefen da bai jike ba kusa da Afaf. Ya dan tsaya ya karewa dakin kallo, sai kuma ya juya ya fice.Gaba daya kansa ya kulle; wai dama haka yaran nan suke ko kuwa don sun ga mahaifiyarsu bata nan ne kuma Khadeeja bata nan suka saka shi a gaba suka hanashi sakat, domin wasu abubuwan da suke yi ma kamar da gayya musamman Shukra.Har zai zauna a parlor din kuma ya tuna sai ya dafa abinda zai yi sahur don haka y wuce kitchen, ya janyo indomie ya debo park uku sannan ya nemi tukunya ya dora; Afaf da Habib sun yita fushi a kan jiya bai tashe su sahur ba don haka yau idan ya gama dafa abincin sai ya tashesu. Nan da nan ya dafa idomie din ya zubawa kowa a plate ya dora a dining table sannan ya hadawa kansa shayi. Bayan ya gama ya wuce dakinsu, ya kunna fitila sannan ya karasa ya tashi Afaf, ta zauna a kan gadon tana mittsike ido sanna ya wuce ciki ya tashi Habib.Yana juyawa ya bude ido yace ‘Abba asuba tayi ne?’‘No da saura, sahur zamuyi tukunna ga indomie can na dafa.’ Ya bashi amsa.Ya gyara kwanciya yana janyo abun rufarsa yana cewa ‘Ni ba zan yi azumi ba Abba, sai gobe.’ Ya rufe ido ya cigaba da baccinsa ba tare da ya sake bi ta kan Abban nasa ba.Afaf wadda take zaune a bakin gadonsu ta juyo tace ‘Abba wai sahur zamu yi.’‘Eh.’‘To Abba ai jiya ne ya kamata muyi azumi kuma baka tashemu ba, nima dai gaskiya yau ba zan yi azumin ba sai gobe. Dama haka mukeyi da Anti; muyi daya mu sha daya.’ Ta fada cikin halin ko in kula.Bata ma tsaya ta saurari amsarshi ba ta koma ta kwanta ta rufe ido.Nan ya tsaya yana kallonsu cike da mamaki; wai su yaran nan me yake damunsu ne? yanzu zasu ce zasu yi abu kafin wani lokaci sun canza ra’ayi. Gaskiya ya jinjinawa mata, ai idan ba mace ba babu wanda zai iya raino; jiya fa Afaf fushi tayi da shi saboda bai tasjeta ba amma yau kuma ita yake tashi tana ce masa wai yau bai kamata tayi azumi ba.Yana fitowa daga dakin ya hada indomie din ya juye a tukunyar ya rufe ya ajiye musu a kan idan gari ya waye sa ci abincin safe, sannan ya dawo ya karasa sahur dinsa.………Kamar yanda suka saba yau din ma da tunasuba suka tasheshi a kan yunwa suke ji, haka ya shiga kitchen Afaf ta taimaka masa ya hadawa kowa cereal domin duk sunce ba zasu ci indomie ba don tayi sanyimkuma basa son dumame, da ya takura musu ma sai Nasree cewa tayi ‘Abba kai fa idan ka dafa indomie bata dadi, ka bari idan Anti ta dawo ta koya maka.’Don haka kawai sai ya mayar da indomie din ya rufe.………Tun wajen goma na safe yake sa ran shigowar Ummi don ya riga ya gaya mata yau ma tazo, sai dai ga mamakinsa har wajen sha daya saura bata shigo ba; gashi har na fara yi masa korafin yunwa kuma ana bashi warning ba za aci indomie ba sai da taliya ko macaroni. Yana shirin fita ya je gidan su Ummin aka buga gate; kanwarta ce wadda suke kira Nana, wadda bata fi shekaru bakwai ba.Bayan ta gaisheshi tace ‘baba yace na gaya maka Ummi ba zata sami zuwa wajen su Afaf ba yau don ta tashi da mura me zafi tana kwance, yace sai dai ko zuwa gobe idan ta sami sauki zata shigo.’Jiki a sanyaye ya amsa ‘To, kice ina mata sannu kuma kice ina gaida Baban.’

Back to top button