Hausa novels

Haihuwa Da Hanji Page 12 Hausa Novel

Ta ɓangaren Afeefah anan bakin ƙofa ta ci kukanta har bacci ya sure ta ba tare da ta sani ba, mummunar mafarki da tayi da Aunty zee ne ya sakata farkawa a razane, fitsari ne kaman zai zube mata hakan ya sa tayi single kofa guda ɗaya da ta gani a ɗakin sai ta samu madaidaicin bayi ne, bayan ta gama abinda take ta fito ne ta fara bin ɗakin da kallon tsanaki don wutar a kunne tarrr kaman rana.Matsakaicin ɗaki ne a lailaye yake da farin tiles, fanka da bulbs duk suna aiki daga chan dungu ‘yar ƙaramar katifa ce da babu ko shimfidi a kai, sai agogon bango da ɗakin ke dashi, time ta kalla ƙarfe biyu na dare har ma da mintuna ashirin da uku, juyawa tayi ta koma bayin ta yo alwala ta zo ta sake shimfida dankwalinta ta saka hijabinta ta tada sallah, raka’a shidda tayi a sujadar ƙarshe ne ta saki kukan dake dukanta a kirji tana jerowa Allah kirari bayan ta jera sunayen shi masu daraja casa’in da tara ta bi da salati annabi kan ta fara jero matsalolin ta da neman sassauci ta yiwa iyayenta da sauran ‘yan uwanta da ta rasa Adu’a ta roki Allah ya kawo mata sauƙin rayuwa ya warware mata matsalolin ta ya kuma cigaba da bata zuciyar karbar ƙaddarar ta a duk yadda ya zo mata. Kusan ƙarfe uku da rabi ta sake kwanciya a wurin sanyin tiles na ratsa ta har wani baccin ya ɗauke ta.Ta makara don tana bude idanunta ta ga haske daga Window, da sauri ta miƙe ta shige bayi tayi saurin yin alwala ta zo ta gabatar da Sallar asuba tana sallame wa bata wani zauna Adu’a ba don tsoron laifi abincin jiya da ya ƙanƙare saboda sanyi ta cuccusa kan ta fito riƙe da plate ɗin ta nufi inda ta ga sun fito jiya.Tsaye bakin kofan kitchen ta ci karo da mommy sanye da hijabi, duk da zuciyarta ya buga haka ta ƙarasa ta zube a ƙasa tana gaisheta.”Sannu isasshiya sai yanzu za ki fito? Ban gaya miki aikin ki shara da wanke wanke bane, sai karfe nawa ake shara a gidan ku?”Murya a sanyaye tace”Ki yi haƙuri”Tsaki ta ja kan ta juya cikin kitchen ɗin “Talatuwa miƙo mata kayan sharar nan da mopping ta ajiye su chan baya don bana son kallonta gangar abincin da yarana za su ci ban san me za ta iya jefawa ciki ba ko jini ko tsoka”Abubuwan sharan wata dattijuwar ta fito mata da su, ta karɓa ta fara share parlorn zuwa dining area daga nan bayan ta gama ta shiga mopping da goge-goge aiki ba baƙonta bane don wannan a wurinta mai sauki ne sossai ma, haka zagi ko hantara duk ta riga da ta saba sai dai ba rayuwar da take fata tayi ba kenan, ba rayuwar da take buri ba kenan tana so ta ga tana karatu tana so ta ga tana hulda da mutane kaman kowani dan Adam, tana so taga ana hira da dariya da ita kaman yadda ta samu gidan Aunty zee, sai dai da kaman wuya wai guguwa da auren nesa.A gefe ta tsaya tana kallon Talatuwa dake ta aikin shirya abincin mutanen gidan bisa dining bayan ta gama ta dubi Afeefah tace mata “Ki zuba turarukan wuta ‘yan dai-dai a cikin wanchan abin ki kunna” ta ƙarasa tana nuna mata burner, show glass ɗin ta tafi a hankali cikin natsuwa ta buɗe ta ɗauko ta saka ta kunna yadda aka gaya mata ta koma bakin kitchen ɗin ta tsaya tana cewa Talatuwa ta gama..”Akwai abincin ki na saka miki a plate ɗinki ki ɗauka kije ki ci sai yaran sun gama karyawa tass sun wuce makaranta ake wanke-wanke”Da to ta amsa kan ta ɗauka ta fice, a hanya ta gamu da Ishaq so take ta gaishe shi amma kaman walƙiya haka ya wuce ta, bata damu ba ta shige ɗakin da yake da sunan nata ta rufo kofan.Ba za ta ce rayuwa a gidan yayi mata tsanani ba, saboda kwata kwata aikinta bashi da yawan da zai dameta, tana idar da Sallar asuba take zuwa tayi share share da su goge goge ta ɗauko abincinta daga nan ta tafi, sai wuraren sha ɗaya take komawa dining ta tattaro duk abubuwan da suka ɓata na karyawan ta fitar waje ta wanke ta kawo bakin kitchen ta ƙira talatuwa ta shigar, lokacin ita kuma Talatu za ta fiddo mata da abubuwan da ta bata na rana za taje ta tara su wurin wanke wanken ta rufe ta ɗauki abincin ranar ta ta tafi, sai bayan la’asar za ta fito tayi wanke-wanken haka na dare sai wuraren takwas tara. Ba Ta da abokin hira don talatuwa tsakaninsu ki yi kaza ne kar ki yi kaza ita kuma amsar ta ɗaya a komai to.Su iliya gudunta suke bata sani ba ko sun samu labarin ita ɗin annoba ce oho, bayan Hajiya da suka gamu sau ɗaya ‘yan mata ukun ko ganinsu bata sake yi ba, kaman yadda bata sake saka saleem a idanunta ba tun ranar da ya kawo ta zuwa yau da take neman sati uku.Bata sani ba shin rayuwar zai cigaba da tafiya a haka ne ko zai sauya? Shikenan ta sallamar da burin ta na yin karatu kenan?Shikenan ta tabbata Mayyar za ta ci gaba da rayuwa ita kaɗai tamkar a fursuna kenan? Bata da mai bata amsa.Da misalin ƙarfe biyu na dare chan cikin baccinta ta ji kaman ana buga mata ƙofa, a ɗan tsorace ta farka sai ta ji ana ambaton sunanta “Afeefah! Afeefah!!”Tun ranar da ta sanya kafafunta cikin gidan yau ne karo na farko da ta ji sunanta na fita a bakin wani hakan ya sake razana ta, da ta kasa kunne kuma sai ta ji kaman Muryar salim a maimakon ta ji sauƙi sai ta ji tsoro ya sake dabaibaye ta. Me yake yi a kofar ɗakin ta da wannan tsohon daren? Ashe bai ma manta da ita ba yadda tayi tunani? Miƙewa tayi ta nufi kofan wani zuciyar na cewa idan kuma hajiyarshi ta ganshi fa? Allah ya isa fa zata mishi sanadiyarta, sai ta girgiza kai tana dakatawa.”Afeefah saƙo zan baki ki buɗe don Allah, na san kina jina please buɗe ba zan jima ba”A hankali yayi maganan amma ta ji shi tsaff kasancewar dare ne, ta gyaɗa kai tana ba zuciyarta tabbacin saƙo kawai zai bata ya juya ba wani abu bane, da sauri ta je ta buɗe kofan sai suka tsaya chakk idanunshi cikin nata yana ƙare mata kallo kusan seconds biyar bai ce komai ba sai ita ce tayi ƙarfin halin ɗauke idanunta daga kanshi ta ɗan duka ta ce “Ina kwana Ya salim?”Ɗauke idanunshi yayi ya lumshe su kaɗan ya saki ajiyar zuciya mai dan nauyi, matsota yayi sossai ta matsa baya tana kallonshi da manyan idanunta, ya leƙa ɗakin kaɗan kan ya dawo baya, time ya kalla inda seconds ke reading, babbar leda jumbo dake hannunshi ya ajiye mata don baya so ya shiga ɗakin nata ba da wannan dare ba, kai ko da rana ne ma baya jin zai iya kebewa da ita inuwa guda ko don addini da ya haramta hakan.”Ki kula sossai za mu yi magana”Yana kai nan ya juya ya fice, ta bishi da kallo har ya ɓace mata kan ta runtse idanunta tana kokarin mayar da kwallarta ta tura kofar ta rufe, ledan da ya fi ƙarfinta ta shiga ja har gaban katifa ta barshi nan ba tare da ta buɗe ba tayi kwanciyar ta, sai dai duk yadda ta so baccin ya sake ɗaukar ta baccin ya ƙi zuwa, tuni ta buɗe idanunta ledar ta janyo gabanta ta shiga buɗewa a hankali.Da wani bargo mai taushi ta fara cin karo kaman ya san tana matuƙar bukatar bargon don tana shan wahalar sanyi da aka fara shiga, gashi bayin ta babu ruwan zafi wani lokacin hatta alwala da kyar take iya yi, wanka kam ba’a magana in dai tana so tayi sai ta bar ruwan a rana wuraren sha biyu zuwa karfe biyu nan ma da kyar za ta watsa bata gama tunanin ba ta ci karo da kwalin heater, irin wanda ake maƙalawa jikin bokiti ɗin nan a kunna ta ɗora shi kan bargon tana ɗan murmushi, ta sake mayar da hannunta ciki ta zaro hijabai ninkakku har kala huɗu kuma duk za su iya kai mata ƙasa Brown, Ash, purple da onion colour su ma gefe ta ajiye su, ta sake mayar da hannu ciki ta zaro kananun catons na biscuit da wasu small chops dai waenda za su dan kwana biyu basu lalace ba daban daban masu ɗan yawa, har da su five Alive kananu catons uku. Ganin abubuwan dake ciki sun kare ta ɗaga ledan domin matsarwa don ta sake kallon sayyayarta sai taji da ɗan motsi a ciki, ta buɗe gabaɗaya ta ci karo da ƙaramin kwali jikinshi da zanen waya, buɗewa ta yi ta ci karo da karamar Villion mai kyau da tsari Dukda keypad ne amma sossai ya mata kyau, fuskar wayan ne yayi haske alamun a silent yake saƙon akwati na SMS ya bayyana tare da sunan.”Saleemullah”Sai ta saki murmushi karo na farko ta buɗe saƙon.”Ba ki yi bacci ba?”Numfashi ta sauƙe kan ta shiga reply don ta iya sossai a wayan Aunty zee da ma wasu ‘yan ajin su na islamiyya lokacin da take zuwa makaranta ta amsa da “Eh, Na gode sossai da saƙon ka duk abinda ka saka a ciki kaman ka san ina da buƙatar su”Bata ajiye wayan ba ta ƙurawa screen ɗin ido chan sai ga reply ɗin shi. “Na kasa samun natsuwa da tunaninki zuciyata ita ta lissafo min duk abin da zuciyarki ta raya tana da buƙata. Kin ga ko zuciya bata ƙarya”Ta karanta saƙon ya fi sau abin da ya fi sai ta rasa amsar bashi, bata motsa ba har wani saƙon ya sake shigowa daga gareshi.”Na san baki jin daaɗin yadda kike zaune amma kiyi haƙuri zan yi iya ƙoƙarina in ga na yi settling komai, za ki yi karatu har sai kin ce ya isa, ga wayan nan zan dinga yi miki saƙo ki tabbatar kina yi min reply, duk kuma abin da kike so do not hesitate ki sanar da ni zan kawo miki. Akwai full qur’an a memory ɗin idan kin ji kaɗaici ki rage lokaci da shi kin ji?”Tana murmushi a lokaci ɗaya idanunta na zubar da kwalla ta rubuta “Wallahi samun mai irin zuciyarka sai an tona Yayana, na gode na gode Allah ubangiji ya ba ni ikon saka maka”Ta tura tana murmushi “Never mention my dear, ki kwanta kar ki makara da safe byeee”Ta sake sakin murmushi kan tayi reply “Allah ya ba mu alkhairi Soja Mai kirki”Dariya yayi daga ɓangaren shi ya rubuta “Au akwai marasa kirki ne?””Eh mana, abokin kan nan Dukda gaskiya ya faɗa amma in a wrong way, su ne suke ɓata muku suna ake yi muku kuɗin goro”Ya girgiza kai yana cigaba da murmushi “Ryan kenan! Haka Allah yayi shi, oya sleep Good night”Bata yi reply ba sai lumshe idanu da tayi razanannun idanunshi da yake zare mata su da sautin dakakkiyar muryarshi suka dawo mata kaman yanzu yake yi, da sauri ta buɗe idanun gabanta na faɗuwa ganin ita kaɗai ce sai ta saki murmushi a hankali ta maimaita sunan”RYAN” tana lumshe ido.

Back to top button