Uncategorized

Tsatsuba Na 1 Complete Littattafin Yaki By Abdulaziz Sani M/Gini

TSATSUBA

Book 1

Part A

Marubuci Abdul’aziz Sani Madakin Gini

Posting By Abubakar Saleh AlQuyraemey

Domin Samun litattafan Yaƙi Contact 08138873799.

Marubucin ya fara da cewa….

Sarauniya Larbisa ta kasance gagarumar attajira, kuma gagarumar mayakiya mai mulkin wata kasa babba wacce tafi dukkan sauran kasashen duniya girma da yawan jama ah a zamaninta sarauniya larbisa ta tara zakakuran mayaka wadanda suka kasance GUGUWAR ANNOBA domin duk kasar da suka durfafa da yaki sai sun murkusheta komai karfin mayakanta babbar matsalar sarauniya larbisa itace bata tsafi kuma tsafi baya cinta bokaye sun tabbatar mata da cewa ba zata taba haihuwa ba sai ta lalata dukkan tsafin dake duniya gaba daya idan kuwa tana son ta lalata dukkan tsafin duniyar dolene ta tura a nemo mata wani littafi mai suna TSATSUBA wanda aka rubutash sama da shekaru dubu arbaIn da suka gabata.

.

Asalin wannan littafin mallakin sarkin bokayan Aljanu ne na farko wanda shine ya kirkiro dalasiman tsafi guda miliyan dubu Arba’in daya rubucesu tsaf a cikin wannan littafi kuma yayiwa littafin lakabi da suna TSATSUBA. Duk wani tsafi na duniya mafarinsa kenan kuma makarinsa na cikin wannan dalasimai tsawan shekaru dubu Arba in din da suka gabata bokayen duniya da yawansu suka bazama neman wannan littafi har suka  hallaka bisa wannan tafarkkuma duk wanda ya tsananta nemansa hallaka sukeyi saboda tsananin tsaron da aka yiwa littafin. Lokacin da sarauniya sarauniya Larbisa taji wannan batu na littafin TSATSUBA sai hankalinta ya dugunzuma ainun ta rasa abinda ke mata dadi a duniya bayan tayi dogon tunani da nazari saita watsa shela a ko ina a cikin  duniya cewa duk wanda ya samo mata wannan littafin na TSATSUBA shi zata aura kuma zata raba kasarta da dukiyarta ta bashi kaso daya shidai wannan littafi na TSATSUBA duk wanda ya mallakeshi sai ya mulki komai da kowa na duniya hatta dabbobi da tsuntsaye kuwa domin zasu rinka bin duk umarnin da ya basu bisa wannan dalili ne matsafa da sarakai da manyan jarumai suka bazama neman littafin TSATSUBA suka rinka mutuwa a kokarin neman nasa.

.

Abin tambaya a nan shine waye zai iya baiwa sarauniya Larbisa littafin TSATSUBA alhalin yasan cewa idan yana tare da littafin ita kanta zai iya mallakarta kuma zai sami kowace irin dukiya da yake so ko matsayi?

.

Masana da matsafa sun tabbatar da cewa babu wata mai kyan fuska da kyan jiki tamkar gimbiya Larbisa a zamaninta kuma a wannan lokaci data bayar da shelar a nemo mata littafin TSATSUBA shekaranta ashirin daidai a duniya kuma tun tana da shekara goma sha biyu ta hau kan karagar mulki.

.

Sarauniya Larbisa bata da wani buri wanda yafi ta sami magajinta kafin tsufa ya risketa don kada mulkinta ya tafi hannun wanda ba jininta ba kasancewar itace kadai ta rage a irin zuri ar gidansu. Wata rana sarauniya Larbisa na zaune a fadarta ana tafiyar da harkokin mulki kamar yadda aka saba saiga wani almajiri ya shigo yana bara har dakaru sun tareshi zasu koreshi waje sai sarauniya Larbisa tayi musu tsawa suka kyaleshi nan take Larbisa ta mike tsaye daga kan karagar ta taka taje har wajen almajirin ta kama sandarsa ta rike ta dubeshi tace zan baka abinci kaci ka koshi yanzu ya kai wannan tsoho amma ba zaka iya biyana ba da komai domin ni bana bukatar abinci ko dukiya koda gama fadin haka sai sarauniya larbisa ta juya ta ja tsohon har zuwa cikin gidan sarauta. Al amarin da ya baiwa kowa mamaki kenan hatta mutanan gari da sauran masu fada aji saboda ita dai sarauniya larbisa bata kasance mai tausayi da jin kan talakawa ba kuma tana da tsananin rowa bata bayar da abin hannunta face akan bukatarta kawai. 

.

Lokacin da sarauniya Larbisa takai wannan almajiri cikin babban falo na turakarta wanda girmansa yakai na wani gida guda sai tsohon ya zama cikakken dan kauye ya kama kalle kalle domin bai taba tsintar kansa a cikin waje mai ni ima da daula ba irin wannan gaba daya falon a shimfide yake da wata irin dadduma mai tsananin laushi da zarar ka taka daddumar sai kaji kamar zaka nutse a cikinta saboda taushi kujerun dake zagaye a falon gaba daya anyi sune da zinare kuma sun kai kamar guda dari biyu. A tsakiyar falon an ajiye wani katon gunkin tsuntsun dawisu akayi shi da karfen jauhar mai launin kore da rawaya kuma anyi masa wata hikima ruwa na ta zuba a cikin dawisun yana taruwa akan wani katon faranti na lu’u lu’u abin dai akwai ban sha awa da ban al ajabi.

.

A saman rufin falon kuwa wadansu irin fitilu ne sama da guda dubu daya wadanda suma da lu u lu u akayisu sai sheki da walwali suke tayi. Baya ga wannan wani irin kamshi na tashi a cikin falon wanda mutum bai san ko daga ina yake fitowa ba duk inda almajirin ya duba a cikin falon sai yaga kuyangi ne tsala tsala sunata hidimar goge goge da gyare gyare tabbas wannan wuri Ya cika aljannar duniya. Almajirin ya dubi kujerar sai tayi masa kwarjini ainun ya ga cewa shidai bai kasance basarake ba ina shi ina zama akan irin wannan kujera kawai sai ya zauna a kasa dirshan bisa wannan darduma mai taushi koda ganin haka sai sarauniya Larbisa da kuyanginta suka bushe da dariya domin basu taba ganin wanda yayi wannan kauyancin ba. Sarauniya Larbisa ta dubi shugabar kuyangin wacce ake kira da suna HULAIRA tace da ita aje a kawowa bakona duk irin kalar abincin dake gidan nan hulaira tace an gama ya shugabata nan take hulaira ta juya ta fice daga cikin falon ita kuma sarauniya larbisa saita dubi almajirin tace bayan ka huta zan dawo gareka da yamma domin muyi yar hira kafin na sallameka ka tafi saboda kazo mini da bayani wanda yaje fani a cikin wasi wasi da kace idan na ciyar da kai zaka ciyar dani har abada alhalin ni babu abinda na nema na rasa na gada abinci ko dukiya lallai ba zaka tafi ka barni a cikin duhu ba saika wayar mini da kai.

.

Koda gama fadin haka sai sarauniya ta wuce izuwa can cikin turakarta sai data jima tana tafiya sannan ta kule almajirin ya daina hangota nan fa almajirin ya shiga sakar zuci yana mai cewa a ransa wai shin yaya cikin turakar sarauniya zai kasance a kyau da kawatuwa?

.

Lallai dole ne ya ninka nan falon a komai jim kadan da tafiyar sarauniya Larbisa saiga wadansu kuyangi daban su goma sha biyu sun shigo cikin turakar kuma kowacce na

dauke da katon faranti abinci akan kowanne faranti akwai abinci kala shida nan take kuyangin suka ajiyewa almajirin farantin abincin a gabansa suka juya suka fice.

.

Al amarin daya firgita gaba dayan kuyangin dake cikin falon kenan suka fara tunanin anya kuwa wannan almajirin mutunne a iya zamansu a gidan sarautar basu taba ganin

mutumin da ya taba cinye koda kwano daya na abincin kasancewar kwanukan manya ne kuma cike suke taf da abinci sau tari sai mutane biyar sun taru suke iya cinye kwano daya lokacin da almajirin ya gama da abincin farantin dake gabansa sai ya janyo wani farantin ya gwamutsa abincin kwanon shidan akan farantin duka ya kama ci nan da nan ya karar da abincin ya janyo faranti na uku koda ganin haka sai gaba dayan kuyangin suka firgice suka ruga wajen falon a dimauce suna ihu kuma suka tsaya a can bakin kofar falon suna leken almajirin.

.

Abu dai kamar wasa sai da almajirin ya cinye gaba dayan abincin dake kan farantin yayi gyatsa dama an kawo masa ruwan inibi cikin tambulan guda koda ya kafa tambulan din a bakinsa sai yayi masa kurba uku ya zukeshi duka shi kuma wannan tambulan din sau tari idan aka cikoshi da ruwan inibi komai yawan bakin da sukazo gidan basa shanye shi gaba daya sai kaga sun rage wani abu sa adda kuyangi sukaga almajirin ya cinye gaba dayan abinci kuma ya shanye ruwan inibin sai suka kara dimaucewa suka ruga izuwa cikin gidan sarautar suna ihu da fadin cewa tabbas Aljani ne a cikin falon sarauniya ba mutum bane koda jin wannan bushara sai dakarun tsaro na gidan sarautar suka zare makamansu suka ruga zuwa cikin falon sarauniya larbisa suka yiwa almajirin kawanya.

.

Al amarin da ya matukar baiwa almajirin mamaki kenan kuma ya tsorata shi domin bai san laifin da ya aikataba har akazo aka yanyameshi haka.

.

Ana cikin wannan haline sarauniya Larbisa taji wannan abin Al ajabi sai itama ta cika da tsananin mamaki cikin hanzari ta mike tsaye daga kan kujerar da take zaune ta taho cikin falon nata da shigowarta cikin falon ta iske dakarunta sun yiwa almajirin kawanya suna tsuma ba tare da sun afka masa ba ga dukkan alamu suma sun tsorata ne bisa ganin gagarumin aikin da yayi nan take sarauniya larbisa ta dakawa dakarun tsawa suka ja da baya har ta hango almajirin zaune a tsakiyar su yana kyarma cikin alamun tsananin tsoro har ya jike sharkaf da gumi.

.

Al amarin da ya baiwa sarauniya larbisa mamaki kenan nan take ta gamsu a cikin zuciyarta cewa lallai wannan almajiri ba aljani bane mutum ne domin inda aljani ne babu abinda zai sa ya tsorata bisa ganin dakarunta izuwa kansa Larbisa ta dubi dakarun nata da dukkan kuyangin dake cikin falon tace kowa ya fita ya barsu cikin gaggawa suka bi wannan umarnin falon yayi tsit tamkar mutuwace ta gifta.

.

A wannan lokacine sarauniya larbisa ta tashi taje har daf da almajirin ta zauna tana mai yi masa wani irin kallo na rashin yarda tace yakai wannan tsoho bani labarinka ka sanar dani komai bisa gaskiya idan kuwa kayi mini karya ba zaka fita daga nan a raye ba. Lokacin da almajirin yaji wannan tambaya sai yayi ajiyar numfashi nan da nan idanunsa suka ciko da kwalla har hawaye ya zubo masa sannan ya dubi sarauniya yace ni dai sunana HUZAILATUL MARWASU kuma na fito ne daga can kudancin duniya a wata kasa da ake kira MADINATUL SAUWABA mahaifina ya kasance kasurgumin matsafi wanda yayi nisan kwana a duniya domin sai da ya shekara dari hudu da arba in da uku a duniya sannan ya mutu lokacin ina da shekara shida kacal a duniya. Duniya kuma nine dan auta kuma tun ina jariri uwata ta mutu ta barni a wannan lokaci ragowar yan uwana su hudu duk sun haura shekara ashirin sai mai ashirin da yaya wadannan yayye nawa sun taso da hikima gami da saurin daukar ilimin tsafi a wajen ubanmu nan da nan kowannansu ya zamo shahararren boka ni kuwa saina taso da dakikanci duk abinda aka koya mini bana iya yi ko karanta mini dalasiman tsafi mahaifina yayi bana iya biyawa kamar yadda ya biya haka kuma na kasance malalacin gaske bana iya yin aikin komai ko da kuwa sharar gida ne bisa wannan daliline sauran yan uwana suka tsaneni bugu da kari saina taso da tsanancin cin abinci mai yawan gaske amma kuma idan naci na koshi ina iya yin kwana ashirin da daya ban kara cin komai ba sai dai nayi ta shan ruwa wani abin mamaki kuwa shine a tsawon kwana ashirin da dayan bana kawai da bukatar bawali ko bayan gida sai dai ta kai cewa an cinye gaba dayan abincin dake gidanmu wanda mahaifimu ya tanada a rumbu wanda a takaice zamu iya.shekara goma muna amfani dashi duk wani halaiya tawa bata taba sa mahaifina ya tsaneni ba face ma yana dada nuna mini soyayya da janyoni a jikinsa su kuwa yan uwan nawa sai haka yasa suka dada tsanata ya zamana cewa idan mahaifinmu ya aikemu cikin gari ko kasuwa sai suyi mini dukan tsiya akan hanya wani lokacin ma dukan kawo wuka sukeyi mini har sai jama ar gari sun kwaceni sai dai a dawo dani gida jina jina kafin a kawoni gida sai yan uwan nawa su rigani komawa suce da mahaifinmu sun hadune da abokan gabarmu yayan wani bokan garinmu an fafata yaki sau uku hakan na faruwa don haka sai mahaifin nawa ya hanani fita ko ina ya zamana cewa kullum muna tare dare da rana ko barci mahaifina zaiyi sai ya tabbatar da cewar ina kwance akan kirjinsa…

Zan dakata anan sai kuma gobe idan Allah mai kowa da komai ya kaimu a huta lafiya.

Ku Taba Nan Domin Karanta Littafin Tsatsuba Na Biyu Wannan Abdulaziz Sani M/Gini Ya Rubuta.

TSATSUBA

Book 1

Part B

Marubuci Abdul’aziz Sani Madakin Gini

Posting By Abubakar Saleh AlQuyraemey

Domin Samun litattafan Yaƙi Contact 08138873799.

A kullum idan na tuna irin yanayin halittar da na taso ciki na dakikanci lalaci da cin tsiya saina kamu da tsananin bakin ciki nayi ta kuka shi kuwa mahaifin mau sai yayi ta rarrashina yana mai cewa ya kai dana kayi  sani cewa akwai ranar da zaka rabu da duk wadannan matsaloli amma sai a bayan mutuwata bayan kayi wata doguwar tafiya lallai kafin mutuwata zan sanar dakai bangaren da zakaje a cikin duniya domin ka rabu da wannan matsaloli A sannan ne zaka sami wata gagarumar daukaka irin wacce ni kaina ban samu ba kayi hakuri da duk irin musgunawar da yan uwanka zasuyi maka daga nan har izuwa ranar mutuwata domin hakuri naka shine zai kaika izuwa kan tafarkin daukakarka nasan cewa yan uwanka basu da wani buri wanda yafi su hallakaka saboda ya zamana cewa ba zaka mallaki komai ba daga cikin dukiyar dana tara babu yadda basuyi ba don su hallakaka amma sun kasa domin ina baka kariya ta musamman duk abin dake faruwa ayayin da kuka fita kasuwa ina gani daga nan a cikin madubin tsafina duk sa adda kaga jama ar gari sunzo sun ceci rayuwarka daga hannun yan uwanka toba mutane bane sukazo nine na rikide zuwa siffar mutane nazo na muku, wannan bakar  wahalar da kake sha a hannunsu itace alamun samun daukakarka tanan gaba.

.

A duk sa adda mahaifin namu yazo nan a zancensa sai na fashe da kuka nace ya kai abbana yanzu idan ka mutu waye zai iya ci gaba da ciyar dani alhalin yanzu kana ciyar da nine da karfin Sihirin tsafinka ? 

Idan baka nan ya za ayi na tsira daga sharrin yan uwana?

.

Dajin wannan tambaya sai mahaifina yayi murmushi yace nayi maka alkawari ko a bayan raina ba zaka fuskanci matsalar komai ba kuma ba zaka sha wahalar komaiba sannan wahalar ba zata yi dogon lokaci ba.

.

Haka dai mahaifina yaci gaba da rarrashina yana bani mamaki a duk sa adda nake cikin damuwa ko tashin hankali wata rana da farkon dare sai mahaifina ya kamu da matsananncin rashin lafiya har ya kama kumallon jini nan fa muka hadu mu biyar din a kansa a lokacin da hankalina ya yi matukar dugunzuma na fara kuka su kuwa sauran yan uwan nawa ko kadan babu alamar wata damuwa a fuskarsu kawai sai suka kama yake mahaifin namu ya dubi sauran yan uwan nawa yace dasu ku tafi izuwa cikin daji ku nemo mini ganyen bishiyar Suljara Shine kadai abinda za a jika mini nasha na sami sauki koda jin wannan batu sai hankalin yan uwan nawa ya tashi babban cikinsu ya dubi mahaifin namu cikin Alamun matukar damuwa yace yakai abbanmu ka sani cewa bishiyar suljara yana da matukar wuyar samu a duk cikin dazuzzukan garinmu zamu iya kwana a cikin daji muna nemansa dajin haka sai mahaifinmu ya fusata yace shin yanzu wahalar da zaku sha a cikin daji tafi lafiya ta muhinmanci kenan a wajanku idan har ba zaku tafi neman wannan ganye ba yanzu take zan lalata dukkan sirrin tsafin da kuka mallaka kuma ta kone dukkan dukiyata dake cikin gidan nan koda jin wannan batu sai yan uwan nawa suka juya suka fice daga cikin dakin suna gunaguni cikin fishi sai bayan yan uwana sun dade da tafiya daji sannan mahaifina ya mike zaune da kyar sannan ya janyoni izuwa jikinsa ya rungumeni akan kirjinsa kawai sai naji hawayen idanunsa na zuba akan fuskata cikin karfin hali ya budi baki yace yakai dana ka saurara Da kyau ka nutsu kaji jawabin da zan maka idan har ka ka rike abin da zan gaya maka yanzu lallai zaka sami daukakar da tafi tawama kayi sani cewa na aiki yan uwanka ne izuwa daji domin na sami damar da zan sanar dakai babban sirrin dana adana maka a cikin zuciyata tsawon shekara da shekara ka sani cewa tsananin kaunarka da tausayinka da nake ji bisa.yanayin halittar da ka kasance ne yasa na adana maka wannan babban sirri. A yau kuma nan bada dadewa ba wa adina zai cika na bar wannan duniya da zarar kaga na mutu kayi sauri ka shiga cikin turakata ka dafa bakin akwatina na karfe da hannunka na hagu take akwatin zai bude zakaga wata jakar gata a ciki saika dauki jakar ka ratayata a kafadarka ka fice daga gidan nan, kana fita zakaga gidan nan ya nutse izuwa cikin karkashin kasa ya bace bat tamkar bai taba wanzuwa ba awajen, daga nan sai ka juya ka nausa yamma kayi ta tafiya har saika fita daga cikin garin nan ka nausa daji, duk iya tsawon tafiyar da zakayi ka da kayi wage ko da zakaji sukuwar giwaye a bayanka, duk inda ka gamu da mutum ko aljan kada kayi masa magana kuma idan yayi maka magana kada ka amsa ba zaka riski wani gari ba sai bayan kwana ashirin da daya , kana shiga garin ka bude wannan jaka zaka iske babu komai a cikinta face dinare mai yawan gaske saika nemi abinci mai yawa wanda zai isheka ka koshi ka siya amma ka tabbata cewa a boye zaka cinye wannan abinci ba a gaban jama ba, kada ka kuskura ka kwana a wannan gari da zarar ka koshi saikayi harama ka sayi doki kahau kaci gaba da tafiya ina mai tabbatar maka da cewa saika shekara Arba’n da biyar kana wannan tafiya kana ta keta dazuzzuka da birane a sannane zaka cika shekara hamsin da daya a duniya kuma a wannan lokacine guzurin dake cikin jakarka zai kare, ka iso wani babban birni inda wata mashahuriyar sarauniya ke mulki. A sannan ne yunwa zata gallabeka don haka ka nemi hanyar gidan sarauta kana zuwa fada ka wuce kai tsaye zuwa gaban karagar mulkin kana mai yin bara kana cewa waye zai ciyar dakai yanzu ni kuwa na ciyar dashi iya rayuwarsa?

.

Tabbas wannan sarauniya zata sa a baka abinci da zaka koshi bayan nan ka tambayeta babban burinta na duniya lallai zata zo maka da batun wani littafi waishi TSATSUBA lallai kaine zakayi jagora bisa tafiyar da za ayi ta neman wannan littafi tabbas za a samu wannan littafi har bukatar wannan sarauniya ta biya a sannan ne zaka sami lada mai tsoka daga wajan sarauniyar kamar yadda tayi alkawarin zata bayar ga wanda duk ya samo mata littafin TSATSUBA,

.

A cikin tafiyar da zakuyine zaka sami daukaka irin wacce babu wani boka da ya taba samunta har duniya ta shube ba za a manta da kaiba

a cikin tarihi, amma ka sani cewa zaka sha tsananin ukuba a cikin wannan tafiya kuma zakuga abubuwan Al’ajabi da yawa.

.

Sa adda mahaifina yazo nan a zancensa sai na cika da Tsananin mamaki na dubeshi cikin alamun rashin fahimta nace ya kai abbana yanzu nida nake malalaci matsoraci kuma dakiki ya za ayi na iya jagora a cikin wannan gagarumar tafiya alhalin ma ban san inda za a je ba asamo wani littafi wai shi TSATSUBA?

.

Yayin da mahaifina yaji wannan tambaya saiya ya yunkura domin ya bani amsa amma sai tari ya sarkeshi yaci gaba da aman jini, Al amarin daya dugunzuma hankalina kenan na dimauce naci gaba da matsanancin kuna ina mai kankame mahaifina, daga can saiya daina wannan kumallon sannan ya janyeni daga cikin jikinsa muka fuskanci juna sosai a lokacin da idanunsa ke lumshewa yana budewa da kyar ya budi baki yace yakai dana abin kaunata kayi sani cewa muddin kana tare da wannan jaka ta guzurinka babu abinda zai gagareka kuma babu wani tsautsayi da zai saka rasa rayuwarka.

.

Sai kun shekara daya da rabi sannan zaku isa inda littafin TSATSUBA yake kuma wannan jaka taka itace zata rinka yi muku jagora , ba zaku sami nasarar zuwa inda wannan littafi yake ba sai kun hadu da wadansu jarumai guda hudu, uku mata ne daya namijine ma abota wani addini da ake kira musulunci, wannan jaka taka itace zata kaiku wajen wadannan jarumai guda hudu, sa adda naji wannan batu saina kara cika da mamaki bisa yadda za ace jaka zatayi magana a cikin wannan doguwar tafiya alhalin bata kasance abu mai raiba kuma ba magana takeyi ba har na budi baki zan tambayi mahaifina ta yadda wannan jaka zatayi mana jagora a cikiin tafiyar sai naji gaba dayan jikinsa ya sandare kamar gunki idanunsa kuwa sun kafe, cikin dimauta na girgizashi amma ko motsi baiyiba, kawai saina rungumeshi na fashe da kuka cikin sauri na maida shi shimfidarsa na kwantar dashi sannan na ruga zuwa cikin turakarsa.

.

Da shigata sai naje na dafa bakar akwatin mahaifin namu da hannu na na hagu faruwar hakan keda wuya sai akwatin ya bude nayi arba da wata jaka wadda akayi ta da fatar damisa koda na dauki jakar sai naji tana da dan nauyi kawai saina rataya jakar a kafadata na fita da sauri daga cikin gidan, ai kuwa ina fita sai naga gidan namu ya kama nutsewa cikin karkashin kasa har saida ya Lume gaba daya. A dai dai wannan lokacine hawaye ya zubo mini saboda na san cewa shi kenan na rabu da mahaifina kasarmu da yan uwana har abada yanzu ne zan fuskanci sabuwar rayuwa irin wacce ban taba tsintar kaina ba a ciki kamar yadda mahaifina yayi mini bayanin tafiyar da zanyi da sharuddan daya gindaya mini a cikinta banyi wasa da guda daya ba haka naci gaba da tafiya babu waige kuma babu magana hakika naga abubuwan Al’ajabi da yawa a cikin tafiyar tawa kuma na sami ilimi mai yawa da wayewa akan sanin mutane da al adu iri iri gaba dayan rayuwa ta ta shekara arba in da biyar din a cikin tafiya ce ta kare na shiga dazuzzuka iri iri masu mugun hadari amma duk bala in da na shiga da duk masifar da ta tunkaroni sai naga na tsira daga sharrinta, babban abinda ya bani kariya kuwa ba komai bane face wannan jakar sihiri ta Abbana sau tari sai naji wani abu mai rai yana ta motsi a cikin jakar harma nakanji kamar yana magana amma idan na bude jakar sai naga babu komai a ciki face tarin wannan zinare haka kuma idan na kasa kunnena akan jakar sai naji tsit babu wani surutu a ciki a ranar da na iso wannan birni ne guzurina ya kare na kamu da tsananin yunwa

na tunkari wannan gidan sarautar sai naji wani abu na tsalle a cikin jakar sihirin kawai saina bude jakar duk da cewa ina da yakinin ba zanga komai ba bisa mamaki sai nayi arba da wani dan mitsitsin Aljani mai rafkeken kai wanda girman jikinsa bai wuce na fara ba cikin tsananin firgici na yarda jakar a kasa na ruga da guda ina waige, sai da na iso daf da kofar gidan sarautar nan sai kawai naga wannan jaka ta baiyyana a gabana tsaye cikin iska cikin firgici na yunkura da nufin na juya da baya kawai sai naji an rikeni gam na kasa koda motsa dan yatsanan hannuna take naga wannan dan guntum Aljani ya baiyana akan hannuna yana mai kyalkyala dariya wani abin mamaki Shi ne mutane nata kai kawo a gabana amma bamai iya ganin Aljanin kuma ba a jin dariyarsa daga can sai aljanin ya murtuke fuskarsa yace yakai HUZALLATUL MARWASU kayi sani cewa yanzu kai ne ubangijina tunda mahaifinka ya bar duniya lallai babu abinda zai rabani dakai face mutuwa sunana SUBAURATU IBN KIMASASA, nine jikan sarkin boyaen Aljanu na farko na dari tara da casa’in da tara nine kadai a cikin fadin duniyar nan nasan inda wannan littafin TSATSUBA yake wanda mahaifina ya rubuta kuma ni kadai ne na rage daga cikin zuri ar gidanmu gaba daya daga yau ka saki jiki dani domin ni ne kadai zan saka a tafarkin da zaka zamo gwarzon jarumi ka daina mugun cin abincin kuma ka sami daukakar dako mahaifinka bai samuba.

Ku Taba Nan Domin Karanta Littafin Tsatsuba Na Biyu Wannan Abdulaziz Sani M/Gini Ya Rubuta.

TSATSUBA

Book 1

Part C

Marubuci Abdul’aziz Sani Madakin Gini

Posting By Abubakar Saleh AlQuyraemey

Domin Samun litattafan Yaƙi Contact 08138873799.

Yanzu saika mayar dani cikin wannan jaka da ke hannunka domin idan na haura rabin sa a a waje iskar duniya zata zamo sanadin ajalina saboda tsananin tsufana.

.

Koda gama fadin hakan sai nayi sauri na dauke aljani subauratu da yan yatsan hannuna biyu ina karkarwar jini na mayar dashi cikin wannan jaka sannan na rataya jakar akan kafadata ka tsaya na shigo cikin wannan gidan sarauta, lokacin da Huzallatul Marwasu yazo nan

a labarinsa sai sarauniya Larbisa ta cika da tsananin mamaki da farin ciki a karon farko a rayuwarta sai ta kama Huzallatul Marwasu da hannayanta biyu ta rungumeshi tana mai cewa tabbas kaine wanda zaka share mini hawayena saida Larbisa da huzallatul marwasu suka shafe sa a bakwai suna hira a wannan rana tare sukaci abincin dare sannan tasa aka kaishi masauki kuyangi sukayi masa wanka aka caba masa ado abinda ya baiwa larbisa mamaki shine lokacin da sukaci abincin loma daya jal Huzallatul Marwasu yayi yace ba zai iya cin komai ba.

.

Sa adda Huzallatul Marwasu ya tsinci kansa a cikin kasaitaccen daki bisa kan luntsumemen gida na alfarma ga kyawawan kuyangi sunayi masa tausa sai ya kama kyalkyala dariyar farin ciki ba sassauci tamkar sabon mahaukaci.

.

A wannan rana dai bai rintsa ba saboda farin ciki kashe gari da sassafe sarauniya larbisa ta fito fada ta zauna kuma ta tura aka kirawo dukkanin fadawanta asannan ne kuma ta tura aka kirawo Huzallatul Marwasu koda aka je sai aka iske huzallatul marwasu yana ta faman shara bacci bai tashi ba da aka koma aka shaidawa sarauniya larbisa saitace a kyaleshi yaci gaba da barcinsa har saiya farka da kansa. Al amarin da ya baiwa kowa mamaki kenan domin ba a taba ganin sarauniya larbisa ta girmama makaskanci ba haka dai Sarauniya Larbisa da fadawanta sukaci gaba da jiran Huzallatul Marwasu har saida ya farka da kansa daga barci yayi wanka ya kimtsa sannan akayi masa jagora izuwa fadar koda shigowar huzallatul marwasu sai gaba dayan fadawan larbisa suka kura masa idanu suka cika da tsananin mamaki domin basu shaida shiba cewar shine wannan almajirin da yazo yai bara yana neman abin da zaici cikin farin ciki Larbisa ta mike tsaye ta taryo Huzallatul Marwasu ta jawoshi har zuwa kan karagarta ta zaunar dashi sannan ta dubi yan majalisarta cikin natsuwa tace yaku yan majalisar birnin DAULATUL LABARUS kuyi sani cewa wannan Almajiri da ya Lume gaba daya. A dai dai wannan lokacine hawaye ya zubo mini saboda na san cewa shi kenan na rabu da mahaifina kasarmu da yan uwana har abada yanzu ne zan fuskanci sabuwar rayuwa irin wacce ban taba tsintar kaina ba a ciki kamar yadda mahaifina yayi mini bayanin tafiyar da zanyi da sharuddan daya gindaya mini a cikinta banyi wasa da guda daya ba

haka naci gaba da tafiya babu waige kuma babu magana hakika naga abubuwan Al’ajabi da yawa a cikin tafiyar tawa kuma na sami ilimi mai yawa da wayewa akan sanin mutane da al adu iri iri gaba dayan rayuwa ta ta shekara arba in da biyar din a cikin tafiya ce ta kare na shiga dazuzzuka iri iri masu mugun hadari amma duk bala in da na shiga da duk masifar da ta tunkaroni sai naga na tsira daga sharrinta, babban abinda ya bani kariya kuwa ba komai bane face wannan jakar sihiri ta Abbana sau tari sai naji wani abu mai rai yana ta motsi a cikin jakar harma nakanji kamar yana magana amma idan na bude jakar sai naga babu komai a ciki face tarin wannan zinare haka kuma idan na kasa kunnena akan jakar sai naji tsit babu wani surutu a ciki a ranar da na iso wannan birni ne guzurina ya kare na kamu da tsananin yunwa na tunkari wannan gidan sarautar sai naji wani abu na tsalle a cikin jakar sihirin kawai saina bude jakar duk da cewa ina da yakinin ba zanga komai ba bisa mamaki sai nayi arba da wani dan mitsitsin Aljani mai rafkeken kai wanda girman jikinsa bai wuce na fara ba cikin tsananin firgici na yarda jakar a kasa na ruga da guda ina waige, sai da na iso daf da kofar gidan sarautar nan sai kawai naga wannan jaka ta baiyyana a gabana tsaye cikin iska cikin firgici na yunkura da nufin na juya da baya kawai sai naji an rikeni gam na kasa koda motsa dan yatsanan hannuna take naga wannan dan guntum Aljani ya baiyana akan hannuna yana mai kyalkyala dariya wani abin mamaki. Shine mutane nata kai kawo a gabana amma bamai iya ganin Aljanin kuma ba a jin dariyarsa daga can sai aljanin ya murtuke fuskarsa yace yakai 

HUZALLATUL MARWASU kayi sani cewa yanzu kai ne ubangijina tunda mahaifinka ya bar duniya lallai babu abinda zai rabani dakai face mutuwa sunana SUBAURATU IBN KIMASASA, nine jikan sarkin boyaen Aljanu na farko na dari tara da casa’in da tara nine kadai a cikin fadin duniyar nan nasan inda wannan littafin TSATSUBA yake wanda mahaifina ya rubuta kuma ni kadai ne na rage daga cikin zuri ar gidanmu gaba daya daga yau ka saki jiki dani domin ni ne kadai zan saka a tafarkin da zaka zamo gwarzon jarumi ka daina mugun cin

abincin kuma ka sami daukakar dako mahaifinka bai samuba.

.

Yanzu saika mayar dani cikin wannan jaka da hannunka domin idan na haura rabin sa a a waje iskar duniya zata zamo sanadin ajalina saboda tsananin tsufana koda gama fadin hakan sai nayi sauri na dauke aljani

subauratu da yan yatsan hannuna biyu ina karkarwar jini na mayar dashi cikin wannan jaka sannan na rataya jakar akan kafadata ka tsaya na shigo cikin wannan gidan sarauta, lokacin da huzallatul marwasu yazo nan a labarinsa sai sarauniya larbisa ta cika da tsananin mamaki da farin ciki a karon farko a rayuwarta sai ta kama huzallatul marwasu da hannayanta biyu ta rungumeshi tana mai cewa tabbas kaine wanda zaka share mini hawayena saida larbisa da huzallatul marwasu suka shafe sa abakwai suna hira a wannan rana tare sukaci abincin dare sannan tasa aka kaishi masauki kuyangi sukayi masa wanka aka caba masa ado abinda ya baiwa larbisa mamaki shine lokacin da sukaci abincin loma daya jal huzallatul marwasu yayi yace ba zai iya cin komai ba sa adda huzallatul marwasu ya tsinci kansa a cikin kasaitaccen daki bisa kan luntsumemen gida na alfarma ga kyawawan kuyangi sunayi masa tausa sai ya kama kyalkyala dariyar farin ciki ba sassauci tamkar sabon mahaukaci.

.

A wannan rana dai bai rintsa ba saboda farin ciki kashe gari da sassafe sarauniya larbisa ta fito fada ta zauna kuma ta tura aka kirawo dukkanin fadawanta asannan ne kuma ta tura aka kirawo huzallatul marwasu koda aka je sai aka iske huzallatul marwasu yana ta faman shara bacci bai tashi ba da aka koma aka shaidawa sarauniya larbisa saitace a kyaleshi yaci gaba da barcinsa har saiya farka da kansa Al amarin da ya baiwa kowa mamaki kenan domin ba a taba ganin sarauniya larbisa ta girmama makaskanci ba haka dai sarauniya larbisa da fadawanta sukaci gaba da jiran huzallatul marwasu har saida ya farka da kansa daga barci yayi wanka ya kimtsa sannan akayi masa jagora izuwa fadar koda shigowar huzallatul marwasu sai gaba dayan fadawan larbisa suka kura masa idanu suka cika da tsananin mamaki domin basu shaida shiba cewar shine wannan almajirin da yazo yai bara yana neman abin da zaici cikin farin ciki larbisa ta mike tsaye ta taryo huzallatul marwasu ta jawoshi har zuwa kan karagarta ta zaunar dashi sannan ta dubi yan majalisarta cikin natsuwa tace yaku yan majalisar birnin DAULATUL LABARUS kuyi sani cewa wannan Almajiri da yaZo ya nemi abincin da zaici a wajena shine wanda zai cika mini babban burina na duniya koda jin wannan batu sai fadawan suka sake cika da mamaki larbisa taci gaba da bayani tana mai cewa yaku yan majalisata ina so ku sani cewa na taraku ne a nan domin na sanar daku cewanan da kwana uku zanyi shiri nida wannan bako nawa mai daraja domin mu yi tafiya izuwa neman abinda zai biya mini bukatata saboda haka zan bar amanar kasata a hannunku kuci gaba da tafiyar da mulki kamar yadda nake gudanar dashi ku sani cewa ina daga can inda nake zan rinka ganin duk abinda kuke yi duk wanda yayi mini wani abu ba dai dai ba sai dai a wayi gari aga gawarsa idan akwai wani mai korafi a cikinku bisa wannan hukunci da na yanke sai yayi yanzu naji?

.

Lokacin da fadawan Sarauniya Larbisa sukaji wannan batu sai sukayi shiru suka kama kallon junansu aka rasa wanda zaice kala koda ganin haka sai larbisa ta sallami dukkanin fadawan nata suka fita suka barsu su biyu kacal ita da almajiiri Huzallatul marwasu tsawon yan dakiku da fitar fadawan sai larbisa ta dubi huzallatul marwasu tace yakai dan boka mai daraja ina son ka fito da in aljani sabauratu ibn kimasasa daga cikin jakarka ta sihiri domin ina da wadansu tambayoyi masu matukar muhimmanci da nake son zanyi masa dangane da wannan gagarumar tafiya da zamuyi koda jin wannan batu sai huzallatul marwasu ya fiddo jakar sihirinsa daga cikin babbar rigar jikinsa ya ajiyeta a gabansa sannan ya bude ya zura hannunsa a ciki ya dauko aljani subauratu bn kimasasa ya ajiyeshi a kan dan karamin tebur na zinare dake gaban sarauniya larbisa.

.

Nan take subauratu yayi sujjada ga sarauniya larbisa yana mai bude fukafukansa ya kwashi gaisuwa sannan yace da ita yake sarauniyar duniya fadi duk irin tambayoyin da kike son ki gabatar dasu a gareni ko kuwa adadin su yakai na yawan gashin dake jikin rago ko tinkiya domin babu wata iska anan wacce zata dami tsufana. Lallai zan baki amsoshin tambayoyinki ko da kuwa zan kwana dubu a zaune ina yi miki jawabinsu koda jin wannan batu sai sarauniya larbisa ta bushe da da dariya sannan tace aini tambayoyina guda uku ne kacal tambaya ta farko itace naji Huzallatul marwasu yace abokan tafiyarmu izuwa inda zamu samo littafin Tsatsuba su hudu ne kuma ukun cikinsu matane na hudun kuma namijine to wai shin menene amfanin kowanne daya daga cikinsu a cikin wannan tafiya kuma a wane garuruwa zamu riskesu, 

.

Tambaya ta ta biyu itace akan wane dalili wadannan abokan tafiya tamu su hudu zasu yarda suyi mana rakiya zuwa wannan tafiya mai tsananin hadari?

.

Tambaya ta ta uku itace ta karshe shin kasan dalasiman tsafin da za a karanta a lalata gaba dayan tsafin dake cikin littafin tsatsuba?

.

Sa adda Aljani saubaratu yaji wadannan tambayoyi guda uku daga bakin sarauniya larbisa sai yayi shiru yana mai kura mata idanu cikin Al ajabi ba wani abu bane ya sa yayi shiru ba kuma ya kura mata idanu ba face tsananin kyawunta da ya dimautashi.

.

Koda larbisa ta fahimci halin da Aljani saubaratu ya shiga saita daka masa tsawa ta ce shin zaka bani amsar tambayoyina ne ko kuwa zakaci gaba da kallona ne har saika gaji nan take Aljani saubaratu ya shiga taitayinsa ya dubi larbisa cikin nutsuwa ya ce ki gafarceni ya shugabata kiyi sani kinyi mini tambayoyi ne masu matukar mahimmanci a cikin wannan tafiyartamu kuma wadanda zasu dauki dogon lokaci ina yi miki bayaninsu to nima jin wannan tambayoyi yasa zan dakata sai kuma gobe idan mai duka ya kaimu, a huta lafiya.

Ku Taba Nan Domin Karanta Littafin Tsatsuba Na Biyu Wannan Abdulaziz Sani M/Gini Ya Rubuta.

TSATSUBA

Book 1

Part D

Marubuci Abdul’aziz Sani Madakin Gini

Posting By Abubakar Saleh AlQuyraemey

Domin Samun litattafan Yaƙi Contact 08138873799.

.

.

Da farko dai abokin tafiyarmu wanda zamu fara tafiya nema ba wani bane face JARUMA SHUMAIRA yar mafarauci IMSHAL, a halin yanzu duk duniya babu wani mahaluki wanda yafi shumaira ibn imshal sanin sirrin daji da iya farauta da kuma juriyar wahala kafin mu isa kogon kitabul sihir inda aka ajiye littafin tsatsuba sai mun keta ta cikin wadansu dazuzzuka guda uku a cikin daji na farko sai mun shafe wata shida muna tafiya sannan zamuje karshensa,

.

A cikin wannan daji wanda aka yiwa lakabi da shajarul shaljuma akwai

mugayen dabbobi da mugayen tsuntsaye wadanda kaifi da tsini baya tasiri a jikinsu hakama tsafi baya aiki a kansu babu abinda zai ceci mutum daga sharrinsu face wanda ya san sirrinsu kuma ya kware a iya farauta gami da jurewa wahala lallai idan babu jagorancin jaruma Shumaira bamu isa mu ratsa ta cikin dajin shajarul shaljuma ba a raye

.

Abokin tafiyarmu na biyu kuwa ba kowa bane face jaruma Larifat ma abociyar basira da hangen nesa gami da jiyo takun sawu komai nisansa Daji na biyu wanda ke gaban dajin Shajarul shaljun ana kiransa da suna Ujurul majnan babu komai a cikin wannan daji face wadansu irin gabza gabzan dodanni masu cin naman mutane da na aljanu da dabbobi suna da kaifin basira wajan dana mugayen tarkuna kuma suna da tsananin gudun tsiya yadda komai tazarar dake tsakaninsu da mutum suna iya cinmmasa jaruma larifat ce kadai zata iya gano duk irin tarkunan da wadannan dodanni suka dana kuma ta iya jiyo sautin sawayen dodannin suke sannan ta iya jiyo sawayensu a duk sa adda suka rugo don kawo farmaki.

.

Daji na uku wanda ke gaban dajin Ujurul majnan ana kiransa da suna Darul Maut Babu komai a cikin darul maut face wadansu mugayen kunamai da macizai bakake wadanda da zarar sun sami nasarar sarar mutum ko harbinsa sau daya take jikinsa ke zagwanyewa ya narke Abokiyar tafiyarmu ta uku itace jaruma Lubaina Yar sadauki Sulzainu Jaruma lubaina ce kadai zata iya yakar wadannan kunamu da macizai ta hanasu cutar damu saboda duk duniya babu wani jarumi mai zafin namanta kuma tana da wata rantsatstsiyar takobi da babu abin da bazata iya tsargeshi ba koda kuwa dutse ne ko karfe, muna fita daga cikin dajin darul maut Bayan tafiyar wata Hudu zamu riski Kogon kitabul sihir inda aka ajiye littafin tsatsuba.

.

Ya shugabata kiyi sani cewa shiga cikin kogon kitabul sihir dai dai yake da mutum ya siyi ajalinsa da kudinsa saboda tsananin masiful dake cikinsa da kuma irin gagarumin tsaron da aka yiwa littafin tsatsuba babu wanda zai iya samun nasarar shiga har cikin kogon kitabul sihir.ya isa har inda littafin tsatsuba yake a raye kuma cikin kuzari face jarumi Ruhaisu ibn Zaiyanu daga Sarkin Birnin Kufa.

.

A halin yanzu duk duniya babu wani jarumi mai karfin damtsensa sannan kuma yana da tsananin sa a da rabo bisa dukan abinda yasa a gabansa a yanzu haka yana cikin tsananin bakin ciki bisa mutuwar masoyiyarsa wacce yake tsananin kauna fiye da komai a duniya, duk da cewa kama da wane bata wane. Ya shugabata ni ina da tabbavin cewar zaki iya yaudarar jarumi Ruhaisu da tsananin kyawunki ki nuna masa soyayya da haka ne kadai zaki iya ribatarsa ya amince yayi wannan tafiya har ya shiga cikin kogon kitabul sihir ya dauko mana littafin tsatsuba.

.

Lokacin da Aljani subauratu yazo nan a zancensa sai sarauniya larbisa tayi shiru tana mai sunkui da kanta kas ta fada cikin kogin tunani mai zurfi har izuwa tsawon wani dan lokaci daga can kuma sai ta dago kanta ta dubi Aljani subauratu tana mai ajiyar zuciya tace yakai subauratu kayi sani cewa hakika kazo mini da babban al amari mai wuyar fahimta da gamsuwa wanda dole sai dai mutum yayi kundunbala ya aikata shi ni kam babu gudu kuma babu ja da baya a cikin wannan Al amari amma ina da sauran tambaya guda.daya rak a gareka yanzu wacce idan ka gamsar dani da amsarta bani da sauran fargaba tambayar tawa kuwa itace tayaya zamu hada wadannan abokan tafiya tamu su hudu a cikin kankanin lokacin Alhalin kowannansu yana can wani bangaren daban na duniya har muyi wannan tafiya tare dasu wacce takai ta tsawon shekara guda?

.

Koda jin wannan tambaya sai Aljani subauratu ya kyalkyale da dariya , lokaci guda kuma ya hada rai yace ai riskar wadannan jarumai hudu a cikin yini daya jal a wajena dai dai yake da shan ruwa a gareki makurwa daya don haka ki kwantar da hankalinki kawai ki fara shirye shiryen wannan tafiya.

.

Koda jin wannan batu sai fuskar sarauniya larbisa ta fadada da murmushi bata san sa adda ta kama kyalkyala dariya ba koda ganin haka sai tsoho huzallatu marwasu da Aljani subauratu ma suka tayata kyalkyala dariyar… Kamar yadda sarauniya larbisa ta fada haka al amarin ya kasance wato a cikin kwanaki uku dai dai suka kammala dukkan tanadi na wannan tafiya ita da tsoho huzallatul marwasu suka hau bisa wadansu ingarmun dawakai guda biyu sannan aka debi dakaru mutum arba in kacal tare da kuyangi goma masu yi mata hidima gami da isashshen guzuri na abinci da dinare mai yawa aka kama hanya aka fice daga cikin birninta bayanta yiwa ta yiwa fadawanta da jama arta sallama akan cewar ba zata dawo ba sai bayan shekara guda sarauniya larbisa tayi shiga ne ta kayan yaki masu matukar kyau da kwarjini kuma ta rufe fuskarta da wani bakin kyalle idanunta kadai ake gani shi kuwa tsoho huzallatul marwasu kaya na alfarma aka bashi ya sanya irin na sarakai kai kace ma shine da mulkin ba Larbisa ba lokacin da wannan tawaga ta shafe sa a uku ana tafiya a cikin daji ba tare da sanin inda aka dosa ba kuma dama larbisa ce akan gaba saitaja linzamin dokinta ta tsaya cak, Al amarin da ya baiwa huzallatul marwas da sauran abokan tafiyar mamaki kenan kowa ma ya tsaida nasa dokin, huzallatul marwas ya risina a gareta cikin girmamawa yace.ya shugabata lafiya kuwa kika tsayar mana da tafiyarmu a nan?

.

Koda jin wannan tambaya sai sarauniya larbisa ta dakawa tsoho huzallatul marwas tsawa tace akan wane dalili zamu ci gaba da tafiyar da bamu san inda muka dosa ba ka yiwa Aljani Sabauratu ibn kimasasa magana ya gaya mana inda zamu fara dosa domin nemo abokin tafiyarmu koda jin wannan batu sai huzallatil marwas ya bugi jakar hannunsa take aljani subauratu yayi magana yace ku nufi kudu zamu gajarce muku tafiyar wata uku izuwa yini biyu da rabi inda zaku

riski Dajin Falmaz anan ne inda jaruma shumaira take wacce ita ce kadai zata iya wucewa damu ta cikin dajin shajarul Shaljum a saboda kwarewarta a iya farauta sanin sirrin daji dakuma jurewa wahala lallai kusan yadda zaku lallami jaruma shumaira a kan ta amince da yin wannan tafiya tare damu kada ku nuna mata isa ko iko ko dukiya domin in saboda sune ba zata amince ba koda gama fadin hakan sai aljani subauratu yayi shiru ba kara cewa uffan ba nan take sarauniya larbisa ta bayar da umarni aka sauya akalar tafiya aka durfafi kudu aka ci gaba da tafiya ba sassauci bisa mamaki sai kowa yaga tafiyar tana matukar yin sauri fiye da hasashen mai hasashe kai kace akan isaka suke tafiyar ba bisa doron kasa ba nan da nan suka wuce dazuzzuka da yawa har magariba ta riskesu  basu hadu da wani mugun abu ba a sannan ne sarauniya ta bayar da umarnin a tsaya a yada zango domin A ci abinci a huta nan take kuwa akabi wannan umarnin bayan an kafa tantuna an dafa abinci sai sarauniya larbisa ta kirawo tsoho huzallatul marwas izuwa cikin tantinta domin suci abinci tare koda jin wannan tayi sai huzallatul marwas ya risina cikin girmamawa yace ya shugabata ashe har kin manta da ka idata? Ai idan har naci na koshi ba zan sake bukatar abinci ba sai bayan kwanaki ashirin da biyar sai dai kawai nayi ta shan ruwa koda jin wannan batu sai larbisa tayi murmushi tace tabbas haka zancenka yake na sha afat ne amma duk da haka bana son kadaici a yanzu zauna ka debe mini kewa cikin murna tsoho huzallatul marwas ya zauna a gefe guda a lokacin da sarauniya larbisa ta mike tsam ta kwabe kayan yakin dake jikinta ta ajiyesu a gefen shimfidarta ta alfarma ya rage daga ita sai wata riga mai shara shara a jikinta wacce ta baiyana dukkan surar jikinta.

.

Koda tsoho huzallatul marwas yayi arba da wannan kyakkyawar sura ta sarauniya larbisa sai ya rude ya dimauce har kwallar takaici ta ciko a idanunsa. A cikin ransa yace kash amma mazan duniya sun yi asara da basu mallaki wannan kyakkyawar mace ba tabbas inda ni saurayi ne kuma jarumi mai jini a jika to ko da zan rasa rayuwata sai nayi iya kokarina wajen ganin na mallaki wannan sarauniya ta kowane hali

..

Zan dakata anan sai Allah ya kaimu gobe zamu ci gaba kada ku manta da comments, likes da sharing domin hakan shi zai ƙara mana ƙwarin gwiywa.

TSATSUBA

Book 1

Part E

Marubuci Abdul’aziz Sani Madakin Gini

Posting By Abubakar Saleh AlQuyraemey

Domin Samun litattafan Yaƙi Contact 08138873799.

.

https://www.facebook.com/AlQuyraemey360

.

Haka dai tsoho huzallatul marwas ya ci gaba da zancen zuci gami da sambatu har sarauniya larbisa ta zauna tana mai harde kafafunta a gaban kwanukan abincin dake gabanta ta fuskance shi, koda tasa hannu ta debo loma guda ta bude baki, huzallatul marwas yayi arba da kyawawan hakoranta masu tsananin kyau da haske sai ya sake dimaucewa fiye da ko yaushe bai san sa adda kafafunsa suka kasa daukar nauyin jikinsa ba ya zame kasa kawai sai ji yayi sarauniya larbisa ta kece da dariya, cikin sauri tsoho huzallatul marwas ya mike zaune yana mai zazzaro idanu ya dubeta yace ya shugabata ina dalilin yin wannan dariya taki.

..

Koda jin wannan tambaya sai larbisa ta hade fuska kamar zatayi kuka sannan ta ce yakai wannan tsoho kayi sani cewa ina sane na baiyana surar jikina a gareka ba don komai ba sai domin na tabbatar da abin

da bokaye suka fada mini idan gaskiya ne cewar babu wani da namiji da zai ganni bai rude ba saboda kyawuna kaine namijin farko a duniya da ya taba ganin wannan jiki nawa kuma kaima na yarje maka hakanne saboda ka manyanta a kaina tunda ka isa ka haifi kamata yau shekara goma sha tara kacal a duniya kuma gashi babu abin da ban mallaka ba najin dadin duniya tunda gashi ina sarauta ta birnin da babu kamarsa a duniya sannan ina da dukiya mai tsananin yawan da ni kain ban san iyakarta ba abin da ya rage mini kawai shine na sami abokin rayuwa wato mijin da zan aura domin na sami magaji bokaye sun tabbatar mini da cewar ba zan taba haihuwa ba har sai bayan na lalata duk sihirin tsafin da yake cikin littafin tsatsuba bisa wannan dalili ne na ki yarda nayi soyayya da wani da namiji a rayuwata har sai bayan wannan buri nawa ya cika. Abinda nake tsoro shine kada soyayya tasa idanuna su rufe har nayi aure ba tare da na lalata sihirin littafin tsatsuba ba kaga kenan ba zan taba samun haihuwa ba..

.

Lokacin da sarauniya larbisa tazo nan a jawabinta sai tsoho huzallatul marwas yaji ya kamu da tsananin tausayinta cikin alamun tausayawa da murmai mai sanyi ya dubeta ya ce ya shugabata hakika akwai tausayi a cikin lamarinki kuma samun biyan bukatarki ba abune mai sauki ba sannan ina mai shawartarki daki taka tsantsan da wannan kalma ta soyayya domin abace mai hadarin gaske duk da cewar kin danne zuciyarki kin hanata yin soyayya yanzu nan gaba zata iya tankwaraki domin shi so abune wanda baya sallama kuma baya iso zai iya mamayarki a lokaci guda kamar yadda barci yake sace mutum

koda jin wannan batu sai sarauniya larbisa ta bushe da dariya har ta tafa hannayanta.

.

Al amarin da yayi matukar baiwa huzallattul marwas mamaki kenan daga can sai sarauniya larbisa ta nutsu ta daina dariyar ta dubeshi tace ni sarauniya larbisa na cika maka baki babu wani da namiji a wannan doron kasa wanda zai burgeni har na kamu da son sa saboda na tabbatar da cewar duk abinda yake takama dashi na fishi walau kyau, jarumtaka, mulki da dukiya yayin da huzallatul marwas yaji haka sai yayi murmushi yace ya shugabata abin da yasa kika fadi haka akwai kuruciya a tare dake kuma bakisan menene so ba to ki sani cewa shi so na gaskiya babu ruwansa da kyau ko matsayi abu ne kawai na haduwar jini wanda mutum ko aljan baya iya hadashi ko ya rabashi babu wani mai misali ko mai hange wanda zai iya tantance miki karfinsa ko yanayinsa face wanda ya tsinci kansa a cikinsa koda huzallatul marwas yazo nan a zancensa sai ran sarauniya Larbisa ya baci bata san sa adda ta daka masa tsawa ba ta umarceshi da ya tashi ya fice daga cikin tantinsa.

.

Cikin firgita da biyayya tsoho huzallatul marwas ya risina yace ki gafarceni ya shugabata lallai nayi kuskure.

.

Nan take ya mike tsaye da sauri ya juya ya fice daga cikin tantin amma a cikin zuciyarsa dariya yake yiwa sarauniya larbisa yana mai cewa hakika yaro man kaza ne bai san rana ba sai ta gasashi da sannu zaki san cewa wanda duk ya rigaka kwana dole ne ya rigaka tashi a wannan wuri da aka yada zango aka kwana sai kashe gari da safe bayan anyi kalaci sannan akayi shiri aka ci gaba da tafiya ba sassauci

tun da aka fara wannan tafiya sarauniya larbisa bata kara cewa uffan ba kuma fuskarta a murtuke take ko kadan babu annuri alamar cewa tana cikin fishi.

.

Al amarin da ya dugunzuma hankalin dakarunta da kuyanginta kenan shi kuwa tsoho huzallatul marwas da yake yasan dalilin fishin nata sai ya kau da kai ga barin kallonta yama kara gaba yaki yarda su jera tare

yaci gaba da sha aninsa kawai HAKAN NE YASA ITAMA jikinta yayi sanyi kuma taji a zuciyarta cewar abinda ta yiwa tsohon bata kyauta ba don ya fadi gaskiya amma saboda girman kai irin na masu sarauta sai ta basar taki yarda tayi masa magana har suka shafe yini na biyu aka yada zango na biyu.

.

A cikin wani daji mai yawan bishiyoyi da duhuwoyi tabbas wannan daji yana da kwarjini gami da ban tsoro domin komai jarumtakar mutum idan ya tsinci kansa a cikinsa dole ne ya san cewa ya shigo wuri ma hadari, bayan an kafa tantuna sai sarauniya larbisa ta tara gabadayan

dakarunta ta shaida musu dacewa kada dayansu ya kuskura yayi barci domin akwai alamun mugayen abubuwa a cikin wannan daji saboda haka wani abun zai iya kawo harin sumame a yayin da dare yayi koda jin wannan batu sai shugaban dakarun nata wanda ake kira da sadauki muhairu ya risina ya ce ya shugabata kiyi mini izini mu kewaye sansaninmu da dogayen manyan itatuwa domin samar da cikakken tsaro kinga indai wani abune mai rai zai kawo mana harin ba zai samu damar afko mana ba kai tsaye koda jin wannan batu sai sarauniya larbisa tayi murmushi tace hakika kazo da shawara mai kyau amma idan ta nine ban damu da sai an kewaye sansanin ba sai dai saboda ku da kuyangina koda gama fadin haka sai sarauniya larbisa ta juya ta tafi izuwa cikin tantina nan take sadauki muhairu ya umarci wadansu daga cikin dakarunsa dasu je su saro manyan bishiyoyin da za a kewaye su haka ramukan da za a sanya itatuwan.

.

Nan take kuwa dakaru suka kama aiki ba lalaci a lokacin dasu kuma kuyangi suka kama aikin dafa abinci ai kuwa kafin magariba tayi an kammala dukkan aikin ya zamana cewa an kewaye gaba dayan  sansanin da manyan bishiyoyi yadda koda giwaye ne suka zo sai sun sha wahalar gaske kafin su sami damar ture bishiyoyin da aka kewaye sansanin bayan anci abinci sai dakaru suka ki su kwanta sukayi lambo suna masu dana kwari da bakansu masu takubba ma suka zauna a cikin shiri kuma aka kashe dukkanin fitilun iccen dake ci a sansanin ko ina yayi duhu dundum sarauniya larbisa kuwa kayan yakinta ta sanya ta zare takubba guda biyu tayi lambo a gaban dakarun nata saboda ita a jikinta ta san cewa lallai ba za a rasa wani mugun abu ba a cikin wannan daji kuma lallai abin zai iya kawo hari a koda yaushe har dare ya raba ba a ji wani bakon motsi ba a cikin dajin. Al amarin da ya karya zuciyar dakarun sarauniya larbisa kenan suka fara tunanin cewar babu wani mugun abu da zai kawo hari dama a wannan lokaci da yawa daga cikinsu sun fara hamma saboda jin barci.

.

Koda sarauniya larbisa ta lura da halin da dakarunta ke ciki sai ta dubi sadauki muhairu wanda yayi kwanciyar lambo kusa da ita tace maza ka gayawa sauran yaranka cewar duk wanda ya kuskura yayi gyangyadi na dakika daya ni zan sareshi da hannuna.

.

Nan take muhairu ya radawa daya daga cikin wannan batu shima sai ya radawa na kusa dashi a haka sauran gaba dayan dakarun suka sami wannan sako bayan faruwar hakan da kamar nisan dakika dari uku sai kawai kawai su sarauniya larbisa suka fara jiyo wani irin gurnani mai yawan gaske daga can nesa gurnani ne na wadansu irin halittu masu yawan gaske kamar na dodanni ko manyan birirrika inka dauke sarauniya larbisa da sadauki muhairu babu wanda hantar cikinsa bata kada ba a sansanin shikuwa tsoho huzallatul marwas kuwa fitowa yayi daga cikin tantinsa ya tsaya a tsaye yana mai rike kugunsa yana kallon can bakin kofar sansanin don yaga abinda zai faru alhalin kowa ya sami wuri ya buya a wannan lokaci.

.

kwatsam! sai yaji jakarsa ta sihiri ta bude aljani subauratu ya baiyana a sama dai dai fuskarsa yana mai kare hancinsa da hannu sakamakon iska mai kare hancinsa da hannu sakamakon iska mai karfi dake kadawa yace yakai mai gidana me kake takama dashi har da zaka fito ka tsaya a cikin wannan sansani alhalin kana gani cewar jaruman ma da suka yarda da kansu kwanciya sukayi a kasa sukayi lambo ko kuwa kunnenka baya jiyo sautin gurnani halittun dake shirin kawo farmaki izuwa wannan sansanin?

.

Lokacin da tsoho huzallatul marwas ya ji wannan tambaya sai ya bushe da dariya sannan yace haba yakai subauratu in banda abinka akan wane dalili tsoho zaiji tsoron mutuwa musamman ma kamata wanda bashi da kowa kuma bashi da komai ka tuna fa cewa ni yanzu na rasa babban masoyina wato mahaifina kuma na rasa uwata tun ma ina jariri na rabu da yan uwana na jini wadanda a halin yanzu ma bani da tabbacin suna raye ko sun mutu idan ma suna raye basu da wani amfani a gareni tunda sun kasance manyan makiyana a doron kasa.

.

Lokacin da tsoho huzallatul marwas yazo nan a zancensa sai Aljani subauratu ya dubeshi yayi murmushi yace ai yan uwanka suna nan a raye duk su hudun amma a halin yanzu duk duniyar nan babu matsafan da suka fisu karfin sihirin tsafi amma hadin kansu ya watse sun zama abokan gabar juna ba don komai ba sai saboda kowannansu yana

son ya mallaki littafin tsatsuba shi kadai saboda ya mulki komai da kowa na cikin wannan duniya.

.

Koda jin wannan batu sai mamaki ya kama huzallatul marwas kuma hankalinsa ya tashi ya dubi Aljani subauratu cikin alamun tsananin damuwa yace kai kuwa menene dalilin da yasa tuntuni baka labarta mini wannan labari ba tun ina da sauran kuruciyata da karfin jikina ba yanzu ba da shekaruna suka haura hamsin?

.

Koda jin wannan tambaya sai Aljani subauratu ya kyalkyale da dariya sannan yace ai gaya makan bashine wani amfani tunda ba zaka iya yin komai ba akan lamarin dolene ka jira har zuwa lokacin da zaka sami daukakar da tafi tasu kafin huzallatul marwas ya budi baki ya kara cewa wani abu sai kawai sukaji kasa ta kama girgiza tamkar zata tsatstsage su rufta cikinta kuma sai gurnanin da suke jiyowa a can nesa ya kara kusantosu sosai bayan kamar dakika hamsin sai sukaji gurnanin ya cigaba da wanzuwa a lokacin da yake kara kusantosu suna nan a tsaye sai kawai suka ga dandazon cincirindon tarin birirrika sun durfafo inda suke kai tsaye yayinda huzallatul marwas yaga haka sai yayi maza ya mayar da Aljani Subauratu cikin jakar sa a lokacin da sarauniya larbisa ta fito daga cikin tantinta suma sauran dakaru haka suna fitowa ne sukayi Arba da tahowar wadannan birirrika nanfa hantar cikin kowa ta kada Amma banda na sarauniya larbisa saboda ita tasan cewa Jarumar gaske ce

amma kuma matsalar itace basu da zafin nama da jarumtakar da zasu iya yakar wadannan birirrika nan take sarauniya larbisa taji nadama tazo mata bisa bitowar da tayi neman wannan littafi na tsatsuba tunda gashi tun ma tafiyar batayi nisa ba zata rasa rayuwarta….

Wow nima AlQuyraemey a nan zan dakata sbd ganin wadannan birirrikan kuma nake cewa sai Allah ya kaimu gobe zan ci gaba.

Ku Taba Nan Domin Karanta Littafin Tsatsuba Na Biyu Wannan Abdulaziz Sani M/Gini Ya Rubuta.

TSATSUBA

Book 1

Part F

Marubuci Abdul’aziz Sani Madakin Gini

Posting By Abubakar Saleh AlQuyraemey

Domin Samun litattafan Yaƙi Contact 08138873799.

.

https://www.facebook.com/AlQuyraemey360

.

Nan take sarauniya larbisa taji nadama tazo mata bisa fitowar da tayi neman wannan littafi na tsatsuba tunda gashi tun ma tafiyar batayi nisa ba zata rasa rayuwarta, gama aiyana hakan keda wuya sai wani daga cikin birirrikan ya shammaceta ya gabza mata naushi a haba saboda karfin dukan sai da tayi sama tamkar an janyeta da majajjawa koda shugaban dakarun nata sadauki Humairu ya hango shugabarsu a can sama kuma ya tabbatar da cewa idan ta fado kasa cikin wadannan birirrika ta zama gawa sai ya falfala da gudu izuwa kan birirrikan yana mai kwalla ihu. 

.

Ai kuwa sai birirrikan suka raba hankulansu biyu ya zamana cewa wasunsu sun daga kawunansu sama suna jiran sarauniya larbisa ta fado cikinsu su dasa mata wawa

wasunsu kuma sai suka ruga izuwa kan sadauki Humaisu

yayinda ya rage saura yan dakiku kadan larbisa ta fado kan birirrikan shi kuma humaisu yayi karo dasu sai kawai humaisu da larbisa sukaji an suresu anyi sama dasu cikin tsananin gudu na ban al ajabi tamkar za a taba hadari dasu kawai sai gani sukayi an diresu a tsakiyar sansaninsu nan take Aljani subauratu ya baiyana tsulum a gabansu yana mai kyalkyala dariya ya risina ga tsoho huzallatul marwas  yace yanzu na cecesu ya shugabana amma kayi sani cewa anan ne kawai zan iya taimakonku amma da zararr mun kara gaba sai dai ku ceci kanku kafin larbisa ko tsoho huzallatul marwas dayansu yace wani abu tuni Aljani subauratu ya rikide ya zama guguwa. Guguwar ta tafi da tsananin gudu irin na tauraruwa mai wutsiya ta fada cikin dandazon birirrikan kawai sai gani akayi kawunan birirrikan suna guntulewa suna faduwa kasa gangar jiki na bingirewa sai dai kaga jini na tsiri da feshi daga cikin wuyansu koda birirrikan suka ga suna ta mutuwa kuma sun rasa wanda yake yi musu wannan barna sai suka haukace suka rinka ruri da kururuwa suna kaiwa iska duka amma duk a banza domin dada ragargazarsu ake yi suna zama gawa tabbas wuya ba dadi kuma idan kaji ana cewa ga ki gudu to tabbas sa gudu ne baizo ba lokacin da wadannan birirrika sukaga sun kasa kare kansu daga sharrin guguwar da ta addabesu sai suka

fara juyawa da baya a guje suna kokarin komawa inda suka fito amma sai guguwar ta rinka kure musu gudu tana ci gaba da cire musu kawuna har saida ya zamana cewa babu sauran daya daga cikinsu wanda ya tsira da rayuwarsa.

.

A wannan lokacine dakarun sarauniya larbisa suka fara firfitowa daga cikin wuraren da suka buya cikin alamun kunya suna masu sunkui da kai kas cikin fushi sadauki Humaisu ya rufesu da  fada yana kokarin hukuntasu kawai sai sarauniya ta tari numfashinsa tana mai kallonsa cikin murmushi tace kada ka hukunta su domin banga laifinsu ba bisa guduwar da sukayi suka buya kai kanka ai kasa tarar birirrikan kayi sai da kaga zan hallaka sannan kayi kundunbala ka rugo domin ka kawo mini dauki hakika kayi gagarumar gwaninta wacce ta burgeni don haka idan mun koma gida zan yi maka wata gagarumar kyauta wacce ban taba yiwa wani mahaluki ba.

.

Koda jin wannan batu sai farin ciki ya lullube sadauki Humaisu ya zube kasa bisa guowoyinsa a gaban larbisa yana godiya nan dai larbisa ta bayar da umarnin aje a kwanta ba tare  da wani bata lokaci ba kuwa kowa yaje ya kwanta cikin kwanciyar hankali ba tare da fargabar komai ba.

.

Kashe gari kuwa da sassafe aka kimtsa bayan an yi kalaci

sai sarauniya larbisa tsoho huzallatul marwas tace aljaninka ya gaya mana cewar tafiyar yini biyu da rabi zamuyi mu riski dajin da jaruma shumaira take tabbas yanzu mun shafe tafiyar yini daya kunga kenan saura ta yini daya jal a gabanmu shin akwai sauran wani mugun abune da zamu hadu dashi kafin mu isa dajin da jaruma shumaira take?

.

Koda jin wannan tambaya sai tsoho huzallatul marwas da sadauki Humaisu suka dubi juna sukayi shiru larbisa ta dubi huzallatul marwas cikin fishi tace ai kai ne ya kamata ka bani amsar wannan tambaya. Huzallatul marwas yayi ajiyar numfashi sannan yace ya shugabana aini a ganina yanzu bai kamata kiyi shakkar wani abu ba tunda dai gashi mun ga bayan wadannan mugayen birrirrika saboda nasan cewa abu ne mawuyaci mu sake haduwa da wani mugun abu wanda ya fisu hadari koda jin wannan batu sai sarauniya larbisa ta yi murmushi tace tabbas kazo da magana mai ma ana yanzu kawai saimuci gaba da tafiya ba tare da bata wani lokaci ba kuwa aka hau kan dawakai bayan an debe komai aka ci gaba da tafiya ba sassauci tsoho huzallatul marwas ne akan gaba yana jagorantar rundunar, sarauniya larbisa, da sadauki Humaisu na biye da shi sannan sauran dakarun, Kamar yadda Aljani subauratu ya fada haka Al amarin ya kasance wato sai da

suka shafe tafiyar rabin yini guda sannan suka iso wani katon daji mai yalwar Bishiyoyi, koramai da fadamomi, kai da ganin wannan daji kasan cewar dajine mai ni’ima irin wanda mafarauta ke so domin dole ne a samu dabobin daji da tsuntsaye masu yawa a cikinsa da shigarsu sai suka hango wani katon garke na ragon dawa cike da raguna da tinkiyoyi abin mamaki shine an kewaye garken ne da siraran itatuwan bishiya marasa kwari wadanda dabbobin zasu iya kakkaryasu su watsu amma kuma dabbobin basu ture itatuwan ba sun gudu.

.

Koda dakarun sarauniya larbisa suka hango garken wannan dabbobi sai suka cika da farin ciki suka ruga izuwa cikin garken suka dasawa dabbobin wawa da nufin kowa ya kama iya rabonsa. kwatsam! ba zato ba tsammani sai sukaji ana naushinsu ta sama suna zubewa kasa duk wanda akayi wa naushi daya sai dai kaga yayi sama ya fado kasa a matukar galabaice wanda ke naushin nasu kuwa a samansu yake shawagi kamar tsuntsu har sai da ya gama bazar dasu kasa sannan ya duro kasa bisa kafafunsa aka fara kallon kallo tsakaninsa da sarauniya larbisa ba wani bane yayi wannan gagarumar jarumtakar

ba face jaruma shumaira kai da  ganin irin kallon da sarauniya larbisa ke yiwa jaruma shumaira kai kasan cewa

tana cikin tsananin mamaki ba wani abu bane yasata wannan mamaki ba face a rayuwarta  bata taba zaton cewa zata ga wata ya mace ba mai kyau kamarta ba amma a yanzu da tayi arba da shumaira saita raina kanta kuma ta tabbatar da cewar babu abinda zata fi shumaira dashi face mulki da dukiya cikin tsananin fishi shumaira ta dubi su larbisa tace dame kukazo wannan daji shin yan fashine ku ko kuwa matafiyane wadanda basu san ya kamata ba duk mai hankali idan ya dubi wadancan dabbobi ya lura da yadda aka kebancesu yasan akwai mai su duk da cewa kuwa a cikin daji suke kuyi sani cewa wannan daji nawa ne don haka komai na cikinsa mallakina ne babu wanda yake da ikon yin farauta a cikinsa face ni.

.

A cikin wannan daji kakana na bakwai yayi rayuwarsa kuma tun daga zamaninsa kawo i yanzu babu wanda ya isa ya taba komai a nan sai da izininmu da yardarmu ku gaya mini abinda ya shigo daku cikin dajin nan in ba haka ba kuwa sai dai na yakeku koda jaruma shumaira tazo nan a zancenta sai larbisa ta matso gaba kusa da ita ta sauko daga kan dokinta ta dubi shumaira cikin murmushi tace yake shumaira yaga mafarauci Imshal ki yi sani cewa nice Sarauniya Larbisa mai mulkin birnin darul kaizul kuma musamman nazo wannan daji naki domin na gana dake bisa wata muhimmiyar bukata tawa koda jin wannan batu sai jaruma shumaira ta gyada kai cikin alamun fishi da rashin yadda tace mu bama mu amala da masu mulki kuma baki da wani abu wanda zaki iya biyana dashi na taimakeki saboda haka ina mai shawartarku daku gaggauta fita daga cikin wannan daji nawa idan ba so kuke muyi yaki ba koda gama fadin hakan sai jaruma shumaira ta juya da baya ta nufi wannan garke na dabbobin ta ta shiga gyara turakan dake ciki tana daure dabbobin.

.

Koda ganin haka sai sarauniya larbisa ta dubi gaba dayan dakarunta tace duk abinda zai faru tsakanina da jaruma shumaira kada ku saka baki ko hannu nan take larbisa tabi

shumaira izuwa cikin wannan garken dabbobi ta kama tayata aikin daure dabbobin.

.

Al amarin da ya fusata jaruma shumaira kenan ta kaiwa larbisa wawan duka da kafa a wuya, cikin bakin zafin nama larbisa ta kaucewa dukan nan fa suka kaceme da azababben fada suka wanzu suna masu kaiwa junansu sara da suka cikin tsananin zafin nama juriya da bajinta tun da su jarumi Humaisu suke ganin gumurzu na fadan hannu tsakanin jarumai basu taba ganin fada mai tsananin ban tsoro ba kamar wannan domin gwanintar ta hadu da gwaninta kuma sadaukantaka tayi kada da kishiyarta.

.

Sai da wadannan jarumai biyu suka shafe rabin sa a suna naushi da bugun juna hannu da kafa ya zamana cewa sun hadawa junansu jini da majina kuma sun fara galabaita amma saboda bakar zuciya sunki su daina fadan amma kuma jaruma shumaira tafi sarauniya larbisa jure duka domin ita tana iya shanye duka uku na larbisa amma data naushi larbisa sau daya sai kaga ta fadi kasa sai dai tayi hanzari ta mike taci gaba da fadan

.

Al amarin da ya dugunzuma hankalin su sadauki Humaisu kenan domin sun tabbatar da cewa idan aka ci gaba da wannan fada a haka har zuwa wani dan dogon lokaci shumaira zata iya sumar da larbisa ko kuma tayi mata wawan rauni Gashi kuma larbisa ta gargadesu akan kada su kuskura su shiga cikin wannan fadan.

.

Ana cikin wannan bakin gumurzune shumaira ta shammaci larbisa ta daka tsalle sama ta doki fuskarta sau uku da kafa take larbisa ta dimauce kuma ta gigice ko da taji zafin dukan saita zare takobinta ta kaiwa shumaira sara cikin sa a kuwa ta yanki shumaira a damtsen hannunta na hagu har wajan ya dan dare kadan jini ya fito

shumaira tayi tsalle gefe daya tana mai yin yar kara bisa jin zafi da zugin da taji koda ta dubi hannun nata taga raunin da larbisa tayi mata sai ta fusata ainun itama ta zaare rantsatstsiyar takobinta ta ruga izuwa kan larbisa

itama larbisa saita  rugo izuwa kanta koda ya rage saura baifi taku uku su hadu ba sai kowacce ta daka tsalle sama suna masu kai mugun sara Takubbansu na haduwa saita larbisa ta rabe gida biyu, A saman shumaira ta doki kirjin larbisa ta fado kasa a dimauce kafin larbisa ta mike tsaye shumaira ta duro kanta da nufin ta soka mata takobinta a gefen jikinta……

.

Wow lallai Yakamata nIma AlQuyraemey nakaiwa Larbisa Dauki Amma bari naje na dauko Rantsatstsiyar takobina sannan na dawo

.

Anan ne kuma littafin Tsatsuba Na daya yazo Karshe marubucin yace…

SHIN SHUMAIRA ZATA SAMU DAMAR SOKAWA SARAUNIYA LARBISA TAKOBINTA KUWA?

.

SHINSU SARAUNIYA LARBISA ZASU SAMI NASARAR SAMUN ABOKAN TAFIYARSU?

.

WANE IRIN MASIFU DA TASHIN HANKALI ZASU FUSKANTA KAFIN SU ISA KOGON KITABUL SIHIR?

.

SHIN SARAUNIYA LARBISA ZATA CIKA BURINTA NA MALLAKAR LITTAFIN TSATSUBA?

.

Ku Taba Nan Domin Karanta Littafin Tsatsuba Na Biyu Wanda Abdulaziz Sani M/Gini Ya Rubuta.

Back to top button