Zakuna Biyar Page 2 By Princess Teema
NEW YORK.🔥Jami’an sun yi iya bincikensu amma ba su iya gano menene ya haddasa wannan gobara a cikin gidan ba, iya abunda suka sani kawai shine gas ne ya fashe. Haka suka kwashi jiki suka bar gidan jama’a cike da jimami kowa ya koma bakin aikinsa. A gaskiya jama’a sunyi babbar rashi, domin dr mace ce wace kowa ya shaida tana da kyawawan ɗabi’u da kyawawan halaye, duk anguwan kowa yana alfahari da ita kuma kowa yana son kasancewa tare da ita, ko me dare in baka da lafiya ka kirata zata fita ta duba maka, bugu da kari abin hanunta bai rufe mata ido ba, kome ka tambaye ta zata baka kyauta in dai bai fi karfin ta ba, gaskiya jama’a sun ji babu daɗi sosai. Haka unguwar yau ta kasance shiru, dik da dama suna kasancewa a cikin shirun babu hayaniya, amma na yau daban ne saboda mutuwar doctor da ƴarta. 9:00PM. Agogon birnin new york ya sake bugawa, kasancewar unguwar ta manyan mutane ne sai ya zama kowa ya shiga gida, ga kuma mutuwar da ya faru sai ya kara sanyawa ko’ina yai tsit sosai, then akwai alamar ruwan sama a sararin samaniya, hadari bakin kiri, shi ya kara kora kowa gida…….. A hankali sauti na wasu irin jiga-jigan motoci da suka amsa sunansu motoci ya fara ratsowa cikin unguwar, tun daga kan yanayin sautin kukansu zaka san motoci ne na manyan kai, ajere suka keto titin wannan unguwa suna tafiya a wani irin slow montion. Motoci ne guda biyar cip.Kai tsaye a ƙofar gate ɗin gidan dr suka paka, suna parking a tare aka buɗe kofofin motocin, kan ka ce me wasu irin jiga-jiga mutane madaka katti sun danno waje, dikkansu sanye suke da baƙar wando da kuma farar t-shirt a jikinsu, while sun ɗaura tail coat a saman T-shirt ɗin wacce ta kai masu har gwiwa. Da ka gansu ko ba a faɗa maka ba kasan wasu tawaga ne na daban, imma jami’ai ko kuma gangsters, mutane biyar ne suka fito a cikin motoci biyar, kowane daga nashi motan daban-daban. Bawai iya su biyar ba ne a cikin motoci, a’a, akwai wasu sannan da drivers daban, dan dukansu daga back seat suka fito, cikin gidan dr suka wuce, a tare suke tafiya, in short a tare suke ɗaga kafa su kuma sauke, yadda kuka san kwararru kuma shahararrun gangster’s, a haka suka shiga cikin gida. Gabaɗaya mutanen unguwa suna cikin gida babu wanda ya san meke faruwa, saboda motocinsu ba irin motoci masu karan nan ba ne, mota ce da saita matsa kusa da kai zaka san tana zuwa, asali irin wannan motocin jami’an sirri sun fi amfani da ita ko kuma manyan gangsters da suka shahara a duniya, mota ce bata kowa ba. Sun ɗauki a kalla minti 10 a cikin gidan dr kafin su fito a jere, ɗaya daga cikinsu hannunsa ɗauke da wata ƙatuwar abu kamar kwali aka nannaɗe, dikka sauran huɗu akwai abubuwan da suka rike a hannunsu, da alama daga cikin kayan doctor wa inda basu ƙone ba suka tattaro ko dai wani abin, dik yadda aka yi suna da alaka da ita ko makamancin haka. Cikin motocinsu suka koma, a jere suka bar unguwar kamar da suka shigo TO FA, TAFIYAR YANZU TA FARA FA WACECE DR? ME KUKE TINANIN ZAI FARU? SU WANENE WAƊAN NAN MUTANE? MU JE ZUWA DAI. ——————————-🔥KASAR AVARIS. Avaris kasa ce dake makotaka da Us a kudu ta tsakiya. Kasa ce wacce take da tarin tattalin arziki, kama daga kan man fetur, gold, red diamond, har da su uranion suna da shi, suna da tattalin arziki daga albarkatun kasa da ruwa fiye da yadda mutum yake zata. Kasa ce dake cin gashin kanta, kasa ce dake da karfin siyasa da soji, sai dai gabaɗaya mafiya yawa daga cikin states na kasan a lalace suke, ga fama da yunwa da talauci, dik da wannan tarin arziki da suke da shi, ƴan ta’addan sun hana wasu daga cikin yankunan kasan zaman lafiya, kidnappers, da ɓarayin fili dana ɓoye, cin hanci da rashawa, gurɓatattun shuwagabanni, a wasu yankunan ma ƴan’ta’addan sun fi gwamnati karfi, su ke juya gari har da karɓar haraji da sauransu, abu kamar shirin film, amma zallar gaskiya ce!! Amma mu kutsa cikin labarin zamu fahimci daga ina matsalar Avaris ta samo asali.Eldoria State. Nan ne babban birnin kasar Avaris wanda suke ji da ita, birnine da ta ƙawatu matuƙa, domin a nan Diamon palace take, wato fadar shugaban kasar Avaris, birni ne na manyan alhazai mai ɗauke da dogayen gine-gine na alfarma, benayen da aka yi su high rise building masu design daban-daban, ga manya-manyan estate na gani na faɗa masu tsarin ginin turai, da su urban complex, glass towers, residential towers da dai sauransu. Wannan kasa tana da kyakkyawar alaƙa da turawan yamma, akan kasuwancin fili dana ɓoye, kai akwai fa abubuwa sosai sai mun kutsa ciki zaku gane karatun. ———————–🔥 AZURE BARRACK. Babban barikin soji na birnin Eldoria. Shinfidaɗɗen ginine wanda aka shinfiɗa tamkar ba za’a mutu ba, ka kai iya kallonka baka iya ganin karshen wannan gini saboda girmansa, gini ne dake ɗauke da Academys kala biyu bayan sansanin soja, sannan gini ne da sai mun kutsa ciki kawai zaku iya ganeta. Dik wasu manyan jami’an da suka shahara a manyan kasashe duniya ta sansu, to AZURE BARRACK ne ta kyankyashesu, daga ƙasashe da dama ana kawo manyan gifted jami’ai dan a horar da su, dik manyan jami’an manyan kasashen dake ji da kansu a nan ake horasu cikin sirri ba tare da sanin duniya ba!.Katafaren gate ɗin farko na shiga. Gate ɗin dakakkiyar ƙarfe ce mai ƙarfi tare da tsarin tsaro na zamani mai matukar ban mamaki, akwai kamar CCTV mai karfin gani daga nesa kilomita 5, da na’urorin tantance mutane wato biometric scanner wanda in dai zaka gifta wannan gate ɗin to sai ta yi scanning ɗinka ta turawa ɗakin da jami’ai na musamman ke kallon shige da fice na Barrack ɗin. Akwai katafaren office a bakin gate ta ciki dan karin masu gadin da zasu tarbi masu shigowa!.Mu kutsa ciki ta shinfiɗaɗɗiyar titin da ta miƙe tin daga gate na farko har izuwa can cikin Barrack ɗin, ta ko’ina ka juya a cikin barikin nan dakakkun jiga-jigan jami’ai ne ke shawagi, ga fuskokinsu sam babu kyan gani saboda yadda suka ɗaure tamau, suna wani muzurai tamkar ba mutane ba!. Manya-manyan gine-gine ne masu balain kyau a cikin wannan bariki, har da upstairs masu matukar tsayi dan manyan jiga-jigan sojoji. Akwai babban parade ground, babban fili mai ɗaukar mutane da yawa dan horo da taruka. Filin ya kasance da tsananin kyau tare da alamomi dan sauƙaƙa atisaye. Ga abubuwan training daban-daban a cikin wannan waje.Yankin da offices na jiga-jigan soja yake watau headquarters yana gefe guda cikin tsari da tsaruwa. Office ɗin The General Of The Army, watau shugaban dikkan sojoji kenan, daga kansa babu wata muƙami a soji, office ɗinsa babban gini ne mai ɗauke da offisoshi daban-daban dan manyan Generals na soji kamarsu Brigadier General, Lieutenant General, Major General, General, Colonel, Captain da dai sauransu. Kowani office cike yake da kayan more rayuwa dan jin daɗisu suma. Dik wanda bai san ya barikin soja take ba to yau zai sani.Akwai katafaren Training Academy, watau makarantar horarwa. Babban gini mai cike da ɗakunan karatu, laboratories, da ɗakunan nazarin makamai. A gefe ga filin horar da dabarun yaki da training na jiki. Ga tsarin dijital dan koyarwa, akwai allunan zamani irinsu smartboards da na’urorin koyarwa ta yanar gizo kai tsaye.Gefe guda akwai katafaren masaukin sojoji watau Barracks. Ƙayatattun ɗakuna masu tsabta da kyau, tare da kwanciyar kula ga sojoji ko ɗalibai na musamman masu bincike tamkar aljanu, yadda kuka san hostel haka Academy ɗinsu yake, ɓangaren mata daban ɓangaren maza daban, ga tsari mai kyau. Gidan kowane soja mai muƙami ba wai ɗalibai ba ya kasance tare da wutar lantarki, ruwan famfo, da tsarin ɗumama ko sanyaya wuri.Daga gefe can kuma akwai Military Hospital. Babban asibiti mai ɗauke da dukkan kayan aiki tamkar a wajen barrack, ɗakunan gwaje-gwaje, ɗakunan tiyata, da ɗakin kulawa na musamman watau ICU. Likitoci da ma’aikata masu kwarewa amma dikkansu sojojine, kuma su ake yiwa lakabi da surgeon Brigadiers ko surgeon Generals, to su ne likitocin sojoji.Sannan akwai sports complex, filin wasanni daban-daban kamar na kwallon kafa, kwando, da gudun tsere. Wurin motsa jiki watau gym na zamani tare da kayan zamani.Sai uwa uba wajen obstacle course, filin ne da aka tsara dan gwaje-gwaje da horaswa na sojoji kamar hawan igiya, gudun duwatsu, da tsallake rami, ko shiga ruwan teku, daga jin wanna abin da na kirga nasan kun gane ya yanayin wajen yake, cike da duwatse, tsaunika, bishiyoyi da kuma teku a gefe, shi a can nesa da barrack ɗin yake, dik a ciki ne, amma yana da nisa da wajen da sojoji suke rayuwa.Kada mu yi tuya mu manta da albasa, akwai mess hall, watau wajen cin abinci kenan. Babban ɗakin cin abinci mai iya ɗaukar mutane da yawa. Kayan more rayuwa kamar ɗakunan girki na zamani masu manya-manyan gas, da tsarin rarraba abinci cikin tsari da natsuwa.Sannan akwai armory and tech hu, waje ne dan ajiya da gwajin makamai, kamar irin su drones na yaki haka da sauransu, nasan tin daga nan zaku gane girman wanna GIDAN SOJA ya wuci yadda na faɗa a bakina ko? Sannan a cikin armory tech hu akwai gefe da aka tanada dan bincike da kirkire-kirkiren kayan fasaha na soja. Ina daurewa ne in yo maku bayanin komai dan ba zan sake dogon bayani a kan Barrack ɗin ba, Sannan kusan yadda yake da kyau idan ina rubutu kan wani ɓangare ba sai na sake tsayawa dogon bayanin yadda yake ba. Security control center, wannan ba sai na yi magana ba tin da na ce maku waje ne da ake yaye gifted jami’ai nasan kun san tsaron wajen ai ba’a magana. Muleƙa senior officers quarters. Gidaje masu kyau tare da kayan more rayuwa ga manya-manyan mukaman soja. Harabar gidan kowani babban jami’i ta kasance mai tsabta da shuke-shuke masu kyau dan morewarsu suma, ba iya yaki kawai aka sansu da shi ba.Lastly akwai recreation center, wajen nishaɗi a yayin hutun aiki, akwai irinsu sinima, ɗakin wasa na zamani, da wurin zama dan shakatawa a lokacin da ba lokacin aiki ba. Lambunan zamani da shuke-shuke masu kyau dan ƙara kyawun wuri, fitillu masu kyau a kowanne ɓangare dan inganta tsaro da kyau, wutar lantarki 24h ba ɗaukewa. Hanyoyi masu kyau da babu gargada, da alamomi na kwatance watau alamomin nambobi a kan titin. Dik wani barrack na kasashen ƙetare haka suke gwanin ban sha’awa da burgewa. Bari in yi tambaya! Shin ya barrack na kasarku take? Wani tsari aka yi wa sojojinku dan suma su ji daɗi kamar kowani ɗan kasa? Wani irin yanayi ake barinsu a ciki? Suda suka sadaukar da rayukansu saboda kare ƙasa, al’umma da dukiyansu, wani irin sakayya ake yi masu?. ALLAH YA TSARE MANA KU SOJOJINMU YA INGANTA AIKIN NAN NAKU!. ————————🔥Yau takama Monday, dubbannin sojoji ne suke shawagi a ko’ina, tamkar za’ayi yaƙin duniya ta uku, sai kai komo suke yi, kowanne ka ɗaga ido ka kalla ba zaka sake sha’awar kallonsa ba, dan sai hantar cikinka ta kaɗa, idanunsu jajir kamar wuta, sai wasu muzurai suke yi, ga jiga-jigan makamai rirrike a hannayensu.A gefe guda kuma ga matasan sojojin da aka ɗauka cikin satin nan dan horarwa, kowani matashi yana shirye cikin kayansa masu balain kyau, dik sabbin matasan da suka zo suna tsaitsai ne a cikin tsakiyar assembly hall ɗinsu, kowani matashi ka ɗaga idanu ka kallah zaka gansa cike da tsantsar muradinsa na son wanna aiki game da kwarin gwiwa, dayawansu suna tsaye ne da abokansu, wasu zaka gansu group uku, wasu su huɗu a wajen, wasu ma su biyu, sai hira suke yi, kuma dikkansu suna sanye da p-cap na sojoji a kansu, kowa jinsa yake yi a sama yau, suna jin tamkar sun zama sojoji, dan dik wanda yake wajen burinsa kenan. TO ALLAH yasa kuna da rabon haye atisaye ku zama sojojin da kuke fata, kuma ALLAH yasa aikin ya zame maku alkhairi har ku yi alfahari da shi!. Lokaci guda dikkan sojojin hankalinsu ya tattare izuwa kan hanyar shigowa hall ɗin sakamakon karar sautin tsaro da suka ji yana tashi alamar an dinfaro hall ɗin. Kan ka ce me kuma sun jera line by line tamkar assembly a primary school, sai dai tsayuwarsu cikin jarumta da karfafa kai ne.Wani kyakkyawan matashi fari tas da ba zai wuci 33 years haka bane ya shigo cikin hall ɗin, sanye yake cikin kakinsa, kana ganinsa kaga jarumi dakakken namiji, fuskansa babu annuri babu alamar wasa, kai tsaye kan stage dake hall ɗin ya nufa cikin takun dake nuna lallai jininsa a tafashe yake. Yana hawa ya furta attention babu wasa yana kara haɗe rai. Da karfi suka buga kafa ɗaya a ƙasa game da sara mashi, wannan ma yana daga cikin dokokin GIDAN SOJA da suka karanta kafin su zo nan.CAPTAIN ONBISH CO shi ne sunan dake a gaban uniform ɗinsa. Captain kallonsu ya fara yi one by one yana karawa kamar yana karantar wani abin a tattare da su kuma kamar yana karantar yanayinsu. A daidai wannan lokacin commander ya shigo, shi ma cikin jarumta da nuna kwarin jiki, amma shi zai iya kai 43 to 45 years haka. A saman stage ɗin shi ma ya zo ya tsaya yana kallon yadda matasan sojojin nan suke a tsaitsaye cikin ƙamewa, ya ji daɗi har cikin ransa, dan tin daga kan yanayin tsayuwarsu ya fahimci suna da zumman cinwa abin da suka sa a gaba. Hall ɗin nan gabaɗaya kewaye yake jiga-jigan sojoji jaruman gaske.Captain ne ya ɗaga hannu ya sarawa Commander cikin girmamawa da kwarewa a aiki. Sara mashi Commander ma ya yi kafin ya juya ya fuskanci matasan nan, a take suma suka ɗaga hannu suka sara mashi, jinjina masu kai ya yi kafin cikin kakkaifar harshe ya ce. “Attention!”. Kafa ɗaya suka sake bugawa a kasa da karfi tare da kara kamewa kam!. “1, 2, 3 start”. Commander ya sake faɗa cikin ɗaga muryar!.Yana cewa start suka buɗi baki game da ɗaga murya suka fara rera taken GIDAN SOJA da suke yi a kowacce safiya kamar haka…… “We march through fire, through storm and rain, With steel in heart, we bear the pain. For land and honor, we stand so tall, United as one, well never fall. Oh, we rise, we fight, we stand as one,Through darkest nights, til battle’s won.With fearless hearts, our banners wave,We are the strong, we are the brave! Our boots leave echoes on the ground,A thunderous beat, a mighty sound.No chains can break the will we hold,Our spirit fierce, our hearts like gold. Through blood and dust, through fire and war, we march ahead, forevermore. For freedom’s call, for justice true, Our oath is strong, we’ll see it through. Oh, we rise, we fight, we stand as one,Through darkest nights, til battle’s won.With fearless hearts, our banners wave,We are the strong, we are the brave!”. Bakinsu a haɗe suka rera wanna zazzafar taken nasu, dan yana rubuce cikin document ɗinsu, kafin su zo sai da suka haddace taken da dik wani dokan soja. Suna kai karshe suka daddage suka buga kafa ɗaya tare da sarawa manyan nasu. Watau tun da suka fara rera wannan take dik wani soja dake AZURE sai da ya miƙe ya kame a in da yake, wannan take nasu yana sanya sojojin su ji tamkar a filin daga suke, yana balain kara masu kwarin gwiwa, motsa zuƙata da gangan jikinsu da tsumasu yake, ga shi assembly hall ɗin akwai las speaker a ciki da in suna taken dik wanda yake cikin GIDAN SOJA sai ya ji, hakan zai sanya su mimmiƙe su tsaya cak game da sanya hannu a goshi alamar girmamawa ga GIDAN SOJA GIDAN WUTA!!!!. Idan aka kamaka ana rera taken baka miƙe ka ƙame saboda girmamawa ga taken ba ma sai ka sha horo sosai! Haddace taken wajibi ne a gareka!. Bayan sun kammala suna sauke ajiyar zuciya a hankali hankali ne Commander ya ce “Ina yi maku barka da zuwa AZURE BARRACK, Ina fatan zaku mai da hankali a kan aiki yadda yakamata?”. Dik cikinsu babu wanda ya yi magana, tamkar saƙaguna haka suka ƙame, doka ce baka isa manya suna magana ka yi magana ba tare da an baka izini ba. Kallon Captain Commander ya yi ba tare da ya yi magana ba. Da sauri Captain ya matsa gaba tare da fara magana cikin tsantsar jarumta. “Nasan kun san dokokin GIDAN SOJA, amma zan sake tinasar daku kafin mu bada umarnin zuwa mataki na gaba”. Ya ɗan dakata yana kallonsu. Still ba wanda ya motsa a cikinsu.”Doka ta farko a GIDAN SOJA shi ne biyayya ga manyan Hafsoshi sojoji wajibi ne a kanku, bin umarnin manyan ba tare da gardama ba, ba shawara bace, wajibi ce! Ana buƙatar sojoji su kiyaye dokokin soja da na ƙasa bakiɗaya, abu na biyu shi ne shaye-shaye, an haramta amfani da miyagun ƙwayoyi da barasa a yayin aiki. An hana sata, cin hanci, fyaɗe, da sauran manyan laifukan da nasan kun sansu kuma kun karanta kundin dokokinmu, tunatarwa nike kara yi maku, dan a GIDAN SOJA dik wanda ya karya doka kun san sauran, to gargaɗi ne da jan kunne mai karfi a matsayin na sabbin sabbin ɗauka”. Ya ɗan ja numfashi kafin ya cigaba. “Sai doka ta gaba shi ne yin aure ba bisa ƙa’ida ba. Sojoji suna da ƙa’idoji kan lokacin da za su iya yin aure, misali, a wani lokaci baya an tsare wata soja da ta amince ta auri mai bautan ƙasa (NYSC) ba tare da izinin manyanta ba, aka tsareta a prison na soja saboda ta karya dokokin soja kan aure, nasan kun samu wanna labarin a document ɗin da aka baku, sojoji suna da lokacin yin aure wanda sai sun karɓi umarni daga sama! Ba raɗin kansu suke yi ba”. Dakatawa ya ɗan yi yana mai da numfashi kafin ya cigaba da cewa.”Horon fisika da na Ilimi wajibi ne a kanku, sojoji dole ne su halarci horo na jiki da na ilimi dan inganta kwarewarsu. Dole ne sojoji su kula da tsabtar kayan aikinsu da muhalli. Ana buƙatar sojoji su kasance a shirye dan kowane aiki a kowane lokaci. Yin ritaya daga aiki yana da tsari da dokoki da dole ne a bi. Sojoji da suka karya dokoki suna fuskantar shari’a a kotun soja dake cikin Barrack ɗin nan. Wannan shi ne dokokin GIDAN SOJA, fatan kun ji da kyau?”. Ya kai karshen maganar yana rarraba idanunsa a kansu.Nisawa ya ɗan yi kafin ya cigaba da cewa. “A yau zaku karɓi manyan allurorin da ake yi wa dik wani sabon ɗalibin soja na kariya da sauransu, cikin alluran da zaku karɓa sun haɗa da allurar rigakafin cutar tetanus da diphtheria Tdap, waɗanda ka iya zama haɗari ga rayuwar soja, wannan allura ana yi wa sojoji a lokacin horo na farko kamar ku kenan, idan aka yi maku yanzu kuma sai bayan shekaru 10 za’a sake yi maku. Allurar na biyu kuma shi ne rigakafin cutar hepatitis A da B. Alluran yana kare hanta daga ƙwayoyin cutar Hepatitis A da B. Allura na uku shi ne allurar meningitis, watau meningococcal vaccine, yana kare kai daga cutar kumburin kwakwalwa watau meningitis, abin da yasa za’ayi maku shi dan horon da zaku fuskanta, gujewa ƙwaƙwalenku su kumbura ko su taɓu. Sai Rigakafin zazzaɓin cizon sauro watau yellow fever, yana kare sojoji daga wannan cutar da ake samu a yankunan tropic, musamman a Afirka da kudancin Amurka, so aikin zai iya kaiku ko’ina, dole ayi maku wannan alluran”. Ya dakata yana ɗan nisawa. Commander ne ya karɓi zancen da cewa. “Waɗan nan su ne alluran da zaku karɓa a yanzu, dan haka ku shirya”. Ya kai karshe yana dawo da kallonsa kan wasu zakwakuran sojojin dake gefe suna kallonsu, basu shiga cikin line ba, horarrun jami’ai ne ta ɓangaren harbi, basu da wasa. “Ku shigo da surgeons generals and nurses yanzu”. Captain ya faɗa a dake. Daddagewa sojoji biyun nan suka yi suka sara mashi kafin su nufi gate na hall ɗin. Jim kaɗan suka shigo tare da malaman asibiti da surgeons brigadiers. Nan Captain ya umarci matasan sojojin nan da su gyara tsayuwarsu da kyau su kuma ɗage hannun rigarsu sama dan dikka alluran a damatsan hannu za’a daddanna masu.Haka kuwa aka yi, dik suka gyara suka tsaitsaya da kyau, nurses ɗin nan suka hau bin line by line suka fara yi masu alluran. Abin ku da jarumai, tamkar ba jikkunansu ake fasawa a danna alluran nan ba, suna tsaye kyam tsabar ma sun sanya aikin a ransu. ——————–🔥A yayin da dikka wannan abin yake faruwa su kuma manyan zaratan general’s na sojoji suna can cikin COMMAND HQ suna tattaunawa dangane da yanayin tsaron kasar Avaris, taro na gaggawa ne suka shiga. To mu leƙa Command HQ ɗin mana mu ga me suke tattaunawa, dan yana da amfani a garemu kwarai da gaske.. COMMAND HQ.Ɗakin meeting na sirri na AZURE, bangon ɗakin ma Soundproof, common view bulletproof ne wanda babu wani bullet da zai iya fasashi, dik da ya kasance ɗaki ne mai matuƙar tsaro, amma an saka bulletproof glass sosai saboda tsaro, ga na’urorin leƙen asiri da ke bin duk motsi waɗan dake ciki da waɗan dake waje ko in ce tunkaro ɗakin. Wurin yana da ƙofar shigowa ɗaya da kuma ɗakunan bincike guda biyu kafin a isa ciki. Kai bincike sosai fa ake yi kafin kowa ya shiga, ma’ana kafin manyan Generals ɗin ma su shiga, sai an binciki ID, fingerprint, retina scan. Sannan ga wasu jiga-jigan sojoji guda biyu masu rike da jiga-jigan bindigogi suna tsaye a ƙofar ɗakin ta ciki da waje, ma’ana biyu ta ciki biyu ta waje, sai ka rantse da ALLAH sojojin nan basa numfashi saboda yadda suka kame kam. An kunna jammer na’urorin hana leƙen asiri, anti-drone radar, da surveillance 360 wacce ko yaya aka motsa dan leƙen sirrin cikin ɗakin sai an gano mutum, ko wata na’ura ka tura dan leƙen asiri jammer sai ta ganota. Daga nan zaku san ba ɗakin wasan yara bane a wajen! Kuma ƙananan kai basu zuwa wannan waje!. Manyan Generals na zaune a saman chair na table dake zagaye da ɗakin, irin round table ɗin nan ne, sannan a saman tables ɗin gaban kowani chair akwai sunan jami’in da zai zauna a wajen, wani ɗan karamin sing post ne da sunanyesu.Shugaban sojojin watau THE GENERAL OF THE ARMY THOMAS (G.A.T) yana zaune a tsakiya ta gaba, sauran Generals na a gefen dama da hagunsa bisa rank ɗinsu. A tsakiyar round na table ɗin ga jagorar rubuce-rubuce, da sashen bayanan leƙen asiri, da kuma wani soja mai ɗaukar hoto da recording idan an buƙata. Ƴan jaridu basu isa shiga wannan waje dan ɗaukar bayanai ba, sai dai su jira a waje idan an fito wani daga cikin General ya faɗa masu ga abin dake wakana dangane da tsaro ga kuma irin tattaunawar da aka yi!.Dikka dakakkun Generals ɗin dake wajen suna zaune ne cikin ladabi da biyayya game da nuna alamar girmamawa ga GAT dake wajen, kama daga kan lieutenant general, major general, brigadier General, General, dik suna cikin wannan ɗaki, kun san akwai bambanci tsakanin Lieutenant General da kuma Lieutenant, sannan akwai banbanci a tsakani Major General da kuma Major kawai, su waɗan da zaku ga General ya shigo cikin sunansu ana nufin su ne manya, misali Major General shi ne shugaban dik wasu Majors dake Barrack ɗin, kun gane ai? Wannan General ɗin na nufin mai wakiltan ko shuganan dikka Majors or Lieutenant ko dai wani runduna. Nasan kun gane nufina In Sha ALLAH.Zama yana tafiya cikin ladabi mai tsauri, dan kowa sai an bashi izini kafin ya yi magana. Wani kyakkyawan soja ne ya mike, hannu ya sanya ya buɗe taswirar kasan Avaris a gabansu. Katan taswira ne sosai wanda yake ɗauke da dukkan sassa na kasar, da yankuna da dama sai dai kuma a wasu yankuna akwai alamar jan marks, hakan alama ce da ke nuna yankunan da yan ta’adda su kaiwa kawainiya, su ake wa wannan mark ɗin.Still wannan kyakkyawan soja da ya buɗe taswira shi ya sake buɗe wasu takaddu a saman table ɗin. Takardun ne da suka fito daga hannun sojojin amma ta fannin kwararru kuma gifted waɗan da suke kamar jami’an leken siri na ƙasa, su horo na daban ake basu, ba zaku fahimci irin jami’an da nike nufi ba, dan ba kowa ya sansu ba, su ɗin sirrin ƙasa ne, amma bari mu kutsa ciki zaku gane irin jami’an sirrin cikin soja da nike magana. Duk wani soja da ke wajen a saman table a gabansa akwai coded notebook da pen da wani taswirar na manyan states na ƙasar, rahoton leƙen asiri, da hotunan jiragen yakin maƙiyan ƙasa da ƙasa, wannan kyakkyawan sojan ya sake budewa.Bayan ya kammala buɗe su gabaɗaya sai ya koma saman kujerarsa ya zauna ya kame ƙam, dukansu suka kara natsuwa sosai. Cikin nuna tsantsar isa da girma G.A.T ya mike tsaye, yana miƙewa duka sauran sojojin suka kara nutsuwa sosai. Ɗan gyaran murya yayi cikin kwararriyar turancinsa ya fara magana a natse bayan ya kunna mic dake gabansa, ya kuma kunna recording system na sirri dan su ajiye tarihin kowane zama. “Ina yiwa kowa da kowa barka da zuwa wannan taron, na san kunsan abinda ya tara mu anan, dan dik karshen sati muna yi, domin sanin halin da kasar mu take ciki da kuma sanin irin nasaran da muka cimmawa, kamar dai kullum zamu fara gabatar da abunda ya tara mu ba tare da ɓata lokaci ba, ina son bayanai daga bakin kowannenku, ina son jin wani nasara aka samu da kuma cigaba da muka kara samu a yankunan da ƴan ta’adda sukayi wa kasan nan kawanya”. Ya ɗan dakata da yin maganar yana bin fuskokin kowannensu da kallo. Dukansu sun wani natsu suna bin shi da kallon suma, wasu da kallo mai cike da tuhuma, wasu kuma da kallo mai cike da tsantsar ƙauna. In faɗa maku gaskiya? Kowa ya ga GAT sai ya sake kallonsa, kyakkyawan dattijo ne ajin farko, fari tas tamkar ka taɓa jini ya fita, ga balain kwarjini da farin jini, dik in da ya je ana sonsa kuma ana haukar tsoronsa, fuskansa babu alamar wasa ko fara’a, amma a haka kowa son shi yake yi, yana da jajircewa matuƙa a kan aikinsa, idan ya wurgawa mutum waɗan nan dara-daran eyes ɗin nan nasa wlh sai ka ji fitsari ya kubce maka, eyes ɗinsa suna da zurfi da firgitarwa, gasu milk color mai ɗan duhu, kwayar kuma tiger brown, a shekaru zai iya kai 45 to 47 years haka, amma idan kuka gansa wlh ba zaku bashi even 30 yrs ba, yana da kyan jiki matuƙa, ga gashin kansa bakinkirin babu alamar furfura, ba dan na san shekarunsa na gaskiya ba da na ce karya ne bai wuci ɗan 25 ba! Saboda jajircewansa a kan aiki ya tara uban makiya da masoya, babu mai shege mashi gaba bai takesa ba, baya hawa tsarin kowa, sai dai a hau nasa!. (WANI IRIN RAWA KUKE TINANIN ZAI TAKA A WANNAN LITTAFI BAYAN WANNAN YABO DA YA SHA DAGA GARENI?) Cigaba ya yi da cewa. “Ina fatan samun sakamako mai kyau daga gare ku a wannan zama, lokacinku ya fara daga yanzu!”. Yana kai karshen maganar ya koma ya zauna a saman kujerarsa.Yana komawa ya zauna wani dakakken soja ya mike wanda akalla zai iya kai shekaru 40-45, fuskansa a ɗaure tamau babu alamun wasa a tattare da shi, ga razani da kwarjini irin na sojoji a tattare da shi, BRIGADIER GENERAL AMEEZAN (BGA) shi ne sunan dake rubuce a gaban kakimsa. Mic dake gabansa ya kunna, sannan ya fara da cewa. “A gaskiya a nawa ɓangaren an samu cigaba sosai, an samu nasara, mun kashe ƴan’ta’adda a cikin wannan satin a kalla sunkai talatin zuwa arba’in, sannan mun tashi guraren da suke zama, mun hana su zaman gari mun hanasu zaman daji, mun dai samu nasara sosai……”. Ya ɗan dakata yana kallon fuskokin sauran sojojin, ya fahimci wasu suna kallon shi ne cike da tuhuma wasu kuma suna kallon shi cike da gasgata shi. Bai damu ba ya cigaba da cewa. “Mun raka yan ta’adda a guje tamkar karnuka, mun hana su sukuni, babu abunda zamu ce sai dai godiya ga sojojin mu da suka sadaukar da rai domin bawa wannan kasa kariya, amma mun rasa sojoji a kalla zasu kai goma, ina jajanta wannan al’amari”. Ya kai karshen magana tare da buɗe takardar dake gabansa, rahoto ne na shaidan aikin da yake ikrarin sanyi.Tunda ya fara magana har ya kai karshe akwai wasu generals na sojoji guda biyu da ke zaune a gefensa, sai kallon juna suke suna sake kallon shi, da alamar shakku a kan fuskokinsu, amma babu wanda ya tankasa, dan babu wanda yake magana idan ɗaya yana magana. Gaban General of the army ya turo wannan rahoton nasa yana kara ji da kansa a matsayin sunyi aikin ƙwarai, sai ya koma ya zauna. Wani dakakken soja ne ya sake mikewa cike da nuna tsantsan jarumta. MAJOR GENERAL RAHEEL (MGR) shi ne sunan dake rubuce a gaban kakakinsa.A kaifafe ya fara magana kamar haka. “Gaskiya ne BGA, ana samun cigaba sosai a ɓangaren tsaro saɓanin baya, a nawa yankunan da nake wakilta an samu nasarori da dama, mun kama ƴan ta’adda sun kai goma sha biyu, muna fatan mu cigaba da samun nasara haka har mu karar da su”. Shima ya kai karshen maganarsa tare da buɗe takardun dake gabansa na rahoton shaidan abinda ya fada ya turata izuwa ga GAT. 1 by 1 haka gabaɗaya sauran sojojin suka mike sukai jawabansu. Sai soja guda ɗaya ne bai tashi ba, wani kyakkyawan matashin soja da akalla zai kai shekaru talatin da uku zuwa da biyar a duniya, fari tas da shi, kyakkyawan gaske.Yana zaune shiru yana binsu da ido saboda shi sabo ne a karin girman, satin da ya wuce ya taka matsayin irin nasu bisa ga jajircewa da kokarinsa, karfi da aikinsa ya bashi wannan matsayi, so bai fara aiki ba tukuna, cikin satin nan zai fara aiki shiyasa bai bada rahoton shi ba. Tattara dukkan bayanansu GAT ya yi sannan ya mike ya rufe masu taron a zuwan zai duba rahotannin nasu sannan kuma zai zurfafa bincike saboda tabbatar da gaskiya suke faɗa ko ba haka ba, a bayaninsa na rufe taron ya kara masu karfin gwiwa, ya nuna musu su kara jajircewa dan tabbatar da tsaron wannan ƙasa, ya ja kunnensu sosai ya kuma tsawatar musu a kan su tsaya suyi aiki, su kawo karshen ƴan ta’adda, ya kwarara musu gwiwa sosai sannan ya rufe musu taro da addu’a irin tasa. Bayan rufe taron shi ya fara fita kafin dukkan sauran sojojin su rufa mishi baya. Suna fitowa BGA ya tsaya gaban ƴan jaridu domin basu rahoton abin da suka tattauna a yanzu, ya sanar da su cewa ana kara samun nasara ɓangaren tsaro, sannan ya kara da cewa an yi nasarar kama wasu daga cikin ƴan ta’adda, daga karshe ya rufe masu da cewa ƙasarsu ta kusa tsabtata daga datti ƴan ta’adda, sun kusa kawo karshen ta’addanci da duk wani tada kayan baya, yana masu albishir da za’a samu zaman lafiya mai ɗorewa, ransu fansa ne a kan wannan ƙasa. Yana gama zuba musu kalaman nasa da kowani ɗan ƙasa yake fatan ji, sannan ya wuce zuwa office ɗinsa dake bene hawa na 4 kusa da office ɗin GAT, ya yi amfani da elevator dan haurawa sama. Sauran Generals duka kowanne ya wuce nasa office. Su kuma ƴan jaridu suka fita suka sanar da al’umma halin da tsaron kasar take ciki. (A gaske haka tsarin yake, haka ƴan jaridu ke yawon faɗa mana halin da ƙasa ke ciki bayan manyan sun faɗa masu son ransu, uhm a wannan karon komai zan rubuta shi ne yadda yake In Sha ALLAH, sai ɗan gyara dan armashin labarin da kuma jin daɗin masu karatu!.) ————————-🔥A gefe guda kuma an kammala yiwa dukkan matasan sojojin nan allura, nan captain ya bukaci da kowa ya wuce ɗakinsa dan ya huta alluran tabi jiki, za su fara karɓan horo cikin kankanin lokaci. Cikin natsuwa suka fara watsewa ɗaya bayan ɗaya suka nufi inda ya kasance ɗakunansa suke.A tare wasu matasan sojoji su uku suka nufi inda ya kasance ɗakinsu, suna tafiya ne a natse kasancewar yau suka fara sanin juna a assembly hall, da alama dukkansu sunyi maraba da juna, daga yanayin yadda suke tafiya za ka fahimci cewa lallai sun fahimci juna. Room number 1 shi ne ɗakin da suka shiga, dik da kasancewar sun san babu kowa a ciki, hakan bai hana ɗaya daga cikinsu daka sallama ba. Sai dai ga mamakinsu kuwa suna sanya kai a cikin ɗakin suka yi arba da mutum a tsaye a tsakiyar ɗakin. Sun yi matukar mamakin ganinsa dik da cewa sun san mutane huɗu ne a kowani ɗaki, amma sai suka kawar da mamakinsu su ka karaso ciki.Ɗaki ne na matasan sojoji, gadaje ne guda huɗu a ciki, akwai komai na bukata, kowane ɗaki akwai toilet nasa a ciki, toilet guda biyu, gadon nasu irin sama da kasa nan ne, irin gadon ƴan boarding school, ya yi kyau sosai gadon, kowane gado yana shimfiɗe da zanin gado da bargo na lulluɓa, duka kalan uniform nasu na sojoji ne, ga karamin freezer. (Kada ku manta ba wai iya makarantar soja bane kawai a wajen, fili ne na yaye kwararrun jami’an da manyan kasashe suka aminta da kwakwalwarsu, waje ne na yaye gifted a ɓangaren kwakwalwa, karfafa a ɓangaren jiki, zaku gane nufina idan tafiya ta yi nisa, amma kafin nan me kuke tinani a wannan gida na soja? Ya ɗakunan kwanciya na sojijin kasarku yake? Irin na AZURE BARRACK ne?.) Wannan matashi dake tsaye yana goye ne da katan jakansu irin na sojoji a bayansa, da alama kayansa ne a ciki, hannunsa rike da takarda yar karama kaman yana karantawa, kansa sanye da army p-cap. Kusan a tare waɗannan matasa 3 da NOORIEL, ARVASH da ZAYNASH, kusan a tare suka yi mishi sannu, sai dai ga mamakinsu bai amsa su ba. Kallon juna sukayi cike da mamaki, dan dukansu a lokacin da suka fara gabatarwa da juna kai a assembly hall lokaci guda suka sake suka amsa wa juna kasancewar sun san ba su da kowa a nan, kuma wlh jininsu yai mugun haɗuwa cikin ƙanƙanin lokaci tin kafin ma su gane ɗaki ɗaya suke kuma rukuni ɗaya zasu karɓo horo, amma how comes shi suke mishi magana ya ƙi amsa musu?.NOORIEL ne ya gagara hakura da alama shi yana da zalama da son mutane sosai, karisawa gaban matashi ya yi, ya tsaya suna fuskantar juna, cikin ɗan nuna alamar rashin jin daɗin amsa musu da bai yi ba ya ce. “Amma dai ba ka ji mu bane muna yi maka magana baka amsa ba ko?”. Babu alamar gayen zai tanka mishi, sai ma raɓawa gefensa da yayi ya wuce, a saman gadon da ya kasance ita kaɗai ce a cikin ɗakin saura biyu duka ɗaya kan ɗaya ne, ita kaɗai ce babu na biyu akanta. A samanta ya ɗaura takardan dake hannunsa, sannan ya kwakkwance igiyar jakar dake bayansa tare da sakko da ita, ya ɗaura jakar itama a saman gado, bai ko kalli in da suke ba. Abin ya basu mamaki sosai, sun san cewa a lokacin da suka zo wannan barrack ɗin, sun ajiye jakunkunansu a ɗakin, ba suje assembly hall da su ba, amma shi kaman bai yarda da su ba, da jakarsa ya tafi. Sororo NOORIEL ya tsaya ya saki baki yana kallonsa cike da mamaki, basu tsammace hakan ba. Shi kuwa yana ajiye jakarsa ya cire p-cap dake kansa. Yana cire hular kyansa ya bayyana, kyakkyawan gaske ne, shekaru ba zai wuce 24 ba, launin fatansa irin pure with ɗin nan ne tamkar madara, yana da dara-daran idanu milk color, idan kuka ga idanun nasa zaku zaci baya kallo sosai saboda yanayinsu kalar cool zubin sleeping eyes kuma. Ba abin da ya fi baiwa matansan mamaki kamar gashin kansa, gashinsa irin golden ɗin nan ne wanda ake kira da (blonde hair.) mai balain kyalli da ɗaukar hankali, ya yi mugun kyau sosai, ya kuma sha gyara sai kyalli yake yi, ga wasu kitson kalba manya-manyan da ya zuba a kan nasa, basu taɓa ganin irin gashin a zahiri ba gaskiya sai yau, bugu da kari da kitso a kansa, hakan ya yi mugun tafiya da imaninsu, and gashin da kitson ya yi balain kara mashi kyau sosai, ai sai suka saki baki suna kallon kyan gashin nan. Shi kuwa, jawo jakansa ya yi ya hau buɗewa, abubuwan da zai yi amfani da su ya ciro, kama daga kan towel, brush, mangoge baki, wani set of lotions na Companyn STARS BODYS LOTIONS, company ne da kaff duniya basu da na biyu a mayuka da sabulan gyaran jiki, ciro lotions da kuma perfumes kala daban-daban masu daɗin kamshi ya yi. Ya kwashesu ya yi hanyar toilet da su. Da kallo suka bisa cike da mamakin yanayin kyakkyawar surar jikinsa, da alama ya jima yana gym ba sai yanzu zai fara ba, kurawa gashin gerarsa idanu NOORIEL ya yi har ya shige toilet, gerarsa yai matuƙar burge Noor, abin da yasa ya burgesa kuma shi ne, a jikin gerar ta gefen dama akwai tsagu guda biyu da suke tamkar yankan wuƙa aka mashi, hakan yasa ya raba gerar biyu daga ta karshe, ta kara mashi tsantsar kyau matuƙa, ba shi ya raba ba, ciwo ya taɓa ji a wajen sai ta zama haka, gwanin burgewa, idan kuka kalli guy ɗin a farko zubin tantiran ƴan duniya ne da shi, amma asalin halinsa shi kaɗai ya santa!.Uhm NIRASH MUHAMMAD HAIZAAN inkiya LEO kenan, jajirtaccen matashi kaifi ɗaya, bayi da wasa kuma baya ɗaukar wasa, mutum ne da abin dake gabansa kawai yake yi, baya shiga harkar kowa kuma ya tsani a shiga tasa, ya fi son zama shi kaɗai, bashi da magana kuma baya son ana magana a kusa da shi, jinin jarumta ne ke guda a jikinsa, ya fito ne daga kaɓilar Pamiri People da suke Tajikistan & Afghanistan, kabilun da aka ce sun fi kowani kabilu kyau a duniya, kyau tamkar su suka baiwa kansu, ko halitta aka ce NIRASH ya yi wa kansa, dik buri irin na ɗan adam na tabbata ba zai yi wanda ya kai rabin nasa da ALLAH ya bashi tsantsar kyau ba, dik da haɗama irinta ɗan adam, saboda kyansa wasu kiristoci a primary school ɗinsu har ce mashi suke yi mala’ika ne shi, saboda basu san mala’ikan ba, dik in da ya yi Seraph zaku ji suna faɗi, watau mala’ika mai tsantsar kyau da haske. Kyansa ya ja mashi kalubale sosai wanda yasa ya kara ja baya da mutane yake rayuwansa shi kaɗai. Ƙabilun Pamiri su ne kabilun da suka yi kaurin suna wajen kyau a duniya, suna da hasken fata pure white sosai, sannan idanunsu dara-dara mai haske da zurfi ga su siren eyes, watau idanu masu kamar zanen kifi haka, sai dai yana da matuƙar wahala ku samu mai bakin ido a cikinsu, idanun pamiran people kala uku ne, olive green shi ya fi yawa a cikinsu, sai kuma ash, na karshe violet wanda daga cikinsu dama ya fara fitowa, yauwa ana samun masu brown eyes ma a cikinsu amma ba sosai ba. Kazalika su da wuya ki samu masu baƙin gashin kai a cikinsu, always gashinsu golden ne ko kuma ash color, sai brown da shi ma ɗaiɗaiku ne, suna da tsawo sosai ga cikar halitta, musulmai ne, dan haka NIRASH cikakken musulmi ne sosai. Tsayayyen namiji ga tsawo ga ƙira mai kyau. Amma mahaifiyarsa ce pamira ɗin ba mahaifinsa ba.Kamar yadda kuka ga fulani akwai na daji akwai na gari to suma kabilun Pamira su ne na gari, kamar yadda ake cewa fulanin daji bororoji to su kuma Pamira na dajinsu ana kiransu da tajik, to shi NIRASH mahaifiyarsa pamira ce ba Tajik ɗin ba.(Oh ni Star Lady yau kuma na zaƙulo maku ƙabilun da suka fi kowa kyau a duniya, bari mu yi labari a kansu dan ku ji yadda suke da komai nasu saboda ku samu karin ilimi, mu je zuwa, yau ta Afghanistan muka leƙa dan zaƙulo wasu sabbin abubuwan.)NIRASH ya fito ne daga babban gida mai ɗauke da family guda biyu, daga Big Bro ɗinsa sai Granny ɗinsu wanda baya a tare da su a gida guda, sannan su mazauna Us ne, bala’in son aikin soja ya kawoshi AVARIS, dan dik duniya babu makarantar horon sojoji da ake basu ingantaccen horo irin AZURE ɗin, shi ne yasa NIRASH ya zaɓi nan. Sauran bayani zaku ji a gaba. Note, dik wanda kuka kallah a AZURE babban kai ne, dan sai kana da hanya kake samu!. ————————🔥Dawo da kallonsu a kan junan suka yi, ɗan daga kafaɗa Noor ya yi alamar anyway ba damuwa, dukansu wajen beds ɗinsu suka wuce, gabaɗayansu suma cire hulunan kansu suka yi, dukansu kowa da irin gyaran gashin kansa. Noor yana da gashi irin mai tsananin bakin nan, yana wani irin sheƙi, ga shi a kanannaɗe yadda kuka san indomie, kamar a nannaɗa mashi da gangan ne, irin nannaɗa sosai ɗin nan fa, kuma gashin tana da tsantsi sosai, Noor matashi ɗan baruwana, yana da hakuri, kuma yana da cutar tsoro, kamar akwai abin da ya taɓa faruwa da shi a lokacin da yake jariri ko yake cikin uwa, dan yana da irin saurin razana a abu, ko tsoratar da shi unexpected aka yi in ba’ayi sa’a ba yana iya sumewa ko ya kame, amma kuma yana da balain zuciya sosai, wannan ciwon tsoro nasa yasa mahaifinsa ya ce a kawosa AZURE, wai kila idan ya sha horo ya shiga cikin maza cutar zata rabu da shi, dan an nemi magani har an gaji ba sauki. Bugu da ƙari Noor yana da yanayin mata sosai. Dan a gidansu dikka mata ne, shi kaɗai ne namiji, shiyasa harta maganarsa zaku ji sautinta kamar ta mata saboda sabo da zama a cikinsu, ga shegen son jiki, dik dai wani halin mata sai ka same shi da su, babu abin da bai iya ba wanda mata suke yi, shi ne karami a gidansu, dik matan sun girmesa .Ɗaya na gefen Noor shi ne ZAYNASH, shi gashin kan nasa ya cika kansa sosai, bashi da tsawo sai cika da laushi sosai, ga shi irin light brown ɗin nan ne, guy ɗin bashi da saukin kai ko kaɗan, amma yana da hakuri da jurewa dakon abu, sai dai akwai zuciyar balai idan aka taɓasa, sannan in aka kuresa ya fara faɗa bai san dainawa ba. Mahaifansa ƴan ƙasar Niger ne a Africa. (Ina mutanena ƴan Niger? Ku zo ga ZAYNASH naku ne ɗan Nijer! ) kyakkyawan gaske ne, mahaifiyarsa buzuwa ce, mahaifinsa bahaushe, kun san suma ba baya ba wajen kyau da kamala. Uhm ZAYNASH ɗan gasa kenan, yana da bala’in kishi, baya son ya ga wani ya wucesa, shiyasa a makaranta baya bawa wasu damar zuwa first class, bashi da matsala da kowa, amma kada ka nuna mashi iko ko ka fishi, ba zaku shirya ba, yana da ƙoƙarin matua, dik dan farincikin family ɗinsa yake yi, saboda su ya shiga aikin soja!!Daya na gefen kuma gashin kanshi yana da cika sosai sai dai shi yana da tsantsi sosai yana kwance har gaban goshinsa, ga shi bakinkirin, sunansa ARVASH MUHAMMAD KHAIZA’AN, shi ɗan baruwana kenan, komai ka ke yi sai dai ya bika da ido kawai, ga shi da zurfin cikin balai, hakuri da juriya dik ya haɗa. Dukkansu huɗun nan karshen haɗuwa ne, idan ana maganan haɗuwa aka zo nan to fa sai dai a rufe baki, very classy da su, ga class da girmama kai, musamman NIRASH and NOOR, kyansu na daban ne, halittarsu ta sha bamban da tasu. Dikkansu fatarsu tana tsananin sheki da kyau except ZAYNASH dake da African skin, su ukun nan dik suna amfani ne da STAR BODY LOTION OR SOAP shiyasa yanayin kyan skin ɗinsu iri ɗaya, shi kuma Zaynash da namu man yake amfani!.Bari in takaice maku labari haka suka kwana cikin ɗakin nan ba wanda ya sake yiwa Leo magana, kuma shima baiyi masu magana ba, amma fa sunyi gulman shi sosai, musamman gashin kansa yanda basu taɓa ganin irinsa a zahiri ba, suka dinga yabon gashin sosai har Noor yana cewa dama ace ya samu irin wannan gashi ai da ya more. —————————-🔥 4:30AM watau asuba. Wani irin busa ne ya karaɗe gabaɗaya barrack din, tamkar busar ƙaho, wannan busa tayi sanadiyyar farkawa kowanensu, su Noor a tare suma suka farka, sai dai ga mamakinsu sai suka samu Leo a zaune a saman gado yana rike da wayarsa yana latsawa alamar tun ɗazun ma ya tashi koma dai bai yi barcin ba ma kwata-kwata, sun ɗan yi mamaki.NOTE: A gidan soja a lokacin horon matasan sojoji ba’a basu waya har sai sun kammala horo sun fara aiki za’a maido masu da wayoyinsu, sai dai suna iya kiran gida sau ɗaya ko biyu a sati amma ba da wayoyinsu ba, wasu ƙasashe suna basu wayoyinsu su kira gida, wasu kuma ana kira masu ne da wayar securitys officers, amma rike waya ba’a yarda ba, to amma ni na saka suna tare da wayoyinsu saboda wani dalilina kuma wannan part ɗin sai da wayoyi a hannunsu zan samu damar yin wani abu a wajen. Meyasa ake hanasu wayoyinsu a lokacin horo? ana hanasu wayoyinsu ne saboda abu biyu, na farko dan kada su fitar da sirrin irin horon da ake yi masu, watau su ɗauki video ko hotuna, shiyasa da wuya ku ga video ɗin yadda ake ainahin horar da sojoji, ainahin horonsu ba wai tsallake dutse, ko gudu or iyo cikin ruwa ba, ainahin horon ɓoyesa ake yi matsayin sirri, sai ka shiga zaka sani, zan rubuta yadda rayuwar sojoji suke a gaske da dik wata wahalar da suke sha da komai dai, ba zan rage komai ba! Zaku san su waye soldiers ba sunansu da kuke ji kullum ba, akwai abin da zan ɗan sakaya, abu na biyu da yasa ba’a basu waya shi ne zai ɗauke masu hankali daga kan horon da suke yi, musamman karatu da nazarin makamai da suke yi, yana ɗauke masu hankali. Dan haka kada ku manta da na faɗa maku ni zan barsu tare da wayoyinsu ne saboda labarina ya tafi mun yadda nike so, bana son abin da ba haka ba in saka maku shi tin da baku sani ba sai ku ɗauka gaske ne, shiyasa na faɗa maku ba’a basu wayoyi ni ne kawai na basu fatan kun game?! ————————-🔥ARVASH ne ya ce. “Wannan wani irin ƙara ne ya tashi mutane ba lokacin tashi ba?”. ZAYNASH ne ya kalli ARVASH idanunsa dik barci ya ce. “Awww kai nan baka san gidan soja ka zo ba ne kake tambayar me ya tasheku yanzu? Tab lallai ma, watau lokacin tashi bai yi ba, to ai a wannan gidan babu zancen lokacin tashinka, ba kamar gidanku bane da zaka yi barci lokacin da ka ga dama ka tashi lokacin da ka ga dama, nan lokacinsu zaka bi, dallah tashi ka yi abin da za yi yanzu, karfe biyar da rabi za ka fara karɓar horon, GIDAN SOJA GIDAN WUTA kake!! Kai baka karanta a document na biyu da aka bamu bane?”. Ɗan turɓune fuska Noor dake jinsu ya yi yana ɗan miƙa kafin ya ce. “Ni wallahi daddynmu ne ya matsa mun gabakiɗaya akan wannan aiki, wai na taso cikin mata, na taso a rago shi ne fa kawai ya ce sai na shiga aikin soja, gaskiya ni barci bai ishe ni ba”. Ya faɗa tare da koma ya kwanta.ZAYNASH da yake kokarin fitowa ƙasa daga gadonsa ne ya ce. “Kwanciya ko? Hhhhh yaro man kaza, kwanta bari Captain ya shigo cikin ɗakin nan sai ka gane annabi isa ba ɗan ALLAH bane manzon ALLAH ne, sai yafi maka sauƙi ka tashi da kafarka ka je wajen training akan ka bari ya zo ya same ka”. Yana rufe baki VASH ya karɓa da cewa. “Kyaleshi, idan Captain ya shigo zai nuna mashi a GIDAN SOJA GIDAN WUTA yake ba a gidansu ba”. Ya faɗa tare da dirowa kasan gadon ya nufi in da ya kasance toilet ɗinsu. Kwanciyansa Noor ya koma yayi yana cewa. “Bazan tashi yanzu ba, sai anjuma, dik abin da zaku yi sai dai ku yi, ba Captain ba komawa zai zo sai nayi barci na, a gidan mu karfe takwas nike tashi, dan haka sai takwas ɗin ta yi zan tashi”. Ya faɗa tare da jawo bargo abinsa. A cikin ƙasa da mintuna arba’in da biyar suka yi wanka suka shirya cikin ƙananan kaya yanda zai musu daɗin karɓan horo, sannan suka fito, suna fitowa suka nufi inda ya kasance masallaci, a nan suka yi sallah sai dai kafin su fita sun yi ƙoƙarin tayar da Noor daga barci, amma yaki tashi, ya ce su barshi, haka suka rabu da shi, dan a gidan soja dama ba’a taimakon juna ai a lokacin horo, barin mutum zaka yi jikinsa ya gaya mashi.So sun fita suka bar Leo a tsakiyar gadonsa yana zaune yana latsa wayansa, basu yi mashi magana ba shi ma bai yi masu ba!.Sai dai ga mamakin su kuma shine ya riga su zuwa masallaci, a can suka iskoshi, da yake hanyar zuwa masallacin yana da yawa, sai suka yi tinanin kila yanke ya bi. Karfe biyar da rabi daidai suka fito daga masallaci, suna fitowa gabaɗayansu suka nufin wani tapkeken fili, dama already sun sani ba yau bane farin zuwansu gidan soja, wata ɗaya da ya wuce sun yi cike-ciken form da zasu yi, sannan sun zauna na sati ɗaya a nan a nunnuna masu abubuwa kafin su koma su yi shirin zuwa karɓar horo, so sun san komai kuma yana cikin tsarin da aka tsara musu kafin a dauke su, ba saɓa lokaci! Babu wasa da aiki! Babu karya doka. GIDAN SOJA GIDAN WUTA, WAI ME KUKE TINANIN ZAI FARU NE?. NASAN HAR YANZU BAKU FARA FAHIMTAR KOMAI BA, TO KU YI HAKURI KU CIGABA DA BIBIYA, NAN GABA KAƊAN ZAMU ISA IN DA ZAKU FARA GANEWA! YANZU FARKO NE SAI NA DAURE NA YI MAKU NAYANIN KOMAI YADDA ZAKU FAHIMTA! DAN GABA KU JI DAƊI!.*Wannan littafi na ZAKUNA BIYAR tin daga page 1 na step 1 har zuwa karshen step 1 sadaukarwa ne ga mutanena na ƙasar Niger, ƴan Niger ƴan amana, ƴan Niger sun mun abin da ba zan taɓa mantawa da shi ba, Niger gidan karaminci da mutunci, gidan amana da kyautatawa, kai ƴan Niger baki na ya yi kaɗan wajen iya faɗan alkhairanku, kun mun na gani! Ban san da me zan biyaku ba shiyasa na yi maku wannan sadaukarwan, ALLAH ya kara maku lafiya da zaman lafiya, kwanciyar hankali da farinciki, jin daɗi da walwala mara yankewa har illarh Masha ALLAH, hakika ina kaunar mutanen ƙasar Niger kauna sosai mara misiltuwa, much love.*🌹♥️STAR LADYN TAKU CE TA AMANA.🔥ALLAH KA ƘARA MANA SOYAYYAR MANZON ALLAH.♥️



