Health

Yadda Ake Korar Tsaka, Kyankyaso, Sauro Da Wasu Kwaruka Daga Gida.

MUMMUNAR ILLAR DA TSAKA KE DA SHI GA LAFIYAR JIKIN DAN-ADAM MACE KO NAMIJI YARO KO BABBA

Wannan bayanin an Ciro shi ne daga cikin littafin nan me suna LIKITAN KAINA Volume two 2 Wanda ABDURRASHID ADAMU AHMAD (DANBAIWA) ya wallafa shi.

 

Karanta>>> Amfanin Hulba A Jikin Yan Mata Dama Matan Aure.

 

MECE CE TSAKA KUMA YAYA KAMANNINTA SUKE

Tsaka wata halittace daga cikin halittun ubangiji Daga cikin halittun sa na dabbobi, tsaka tana da kamannin qaramin kadangare, saidai ita tsaka bata da nau’in kala-kala, ba kamar kadangare ba akwai jah, blue, ita tsaka kalarta daya ce kawai ruwan kasa (brown), kuma ita tsayinta da girmanta gabadaya bata wuce tsayin yatsa manuniya amma banda jelarta, tana da wutsiya sissira, kuma wutsiyarta ba me tsayi ba ce sannan tana dauke da wata guba a cikin yawunta kamar na dragon saidai ita ba wuta take futarwa ba kamar yadda dragon take yi
. Amma dai tsaka yawunta kamar fetur yake wajen angiza wuta Akwai abubuwan da suke kawo tsaka cikin dakuna ko gidajen mutane suna da yawa, amma zan kawo kadan daga ciki:

Karanta>>> Amfanin Zogale Guda 18 A Jikin Dan adam

1. Hasken wutar lantarki da dare musamman lokacin damina🌧 shiyasa ma annabi s.a.w ya ce: in zaku kwanta barci da dare Ku kashe wuta saboda ita maqiyarku ce wutar a abinda take jawowa fitina ce ga lafiyarku da kuma dukiyarku.
2. Lokacin zafi takan fito shan iska waje
3. Damshin jikin gini me zuqar ruwan sama🌧 sai ta mannu da shi don jin sanyi lokacin zafi.
4. Tara shirgi ba gaira ba dalili.
5. Rashin tsaftar muhalli, da barin kayan sanni. E.t.c

Karanta>>> Amfanin Kubewa Musamman Ga Ma’aurata

KADAN DAGA CIKIN ILLOLIN DA TSAKA KE DA SU NA CUTARWA GA RAYUWAR DAN-ADAM.

Subhanallah!!
Subhanallah!!

1. Idan aka bar gari a bude, sai ta shiga ta yi birgima a cikin garin, sai a kamu da cutar baras (kuturta) ko Wasu muggayan Kuraje masu 6ata fata.

2. Idan aka bar ruwan sha a bude, sai tayi
amai a cikin ruwan sai a kamu da
shanyewar 6arin jiki (paralyze), ko lalacewar wani sassan jiki.

Karanta>>> Dalilin Daya Sa Matan Hausawa Ke Tsufa Da Wuri Da Zarar Sunyi Aure

3. Idan mutum ya kwanta bacci bai yi Addu’aba Ma’ana (Azkar), tana yin busa a cikin idon mutum sai ya makance
ko ya kama ciwo me tsanani
4. Kwanakin baya mun samu labarin matar da ta dafa shayi ba ta san da tsaka a cikin butar shayin ba, mijinta da ‘yayanta suka sha duk suka mutu.
5. Idan tsaka ta riqa ta girma sosai tana haddasa gobara.

Karanta>>> Ina Mata Masu Fama Da Rikecewar Al’ada Ga Magani Da Izinin Allah

musalin ire iren yawan gobarar da take
faruwa yanzu haka a garuruwa kamar irin su, gombe, Bauchi,sokoto da dai sauransu, don tana tare da muggayan, Aljanu dama Manzon Allah SAW yace Ita ce ta yi busa a wutar da aka jefa Annabi
Ibrahim (AS). Har ma wasu malaman suka ce matar da aka sa ta shiga cikin Ramin da za a jefa annabi Ibrahim a.s ta kunna wuta ita ce Allah ya mai da ita matar ta koma tsaka sai ta zuba gubar yawunta a cikin dakin sai wutar ta kama ALLAH MAFI SANI.

Karanta>>> Maganin Toilet Infection Da Kuma Rashin Sha’awa Ga Mata

Kadan kenan daga illolin Tsaka, saboda
haka lallai mu kai matuka wajen kula da
abincin mu da abin shan mu tare da kula wajen tsaftace muhallinmu.

Da zaran an ganta Agida a hanzarta kasheta da Bismillah saboda suna tare da shaytanu suna iya cutar da mutum ayi anfani da tsintsiya ko takalma wajen kasheta kokuma a sa mata maganin kashe kwari.
.
Manzon Allah ya cika mai gaskiya abin gasgatawa.

YANDA AKE KORAR TSAKA DA KENKESO A GIDA
………………………………………………………….

Duba da hatsurran dake tattareda wadannan halittun guda biyu,sai muka ga ya dace mu zo da bayanin tiryan tiryan kan yanda ake korar tsaka da kenkeso ga baki daya a cikin gida.

Karanta>>> Sakonnin Soyayya Na Mata Na Barka Da Shan Ruwa Ga Samarinsu 2023

Ta’ammali da tsaka a cikin gida masifa ce,mun yi rubutu kan dimbin illolin da take haifarwa a gida,ko baya ga haka halitta ce munafuka da addinin musulunci yaiyi umurnin idan an ganta a kashe ta.Akoi lada ga Wanda ya aikata haka.
Shi kuma kenkeso yana dauko kwayoyin cuta daga najasa a toilet ya zo ya cudanyasu ga abinci,ruwan sha,ko abin shan da aka ajiye.
Halitta ce da take da tsawon rayuwa zata iya daukar shekara da shekarru tana rayuwa a bayi,tana haddasa cutukan polio,cholera, typhoid,da matsanancin basir,da gudawa marar misali.Duk abinci ko wani abin shan da ta fada a cikinsa to ka zubda wannan abin kada ka kuskura ka ci ko ka sha,wallahi hatsari ne ga lafiya matuka.

Karanta>>> Amfanin  Zobo Ga Lafiyar Jiki Da Kuma Illolinsa

Domin korar tsaka a gida,ka nemi gishiri ka gauraya da garin tafarnuwa sai ka marmasa a kowace korkoda a gidanka,tsaka zata bar wajen a cikin gaugawa.

Shi kuma kenkeso, ka nemi albasa guda daya,da cokali daya na baking soda (sodium biocarbonate) bafa baking powder ba,sai a kula.
Sai ka yayyanka albasara ka gauraya da baking soda din ka ajiye a korkodar kitchen ko a toilet, zaka ga yanda kenkesai zasu mutu.

Karanta>>> Amfanin Dabino Da Kuma Magungunan Da Yake Yi Guda 50

Back to top button