24
Farooq ya daga kai ya kallesa har sannan kuma wayar na hannunsa yana jujjuyawa, karasowa parlon Khalil yayi ya ajiye ruwa da glass din hannunsa, ya ki yarda su hada ido da Farooq yace “Oh kamar fa na makotanmu ne da suka shigo daxu, babu tantama wayar daya daga cikinsu ne, ban ma kula ba sai yanxu….” Farooq dake ta kallonsa ko kiftawa babu kamar baxai ce komai ba sai kuma yace “Now tell me who you are Khalil!!!” Khalil ya ɗan yi jim, can yace “Ban fahimce ka ba” duk wannan abun ya ki yarda su hada ido da Farooq, mikewa Farooq yayi ya dafa sa yace “Tell me what ur mission is, what is ur intention of coming to stay with us? ka gaya min kai wanene, menene manufar xuwanka gidanmu” Sai a sannan khalil ya daga kai ya kallesa amma bai ce komai ba, Farooq yace “From day one, i know u are not who u claim u are, u lied about ur personality to us, you have a mission definitely, be it revenge, spy, Dss…. And what have u!” Khalil ya girgiza kai a hankali yace “I have no mission Farooq, and my intentions of staying with u people is pure, aiki kawai ya kai ni gidanku, baya ga shi kuma babu wani abinda ya kai ni gidanku….” Farooq na kallonsa keenly yace “I will like to know u more” Khalil ya koma ya zauna, kamar baxai ce komai ba sai kuma ya sauke ajiyar xuciya yace “Duk abinda na gaya maka a kaina a baya hakan yake, i am a nobody like i said earlier, i was just opportune to go to school, i was opportune to be a literate, nayi diploma a fce nan kano wanda har yau ban samu aiki ba, bayan wannan komai game da ni na gaya maka a baya, u can even call Habib and confirm” Farooq yace “But meyasa kace iyakarka secondary?” Khalil yace “Ina tsoron kar a ki bani aiki a gidan ne” Farooq dai kallonsa kawai yake as if forcing himself to believe him, Can yace “Wani course din kayi?” Ba tare da Khalil ya kallesa ba yace “Business Admin” Farooq ya koma ya zauna kamar me naxari, ta gefen ido Khalil ke kallonsa hoping he is fully convinced, Farooq na daga kai Khalil yayi saurin dauke idonsa daga kansa, Farooq ya sauke wani ajiyar xuciya yace “Ohk then, in sha Allah xa mu yi magana da Abba, nasan xai yi iya kokarin ganin ya samar maka aiki dai dai da qualifications dinka” Khalil yace “Toh nagode sosai, Allah ya saka da alkhairi” Farooq yace “Ameen” Bayan few minutes Farooq yace “Ina Nihad din?” A hankali Khalil yace “Ban san inda ta tafi ba” Da wani expression Farooq yace “Ban gane baka san inda ta tafi ba, isn’t she under ur control now?” Khalil yace “Nayi kokarin hanata fita amma ta ki” Farooq yace “What? Sai kai kuma ka saka mata ido har ta fita?” Khalil dai yayi shiru. Nihad ce ta sauka bakin gate ita da Husnah da tayi ma kawayensu karyan xata je park ta amso sako, nan kuma ta gaya ma Nihad inda xata jira ta su hadu sannan su taho gidan gaba daya, Sosai gaban Nihad ya fadi ganin motar ya Farooq a waje, Husnah ta zaro ido tace “Toh yanxu ya xa mu yi kenan?” Nihad ta hade rai tace “Toh ba daga makaranta nake ba, shiga kawai za mu yi, ai ba yawo na tafi ba” Husnah tace “Aa, kinsan yayan nan naki ba saiti garesa ba haka kawai inje ya ritsa da ni” Nihad tace “To me xai min? Kawai mu shiga idan ya so sai ki zaga bayan gidan ki nemi waje ki zauna, idan ya tafi xan fito in gaya maki sai ki shigo” Husnah tace “Toh gwara haka dai” A tare suka shiga gidan Nihad ta kulle gate, duk da yanda gabanta ke faduwa hakan bai hanata dakewa ba ta nufi cikin gidan kamar wata boss, Husnah ma dai duk a tsorace take, tayi sauri ta zaga bayan gidan ta nemi waje ta zauna, a hankali Nihad ta murda kofar parlon ta shiga ciki da sallama, ta kara kicin kicin da fuska ta karasa cikin parlon tana kallon yaya Farooq da ya bi ta da ido, ta ɗan durkusa tace “Yaya ina yini” Mikewa yayi, yayi ball da ita cikin xafin nama, yace “Daga gidan uban wa kike?” Ta fashe da kuka ta mike xata gudu ya fincikota, jikinta na rawa tace “Yaya wallahi makaranta na tafi ba ko ina ba, ka kira makarantar ma ka tambaya” Duk a gigice take don a wajen duka xa a iya ba Farooq A1, Ya kai mata wani wawan mari yace “Uban wa ya baki izinin tafiya makaranta?” Ta rushe da kuka jiki na rawa tace “Wallahi na gaya ma Umma kafin in fita, ita tace in tafi, ka kirata ka tambayeta” Hauri ya kai mata yace “Ke da Umma ce a gidan nan? Ko Umma ke da iko dake yanxu?” hankali tashe tace “Don Allah kayi hakuri yaya baxan kara ba wallahi, kaji har na rantse maka” Shi dai khalil na xaune bai ce komai ba sai kallonsu yake, Har baya Husnah ke jiyo muryar Nihad tana ihun neman agaji, ba shiri ta mike ta nufi gate da gudu tun kan Nihad tace tare su ke, da hannu farooq ya dinga makan Nihad, mari kuwa yayi mata har sau uku, kuka take iya karfinta tana basa hakuri tana cewa baxata kara fita ba, daga karshe yayi ball da ita ta mike tsaye da gudu ta shige dakinta ta sa makulli tana rusa kuka, Farooq yace “Gobe ko nan da gate ki fita in samu labari ki ga yanda xan faffasa maki jiki da belt, munafuka kawai” Ko minti uku bai kara a gidan ba yayi ma Khalil sallama, khalil ya rakasa har mota, farooq na kallonsa da kyau yace “Kar ka kuskura ka raga mata ko na second daya idan tace xata dinga kawo maka raini” Khalil ya ɗan yi murmushi kawai, Farooq yayi masa sallama ya ja motarsa ya bar layin, juyawa khalil yayi ya koma cikin gidan, ya zauna saman kujera ya dau Iphone dinsa hade da sauke ajiyar zuciya, tashi yayi ya tafi daki ya ajiye wayar, Nihad na jin ya bude kofar dakinsa ta fito da sauri, parlor ta tafi ta tabbatar da gaske yaya farooq ya tafi, sai da ta kara duba takalmansa nan ma taga babu alamar dai ya tafi, share hawayenta tayi ta nufi dakin nasa ta bude hade da turawa da karfi, tana kallonsa cike da rashin mutunci da tsiwa tace “Toh da ka kirasa ka gaya masa sai aka yi yaya? Nace sai me da ka kirasa? Mutuwa ka ga nayi bayan muguntan da yayi min? Kuma ka zata xan fasa fita in tafi makarantana ne ko in tafi duk inda nake so? To wallahi karya kake yaro don ko gobe ma ba a haifi wanda xai hanani xuwa makaranta ba kaji in gaya maka, Kuma da kai da ka kirasa da shi da dokeni Allah ya isa ban yafe maku ba….” Wani tsaki ta ja tana hararansa cike da tsana, ya girgiza kai yace “Akwai lkcn da matsayin tsayawa bakin kofar dakina ma baxa ki samu ba balle ki gwada min halinki na rashin tarbiya… bari kiji ba bakin kofar dakina ba har bangarena ma sai ya haramta gare ki wataran wallahi….” Sai kuma ya mike ya nufeta, sosai gabanta ke faduwa ganin yanda ya daure fuska amma ta dake ta tsaya bakin kofar, ya tsaya dab da ita yace “Kinsan me yasa baxan ke kulaki ba idan kina nuna rashin tarbiyar ki? Saboda ke din ban dauke ki a bakin komai ba, ban dauke ki mace ba, ba kuma kallon mace nake maki ba, kallon yar titi kuma er bariki nake maki, na dai girmama mahaifinki na amshi tayinki da yayi min don shi din mutum ne me daraja da kima a idona, banda haka ko da duk arxikin duniya aka hadani da ke wallahi wallahi baxan aureki ba don ni ba ajinki bane ta ko ina na fi karfin ki….” Nihad ta zaro ido hade da bude baki tana kallonsa, sai kuma ta cakumo kwalarsa cike da tsiwa tace “Ni kake ce ma yar titi kuma er bariki??” Shaketa yayi ya hadeta da kofa ba shiri ta sakesa gabanta na mugun faduwa, ya dinga kallonta fiercely yace “ina me baki shawara da kakkausar murya, Kar ki sake gigin kai hannunki jikina, idan ko kika sake yin wannan kuskuren to xaki sha mamakin abinda xan maki a gidan nan” Yana gama fadin haka ya turata waje ya kulle kofarsa, kiris ya rage ta fadi, tana huci bayan tayi regaining balance dinta tace “Kai din banza zaka bani shawara da kakkausar murya, aa sai dai karyayyen murya, waye kai kuma me kake takama da shi, kuma wallahi ni ba er titi bace don ina da gatana kuma da arxikin iyayena, kai kuma fa? Naga sai kayi tuki kake samun na xubawa a aljihu?” Sai kawai ta fashe da kuka ta shige dakinta ta fada kan gado tana rera kuka, duk Abba ne ya ja mata yau wai driver din gidansu ke kiranta yar titi kuma yar bariki, kuka take kamar ranta xai fita, gaba daya ta mance da wata Husnah, sai da taji ana kiran magrib sannan ta tashi ta goge idonta ta xauna saman gadon, tana jinsa ya fita masallaci, banda muguwar tsanarsa babu abinda ya cika xuciyarta, wallahi ta tsanesa, she hate him with passion, tana jin ya fita masallaci ta mike ta dau mayafinta ta fita xuwa baya wajen Husnah, wayam ta ga wajen, ta juya ta koma ciki, wayarta ta fiddo can kasan jakarta ta hau dialing number Umma, Sai da ya kusa katsewa Umma ta daga, bayan sun gaisa ta fashe da kuka tace “Umma ya farooq ya zo har gida ya zane ni saboda na tafi makaranta wai” Umma ta bude baki tace “Shi farooq din?” Cikin kuka tace “Ehh Umma” Umma tace “Yi shiru xan yi maganinsa don ubansa” Nihad na shessheka tace “Toh Umma yace kada in sake fita makarantar kuma” Umma tace “Ai ba shi ya haifeki ba da xai hanaki xuwa makaranta, kanki tsaye gobe ma ki shirya kiyi tafiyarki duk inda xa ki ba ma makaranta kadai ba, ki kyaleni da shi kawai xan yi maganinsa” Nihad tace “Toh” Umma tace “Kar ki sake asaran hawayenki a banza, kinji abinda nace maki” A hankali Nihad tace “Na ji” Umma tace “To sai da safe” Daga haka ta katse wayar, mikewa tayi direct ta tafi dakin farooq, luckily ta samesa xai fita Masallaci, strictly tace “Farooq daga yau sai yau in har ba baki kake son in maka ba bana son in sake kara ganin ƙafafuwanka a hanyar gidan Nihad, kuma babu ruwanka da harkarta da abinda take yi, in dai ba so kake in ce maka je ka ka gani, kai ko a waya na haneka da kiranta” Da mamaki Farooq ke kallonta, tace “Ni dai na gaya maka, kana kiranta ko da a waya ne Allah ya isa, balle har ya kai ka taka har gidanta, daga yau bana son magana ya sake hadaka da ita ko a ina kuwa” Tana gama fadin haka ta juya fuuu ta fice ya bi ta da kallo, a parlor ta tadda Amina xata fita, tace “Ke kuma ina xa ki?” Amina tace “Umma kati xan amso” Umma tace “Ban hanaki fesa turare haka ba idan xa ki fita? Kuma ba nace maki wannan hijabin bana son kina sa shi ba? Meye amfanin hijabi da xai dinga nuna surarka? Maza koma ki dau wani hijabin” Amina ta juya tace “Dama kyautar da hijab din xan yi Umma, kawai bana son daukan gogagge ne shi sa na sa shi yanxu” Umma tace “Maxa ki bayar idan ba haka ba in kona, bana son sake ganin ɗan iskan hijabin nan a gidan nan” Amina ta juya ta koma daki, Umma ta wuce ɓangarenta. Karfe tara da wani abu Nihad ta gama shirinta xata kwanta, har sannan taki daina kukan maganganun da Khalil ya gaya mata, wai er titi, sannan har da cewa tayinta Abba ya basa, takaici kamar ta hadiye xuciya, can ta mike ta fita daga dakin nata, a parlor ta gansa xaune yana kallo, tana harararsa tana huci tace “Ba dole ka sa tv a gaba ba tunda babu a house” Shi dai bai ko kalleta ba, tace “Kuma da kake cewa Abbana tayina yayi maka, in ka cika ɗan halas ka sakeni yanxu yanxu mana…” Sai a sannan ya daga kai ya kalleta, ta maka masa wani harara tace “Idan kuma baka da takarda da biro ni ina da su” Bayan few seconds yace “Ohk ashe dai kinsan da aurena a kanki?” Ta wani kyabe baki tace “Oho dai” Ya gyada kai yace “Kar ki damu akwai lokaci, kawai mu jira lokacin, ina son sai sanda kika fahimci ni ba sa’an aurenki bane sannan xan sake ki….” Tace “Aikin banza kenan, yanxu ya kamata ai, don tun yanxu nasan ni ba class dinka bace, kuma baxan ta6a xama class dinka ba” Khalil bai sake tanka ta ba, ta juya fuuu ta koma ciki, wayarta ta dauka a karkashin pillow tayi dialing number Aliyu, amma ta kasa samunsa sbda ba shi da number, Naf ta kira tace “Naf don Allah ki kira Aliyu kiyi mashi sending wannan number nawa yayi saving i want to talk to him” Naf tace “Ohk” Daga haka ta katse wayar, bayan wani lkci Naf ta sake kiran Nihad tace “Nihad na tura masa number taki yace xai kiraki” Nihad tace “Toh nagode sosai” Nihad na kwance tayi lamo kan pillow tana ta jiran kiran Aliyu, sai ga kiran nasa, farin ciki ne ya cikata ta mike xaune da sauri ta daga kiran, a hankali tayi masa sallama, ya amsa yace “How are you?” cikin sanyin murya tace “Alhmdlh” Yace “Are okay?” Lokaci daya hawaye ya kawo idonta tace “No” Da damuwa yace “Me kuma ya faru?” Tana girgiza kai hawaye na sauka idonta tace “Baxan iya jure xama waje daya da wannan drivern din ba, Har xagina sai da yayi daxu fa” Aliyu yace “Ya zage ki?” Cikin kuka tace “Ehh, wai ni ya ce ma er titi, er tasha, har da cewa Abbana tayina ya basa” Aliyu yace “Shi Drivern?” Tace “Ehh” kasa cewa komai Aliyu yayi, can yace “Wait u mean driver ne ya gaya maki wa ennan maganganun?” Nihad tace “Wallahi” Rai bace yace “Har ya kira ki da er titi?” Cikin rawan murya tace “Haka yace” Aliyu ya fuzar da iska yace “Kar ki damu, ki kwantar da hankalin ki, xan dawo Nigeria soon, and everything will soon come to an end in sha Allah” Tana share idonta tace “Nagode” Yace “Kar ki sake xubar da hawayenki, sai yayi da ya sanin zagin nan da yayi maki wallahi” Nihad tace “Sannan nace ya sakeni ya ki” Aliyu yace “He just have to, cause u are not meant for him….” Ɗan murmushin jin dadi tayi, yace “Are u on WhatsApp?” Tace “Aa xan bude yanxu” Yace “Idan kin bude, ki kirani” Tace “Ohk” Daga haka ya katse wayar, sosai hankalinta ya kwanta da abubuwan da Aliyu ya gaya mata, bayan ta bude WhatsApp din Video call suka yi da Aliyu har kusan karfe dayan dare, tun bayan da Video dinta ya tafi viral sai ranan tayi bacci cikin dadin rai. Cikin dare taji kamar ana daga pillow din da ta daura kanta, ta bude ido da sauri, bata ga kowa ba banda duhu dake dakin, gabanta ya dinga faduwa don da gaske taji kamar ana daga pillow dinta, ta mike xaune tana bin ko ina da kallo duk da duhun dake dakin, hannunta ta kai xata yi switching wutan dakin taji ta daura a kan hannun mutum, wani ihu ta fasa a mugun tsorace xata sauko daga kan gadon taga an kunna wutan dakin haske ya gauraye ko ina, yana jingine jikin bango kusa da bed side drawer, tsaye tayi bakin kofa tana kallonsa a mugun tsorace kuma da mamaki, ya daga pillownta ya dau wayar dake ƙarƙashi, xaro ido tayi ta taho da sauri tace “Wallahi kar ka kuskura ka ta6a min….” Wani mugun kallo yake mata yace “Kar ki matso kusa da ni” Ta fashe da kuka sosai tace “Wallahi ka bani wayata, kaga ba kai ka siya min ba, ba kuma da sisin ka aka siya ba” Kofa ya nufa ta koma gefe tana kuka tana kallonsa har ya fice daga dakin, da sauri ta bi sa dakinsa tana cewa “Wallahi ka bani wayata” Bude kofar bandaki taga yayi tana kallo ya tara ruwa a bucket sannan ya cilla wayar a ciki ya fito ya sa ma bandakin makulli, saboda shock kasa ce masa komai tayi ta tsaya tana kallonsa ko kiftawa babu, bai ko kalleta ba ya kashe wutan dakin yayi kwanciyarsa saman gado…. Har gari ya waye Nihad bata yi wani bacci ba, ta ci kuka har ta gode Allah, ta sake tabbatar da cewa bata ta6a tsanar mutum a duniya irin khalil ba, karfe takwas saura taji kamar ana welding a bakin gate, ta mike da kyar ta fito parlor ta tafi kofar fita parlorn, tsaye ta gansa a compound, ga kuma me welder da me canza lock din gate suna ta aiki a bakin gate, juyawa tayi da sauri hawaye cike idonta ta koma dakinta, ta xauna gefen gado tana shessheka, ta shi tayi ta tafi dakinsa ta bude kofar bandakin ta duba bucket din da ya jefa wayarta taga babu wayar a ciki, ta fito ta ga karamar wayarsa a gefen gado, da sauri ta dauka ta fito ta shige dakinta, Call logs ta shiga taga number anyi Saving da Nadeeyah with love Emoji, kallon Number ta dinga yi sai kuma tayi scrolling xuwa kasa taga number Nihal wanda ko jiya ma sun yi waya, shiga tayi taga maganar minti nawa suka yi taga kusan minti goma, dialing number tayi yana fara ring Nihal ta daga, Rai bace Nihad tace “Ban san ke munafuka bace kuma algunguma sai yanxu Nihal, kuma in sha Allahu ke abinda xai sameki sai ya fi wanda ya sameni ki rubuta ki ajiye, don naga kamar farin ciki kike da condition din da nake ciki, banda kina farin ciki da abinda ya sameni wayar me xaki dinga yi da enemy din nan nawa? Me yake gaya maki, me kike gaya masa?” Nihal tace “Haba Nihad, what is this u are saying? Da kinsan wayar da nakeyi da shi da baki kirani kina gaggaya min wa ennan maganganun ba, kema kinsan baxan ta6a farin ciki da bakin cikin ki ba…” A fusace Nihad tace “Babu abinda xa ki gaya min da xai gamshe ni, kuma xan ga ta inda xaki sake waya da shi” Nihal tace “Toh shikenan, amma ki sani ko na kirasa ke nake cewa ya ba waya sai baxai baki ba” Nihad tace “Oho wannan ke da shi ya shafa” Nihal tace “Jibi xa mu yi hutu, and we need to talk idan na dawo Nihad” Nihad bata kuma sauraronta ba tayi ending call din, Yanxu tasan xamanta da kowa a duniya, Abba ne oo, Mumy, Ya farooq, Nihal, duk ashe ba sonta suke ba, kuka sosai ta saki, sai kuma tayi blocking number Nihal a wayar sannan ta bi duk calls din ta goge, Kallon Number Nadeeyah ta dinga yi ganin how special the line is with multiple 2’s, can ta ja wani tsaki ta danna masa block sannan tayi deleting shi ma gaba daya a call logs, sai kuma ta tuna cewar she needs to tell Aliyu cewar ya amshe mata waya incase zai yi ta nemanta, dialing number Aliyu ta fara yi, ko digit hudu bata sa ba sai taga number ya fito barau barau amma ba tare da suna ba, still tayi tana ta kallon screen din karamar wayar baki bude da mugun mamaki, to ko dai jiya da ya dau wayarta ne ya kwashe number??? lkci daya ta juya da sauri jin taku, wani irin faduwa gabanta yayi ganinsa a bakin kofar dakin yana kallonta, cikin rikicewa ta ajiye wayar hannunta gefen gadon gabanta na faduwa, shigowa dakin taga zai yi, ta marairaice ta koma can karshen bangon dakin xuciyarta na bugawa tana kallonsa amma hakan bai hanata hade rai ba, ya kalli wayarsa sannan ya kalleta, daukar wayar taga xai yi ta nufi kofa a guje yayi saurin fixgota, kuka ta saki ta rirrike hannunsa tace “Ni wallahi ka sakeni, me kaga nayi kuma again, ba yar uwata na zo inyi magana da ba na dade ban ji muryarta ba….”
Click Here To Read Nihaad Chapter 25 By Khaleesat Haiydar
Nihaad is 500 via 3276052019 Fcmb Hauwa Bello Jiddah
And u show ur evidence via👇🏻
07087865788📚✍🏻