Page 66
Jin shirun ya yi yawa, sai da ta yi zaton, ko wayar ya katse, ta sake ɗaga kanta, ta ce “Ina wuni yaya umar?”.
Wata ɓoyayyiyar ajiyar zuciya ya sauke, ya ce “Lafiya ƙalau, ya mutan gidan?”.
Cikin jin daɗi ta ce “Suna nan lafiya, ya mama da su Yaya Aliyu”
“Lafiya ƙalau, na ga message ɗin wannan Yarinyar ne, na mijinta ba shi da lafiya”. Yayi maganar yana sake fatan iman ta ɗago kanta ya kalleta, ko ya cigaba da jin nutsuwa a zuciyarsa.
Ba tare da ta ɗago ɗin ba ta ce “Eh, ba shi da lafiya, su na gida ita da shi”.
“Za su koma gidansu yau ne, ko su na nan?”
“Wallahi yaya ban sani ba, amma dai ba na tunanin su koma yau, bari na kai mata wayar, yanzun nan ta tashi”.
“No ƙyaleta, idan ta dawo ki ce mu na yi masa sannu, Allah ya bashi lafiya, a gaida sabir”.
Murmushi ta yi ta ɗan ɗago ta ce “To in sha Allah zan gaya musu, mun gode sosai”.
“Zan shigo zuwa an jima, sai na duba shi”.
“To yaya umar, Allah ya kawo ka lafiya”
Ji yake tamkar kar ya katse wayar, wata irin narkewa zuciyarsa take yi, da jin iya muryarta kawai. Mussman idan ta kira shi da yaya umar, ji yake tamkar ta fi kowa iya faɗar sunan.
Kamar wanda aka yi wa dole, haka ya kaste kiran wayar, ya lumshe idonsa ya na haki, ya na gazgata zuciyarsa da babu tantama wannan shi ne so.
Girgiza kansa ya yi ya ce “Ya salam, why? Why? Abun da ban taɓa yi ba, ni ko shirin aure ba ni da shi, ina zaman zamana meya aikeni” ya tambayi kansa. Gashi Abubakar ne abokin hirar sa, Abubakar baya nan, kuma duk da haka ma, ya san idan ya gaya masa dariya zai ta yi masa, abun da ba ya so, dan haka yake jin, zai iya jure koma menene.
A ƙasan zuciyarsa ya ji kamar dama ce, da zai yi amfani da zuwa duba Adam, ko zai samu ya ga iman.
Rumaisa kuwa, takawa ya ga reaction ɗin ta, ta ƙarasa wurinsa ta ce masa “Wai dama ka tashi, ina ammin?”.
“Ta fita ita da Nusaiba” ya bata amsa.
Ta je ta zauna a kusa da shi, ta ce “To meyasa baka ce a kirawo ni ka tashi ba?”
“To yanzu ba ga shi kin zo na tashi ba”.
“Ammi zan mutu, ki zuba mini ruwan sanyi, idan mutuwa ce hutu a gareni Allah ya sa na mutu, to ba in da za ka mutu ka tafi, sai na gama makaranta mai lilo” ta yi maganar farko tana kwaikwayon sa.
Murmushi ya yi, da sai da haƙoransa suka bayyana, ya ce “Rashin lafiyar ta wa ce, ta zama abun tsokana kuma”.
“Wane irin wulaƙanci ne, ina magana da ɗan uwana zaki zo ki zauna ki na wasu surutan banza?”
Rumaisa ta kalli Samha ta ce “Au dama ɗan uwanku ne? To ni kuma ƙarewar ƴan uwantaka gidansa a kai ni na zauna, ke meyasa ba a kai ki ba? Me ɗan uwa?”
“Shut up” yayi maganar yana matse mata baki.
“To ina ruwanta da ni, ba bu kyau wata ta kula mijin wata ba?” Kallonta kawai yake yi.
“To ina ruwana. ka ci abinci ne?”
Ya numfasa ya ce”Ammi ta bani, tun da tafiyarki ki ka yi, ki ka barni”.
Ɗan shiru samha ta yi, abun da take gani yanzu, ya sha ban-ban da wanda baba uwani take gaya mata, ƙarya take yi mata kenan ko kuwa? Ta ce mata ba sa wani jituwa, amma alamu sun nuna mata, kamar shaƙuwa a tsakanin su, babban tashin hankalin ta da fatanta, Allah ya sa wani abu bai taɓa faruwa tsakanin su ba, ta kuma fuskanci rumaisan tantiriyar fitsararriya ce.
Ruma ta ce “To yanzu ya ka ke ji, da sauƙi jikin?”
“Eh, Alhamdilillah”
“To sannu, ka tashi mu tafi gida”
Adam ya ce “Mu je gida ki yi yaya da ni, ba iya jinyata za ki yi ba”
Miƙewa Samha ta yi, ta fice zuciyarta na zafi, a gabanta adam ya sakarwa wannan shegiyar yarinyar baki, wata banza da ita mara aji, balle mamora.
“Kuma duk mai kula mijin wata, ɗan wuta ne, kuma sai ya daina magana” ta yi maganar cikin ɗaga murya.
Samha ba ta ko juyo ba, ta yi gaba tana ƙwafa, ba dan Adam ya auri rumaisa ba, da duk hakan ba ta faru ba, ta ɗora zargin komai a kan sa, kuma ya kasa tsawatar mata.
Samha na fita, ya rungumo rumaisa jikinsa, tare da kwantar da kansa a jikin na ta.
“Innalillahi wa Innalillahi raji’un, meye haka kuma, dan Allah ka cikani”
Bai ce uffan ba, ya ƙara lafewa, yana sauke numfashi.
Shiru ta yi, ba ta kuma ko motsawa ba, ta na jin bugun zuciyarsa a jikinta.
“Ita ma haka ka yi mata ko?”
“Ita wa?”
“Wannan matar da ta fita yanzu”.
“Eh, tun da ba kya jin magana, ba zaki saita bakinki ba, idan ta zaneki shikenan” ya sake rungumeta sosai.
Cikin tsoro ta ce “Ba kyau fa”
Yayi ƴar guntuwar dariya, yanzu abubuwanta sun daina bashi haushi, akwai wayo wasu lokutan, wasu lokutan kuwa kanta a kwano yake, gashi dai ta fara girma, amma kamar ba mutum ba, har mamaki take bashi”.
Ya kalleta ya ce “Wani alƙawarin ki ka yi wa fulani?”
Ta numfasa ta ce “Ba yanzu zan faɗa ba. Kuma gaskiya ka ɗagani, ka yi mini nauyi, na ji da matsar hannun da ka din ga yi mini ɗazu, ƙasusuwana sai ciwo suke yi”.
Bai ɗagata ba, ya kwanta sosai a kan cinyarta, ya lumshe idanunsa.
***
A fusace Jamil yake sosai, ya dubi Jabir ya ce “Jabir, har ni wannan Yarinyar za ta yi wa fitsara, wai ba son fulani muke ba, kenan adam zuwa ya yi yana ɓata mu a wurinta, abun da ya wuce ba ya riga ya wuce ba? Shikenan ba ni da zarafin bincike a kan ƴar uwata, ni da a tunanina, na lallaɓata na samu wani abun daga bakinta, yadda ka san na harbeta na huta, ka ga iskancin da ta din ga yi mini?”
Jabir ya ce “Wai kai da na gaya maka halinta baka yadda ba? Kai ka ga zaryar da jami’an tsaro suka din ga yi tana asibiti, amma ta ƙi magana, sai da aka kai ruwa rana, sannan ta yi”.
“Ni anya ba fulanin ce ta gaya mata wani abun ba?”
Jabir ya ce “Ba tabbas, ka san halin Aisha bana tunanin ita ce, bari dai a yi sallar magariba, zan shiga na duba shi”
“Ka dai yi a hankali, ciwon nan nasa ne, ya tashi, ka san kuma shaƙe mutane yake yi”.
Jabir yayi murmushi bai kuma cewa komai ba.
Tamkar mai comedy, haka rumaisa take ta zuba, tana yi wa Adam shirme samfur -samfur.
Can kuma ta ce “Tashi, in ɗauko maka filo, cimyata ta gaji, zan kuma je kitchen in yi girki”.
Gyara kwanciyarsa ya yi ya ce “Ina jin releif a haka, ba zan tashi ba”
“Gaskiya cinyata ta gaji, duk jikina ya yi tsami”.
“Mimi”
“Na’am basarake”
“Meyasa ki ka faɗi maganar ɗazu?”
Ta ɗan yi jimm, sannan ta ce “Wacce?”.
“A kan Mummy, kar ki sake makamanciyar wannan maganar,Idan maganar ta koma kunnenta fa? Zaki iya haddasa rigima, babu ruwanki da irin wannan abubuwan kin ji ko?”.
Ta numfasa ta ce “Waye zai je ya gaya mata, ni fa ba ƙarya nake yi ba, wata mata na gani tare da ita, gaba ɗaya ba kalar mutane ba, kuma da za ta tafi ta tashi ta bita k…..”
Ya katseta ta hanyar cewa “Wannan matar tun ina da shekara bakwai a duniya nake ganinta, take azabtar da ni, ko ta ɗaure ni tamau da sarƙa, ko ta din ga dukana da sarƙar, na yi mamaki da ka ce ki na ganinta, ban taɓa gaya wa kowa ina ganin ta ba. Rumaisa wannan shi ne ainihin adam, kin ga abun da na din ga yi jiya, kamar mahaukaci, dan ma na daina duka da cizo kamar maye, zaki iya cigaba da zama da ni a haka, abokiyar gaba?”
Ga tausayi ya bata, amma hakan bai hanata yin dariya ba, ta ce “I tuntuni na sani, baba uwani ce ta gaya mini, idan ranka ya ɓaci ka na komawa kamar mahaukaci, har yaya Abubakar aka gayawa, kan ka aureni, wai kai maye ne. Sanan ban manta ba, kuma ina nan a kan baka na. Ai sai yanzu na gane ka na da ɗan kirki kaɗan, kar ka mutu sai na gama makaranta mai lilo”
Shiru ya yi jikinsa a sanyaye “Ba ki damu da ni ba sai lilo ko?”.
“Kai fa ka gama addu’a ka mutu, kana mutuwa zan koma gida, idan na ƙara girma na auri Yaya Mahmud” ƙuri ya yi mata da ido, sai kuma ya tashi daga kan cinyarta ya koma kan gado ya kwanta.
Ita kuwa madigar ko a jikinta ta yi nata wuri, dama ba ta son zaman wuri ɗaya.
Abun da ya tsaye masa a rai bai wuce, yadda rumaisa ta ce Baba uwani ce ta gaya mata, ya na komawa kamar mahaukaci ba, sai ya ji kimar dattijuwar ta ragu a idonsa, sai kuma abun da rumaisa ta faɗa na ƙarshe bai yi masa daɗi ba.
***
Tamkar ya janyo dare, haka yake ji, ƙasan zuciyarsa ya na fatan idan ya je gidan ya ga Iman.
Iman ma sai kaiwa take ta na komowa, ta na fatan Allah ya sa mai sunan baba ya zo.
Ammi kuwa da ta dawo, zuwa ta yi aka yi wa adam tofi, wurin malamin da take sawa ya na yi masa, ta karɓo masa, sai dai ta bar shi ya ɗan farfaɗo har da fara’a ta dawo ta tarar da shi sai a hankali.
Sai ta yi zaton kawai jikin ne.
Haka nan iman ta tsinci kanta da yin kwalliya cikin doguwar riga, har ammi ta na tsokanarta, ko siriki za ta kawo mata.
Ta na nan zaune a falo, ta na danna waya, Sabir sai wasan sa yake yi a tsakar falon, gefe rumaisa ta na cin abinci, dan ba ta kuma komawa wurin takawa ba.
Jabir ne ya yi sallama, duk suka amsa masa, ya shigo cikin fara’a, “Autar Ammi da sirikar Ammi, Barkanmu da wannan lokaci”
Ba yabo ba fallasa, Iman ta amsa masa, rumaisa kuwa ta share shi.
“Ina takawan yake ne?” Iman ta nuna masa sashin Ammi, ya ɗan tsaya ya kalli Iman ya ce “Bari in shiga in fito, zamu yi magana dear, kin yi kyau masha Allah”
Iman ta yi masa shiru, rumaisa kuwa ta kwaɓe baki.
Ya na shiga ciki, message ya shigo wayar iman “Na zo” message ɗin mai sunan baba.
Da sauri ta tashi ta yi waje, a harabar gidan ta tarar da mai sunan baba, a cikin ƙanan kaya yake, amma yayi kyau sosai da sosai.
Sai da ta furta Masha Allah, a hankali.
Unexpectedly ya ɗaga kai ya ga Iman, cikin zazzaƙar muryarta ta ce “Sannu da zuwa yaya umar”.
“Yauwwa sannunki” daga nan ta yi masa jagora, har ciki.
Ruma na ganinsa, ta tashi ta din ga tsalle ta na murna, amma ya basar da ita ya ɗauki Sabir, da ya rarrafo wurinsa da gudu.
“Mai sunan baba, ba ka yi murna da ka ganni ba?” Kawai yayi mata murmushi, ya na sake rungume Sabir.
Ko da suka shiga sashin Ammi, Jabir na ganin mai sunan baba ya haɗe rai, ya yin da takawa mamaki ne ya kama shi da ya ga mai sunan baba.
Suka gaisa da Ammi, yake gaya mata rumaisa ce ta ce masa magidanta ba lafiya, ya zo ya duba shi kan ya sanar da mama, dan za ta iya tayar da hankalinta.
Ammi ta ce “Ruma ce ita ma da abun ta, ai ya warware, dan Allah kar ka gaya mata hankalinta ya tashi, ya ji sauƙi.
Mutumin da ya zo dubiya, bai fi mintuna goma ya yi ba, kuma daga takawan har jabir bayan sallama da ya yi musu, babu wanda ya sake kulawa, ya yi wa ammi sallama.
Kayan ciye-ciyen ya ba wa sabir, sai dai sabir ya ƙi yarda ya ajiye shi ya maƙalƙale shi.
Ya fita da shi a kafaɗarsa ya na murmushi, murmushin ba ƙaramin kyau ya yi masa ba.
Jabir ne ya biyo bayan sa, ganin Iman ma ta bi bayan mai sunan baba.
Ya ɗan kalleta sannan ya ce wa Sabir “Ka je wurin antynka, ko da kai zan tafi babana?”
Iman ta yi murmushi ta ce “Baban mai sunan baba”
Murmushi ya yi, ya miƙa mata sabir da yake ta ihu, ya na sake miƙawa umar hannu.
“Ke iman zo ki wuce, ina son magana da ke, na gaya miki tun ɗazu amma kin yi banza da ni, ki ka bi wani” Jabir ya yi maganar cikin umarnin da iman ta ji ya yarfata.
“Amma uncle J, ai gani na yi ka na wurin takawa ne, shiyasa”.
“Shut up malama” yayi maganar cikin fushi da kishi.
“Meye haka? Yayana ne fa, me ta yi maka?” rumaisa ta yi maganar tana harar Jabir.
Magana yake son sake yi, amma mai sunan baba ya ƙura masa ido. Sai kuma ya yi shiru, ya ji ya kasa sake magana.
Rai a ɓace ta wuce, ba ƙaramin haushi ta ji ba, dan tuni ta fara kuka.
Ruma ta ce “Mai sunan baba, bari na raka ka”
“No, ki je ki kula da mijinki, zan ce ki na gaishe su” ya juya ya fice, wani irin takaici ne ya kama mai sunan baba, ba ƙaramin haushi ya ji ba, abun da jabir ya yi wa Iman, kuma ya lura da yadda yake shishshige mata tun lokacin bikin rumaisa, tabbas ba dan a gidansu yake ba, zai nuna wa jabir, ba a shiga shirgin sa”
A harabar gidan mai sunan baba suka haɗu da Mahmud, Mahmud ya yi masa magana, mai sunan baba ya tsaya suka yi musabaha, sai dai ya yi ta kallonsa, ya na tunanin yanzu ya baro Adam a ciki, kuma dai ya san ba shiga sabgar juna suke yi ba.
Mahmud ya ce “Ba Adam ba ne, mahmud ne, amma ka na da alaƙa da rumaisa ko?”.
Mai sunan baba ya jinjina masa kai ya ce “Eh ƙanwata ce”.
“Kamannin na gani ai, sunana Mahmud”
Mai sunan baba ya ce “Babban suna, ni kuma umar”
Mahmud ya ce “Masha Allah, ka gaida gida, a gaida mama, duk ina jin sunanku a bakin ƴa ta, bari na zo na sauke ka a hanya, fita zan yi” Umar ya jinjina kai, dan gaba ɗaya ya ji Mahmud ya burge shi, mussaman yadda ya yi masa magana kamar sun saba.
A ɗaki rumaisa ta tarar da iman, ta na kuka.
Ruma ta ce “Gaskiya kin ba da ni, wai shi waye Jabir ɗin nan ne? Ya san waye mai sunan baba kuwa? Ke ma kin wani zauna ki na yi masa kuka, ni ma ina da saurin kuka amma kin ga ina yi? Meyasa ba a yi wa Nusaiba abun da ake yi miki?”.
Iman ta share hawayen ta, Sabir sai jijjiga iman yake yana cewa Iman, dan ya iya sunanta raɗau, kamar shi ya raɗa mata.
Ruma ta ce “Gidanku, Anty zaka ce ko Mummy”
Iman ta yi murmushi ta ce “Anty Nusaiba ta su ce, kuma ta na da bakin da idan aka yi mata za ta rama, ni bana son tashin hankali ne, baki ga komai ba ma, dan su Fauziyya sun daina zuwa ne, baki ga abun da suke yi mini ba”.
Ruma ta ce “Wallahi ko a kan bola aka haifeni, ba zan yadda da wulaƙanci ba, amma cika mini alƙawarina. Meyasa papa ba sa shiri da daddyna, meyasa kuma ba ya shiri da ammi, Meyasa ki ke cewa kan ki, ƴar tsintuwa?”.
Iman ta ɗan yi shiru, sannan ta numfasa, a dai-dai lokacin da wani hawayen yake zubo mata.
***
ASALIN LABARI…..
1972 Kano state emirate palace, a zamanin sarki Adamu Abdullahi.
Masarautar kano na ɗaya daga cikin manyan masarautu, da ake ji da su a Nigeria, ba iya Nigeria ba hatta turawan mulkin mallaka, suna ji da wannan masarauta.
Sarki Adamu Abdullahi, mutum ne mai adalci, karamci da kuma yakana, kuma jarumi, hakan ya sanya soyayyarsa a zukatan al’ummarsa.
Ya na da tarin dukiya, ƴaƴa, barori da sauran hadimai.
Yana da tarin ƴaƴa, daga matansa da kuma ƙwarƙwarorin sa.
A wannan lokacin, ya na kimanin ƴaƴa goma sha tara, maza da mata, a cikin mazan Allah ya jarrabe shi da ƙaunar ɗan sa Muhammad, da suke kira Sharif, tun ya na iya ɓoyewa har ya gaza, yake nuna masa soyayya muraran.
A lokacin turawa sun kawo harkar karatun boko, wanda a lokacin dama sun tarar da hausawa da karatunsu na allo da tsangayu.
Galibi ƴaƴan sarki a wannan lokacin, suna da sarautunsu, a lokacin da suke ƙallafa rai a kan sarauta, shi kuwa Sharif sam hankalinsa ba ya kan sarauta, ya fi karkata ga neman ilimi, na addini da kuma na zamani, da turawa ne suke koyar da su.
Sharif ya na da zafin zuciya, Mai marataba ne da mai babban ɗaki, wato kakarsa kawai ke iya sarrafa shi, kasancewar mahaifiyar sa ta bar duniya. A wurin mai babban ɗaki yake, sai kuma mahaifiyar Jafaru, wato turaki a yanzu, dan kamar uwa ya ɗauketa ita ma.
Bayan ya kammala karatun sakandare, turawa suka ba shi gurbin karatu a ƙasar Ingila, mai martaba ya ce bai san zance ba, babu mai raba shi da ɗan sa, Sharif ya ƙallafa rai a kan ya na son tafiya. Sai da mai babban ɗaki ta sanya baki, da wasu manya sannan ya amince.
Sai dai mai martaba ya na tsoron rayuwa cikin turawa, ga ƙanƙanin yaro kamar Sharif a wannan lokacin.
Bayan tafiyar sa, ya kammala degreensa na farko, a kan fannin tattalin arziki, ya ji daɗin zaman ƙasar waje, ba takura, babu kana tafe ana take maka baya, duk a hanaka sukuni da kaɗaici, a cewarsa.
Da ƙyar mai martaba ya saka aka dawo masa da Sharif, sai dai da ya dawo duk ya yasar da wasu al’adun, harkar gabansa ce kawai ta dame shi.
Ko zaman fada ba ya zuwa, idan ya shilla ya tafi na sa yawon, sai an ganshi.
Hakan ya fara damun mai martaba, ya fara tunanin yi wa Sharif sarauta, ko zai nutsu, sai dai ya na cikin yaransa ƙanana.
Sharif ya tsiri cewa zai tafi master’s gombe, nan ma sai da aka kai ruwa rana, mai martaba ya ce ya na da sharaɗi, abokin sa wazirin daura, ya bashi ƙanwar matarsa ya aura wa ɗaya daga cikin ƴaƴansa dan ƙarfafa zumunci, dan haka ya ce Sharif ne zai aure ta.
Sharif da fari ya ce “Shi ba ya son ta, daga baya saboda yana so karatu, ya amince, amma sai ya gama master’s ɗin sa, mai martaba ya ce bai yadda ba, lokacin ya yi tsayi, wazirin daura ya ce a saka shekara, ba damuwa kan nan ta ƙara girma ita ma.
Ko da Sharif ya tafi gombe, ya samu abokai ya cigaba da rayuwarsa, yadda yake so, duk da mai martaba ya na turowa, ana saka masa ido a kan sa, duk da akwai manyan mutane da suke bibiyar sharif, saboda karamci ga mahaifinsa.
Ɗalibai ba kowa ya san Sharif ba, yayi ta kashe musu kuɗi, suna bin sa, har sabon babur ya saya, yake yawonsa a garin gombe.
Ana haka yawo ya kai shi wani ɗan ƙaramin gari, nesa da cikin gari kaɗan, ya kusa buge wata yarinya, ya yi ta bata haƙuri, ya kafe babur ɗin sa ya rakata gida.
Tun da ya haɗu da yarinyar nan ya samu wurin zuwa, kusan kullum suna tare, ita kuma a lokacin yarinya ce sosai, yadda yake biye mata suna shirme, yake bin ta gona ya sanya ta saba da shi sosai.
Sunanta Bintu, ƴar wani babban malami ce a garin, shigaban manoma na wannan yankin, dan haka ya na da rufin asiri.
Babanta ya na ƙaunar fura da nono, akwai wata riga da take zuwa sayo masa, duk juma’a, a titi suke haɗuwa da Sharif, ya ɗauke ta a babur su tafi cikin rigar nan, Bintu ta saba da su sosai, bafulatanar da take sayen nonon a wurinta, ta mayar da bintu kamar ƴar ta, haka Sharif ma sun saba sosai, dan kakar bintu ma yake ce mata.
Kwatsam aka je aka gaya wa baban bintu abun da yake faruwa, ya din ga yi mata faɗa, aka hanata fita, hakan ya damu Sharif, ya kasa jurewa, ya bita har gida.
Yayyen Bintu suka kore shi, amma yaƙi tafiya, sai da ya haɗu da mahaifin Bintu, ya ce masa idan har son ta yake ya turo manyansa ayi magana.
Baban bintu yayi haka, dan ya kori sharif.
Sharif ya koma gida ya sakawa mai martaba rigima, shi fa baya son wannan jamilar, Bintu za a aura masa an ce ya tura iyayensa.
Mai martaba da fari ransa ya ɓaci, mai babban ɗaki ta taushe shi, ta ce dama ai so ake yayi auren, a fara aura masa bintun, sai ayi aurensa da Jamila, tun da dama shekara aka saka.
Matan mai martaba suka din ga ƙanan maganganu, suna cewa ya na biye wa yaro, kimar sa na zubewa.
Ya tashi tawaga daga Kano, aje a yi masa bincike a kan Bintu, idan ba su da wani aibu, a nema wa Sharif aurenta.
Mai martaba ya ji daɗin bayanin da ya samu, a kan Bintu da iyayen ta.
Da yawa sun yi mamaki, yadda kamar ɗan sarki daga kano, zai auri ƴar talaka.
Aka yi shagali sosai, aka yi auren.
Daga Bintu har Sharif, yarintar su kawai suke zubawa, dan a lokacin ba ta wuce shekara sha uku ba.
Mai martaba ya tura mutane, da ban haƙuri a kan abun da ya faru, tare da tabattar wa waziri, idan lokaci yayi ba fashi, za ayi auren Sharif da Jamila.
Jamila da yayarta, da mahaifiyarsu, ba ƙaramin tashin hankali suka shiga ba, dan haka suka din ga bin malamai, Allah ya tabattar da auren Jamila da Sharif.
Jin akwai wadda ake so Sharif ya aura, Bintu ta din ga murna, za a kawo mata ƙawa.
Wasa² sai da Sharif ya shekara biyu, kan ya auri Jamila, yau ya bayar da wannan uzurin, gobe ya bayar da wancan.
Ana haka Galadiman wannan lokacin ya rasu, bayan shafe zaman makoki, mai martaba ya sanar da naɗin Sharif a matsayin Galadima.
Ƴaƴan mai martaba da matansa, suka ɗaga hankalinsu, saboda gani suke rashin adalci ne, a bawa wannan yaron da ba shi da cikakken kai wannan babbar sarauta, bayan ga yayyensa.
Mai martaba ya yi burus, kuma bayan naɗin sarauta, aka ɗaura masa aure da Jamila.
Maimakon Bintu ta damu kanta, ita murna take yi, shi uban gayyar ne yake ta takaici, dan har ga Allah ba ya son jamila, ga wannan sarautar da aka bashi, ya na da shekaru ashirin da biyar. Jamila ta ƙudiri aniyar, ɗaukar fansar abun da aka yi mata a kan Bintu.
Rayuwa ta cigaba da garawa, son da Sharif yake yi wa Bintu, ya sanya mai martaba da mai babban ɗaki suma suke son ta, saboda tana da tarbiyya da nutsuwa.
Hakan ya ja mata baƙin jini a cikin facalolinta. Da an yi maganar sirikai, sai mai martaba ya ce “Ƴa ta bintu”.
Sharif da kansa yake koyawa bintu karatu, daga baya ya sakata a makarantar boko.
Sai dai ba ayi shekara da auro Jamila ba, abubuwa suka fara sauyawa a gidan.
Jamila ta fi Bintu wayo sosai, dan ta ba ta shekara biyu ma, kuma ta rayu a gidan wazirin daura, hannun yayarta, dan haka ta san abubuwa, da munafunci na gidan sarauta. Saɓanin Bintu, da neman ilimi kawai ta taso ta na yi a gidansu, dan ita a gidansu ma, ba a banbance ɗan wannan ɗaki da wancan.
Dan haka da bin malamai, da makirci, Jamila ta fara haɗa Sharif da Bintu faɗa, kuma ta din ga shishshigi a wurin facalolinsu, tare da nuna musu ita ta Allah ce, Bintu ba wayo sosai, sai dai ta yi ta kuka.
Tsawon shekaru uku, da aure, sannan ta fara al’ada ma a gidan miji, wataran ta je garin su, ta tarar yayarta ta yaye jaririyar da ta tafi ta bari tana goyo, mai suna laila, ta saka rigima sai an bata ita.
A duk lokacin da ta je gida, sai ta je rigar nan, wurin Ade, wato bafulatanar nan, idan har ta je kamar kaka da jika, za ta tarar ta ajiye mata tsintsiya, man shanu, da sauransu, kuma ita ma Bintu da na ta alkhairi take tafiya ta yi mata.
Bayan ta dawo da laila, sharif bai ce mata komai ba, dan ya na son yara shi ma, mai babban ɗaki ta bata hadima, Uwani, domin ta din ga tayata kula da yarinyar.
Sai dai ba Bintu ba, Jamila ma ba ta taɓa ko ɓari ba, suka kasa zaune suka tsaye ita da ƴan uwanta, Bintu kuwa ko a jikinta, sabgarta kawai take da karatun ta.
Ana haka mai babban ɗaki ta rasu, wanda hakan ba ƙaramin tayarwa al’ummar masarautar hankali ya yi ba, mussaman Sharif da Bintu.
Kwatsam Bintu ta din ga rashin lafiya, babu ƙaƙƙautawa, duk ta rame, Aka kaita asibiti aka tabattar ta na da juna biyu. Saboda tsabar ƙuruciya da murna, Sharif ya je ya gaya wa jamila, wai ta taya su murna.
Aikuwa ta ƙwafe abun nan a ranta, da alwashin ganin bayan cikin, a cewarta tun da aka fara auren Bintu, sai t jira ta fara haihuwa. Dan muraran jamila ke nuna wa Bintu ƙiyayya.
Dan haka maimakonsa bin malamai, Jamila ta fara shiga bokaye, da tsubacce-tsubacce iri-iri, domin ganin bayan cikin nan.
Allah mai jarraba bawa, sai da Bintu ta yi ɓari uku a jere, kowanne sai ta sha wahala kamar ba ta rayu ba.
Hankalin Sharif ya tashi sosai, ya damu, mai martaba ne ke kwantar masa da hankali, ya saka ake yi wa Bintu rubutun Alqur’ani.
Sai a karo na huɗu, sannan cikin ya zauna, sai dai ta azabtu saboda laulayi, dan ƙarshe ba dan Sharif ya so ba, aka mayar da Bintu gida, ya din ga jin haushi, dan ba ya son ta yi nesa da shi, hakan ya sake ƙular da jamila, ta yi amfani da duk wata dama, ta asiri, wurin ɗauke hankalin Sharif daga kan Bintu, tun da ta je gida bai taka ya je dubata ba, sai da ta haihu, aka aiko.
Jin haihuwar ya fi komai saka shi farinciki, ta haifi ɗa namiji, sai a lokacin ya din ga murna, ya je garinsu, abun ka da mutan da, ko da wasa bai ga alamar ta yi fushi da shi ba, sai dai bayan suna yaro ya ci sunan Abdullahi. Aka ɗauki soyayyar duniya aka ɗorata a kan yaron nan.
Watanninsa shida, yayi zazzaɓin wuni ɗaya ya rasu.
Mutuwar nan ta girgiza Sharif, da ƙyar aka shawo kansa. Still sai da Bintu ta sake ɓari, sannan ta samu ciki ya zauna.
Da aka haife shi, aka saka masa Adam, wato sunan mai martaba, mahaifin Sharif. Ake kiransa da takawa, saboda gidan sarautar dabo ba a faɗar sunan saboda girmansa, sunan mai martaba ne, kuma a lokacin Sharif ya yi wa Bintu srautar giwar galadima.
Jamila ba ta sake shiga tashin hankali ba, sai da ta ga, hankalin kowa ya koma kan Adam, ba a kansa aka fara yi wa mai martaba takwara ba, amma an fi nuna masa so, duk soyayyar da mai martaba yake yi wa Sharif ya mayar da ita kan Adam.
Adam na da watanni bakwai, wani cikin ya ɓulla a jikin Bintu, da yanzu ake kira da ammi.
A lokacin laila ta tasa, ba shi da wata ƴar raino, sai Laila da baba uwani, idan baba uwani ta zo ta gama aikace-aikacen ta, sai ta tafi gida ta bar sauran hadimai, laila kuma ta cigaba da raino, dan Ammi ba ta iya komai.
Sharif duk ya shiga damuwa, yana murna zai sake samun ƙaruwa, amma yana jin tausayin Bintu.
Ƙannen Jamila na yawan zuwa gidan, su yi ta faɗa da laila, ko su din ga cin zalin Adam, sai dai laila a tsaye take, ba ta da haƙuri, haka za su yi ta dambe, Ammi ta yi ta mata faɗan ta rage faɗa.
Wannan cikin shi ma ya tsaya wa Jamila, ta yi duk mai yiwu wa ta salwantar da shi, amma abu ya gagara, sai da aka haife shi, shi ma namiji.
Aka sakawa yaron Mahmud, sunan galadiman da ya rasu. Adam ba shi da wayo sosai lokacin, dan bai cika shekaru biyu ba, amma yana son sabon yaron da yake gani a wurin amminsa mai kyau, yana matuƙar kama da Adam da sosai da sosai, tamkar an raba kara biyu, duk kamarsu ɗaya da galadima.
Zigar facaloli, da soye-soyen zuciya, ya tunzura Jamila, ta rasa in da za ta saka kanta, ta din ga jin idan ta samu dama, tsaf za ta iya raba yaran nan da rayuwarsu.
A hakan, Sharif ya cigaba da tsaya musu, akan karatu, duk da ammi na fuskantar ƙalubale, kowa ya juya mata baya, an fi tausayin Jamila, shi kansa Sharif gaba ɗaya ya canza mata.
Sai dai Mahmud ma, bai fi wata bakwan ba, ta sake fuskantar tana da ciki, dan idan ta haihu ta gama biƙi ba ta al’ada sai dai ta ga ciki.
Some Of Related Hausa Novels
Be With Us
-
- Follow our Facebook Page : Ai Hausa Novels
- Follow our Twitter Page : @ Ai Hausa Novels
- Follow our Youtube Channel: Ai Hausa Novels
DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.