Hausa novels

Karfe A Wuta Chapter 39 By Ayshercool

Cikin cunkusa baki ta ce “To kuma shi ne zaka tsorata ni? Ko gama wankan ban yi ba na fito”Ya ce “To mu je na ƙarasa miki”Tsuke bakinta ta yi ta kasa magana, jin abun da yake yi, da ba ta yi zato ba.Kasancewar bayanta, yana jikin ƙirjinsa, yana jin bugun zuciyarta yana fita da sauri-sauri.”Meyasa ki ke shareni? Kwana uku kin yi mini laifi, kuma kina gaba da ni ko?”Ba ta yi mamakin ƙarfin hali, da ƙwarewa a iya rainin hankali, irin na Al’amin ba, wato ma zaman jiran ta bashi haƙuri yake yi.”Kin san zaki yi gaba da ni, meyasa ki ka bari muka saba? Ba ni da saurin sabo, ki ka yaudare ni ki ka sa na fara sabawa da ke, shi ne zaki wani din ga mazewa. A din ga manta abu a kwana ɗaya ya wuce kawai a cigaba da life. Ni kaina ban san dalilin da ya sanya nake matuƙar jin baƙin ciki idan na ga wani abu ya raɓe ki ba”Da ƙarfi ta ce “Master” tayi maganar tana ƙoƙarin miƙewa.Hankali kwance ya ce “Yes” ba tare da daina abun da yake yi ba.Cikin rauni ta ce “Wai meye haka?””Aure” ya bata amsa kai tsaye.Shiru yayi, jin yadda zuciyarta ke cigaba da bugawa da sauri, tana nema ta fara haki, saboda tsoro.A hankali ya ce “Common, relax mana””Babyn roba” tayi masa shiru, “Kodayeke yanzu babyn ƙarfe ce, ki amsa mana” still ta yi masa shiru, yana jin yadda ta saka ƙarfinta ta riƙe hannunsa.Fito yake yi mata a kunne, hakan ya sanya ba shiri, ta saki hannunsa, ta toshe kunnenta.”Ki amsa mana, tambaya zan yi miki mai muhimmanci. Kin san bana mantuwa, kamar na’aura mai ƙwaƙwalwa nake, in dai ka ajiye zaka zo ka ɗauka. Idan ban manta ba kin ce kina so mu rayu tare. Ina ta tsoron taɓa abun da nake ganin ban dace da shi ba. Ba na son cutar da rayuwarki, in yi silar gurɓacewarta kamar yadda tawa ta gurɓata, duk da kin daɗe ki na nuna mini ina rintse ido, Al’amin ba ya abu bisa zalunci””Na nuna maka me?””In faɗa kenan, ko shekaranjiya meya kawo zancen zuriya? Ke ‘yar yarinya kallonki kawai nake yi, amma kar ki damu da hakan ai lafiya ce” wato da wani ne yake ba wa jauhar labarin maganganun nan daga bakin Al’amin suke fitowa, sai ta ƙaryata, amma ƙiri-ƙiri, ya shige duhu yana sakin maganganu yadda yake so, alhalin ya ce ba ya jin komai.Tana cikin tunanin ta ji ya ce “Kin amince mu rayu tare, a matsayin abu guda? Ba na son cutar da ke, ke ma kin shiga ƙalubale da dama, bana son ki sake shiga matsalar rayuwa, rayuwarki ta tafi a haka kawai. Idan kin amince, zan yi iya ƙoƙarina wurin zama da ke da zuciya ɗaya, amma sai kin yi wa yanayin rayuwata uzuri, duk da a yanzu ma kin taka muhimmiyar rawa a rayuwata. Be mine”Haka kurum ta fara kuka, kukan da ba ta san na menene ba ma.”Talk babyn roba”.”To ka ƙyale ni, gobe da asuba sai na gaya maka”Cikin buɗɗiyar muryarsa, da take fitowa daga ƙirjinsa, ya ce “Na ƙi wayon, yanzu zamu gama maganar””Master””Mmmm””To zaka daina saka ni kuka?”Ya ce “In sha Allah”Ta ce “Zaka daina shaye-shaye?””In sha Allah, ina iya ƙoƙarina, ba abu ne da zan daina lokaci ɗaya ba. Mu bar wannan maganar, baki bani amsa ta ba, zaki cigaba da zama da ni, a yadda nake, ina talaka marayan da ya rasa kulawa, sai bayan shigowar ki rayuwata?”Tana kuka ta ce “Dama ai kai ka ke cewa zaka sake ni, ka ke sakani kuka, ina son in zauna da kai”Yayi ajiyar zuciya ya ce “Duk wani abu da ki ka yi mini na alkhairi, yana rubuce a ƙirjina, ba zai taɓa gogewa ba, ban taɓa mantawa da ko guda ɗaya ba, babu wata mace da ta taɓa playing role ɗin uwa a rayuwata sai babyn roba, bashi ne a kaina kulawar da ki ka yi mini”.”Ni saboda Allah nake kula da kai””Ni na isa in biya ki ne dama?”Jauhar ido yayi tsilli-tsilli, bayan da Al’amin ya ƙaryata tunaninta na ko ba shi da lafiya ne.Ya tabattar su a matsayin miji da mata. babu tsammani aka kawo wuta, haske ya gauraye ɗakin, Jauhar ta takure jikinta, sai rawa jikinta yake yi, yayi murmushi ya ja bargo ya rufeta.Ya zuba wa gashin kanta ido, ba baƙi ne wuluk ba, amma mai laushi irin na fulani, ya hargitse, ta cusa kanta cikin bargo sai gashin a waje.Ya daɗe yana kallonta, kafin ya kai hannunsa yana shafa gashin ya ce “Amm ya ma sunan angela ko?” Tayi masa shiru, ta sake dunƙulewa wuri ɗaya.Ya cire bargon daga fuskarta, amma ta rintse idanunta.”Kalleni mana, abu zan gaya miki fa”Ta cunkusa baki, tana ta jan majina a hancinta, fuskarta duk ta yi ja saboda kuka.Wani nishaɗi yake ji, ya cigaba da kallonta yana ta murmushi, kamar wanda aka yi wa Albishir da kujerar makka.Wayarsa da ta faɗa ƙasan gado ce, ta fara vibrating, ya juya ya zura hannunsa ya ɗaukota, ya sake matsawa kusa da jauhar, ya ɗaga wayar.”Maza” muryar liti tayi amsa kuwwa a wayar.”Mmm””Kana ina ne?” A taƙaice ya ce “Gida” yayi maganar yana cigaba da shafa gashin jauhar.”Wai me ka ke yi ne? Ko baka da lafiya ne?”Al’amin ya ce “Meyafaru?””To ai ji nayi kana amsawa kamar ana yi maka dole””Ina jinka ya aka yi?”Liti ya ce “Akwai matsala ne fa””Ta me?””Yaran madaki, duk sun cire pastocin indabo, ka san ɗazu Walid da su guduma suka gama sasskawa, mu na dawowa muka tarar duk sun cire, ya tambaya aka ce masa yaran madaki ne, gashi can ya tafi, nayi-nayi ya ƙyale su, ya ɗau wuƙa ya tafi, shikaɗai kar su yi masa wani abun, ka san Walid da baƙin taurin kai, kamar jinjirin jaka, dan yafi jaki taurin kai”Al’amin ya ja guntun tsaki ya ce “Gani nan, bari na tafi cikin garin, maza ka kira yaran nan, ka yi magana da su guduma ma, zan kira yaran unguwar mu, maza su bishi kar su yi masa wani abun, gani nan” ya yinƙura zai tashi, jauhar ta ja jikinta ta riƙe shi ta ce “Rigima zaka je ka yi ko?”Ya girgiza mata kai ya ce “Ba rigima zan yi ba, amma idan har ba a kai masa ɗauki ba, za su iya kashe shi”Cikin takaici ta ce “Kana ganin halin da ka sakani, a  haka zaka tafi ka bar ni, a wannan yanayin da nake ciki?”Ya ɗagota ya ce “Ki yi haƙuri, bana son a sake asarar rai saboda ni, wallahi suka ga Walid shikaɗai, za su iya kashe shi, am sorry yanzu zan dawo, ki kwanta kar ki tashi kina buƙatar hutu” ya ƙarasa maganar yana kwantar da ita ya bar ɗakin.Ta lumshe idonta, hawaye suka cigaba da zuba, sai da ta yi ta gaji, sannan ta saukko daga kan gadon da kyar, ta haɗa ruwa mai ɗumi sosai ta tsarkake jikinta, ta nemi wuri ta kwanta.Da asuba da ƙyar ta tashi, ko alwala ba ta yi ba, ta tafi ɗakinsa ta duba, ko ya dawo cikin ƙoshin lafiya.Ƙarar buta ta jiyo a banɗakinsa, alamar yana alwala, wani ɗan sanyi ta ji a ranta, yau da kansa ya tashi sallar asuba, ko yaushe ya dawo ma oho.Ta koma ta yi salla, ta sake fitowa ta leƙa, ta ga yana salla, ga kayan shaye-shaye a kan katifarsa, ganin yana salla, ta shiga kanta tsaye, ta tattare kayan ta fice.Bacci ya ƙara kwasheta, tana cikin baccin ta ji ta a takure, ta yi miƙa ta buɗe idonta, ta saka a nasa.”Kalli agogo ƙarfe sha ɗaya, yunwa duk ta yi mini illa, na sayo ƙosai na kasa ci, ya ja mai, kuma farin maggi ya yi yawa a ciki sosai.’ikon Allah, shi ko ɗan rarrashin nan ma ba zai yi bs, zancensa kawai abinci.A ƙule ta ce “In da ka tafi ba su baka abincin ba?”Me ki ka ce?”Ba tare da ta kalleshi ba ta ce “Na ce in da ka tafi ba su baka abincin ba?”.Ya ce “Ba su bani ba, ke zaki tashi ki bani yanzu”Kawai ta juya masa baya, dan daren jiya ta ƙulu yadda ya tafi ya bar ta.Ba ɗaga ƙafa, ba komai, ya ƙara huce baƙar maganar da ta gaya masa, ya gama ya tada kai da jikinta, ya lumshe ido ya hau bacci.Ta gama koke-kokenta, duk iya ƙoƙarin da tayi, ta ture shi ta tashi, ta kasa sai ma ji da tayi tana haki, Al’amin ya gama raina mata hankali ta ko ina.A haka har baccin dole ya sake yin gaba da ita.Ƙarshe har azahar ko wanke-wanke ba ta yi ba.Ta yi wanka, ta canza kaya, ta fito ya basar da ita, kamar babu abun da ya faru, ta tarar da shi da wayarta a hannunsa, yana game, ta share shi ta wuce, sai da ta fita ya bi bayanta da kallo yana murmushi.Ta tarar yayi wanke-wanke, ya share tsakar gidan tsaf, har markaɗen kayan miya ya kai.Ta dawo ta koma ɗakinta, ta ɗaukko bedsheet, zata fita ya ce “Me zaki yi ne?””Wanki””Me ya same shi, zaki wanke? Ko karyawa ba ki yi ba? Ki saka shi a baho, zan wanke, ki samu ki karya”Sai cika take tana batsewa, mazewa kawai yake yi, don dariya yake son yi, amma ya maze shi ma ya sha kunu.Tun da ya kai markaɗen nan, ya dawo bai sake fita ba, wuni guda yana gida, duk da babu wanda yake kula wani, amma zaman kula da ita yake yi.Har isha’i, kowa ya koma ɗakinsa, har ta kwanta, ta ji ya shigo ɗakin, kan tayi magana ya ƙaraso kan gadon ya hau.”Malam ya ne? Menene kuma?””Kamar yaya?” Yayi maganar yana janyo bargonta, ya rufe ƙafarsa.Kamar tayi ihu ta ce “Menene kuma?”Ya ce “Da na kawo miki kajin mutum goma sha biyu, ki ka cinye ki ka yi kyautar wasu, kin tambayi ta mecece?”Cikin rashin fahimta ta ce “Ban gane ba, ka ce a gidan oganka ka karɓo”.”To gaba sai ki dinga tambaya, kwaɗayayyiya, ki ka din ga ci kina rabarwa, ni sai dai ki sammini, yanzu kuma tambayata lafiya? Ba lafiya ba”Cikin rauni ta ce “Master” ya ce “Yes””Dan Allah ka koma ɗakinka” ya kwanta ya ɗora ƙafarsa ɗaya kan ɗaya ya ce “Zuriya fa ki ke so, ki ke wani basarwa” Jauhar ta yi danasanin faɗar maganar nan.Kawai ta zauna a zaune tana kallonsa, sai kaɗa ƙafa yake yi.”Zo ki kwanta, na ga lokacin da baki da lafiya, har wani ƙara lafewa ki ke yi, bisimillah” yayi maganar yana nuna mata ƙirjinsa.Pillow ta gyara ta kwanta a kai, ta ƙi kula shi, mutumin da suka wuni ba sa magana, saboda tsabar son tayar da tarzoma, ya lallaɓo yana tayar da wani tsohon zance.Da asuba ta riga shi tashi, ta shiga ta yi wanka, tayi alwala ta zo tana tashinsa, ƙarshe sai kusan shida da rabi suka yi sallar, bayan ya saka ta canza wani wankan da alwala. A wurin da tayi salla, ta kwanta a kan sallaya ta cigaba da bacci.Iya ƙoƙarin sa yake yi kar ya sha komai, ya kasa jurewa, kamar zai fita hayyacinsa, ya lallaɓa ya dawo ɗakinta, ya tarar tana kwance a ƙasa tana bacci, boti ma yayi lakur a kan sallayar yana bacci.Tankaɗe boti yayi can gaba, ya kwanta a kusa da ita, ya ƙura wa fuskarta ido, ya kai bakinsa ya sumbaci goshinta.A ranar aka saka wa jauhar fankar solar, da ƙwai, ta din ga murna tana yi masa godiya.Sai dai Al’amin ya uzzura mata, duk dare, sai ya ce mata wai shan fanka ya zo, zafi yake ji, sai da ta gaji ta ce “Dan Allah master ka ɗauke fankar nan taka ka mayar ɗakinka , ko na huta”Ya ce “A’a ai dama ke na sayawa, dan haka gara na din ga zuwa nan kawai ina shan isakar, idan na mayar da fankar can, bayan iska kuma takura mini za ta yi din ga yi”.Ta ce “A taƙaice dai, ni ce fankar kenan?”Ya ce “Eh mana, ke ga taki fankar, ni kuma ga tawa” yayi maganar yana nuna ta.***Kwanaki suka cigaba da tafiya, sai dai tsakanin Alhaji mu’azzam da Hafsa sai dai kallo, ranar da uwargidansa ta bari ya zo ɗakin hafsa, kawai ta ga ya nemi wuri ya kwanta.Duk da irin kunya da kawaici irin ta ‘ya mace, sai da ta cire kunya ta ce “Wai ni Alhaji, menene matsayina a wurinka ne? Na kasa gane kan wannan al’amarin”Ya kalli hafsa ya ce “Jauhar, yakam…A fusace ta ce “Wace irin jauhar kuma? Wulaƙancin naka da rashin mutunci har ya fi da, ga mari ga tsinka jaka? Tun ranar da jauhar suka zo, ka rasa sukuni, ka ke kirana da sunanta ba na so”Ya ce “Am sorry mistake ne, ki ƙara haƙuri ki bani lokaci, na yi wa Safiyya Alƙawarin babu abun da zai shiga tsakanina da ke, har sai lokacin da ta samu nutsuwa hankalinta ya kwanta, tana cikin damuwa sosai da sosai, kin san tana da kishi ne sosai da sosai “.Kamar ta ɗura masa ashar ta ce “Au har gaya mata ka ke ba abun da ya shiga tsakanina da kai, har sai ta yadda? Ita take aurena kenan? Bakomai na gode, ta ci lokacinta when it comes to my turn, zata gane shayi ruwa ne” ya girgiza kai ya ce “Kin ga ba na son rigima, ba zaki zo ki sameni, ina zaune lafiya da iyalina ki ɗaga mini hankali ba Please, ina respecting farincikin matata sosai da sosai “Hafsa ta ja tsaki, ta fice ta bar masa ɗakin.Al’amin na zaune a falon Indabo, ana ta tattauna yadda al’amura za su tafi kafin lokacin zaɓe, dan wata ɗaya kawai ya rage babban zaɓe, wanda yake dai-dai da lokacin sallar layya.Ya rage daga Al’amin sai P.A da Indabo yana ta sake jaddadawa Al’amin, idan aka ci kujerar nan za su ji daɗi, dan tun yanzu an ce masa idan ya samu senator ɗin nan, akwai vacancyn mutum uku za a bashi a NNPC.Al’amin ya ce “A cikin yarana, ko Nura guduma ne, ina son a samo masa aiki ko direban manyan motoci ne, yana can na saka ana koya masa jan manyan motoci”Indabo ya ce “Ba ka da matsala, kawai ku yi aikinku, duk akwatin da ku ka ga zata bayar da matsala, ku tayar da tarzoma. Maganar da nake yi maka, a yarjejeniyar da muka yi da uwar jami’iyya ta ƙasa, kan na dawo cikinta, nan da wasu shekaru, za a tsayar da Abdul takarar mataimakin gwamna”Al’amin ya ce “Har masu shaye-shaye ake tsayarwa su yi jagorancin al’umma kenan?””Shaye-shaye kuma, yaron da yake karatu a waje, in sha Allah shi zai zama mutum mai ƙarancin shekaru da zai zama gwamna””Menene sadakin aikina?”Indabo ya ce “Me ka ke so ayi?”Hajiya Bilki ce matar indabo ta shigo da laces, da atamfofi da lesuna sun kai talatin a hannunta, ta shigo ta zube a gaban Indabo.Ya kalleta ya ce “Madam ya dai?”Ta ce “Kala goma zan zaɓa ka saya””Ke dai kullum cikin ɗinka tsumma, ko gajiya ba kya yi””Kana shirin zama distinguish, ba dole na ɗinka sutura ina shiga ina fita, ina barazana ba”.Indabo ya ce “To ki ɗauka, ina ta jiran Kwamishinan ayyuka ne, rage kuɗin wata kwangila, mu ƙara rage na campaign, ya haɗa kayansa yana kan katanga, jami’iyyar da tayi nasara zai koma da an yi zaɓe.Ala’amin ya tashi ya tafi gaban kayan, ya zaɓo zuƙa-zuƙan lesuna, guda uku, da atamfa uku.Indabo ya ce “Yaya saya zaka yi?””Kai dai zaka saya, daga cikin sadakin aikina”.Hajiya Bilki ta ce “Kai, lesunna hannunk fa dubu tamanin guda biyu, ɗaya dubu hamsin da takwas, atamfofin nan dubu arba’in da biyar, har nawa zai baka? Kuɗin da yawa ai”Ya kalleta ya ce “Ke zaki biya? Kuɗin kwangilar mutane za a sata a biya miki ai, wannan ma ya biya, ai ba kyauta zai bani ba, jinina da rayuwata zan saka a hatsari dan samun nasararsa. Ya miƙe da kayan a hannunsa, ya kalli Indabo ya ce “Sauran kuɗina za su zama ajalan a kanka, komai daren daɗewa zan waiwaye su, yadda ku ke ƙwamusar kuɗin mutane ta gajimare dole a din ga kasawa da mu, idan ana son a ga dai-dai, tun da damu ake wahalar waccan ‘yar yarinyar ta gidana, itama yakamata a din ga damawa da ita. Kuma rabon tallafin karatu ma, a saka mini ita a ciki”Indabo ya ce “Aminu kenan, shikenan jeka Allah ya taimaka”Ya haɗa hannayensa biyu ya ce “Sa’a dai” ya fice daga falon.Hajiya Bilki ta ce “Gaskiya honorable, yaron nan yana wuce gona da iri, kamar tsoronsa ka ke ji”Ya ce “Ba tsoronsa nake ji ba, aikin da yake yi mini yana da yawa, kasada duk girmanta yana ɗauka. Akwai lokacin da tilas na yakice shi ai”.Al’amin bai shiga da kayan gida ba, sai cefane da yayi na abincin dare.Ya tarar ta yi dambu tayi wa dambun miyar jajjage, da salad da awara.”Ke dai Allah ya yi miki iyayi, dambun da ake sakawa mai, ki ke yi wa miya, har da wata munafukar awara”.Jauhar ta ce “Idan munafuka ce, bamu mu raba da ni da boti, shikenan ba canji, kullum sai dai dambu da mai? Ai gara a din ga upgrading””Sai dai ya mutu da yunwa kuwa, to ai awarar ce, ‘yar kaɗan””Wai master ba ka iya abun ‘yan gayu ba? Babu naman da zan saka a cikin miyar, sai na haɗa da awara, bai bada ma’ana ba? Ko sai an cika kwanon da awarar passion ce a kai”Ya taɓr baki ya ce “Eh to, gashi nan dai, zoɓon ma kamar yayi tsami, amma kwantai ne na jiya ne ko?””Mmmm, na waccan shekarar ne” ta bashi amsa tana cigaba da aikin gabanta, na shirya stone.Tsoknarta yake yi, ya matsata tayi tsiwa, ita kuma taƙi.”Yaushe WAEC ɗin ku za ta fito ne?”Jiki a sanyaye ta ce “Ta kusa, har ba na son tunawa da ita””Saboda ba ki yi abun arziki ba ko?””A’a lokacin kana tsare, bana iya karatun”Ya ɗan rausayar da kai ya ce “Eyya, abun tausayi, Yallaɓai dan Allah ku sake shi, ba shi da laifi, laifina ne, wallahi ba shi da lafiya ma, master dan Allah ka gaya musu ba ka da laifi” yayi maganar cikin sigar kwaikwayon yadda ta yi waccan ranar.Murmushi ta yi ta ce “Kada Allah ya kawo abun da ba zai wuce ba, a lokacin nan ji nake a duniya kamar nikaɗai aka tsana wallahi. Da aka ce mini an kai ka prison, kawai na saddaƙar ciwon zuciya ya kama ni, kuma wai ka ce kar a kaini na ganka, ai na ji haushi, a duniya ba zan manta da su yaya walid ba, duk da suna taimakawa wurin ƙara ingizaka a shaye-shaye, amma sun tsaya tare da ni a lokacin da kow yake ganin idan ya taimaka mini zai kwana a ciki”Ya ce “Allah sarki ‘yar madara, ba na son in ga kina kukan nan ne, ko kina yi wa ‘yan sanda magana, suna wani yanƙwana mini ke, raina ɓaci yake yi shiyasa na ce kar a sake kawo ki”.Ta ce “Gashi ya wuce, duk da lokacin gani nake kamar ba zai wuce ɗin ba” Ta tashi ta shiga ɗaki, ta dawo ta tarar da robar alawar madarar da take sayarwa, a gefensa bakinsa kuma yana ta tauna, ta ɗaga robar ta ce “Alawata ka ke sha ko?””Eh, ta guda uku na sha sittin, a rage mini naira goma hamsin kenan”Sororo take kallonsa, “To ai ba a jikina ake tatso madarar ba, da zan sayar da ita ashirin ashirin, naira hamsin ce fa duk ɗaya “Ya waro ido ya ce “Ki ji tsoron Allah, har na sha ta ɗari da hamsin, gaskiya saba’in zan bayar”.Abun da yake so ya gani ɗin ta fara, shagwaɓa tana cewa sai ya biya ta.”Gaskiya bani da kuɗi yanzu, zo ki shanye abarki” ya fito mata da harshen sa.Ta harare shi ta ce “Bana so, kuma idan na zo yi maka wanki na tsinci kuɗi, sun zama nawa””Eh ai dama kin saba kwashe mini ‘yan canjina, da kayan cajina shiyasa ki ke yi mini wanki ba dan Allah ki ke yi ba” ya tashi kamar zai tafi, amma ya riƙeta, yayi kissing ɗin ta, ya ce “To kin ga tare muka shanye, yanzu talatin ma zan baki” ya saka hannu a aljihunsa ya ciro dubu biyu ya ɗora mata a wuyanta ya ce “Gashi nan, uwar son kuɗi””Ai talatin ka ce zaka bani, saura dubu ɗaya, dubu uku yakamata ka bani”Ya ce “Biyoni ɗaki ki karɓa” Ta ce “A’a na yafe maka sauran, amma kar ka sake”Sosai wani bond mai ƙarfin gaske ya shiga tsakaninta da shi, har mamakinsa take yi, duk da mai hali baya fasawa, idan miskilancinsa ya motsa, ko kuma ya cake, ba ya sarrafuwa ta daɗi, amma haka take jurewa. Ga babban abun da yake ci mata tuwo a ƙwarya yanzu, wasu lokutan idan ya dawo daga shaye-shayen sa, da ƙaurinsa da komai yake zuwar mata, gashi ba abu ne mai sauƙi ba, ta nuna masa hakan ba, dole sai ta cikin hikima da dabara.Haka zata zauna, komai daren da zai yi sai ta jira dawowarsa, ta saka shi yayi wanka, ya canza kaya.Yau bayan ya bar ɗakinta, bayan ta idar da salla ta je ta same shi, a zaune a kan katifa.Ta ɗauki kwalin sigarin gabansa, ta ciro guda uku ta bashi ta ce “Wannan ta isa, kar a sha sama da haka dan Allah””Bani in je ƙofar gida in sha”Ta ce “A’a ai shan nake so ka rage sosai da sosai, wannan ta isa”Ya juya mata baya ya shanye, tana zaune tana jiransa, ta bubbuɗe window, saboda hayaƙin ya fita.Jira yake ta fita ya kuma kunna wata, amma ta cire masa shirt ɗin jikinsa, ta ce ya kwanta, ya kwanta yana jiran ta fita, amma ta kwanta a jikinsa, a hankali ta din ga karanto azkar ɗin safiya.Babbar salla na ta ƙaratowa, jauhar hada-hadar neman kuɗi, ta cigaba da kankama, Al’amin bai taɓa saka ido a kan abun da take samu ba, dan yanzu iya ƙoƙarin sa yake yi, ya yi cefanensa, duk da kuɗin da take ɗan samu, in dai ya ji kuɗi a jikinsa, a kaso ɗari tamanin, ita zai kashewa, bai fi ya ƙarar da kaso ashirin ba, goma ya rabar goma ya yi shaye-shaye.Idan ta fuskanci da kuɗi a hannunsa, ta din ga lallaɓa shi kenan, ayi wani abu mai muhimmanci, idan ba haka ba, ba zai sai abubuwan da suka fi buƙata ba.Kuma babbar hanyar samun kuɗinsa, wurin Indabo, ya din ga tatsarsa kamar mai, duk da yana samun hanyoyin samun kuɗi yanzu, tun da kakar siyasa ce.Ana jibi salla, ya ba wa jauhar kuɗi, wai tayi kitson salla ita ma, ta je ayi mata zane a hannunta.Ta dawo ta tarar da kaya a kan gadonta, ta zazzage taga kaya na alfarma duk an ɗinka su, har da takalmi da turare.Mamaki ya cikata, yana dawowa ta fito falo ta ce “Master kayan waye a kan gadona?””Na kishiyarki ne””Wace kishiyata?””Ban sani ba, ko ina da wata matar ne bayan ke”Gaba ɗaya ta rikice ta ce “Master wai nawa ne Gaba ɗaya?”Ya ce “Naki ne babyn roba”Har ƙasa jauhar ta durƙusa tana yi masa godiya, ta rasa ma wace kalar godiya za ta yi masa, har da matse ƙwalla.”Ni ba irin wannan godiyar nake so ba, a sheƙa mini girki, a yi wa fankata caji, in sha iska sosai” sunkuyar da kai ta yi, cikin matsananciyar jin kunya.”Allah ya ƙarawa fankata gudu, tana ba da iska sassanya, ƙarfin gudunta, bai sanya tana bada iska mai cutarwa ba””Amm bari na je na yi jajjage” ta juya ta nufi ɗaki.”Dama a ɗaki a jajjagen” ko waiwayowa ba ta yi ba, ta shige.Ranar idin babbar salla ma, tare suka tafi sallar idi. Ta sha kwalliya, tayi kyau sosai da sosai, a abun da bai fi wata guda ba, ta yi ƙiba fatarta ta ƙara fresh. Ta sha ɗaurin ɗan kwali, hannunta yayi kyau da zanen lalle ja da baƙi. Su liti suka din ga kiransa a waya, suna jiransa, yaƙi fita, sai da suka zo har gida sannan suka fita da shi, bayan sun kwashi wainar masa da sinasir da miyar agushi.Bayan la’asar sosai, ya dawo gida da nama kaya guda, har da karfatar sa, ga kayan ciki da uban nama.Kamar tayi kuka ta ce “Master, aiki daf da magariba ya zan yi?””Ke da aiki ba ya yi miki wahala, ɗan wannan aikin zaki yi raki?”.”To aikuwa sai ka tayani, kuma ba ka sayo itace ba”Ya kalleta ya ce “Ba a yi a gas, an hanaki shiga hayaƙi”.”Gas ɗin dubu nawa za a zuba? Dole sai a itace”Ya kalli naman, ya ce “Ki shiga ciki, bari na aika nura ya sayo itacen, su walid suna waje, sai su shigo mu yayyanka”Ƙarshe dai hayaƙin da ba ya so, sai da ta shiga, har sha biyun dare suna aiki ita da shi.Duk da haka aikin bai ƙare ba, sai washegari, ta ce masa tana son zuwa gida, ya ce sai ta gama yi masa kwalliyar salla kan ta fita.Ya samu dambun nama da cin-cin, ya din ga tumurmusa, jauhar ta ce “Ni ban gane wannan lamarin ba, gaskiya rabawa za ayi. Kana ta ci idan cikinka ya ɓaci babu ruwana”.”Ke ki ke da ruwa kuwa”.Sai huɗu ga salla, sannan ya bari ta je gida, ya kaita da kansa.Aka yi sa’a Hafsa ma ta je gidan, tun da ta jauhar ta je, suke kallonta da kayan jikinta.Sai da mama ta magantu ta ce “Jauhar wannan leshin fa?””Mama kayan salla ne””Kin san kuɗin leshin nan kuwa?”Ta girgiza kai ta ce “A’a shi ne ya kawo mini”Ta kalleta ta ce “Wai sana’ar me yake yi haka ne?”Tayi murmushi ta ce “Yana sana’oin sa, kuma kin san yana tare da ‘yan siyasa”.Hafsa ta din ga kallon jauhar, yadda take komai nata cikin walwala, kamar ba ta da wata damuwa, duk da tana auren ɗan daba.Bayan jauhar ta ba su nama, dambun nma da cincin, aka din ga gaya wa jauhar, ai mijin hafsa rago ya kawo.Ta ce “Masha Allah, Allah ya saka da alkhairi” Duk yadda Hafsa ta so mazewa, sai da yanayin ta ya nuna akwai damuwa.Sai yamma Al’amin ya dawo, ya ce ta fito su tafi, babu yadda ba ta yi da shi ba, amma ya ce ba zai shiga ba.Gidansu ma da ya kaita, a waje ya tsaya, a gurguje jauhar ta shiga ta gaisa da Rahila, ta bata naman sallar sai dai ita ma, kayan jauhar kawai take kallo.Ana gama bikin salla, aka shiga hada-hadar zaɓe.Hankalin jauhar ya kasa kwanciya, saboda yawan shige da ficen da yake yi yawa.Yau ake zaɓen sanatoci, dan haka tun kan ta tashi daga bacci ya fice.Har yamma shiru bai dawo ba, kuma wayarsa ba ta shiga.Gaba ɗaya jikinta a sanyaye yake, jikinta  ya din ga bata akwai matsala, har bayan magariba bai dawo ba.Jin ana knocking ɗin gate, gabanta ya faɗi, ta saka hijjabi ta fito, ta ga Nura guduma a tsaye ta ce “Yaya wannan karon me kuma yayi?”Ya ce “Ki sako hijjabinki mu tafi””Mu tafi ina?””Asibiti!””Innalillahi wa Innalillahi raji’un!”

Ayshercool 08081012143.

Back to top button