Hausa novels

Abban Sojoji Chapter 71 Book 2 Complete Novel

Abban Sojoji Chapter 71 Book 2

The Father Of Soldier

Written By: Hafsat Bature

Ga duk maison karanta littafin Abban sojoji,zai biya 300 ne,za’a tura mashi tundaga farko har inda muka tsaya,kuma zai cigaba da samun update dinshi akai akai,ga wanda ke buƙata  zai tura mun message ta whatsapp ɗina (08103884440) kada ku bari abaku labari

 

Abunda ya faru,lokacin da wata mata ta kira junaid da sunan mommynshi don yazo ya ɗauketa a airport,jiki na rawa junaid ya shige cikin motarshi ya kama hanyar zuwa airport bayan ya fita daga gidanne ya tuna da tace in ya fito ya sanar da ita,fiddo wayarsa yayi da niyyar kiranta,tunanin taya zai kirata ma ba number ya shiga yi,adaidai lokacin ta sake kira tambayarshi tayi ya fito ne,ya amsa mata da eh yana a akan hanyar zuwa,cigaba da tafiya yayi zuciyarshi cike fal da son ganin mommynshi,driving yake yi yana ayyana farkon haɗuwarshi da mommynsu baisan wani irin runguma zaiyi mata ba,yayi zurfi acikin tunaninshi kwatsam sae ga wasu jerin motoci sun kusa goma sha biyu,baƙaƙe kuma da black tinted,da gudun gaske suka nufo inda junaid yake,koda junaid ya lura da motocin nan fa hankalinshi yayi mugun tashi,ƙarasowarsu ke da wuya suka zagaye motar shi,yadda bazai iya kubce masu ba,nan fa hankalin junaid yayi mugun tashi,jikinshi ya shiga rawa,tsoranshi kar ace mutanen da mommy azeema ta sanar dashi cewa suna bibiyar rayuwarshi ne,zama yayi acikin motar hankali a matukar tashe,

ɗaya daga cikin motocin aka buɗe,sae ga wani gabjejen mutun faffaɗan gaske sanye cikin suits,kai tsaye ya nufi motar junaid hannu yasa tare da knocking glass ɗin motar,zuge glass ɗin junaid yayi atsorace yana kallonsu sae faman haɗiyar yawu yake yi da kyar,

kafin yayi wani yunƙuri Mutumin nan ya buɗe motar tashi,gaba ɗaya ya cakumi junaid ya toshe mashi baki,ya nufi cikin motarshi dashi,bayan ya sanyashi acikin motor,atare suka tashi motocin da gudun gaske suka bar wurin,

junaid dake a back seat na motar tuni ido ya raina fata,hawaye suka shiga wanke mashi face ɗinshi,muryar shi tamkar zaiyi kuka yace”Su wanene ku?laifin me na aikata maku?dan Allah kada ku rabani da rai na,inason na sake ganin Abbana…..’bai kai ƙarshen maganar tashi ba,ɗaya daga cikinsu ya daka mashi tsawa tare da cewa”Shut up!ko tari ka ƙara yi saina fille maka kai,”

Jin haka yasa junaid yayi tsit zuciyarshi na bugawa da ƙarfi da ƙarfi,

Wani katafaren gida suka shiga tare da shi,bayan sunyi parking ɗin motocin,ɗaya daga cikinsu ya buɗe motar tare da ɗauko junaid asaman kafaɗar shi,ya wuce dashi cikin gidan,a babban falon gidan ya sauke shi,sannan ya juya ya fuce,

To fa,tsayawa junaid yayi cikin tashin hankali yake kallon haɗaɗɗen falon komai a gyare tsaf,tunani ya shiga yi mai yasa suka kawo shi nan suka ajiye shi?ko dae kidnapping ɗinshi sukayi ne?hannu yasa yana share hawayen shi,bai kammala wiping ɗinsu ba,yajiyo takun takalmi kwas kwas,

A firgice ya ɗago don yaga wanene,zuba mata ido yayi yana kallonta,daga saman stairs take saukowa down,jikinta na sanye da doguwar riga fara mai shegen kyau tabi shape ɗin jikinta,ƙafafunta kuma na sanye da takalma high hills farare duk da tsayin da take dashi don sam ba gajera bace,ba ƙaramin kyau shigan tayi mata ba,kasancewarta farar fata,wuyanta na sanye da ziririyar sarƙa fara ta diamond,hannunta kuma na sanye da Zobe ɗaya kacal a middle finger,shima na diamond ne,ta ɗaure gashin kanta abaya,mai tsayi wanda launinsa yake tamkar golden yellow,

 

A hankali ta ƙarasa saukowa daga saman benen,sannan ta tsaya tana kallonshi daga inda yake tsaye,duk da akwai tazara atsakaninsu amma suna iya ganin juna sosai,ƙare mashi kallo tashiga yi,burinta junaid ya fara shaida ita wacece kafin ta sanar mashi,

hakanan ya dinga jin gabanshi na faɗuwa rass rasss,batare da jin tsoro ba ya tunkareta sai da ya kusa kaiwa inda take sannan ya tsaya yana kallonta,ƙwayar idanunta yabi da kallo blue colour wanda hakan ya tabbatar mashi da cewar mommynsu ce, dama kuma yasan ta a hoto,komai na fuskarta irin na Babban yayansu ne,duk da ta kwana biyu aduniya amma hakan bai 6oye kyawun fuskarta ba,tamkar ƴar shekara 30 haka fuskarta take,hatta jikinta yana nan yadda yake da kyau da kuma diri,

A hankali junaid ya furta”Mommy!is you?

jinjina mashi kai tayi alamar eh,da gudun gaske ya ƙarasa tare da faɗawa jikinta,sosai ya ƙankameta saboda tsabar farin ciki ya fashe mata da kuka,nan take itama kukan yazo mata atare suka shiga yin kukan babu mai lallashin wani,tamkar zasu haɗe jikin junansu su koma ɗaya haka suka ƙanƙame kansu,daƙyar Alexandra ta iya dakatar da kukan nata,ta sanya hannayenta tare da ɗago da fuskar junaid tana kallonshi,hawaye sun wanke mashi fuskarshi tass,

muryarta na rawa ta ambaci sunan shi”Ro..meo.ɗina,’

Cikin shessheƙar kuka junaid yace”Mommy,ashe zan sanyaki acikin idanuna,bansan da wasu kalmomin zan bayyana maki irin farin cikin da nake ciki ba,i luv u so much mom….’

Jikinta ba ƙaramin sanyi yayi ba,duk irin watsin da tayi dashi tabar Nigeria,hakan bai hana shi sonta ba,

Kwantar dashi ta sake yi asaman ƙirjinta,ta sanya hannayenta tana ɗan bubbuga bayanshi,kafin ta mayar da hannunta ɗaya acikin sumar kanshi,ta jima tana mamakin girman shi,ta tafi ta barshi a lokacin da yake ɗan jinjiri dashi,amma yanzu tadawo ta same shi ya girma ya zama babba,ba ƙaramin farin ciki taji ba,mara misaltuwa,

ɗago dashi ta kuma yi daga jikinta cikin sanyin murya tace”romeo ɗina,kayi haƙuri ka daina wannan kukan duk da nasan na farin cikin ganina ne,ni kaina bazan iya misalta farin cikin dana ji ba,wai yau ni ce tare da babyn dana bari yana jinjirinshi,ya girma ya zama babba,nayi danasanin tafiya nabarka romeo,nayi kewarka sosai,hakanan na raba kaina dakai,ba don bana sonka ba romeo,zan iya cewa nafi sonka fiye da kowa aduniyar nan…..na godema Allah daya nunamin wannan ranar….inaso na sake neman yafiya a wurinka saboda na cutar da rayuwarka sosai,ko wani yaro lokacin da yake jinjiri burinshi yaji dumin mahaifiyarshi,ya kasance atare da ita don samun kulawa daga gareta a koda yaushe,koda ace yana da uba,amma kai baka samu wannan gatancin ba,ka tashi hannun maza ba’a hannun mahaifiyarka ba,baka samu soyayyar nan ba,duk da mahaifinka yayi ƙoƙari sosai wurin gina rayuwarka tayi kyau,haka ƴan uwanka ma ba su bari ka zubar da hawayenka ba,amma duk da haka nasan abun ya jima yana maka Ciwo…”

Tana ƙarasa maganar,ta zube saman guiwowinta agabanshi,tana roƙon yafiyarshi,hakan ba ƙaramin tayar mashi da hankali yayi ba,cikin sauri shima ya zube saman guiwowinshi suna fuskantar juna ita dashi,

“Mommy dan Allah ki tashi,banason kina duƙamin,komai ya wuce yanzu tun da kin dawo wurinmu da ranki kuma da lafiyarki,har yanzu kina da sauran damar da zaki gyara kuskuren da kikayi abaya mommy,” ashagwa6e ya ƙarasa maganar,murmushi ta saki tana kallonshi,ji take yi da tana da ikon da zata mayar dashi cikin cikinta,taƙara haifo shi da tayi,don kawai ta bashi wannan kulawar daya rasa,

Sun jima a wannan yanayin,kafin daga bisani suka miƙe tare,ta ruƙo hannunshi cikin nata,ta wuce dashi upstairs ɗaya daga cikin bedrooms ɗin dake a wurin suka shiga,ɗakin ya haɗu sosai,

“Mommy me yasa ba kije gidaba?wurinsu Abba su ganki? Yayi tambaryar yana kallonta,

“I just came because of u junaid,inaso mu samu lokaci sosai atare,ka ganni dakyau nima na ganka da kyau,tun yanzu in fara aikina na  baka kyakkwayar kulawa kamar jariri,in yaso gobe zamu shiga gidan da safe ko?

Murmushin jin dadi junaid yayi tare da cewa”Eh,mommy,dama ni yakamata in fara ganinki tunda dama nine ban sanki ba a zahiri”

Download>>>

“Bansani ba ko kana jin yunwa,amma zansa akawo mana abinci,in baka abaki kaci ka ƙoshi,yau dae atare da babyna zamu kwana,’

Dariya junaid yayi,ba ƙaramin daɗin maganarta yaji ba,sosai mommynshi ta shiga bashi kulawa a wannan lokacin,

Kunji yadda akai junaid ya kasance tare da mommynshi,har ta ɗauko ma Abbansu video ɗinsu saman gado ta tura mashi,abunda yasa kuma Abban bai gane Voice ɗinta ba,shine da kanta tayi amfani da wayarta wurin canza muryarta don ta tsoratar da Abbansu.

 

💋Boss Bature💋

 

fitowa Abbansu yayi daga cikin ɗakin nashi fuskar nan tashi awashe saboda tsabar farin cikin dawowar Alexandra,bakomai yafi faranta mashi rae ba face Junaid daya gani rungume ajikinta,yaji daɗi sosai,ko ba komai Junaid dae ya haɗu da mommynshi,hankalinshi zai ƙara kwanciya,

 

Bai sanar masu da zuwan nata ba,saboda sunyi waya da ita ta sanar dashi cewar till tomorrow zasu shigo gidan don tana bukatar kasancewa da junaid don su kara fuskantar juna sosae,hakan yasa ya bari kawai sae goben sannan su ganta unexpected,duk da a kagare  idanunshi suke da suyi tozali da ita.

 

Gaba daya suka haɗu atare suka wuce masallaci,

 

Jin shiru hayaam bata fito ba tsawon lokaci,yasa Azmee leƙawa ɗakinta,anan ta same ta zaune dirshan gefen gadon ta zabga uban tagumi,jin motsin mutun yasa ta ɗagowa fuskarnan a yamutse ta kalli azmee,

“Hayaam wai dama duk budurin nan da akeyi acikin gidan nan kina ɗaki ƙumshe”?

Jin abunda azmee tace yasa tace”hmmmm,to ina zani Aunty azmee?babban yaya ya kore ni daga gidan nan,nasan muddin na leƙa waje ya ganni sai yasa an kora ni daga gidan nan,’

Cike da mamaki azmee tace”Subhanallahi!taya akai hakan ya faru?laifin me kika aikata mashi da har ya koreki daga gidan nan?shi da ma bai damu da mutane ba”

ta6e baki hayaam tayi kafin tace”Ni banyi mashi laifin komai ba,Sehrish ce ta shiryamun makircin da yasa har ya kore ni,batare da nayi mashi laifin komai ba,”

Tunda tasoma magana azmee ke kallonta,ga rashin gaskiya nan ya bayyana ƙarara a fuskarta,taya akai ma Sgr yasan da zamanta da har zai kore ta?dole sai in itace tayi mashi shisshigin da yasa har ya ganeta kuma ya kore ta,

“Allah ya kyauta toh,!yanzu ya zakiyi kenan?kinfa san halin shi!dole fa ki tattara kibar gidan nan!in ba haka ba wlh zaki fuskanci mummunan hukunci daga wurinshi,’

Hankali tashe hayaam ta miƙe tsaye tana kallon Azmee tamkar za tayi kuka tace”don Allah aunty azmee ki taimaka mun,wlh banso in bar gidan nan!na saba da zama acikinshi,anan nake samun duk wani jin daɗin da nakeso,acan gidanmu duk babu waɗannan kayayyakin more rayuwar,nasan zaki taimaka mun,”

Dariya azmee tayi tana kallonta ko yaushe tazo da har zata ce tayi sabo da mutanen gidan ta ayyana a ranta,

“Aunty azmee dan Allah ki taimaka mun,in xauna acikin gidan nan,nasan yana jin maganarki,ki roƙa mun shi akan yabar ni in cigaba da zama,wlh bazan ƙara shiga shirgin kowa ba,zanyi rayuwata cikin salama,”

Azmee tace”Tabɗijancan!so kike kija mun bala’e ko?ina zaman lafiyata agidan nan,Wacece ni?da har kike tunanin Sgr zaiji maganata?kin manta matsayina ne acikin gidan nan?kefa kike da alaƙa dasu ko kin manta ne”? Da biyu azmee tayi mata maganar saboda wulaƙancin da hayaam tayi mata,

Magiya hayaam ta shiga yi mata tana roƙonta akan ta nema mata mafita tamkar zata zuƙunna mata saman guiwarta,don ita sam bata shirya barin gidan yanzu ba,tabb yo mima akai kenan”ta fada cikin ranta.

Sosai abun yaba azmee dariya,

“Hanya ɗaya ce hayaam in zaki iya!idan har kinason cigaba da zama acikin gidan nan”!

jiki na rawa hayaam tace”Ina sauraronki aunty azmee,wlh koma manene zan iya ni,”

Azmee taci gaba da cewa”daga yau zaki dinga yin shigar maza,kinasa gashin baki kamar yadda sehrish tayi a lokacin da tafara aiki acikin gidan nan kinga sai kizama kamar sabon mai tayani aiki”

Waro ido waje Hayaam tayi tare da cewa”Haba Aunty azmee ni zanyi shigar maza?so kike na ƙasƙantar da kaina har yarinyar can ta raina ni”

Azmee tace”that’s the only solution,if not sai dae fa ki tattara kayanki ki bar gidan nan!”ta karasa maganar tana jiran jin ta bakin hayaam din don tasan da kyar zata amince dama shiyasa ta fadi mata hakan,

gyaɗa kai hayaam tayi tace”shikenan zanyi tunani in ga in zan iya,kafin nan zanci gaba da 6oye ma ganinshi”

Azmee tace”to shikenan kiyi yadda kika ga yafi maki,ni dai gaskiya ba ruwana,kuma fa dole ki rika futowa kina taya ni aiki,indai kina a cikin gidan nan, don bazai yiwu ba ki zaune a daki baki komae gaskia ”

Hannu hayaam ta aza akanta tana faɗin”Nashiga uku!

dariya Azmee tayi kafin ta kuma cewa”hayaam zamanki fa bazaiyiyu acikin gidan nan ba,Sgr ya riga da ya kore ki!muddin ya sake ganin fuskarki dole ya hukuntaki,kuma kinga gwaggonsu ta katsina tazo,!matar nan bazata ta6a bari ki zauna acikin gidan nan ba,in har taji cewa ke ƙanwar matar yayyansu ce,nan zaki ga tashin hankali,sae ta kunyataki acikin jama’a,shiyasa nace kiyi shigar maza kawai,Ni zan taimaka maki muna yin aiki atare inyaso duk wanda ya tambayeni xance mashi abokin aiki ne na samo,nasan babu wanda zai zargi wani abu,

Komawa hayaam tayi ta zauna gefen gadon cike da damuwa,gaba ɗaya taji ta tsani kanta,da tana zaman lafiyarta acikin gidan,kwaɗayinta da zalamarta su suka ja mata,gashi ita gskia bata jin zata iya yin wani shigar maza wannan ai kaskanci ne,

“Na manta ban sanar maki ba!”

Rai a6ace hayaam tace”Menene!”

Azmee tace”SEHRISH TAGA ƳAN UWANTA,ASHE ƳAN UKUNE SU,YANZU HAKA SUNA ACIKIN GIDAN NAN!BAKI GANSU BA,ABUN FARIN CIKI KAMANNINSU IRI ƊAYA SAK!BAKI TA6A BANBANTA SU,”

A razane Hayaam ta miƙe tsaye hannunta dafe da saitin zuciyarta tace”WAI DAGASKE AUNTY AZMEE?

AZMEE TACE”Zan maki ƙarya ne?yaran suna nan,kyawawan gaske,HOSANA DA JAHAD!!!!!”

Jiki amace hayaam ta koma ta zauna,gabanta na faɗuwa rasss rasss!tama rasa ina zata tsoma ranta taji dadi,

Murmushi azmee ta saki tare da juyawa ta kama hanyar fita daga ɗakin,buɗe kopar tayi tare da sa kai ta fuce,

Kamar jira take azmee ta fita,nan fa ta fashe da kuka kamar ranta zai fita,saboda tsabar 6acin rai,wani irin ƙululun baƙin ciki ne taji ya tokare mata maƙoshinta,komae ya jagule mata,tabbas tana bukatar tayi magana da Aunty laila,lokaci guda yadda sukai da yaya babbar ya shiga dawo mata, sambatu tashiga yi tana bugun bed mattress kamar wata zautacciya,

 

Bayan kammala sallar isha’e,atare suka dawo cikin gidan,a babban falon suka kuma zama kamar ɗazu dae,

 

Gyaran murya Abbansu yayi kafin yace”Ina yaran suke ne?wani yaje ya kira mana su,domin jin ta bakinsu”

Miƙewa fawan yayi kamar dama jira yake yi,wucewa ɗakin sehrish yayi bayan ya isa ya kwankwasa masu ƙopa,jahad ce ta buɗe mashi kopar jikinta na sanye da hijabi da alama bata jima da kammala salla ba,

Fuskarshi ɗauke da murmushi yace”Abba nason ganinku,idan ba damuwa ku fito mu tafi atare,”

Jahad tace”Toh,bari na kirasu,”ta fadi hakan tare da juyawa ciki ta kira hosana da sehrish wadda har lokacin bata motsaba,tana nan saman gadon ta ƙanƙame jikinta,

“Hosana kuzo Abbansu na son ganinmu!hada sehrish kema ki taso,”

Maƙe kafaɗa sehrish tayi alamar bazata taso ba,

“Sehrish dan Allah kidaina abunda kikeyi,nasan duk don saboda ganinmu ne,idan har baki so zuwanmu ba zamu bar gidan nan,”acewar jahad,

ɗaure fuska Sehrish tayi tare da kawar da fuskarta gefe tana faman hura hanci,

babu yadda basuyi ba akan sehrish tabiyo su amma taƙi binsu,har fawan sae da ya leko yayi mata magana amma ko kallo ma bai isheta ba,

A ƙarshe suka ƙyaleta,suka bi bayan fawan ya shiga babban falon tare dasu,

gaba daya hankalin kowa ya dawo kansu,musamman Abusufyan dake zaune agefen abbansu,ji yake kamar ya tashi ya rungumosu ajikinsa,su twins kuwa dasu irfan zuba masu ido kawai sukayi suna kallonsu,haka Omar da Abbas da kuma hajiya azeema,kowa burinshi yaran su tabbata ƴa’ƴan abusufyan ne,duk sun ƙagu suji cewa yaransa ne,tabbas da ba ƙaramin farin ciki zasu ji ba,

Sgr dae tunda ya ɗago ya kallesu ya gane cewa babu sehrish acikinsu,bayan yaji cewar dukansu Abbansu yace a kira mashi,

Abbansu ne yace”Ina ɗayar take ne?ni bana gane ma wacece babu acikin ku!

Omar yace”waɗannan hosana da jahad ne!sehrish ce babu acikinsu,”

Abbas yace”Masha Allah,gaskiya banta6a ganin yara masu kamanni irin nasu ba,Allah dae yasa mu tabbatar da abunda muke hasashe akansu….’

“Meya hanata zuwa”?muryar Sgr ce ta karaɗe kunnuwansu,har sae da su jahad suka ɗan tsorata dashi,dama tunda sukazo hankalinsu ke kanshi saboda launin kwayar idonshi ba ƙaramin ɗaukar hankali takeyi ba,

Fawan yace”Ba yadda bamu yi da ita ba,amma tace bazata zo ba,kamar tana cikin damuwa sosai,ko kallona fa batayi ba,da naje kiransu,’

A zafafe Sgr ya yunkura tare da miƙewa daga saman kujerar da yake ya nufi sashensu Azmee,

“Kuzo ku xauna kusa dani,”hajiya azeema ce tayi masu magana yayin da takeyi masu nuni da hannunta,

 

Hannunsu ruƙe cikin na juna,suka ƙarasa wurin sofa ɗin da hajiya azeema take,a gefenta suka zauna,duk jikinsu asanyaye saboda basu saba dasu ba,tunda suka zauna jahad ke kallon Abusufyan,saboda tunawa da maganar gwaggon katsina da tayi ɗazu na cewa shine mahaifinsu,kanta ya gama ɗaurewa,tashiga tambayar kanta taya akai hakan zata kasance?meke shirin faruwa da rayuwarsu ne?dama suna da dangi ne?wai su wanene su?ya akai rayuwarsu take a birkice ne?

tambayoyi iri iri tashiga yi ma kanta waɗanda bata da amsar su,

ƙasa ƙasa hosana tayi da muryarta tare da kai bakinta saitin kunnan jahad tace”Wancan mutumin sai kallonmu yake yi jahad,ni duk nabi na tsargu wlh,tsoranshi nake ji,shi da wannan kyakkyawan mai wasu kalar kwayar idanu kaman aljani….’

“Dan Allah hosana ki daina mun magana a kunne na,wai ke bakya ganin mutanene kuma duk idanunsu na akanmu,ni kaina atsorace nake wlh,yaya Omar kaɗae nake kallo naji dan sauki,da ace baya a wurin nan da tuni na gudu…’jahad ce tayi wannan maganar,cikin raɗa tayi mata ita don kar aji su,

 

A lokacin da Sgr ya ƙarasa bedroom dinta,tura ƙopar yayi tare da faɗawa ciki,tsayawa yayi yana kallonta,ta takure kanta,jikinta sae kerma yakeyi yayin da hawaye ke saukowa daga cikin idanunta,sam bata lura dashi ba har sae da yayi gyaran murya,a firgice ta wurga idanunta akan fuskarshi,gabanta ne taji ya faɗi rass,nan take kermar jikinta ya ƙaru sosai,

“Taso muje”!babu wasa a fuskarshi yayi maganar,girgiza mashi kai tashiga yi tana cewa”bazan iya tafiya ba,ƙafafuna ciwo suke yi mun,dan Allah kuyi haƙuri ku ƙyaleni,inji da abunda ke damu na,’

Abun ya ɗaure mashi kai,yadda take yi mashi jayayya,tabbas akwai matsala hakanan dae yarinyar bazata ƙi bin umarninshi ba,

Bai tsaya wani 6ata lokaci ba,ya ƙarasa shiga cikin ɗakin har saman gadonta ya bita,sai faman ja da baya takeyi,gaba daya ya ɗaukota tare da azata asaman kafaɗarshi ya fito da ita,sai kuka takeyi mashi tana cewa ya sauketa ita bazata je ba,su rabu da rayuwarta,suna ƙuntata mata,har bugun bayanshi ta dinga yi da hannayenta don ya sauketa,duk yana jinta,

 

tashin hankalin da ba’a sama shi date!

 

“Ga babban yaya nan ɗauke da sehrish din daman nasan sai dae ya ɗaukota,”acewar fawan,jin sautin kukanta yasa kowa yakai hankalinshi wurinsu,abun ba ƙaramin ɗaure masu kai yayi ba,ƙiri-ƙiri tana gudun ƴan uwanta,bayan duk alamu sun nuna cewa su ɗin fa ƴan ukune,

 

Koda Sgr ya ƙaraso wurinsu, a tsakiyar inda kowannansu yake,sai ya sauko da ita,Kamar dama jira takeyi ya sauke ta ƙasa da gudu ta kama hanya zata bar wurin,aikuwa a zafafe ya damƙo waist ɗinta da ƙarfi ya maido ta jikinshi,

Har Abbanshi na cewa”ka bi ta a hankali don Allah,ta tsorata sosai,bansan meke damunta bane, ko ƴan uwan nata ne ke batasan gani “abusufyan kuwa runtse idanunshi yayi,har cikin ranshi yake jin soyayyar yaran,

Cikin shessheƙar kuka take faɗin”Na bani,na shiga uku!Na lalace!dan Allah ku rabu dani!ku barni na tafi, banason ganinsu!ni ba ƴan uwana bane!ciwon kai suke sani idan ina kallonsu,raɗaɗi nake ji acikin zuciyata kamar ana ƙonata….”

Hankalinsu ba ƙaramin tashi yayi ba jin abunda sehrish ke cewa,yanayin yadda take maganar zai tabbatar maka da cewar da gaske take tana jin duk wani abu da ta faɗi,musamman Sgr daya ruƙota,yaji jikinta da wani irin Zafi,har shi kanshi zafin na shafar jikinshi,

Abusufyan ne yace”kuyi mata addu’a don Allah,zai iya yiyuwa akwai sihiri ajikinta,wani zai iya shiga tsakaninta da ƴan uwanta saboda ni shaidane akan yadda suke son junansu!nagani da idona,basa rabuwa da junansu kullum suna manne da juna,banta6a ganin ƴan uwa masu son junansu ba irin yaran nan,tun kafin su mallaki hankalinsu suke tsananin son junansu…..’

Cike da mamaki Abba yace”meyasa kake tunanin cewa akwai sihiri ajikinta?

 

kowa ya kasa kunne yana sauraronshi,

“In har da gaske sune ƴa’ƴana kamar yadda nake hasashe to tabbas an shiga tsakaninsu ne,saboda mutumin da suka taso awurinshi,nayi bincike akanshi,bama haka ba shi da kanshi ya rabani da bibiyar rayuwarsu da nake yi,kowa zaiyi mamakin taya nabar yaran rayuwarsu ta wulaƙanta batare dana taimaka ma rayuwarsu ba,ko kuma na sanar ma wani daga cikin dangina don a taimaki rayuwarsu,ba laifina bane tursasamun akayi……..’

Kasa ƙarasa maganar yayi saboda hawayen da suka shiga kwaranyowa daga cikin idanunshi,

Abbas yace”Akwai sauran labari kenan, bari mu gyara zama don a idasa warware mana komai,”

 

ɗagowa yayi da idanunshi da suka yi jawur har sun dan fara kumbura ya kalli sgr tare da cewa”idan ba damuwa,inaso ka zauna tare da ita akusa dakai,saboda ka ruƙeta karta gudu,in yaso sai kayi mata addu’ar koda bata dawo hayyacinta ba,zataji sauƙin radaɗin ciwon kan da takeyi,

“Okey,”ya amsa tare da samun wuri ya xauna,asaman laps ɗinshi ya zaunar da Sehrish,sosai ya ruƙota jikinshi,tunda ta kwantar da kanta asaman wide chest ɗinshi,numfashinta ya fara daidaita,a hankali kuma zafin jikinta ya soma raguwa,saitin kunnanta yakai ƙaramin bakinshi yana karanta mata addu’o’i,bugun zuciyarta ne ya soma raguwa,jikinta kuma ya rage kermar nan da yake yi,

“Ina gwaggon take ne?naga bata fito ba inaso ayi komai agabanta tare da Dr haris kuma”abusufyan ne yayi maganar yana kallon Abban nasu

Fawan ne ya kuma miƙewa tare da cewa”Bari naje na kirasu,’

cike da zolaya jahan yace”Messenger,aikinka na kyau,”murmushi kawai yayi tare da wucewa ciki,ae yau ji yake kamar ya zuba ruwa ƙasa yasha don murna don kuwa ranshi ya gama bashi cewa su jahad din yan’uwansu ne.

Ba da jimawa ba,sae ga Gwaggon katsina ta fito har yanzu undin nan ne ajikinta Allah ma yasa irin dogon nan ne mai kauri,tana biye da bayan fawan tana dungurin keyarshi tana cewa”Shegen bisa,da kanshi kamar na tamola,baccin ma baza abar mutun yayi ba,matsalar mutun yazo gidan jikoki kenan duk subi su addabi rayuwarshi…..’

Muryar Abba ce ta katse ta da cewa”gwaggo ku samu wuri ku zauna,magana ce mai muhimmanci zamuyi,”

Har zata zauna idonta suka sauka karaf akan Sehrish dake zaune asaman laps ɗin Sgr,hankali tashe tace”mun shiga uku!yanzu agabanku ake wannan aika-aikar amma babu wanda ya tanka?hosana ce ko jahad?wacece acikinsu?wlh bazan bari a lalatamun ƴa’ƴan Abusufyan ɗina ba,dasu zamu koma katsina ayau…….’

..da sauri Haris ya katseta da cewa”Dan Allah gwaggo kidaina wannan sambatun naki,bakiji abunda abba yace ba!magana mai mahimmanci za’ayi,ki samu wuri ki zauna kuma kiyi shiru,’

Wurga mashi harara tayi kafin ta wuce tare da samun wuri ta zauna,shima haris ya zauna agefenta,sai da suka xauna sannan ta lura da hosana da jahad dake zaune gefen hajiya azeema,

Da sauri ta mayar da idonta kan sehrish don taga wacece ita,ko dae idanunta ne suka fara samun matsala don taga kamar kamanninsu iri ɗaya sak,

“Harisu,kana ganin abunda nake gani kuwa,wai yaran nan har nawa ne masu fuska iri ɗaya”?

A dan ƙule haris yace”Eh,su uku ne!ko kinmanta su nawa ne,na faɗa maku Abu ta haifa!wannan ae cikon ƴar ukun tasu ce,’

“Oh to,yanzu nagane”ta fadi tana faman gyara zamanta,

Sae da kowa ya natsu sannan abusufyan ya kalli su hosana da jahad yace”Ya sunan mahaifiyarku ne?kuma waye mahaifinku”? Yayi masu tambayar ne don ya fara tabbatar da cewar sune ɗin dai dagaske,

Har suna haɗa baki wurin cewa”Sunanta Zainab,amma anace mata abu ƴar buzuwa,sannan mahaifinmu kuma sunanshi Sayyadi…….’tunkan taƙarasa maganar kowanne daga cikinsu ya shiga sakin murmushi,jin sun ambaci dai dai da sunayen da abusufyan ya gama bada labari akansu,tunkan aje ko ina suka tabbatar da cewar sune dae ƴa’ƴan abusufyan ɗinsu,

“Ina mahaifiyarku take yanzu”?ya kuma tambayarsu,

Jahad tace”bamu son inda take ba,amma koma a ina take bata acikin hayyacinta,lokacin da tabarmu tasamu ta6in hankali,’

jiki asanyaye ta ƙarasa maganar,

“Yanzu zaki iya bamu labarin abubuwan da suka faru arayuwarku gaba daya,har izuwa lokacin da kuka rabu da junanku”?

ɗaga mashi kai tayi alamar eh,

Kafin abusufyan ya ƙara cewa wani abu,Abba ya katse mashi hanzarinshi da cewa”Yakamata,ka fara sanar dasu game da alaƙar da take tsakaninka da mahaifiyarsu”

Jinjina kai abusufyan yayi kafin yace”zaku iya tunawa da mutumin daya ta6a zuwa wurinku lokacin kuna ƴan ƙanana,har ya ɗauke ku hoto a wayarshi?lokacin da zan tafi kuka dinga kuka kuna cewa na tafi daku baku son zama da mahaifinku”?

A razane hosana da jahad suke kallonshi yayin da suke ƙoƙarin tunawa da wannan lokacin……’

Murmushi abusufyan yayi tare da cewa”nasan ba zaku iya tunawa da wannan lokacin ba!,amma mun sha haɗuwa daku wani lokacin kuna ku kadae,wani lokacin kuma tare da mahaifiyarku……..’

Batare da 6ata lokaci ba,abusufyan ya basu labarin rayuwarshi da abu a takaice yadda zasu fahimta,sai lokacin suka san asalin mahaifinsu da kuma kakansu baba buzu daya rasu,da kuma irin rayuwar da abu tayi tare da abusufyan kafin su rabu,ta auri ya sayyadi,sunsha kuka sosai,aransu suna jin ƙuncin abunda mahaifiyarsu tayi masu,ashe duk itace taja masu bala’en da suka fuskanta,

Karanta>>> Dalilin Daya Sa Matan Hausawa Ke Tsufa Da Wuri Da Zarar Sunyi Aure

Kowa yayi shiru na wani lokaci suna sauraron kukan dasu hosana da jahad sukeyi gwanin ban tausai,banda sehrish wanda tayi lamo ajikin Sgr,duk wani abu da suke faɗi acikin kunnanta,amma bata ɗago ta kallesu ba,har yanzu dae bata dawo dai dai ba,

Daƙyar su Omar suka lallashe su,kafin daga bisani Abbansu yace”Jahad yanzu ke muke sauraro!munaso muji irin rayuwar da kukayi a hannun mutumin nan!”

Duk wannan abun dake faruwa akan kunnan Haroon,ya jima da shigowa batare da sanin kowa ba ya la6e yana jin labarin da abusufyan ke ba su jahad,na rayuwarshi da mahaifiyarsu,hankalin shi yayi mugun tashi,gaba ɗaya ya tsorata ya rikice,wata irin zufa ce tashiga gangarowa a fuskarshi,bakomai ya razanar dashi ba face ganin Ƴan ukun gaba ɗayansu sun haɗu acikin gidan kuma ga Ubansu da kanshi ya gane cewa ƴa’ƴanshi ne wannan alama ce dake nuna cewar asirinsu ya kusa tonuwa,

Tuni zufa tasoma tsastsafo mashi acikin jikinshi,sharkaf ta jiƙa t shirt ɗin jikinshi duk kuwa da ba zafi,jan ƙafarshi yayi tare da lalla6awa cikin sanɗa ya wuce bedroom ɗinshi,

Zagaye ya shiga yi acikin ɗakin,gaba ɗaya jikinshi sae faman rawa yakeyi,yama rasa inda zai tsoma kanshi kamar wani zautacce haka ya koma,a fusace ya dunƙule hannunshi tare da kai ma madubin ɗakin naushi,nan take glass ɗin jikinshi ya tsastsage ya zube ƙasa,

Hannunshi ya shiga fitar da jini,ko kaɗan baiji xafin hakan ba,raɗaɗin da zuciyarshi ke yi mashi yafi raɗaɗin glass ɗin daya shige shi,

Da ƙarfi ya furta”That’s impossible!ƙaryane ba gaske bane!!wlh bazan rasa rayuwata ba!dole na rayu ko da kowa zai rasa ranshi,zanyi komai zan yi don ganin na kwaci kaina!!

Yana magana yana sakin huci,idanuwan nan nashi sunyi jawur dasu luhu luhu,

Cikin sauri ya zura hannunshi tare da ciro wayarshi daga cikin aljihun jeans dinshi ya danna ma wata number kira,cikin sa’a aka ɗaga kiran!

Wata irin muryace ta karaɗe kunnanshi mai tsoratarwa”Ba saida nace maka karka sake kira na ba!Tun farko ya mukayi dakai?

hankali atashe haroon yace”Ni ba wannan maganar tasa na kira ka ba!ka faɗamun taya akai kukayi gangancin barin yaran nan har suka haɗu da danginsu!!!!!!!

“Wasu yara kenan!”

Haroon yace”Ƴan ukun nan!na gansu da idona acikin gidan nan!yanzu haka gasu can a falon gidan nan sun taru suna jin labarin rayuwar yaran nan!

Nan take muryar mutumin da suke waya dashi ta canza,

“Wai kana nufin hosana!jahad!sehrish!duk sun haɗu anan cikin gidan naku ko mi”?

A ƙule haroon yace”Eh mana!akansu nake magana,wlh kowa yayi ta kanshi!saboda yarinyar nan dole ta ambaci sunanka acikin labarin da zata bayar kuma kasan cewa muddin waɗannan namun dawan guda biyu sukaji mugayen abubuwan da kuka aikata dole su binciko ka duk inda ka shiga kuwa,kuma koda a ƙarƙashin ƙasa ka 6oye,!

Karanta>>> Maganin Karin Hips Mai Sauki Ga Mata

Fashewa da dariya mutumin yayi kafin ya tsagaita da yin dariyar yace”Baza su ta6a iya gano ni ba!nafi ƙarfinsu nesa ba kusa ba!zanyi amfani da ƙarfin sihirina wurin dakatar da tunaninsu…….’

Tun kan ya ƙarasa maganar haroon ya daka mashi tsawa tare da cewa”Ya Isa haka!!zancen ku iri ɗaya da ita!daga kai har ita daga anyi magana sai kuce ƙarfin sihiri,zakuyi amfani da sihiri ku asirce mutun!angaya maku cewa kowane lokaci sihiri ke yin tasiri ne!sam babu Allah aran kowannanku don haka babu wanda zai tsira acikinmu!ko ka manta da irin mutuwar da mahaifinku yayi ne?duk wani sihiri da kuke taƙama dashi ae a wurinshi kuka gado shi,akan idon kowannanku yayi mummunar mutuwa sakamakon farmakar shi da kakanmu salahuddeen sukayi,ku baku da tunani ne?me yasa shi a lokacin baiyi amfani da ƙarfin sihirin shi ba don ya hana kanshi mutuwa?ko don saboda ya tsufa ne yasa nashi sihirin baiyi aiki bane?

 

Gaba daya haroon ya rufe shi da faɗa ta inda yake shiga batanan yake fita ba,ba don komai ba sai don saboda yasan cewa bazai kai labari ba,sun ja mashi bala’e da masifa,

Wata irin gigitacciyar tsawa mutumin ya daka mashi wadda tayi silar dawowarshi cikin hayyacinshi,yayi tsit yana faman sauke ajiyar zuciya,

“haroon!ya kamata ka iya bakinka!kasan dawa kake magana!duk wannan tada jijiyoyin wuyan da kakeyi bazai hana kaga mutuwarka ba!zaifi kyau ka mayar da hankali wurin ganin ka sama ma kanka abokan tafiya,kada ka yarda wannan abun ya tayar maka da hankalinka,babu wanda ya isa ya ta6a ka acikinsu,!abu ɗaya kawai mukeso awurinka!muddin ka aikata hakan komai yazo ƙarshe zaka tsira kuma muma zamu tsira,sannan farin cikin gidansu zai tarwatse na har abada,………………….’

Karanta>>> Ina Mata Masu Fama Da Rikecewar Al’ada Ga Magani Da Izinin Allah

Natsuwa haroon yayi yana sauraron bayanan da mutumin yake kora mashi,sae amsa mashi yake yi da to,toh

Alamar ya amince da abunda suke so ya akaitan,

Acan main palour ɗin kuwa,kowa ya kasa kunne yana sauraron Jahad,

Back to top button