Description/Story:
Rubutacciya! Complete Hausa Novel Document Written By Samira Harun
Description
_Bismillahir- rahamanir-rahim._
*1*
*WANI LOKACI*
Da gudu yayi niyyar fitowa daga falon dan neman agaji, ba dan biyayya da kuma sanin *Mu’az Mika’il* mahaifin sa bane, da a wannan shekarun nashi da ya fara kama ƙasa tsabar ƙarfi, da zai dambatu ne da shi komai girman sa, amma har yau har yanzu bai wuce yayi zaune mahaifin shi na shi na masa dukan mutuwar da ya saba yi masa ba a duk lokacin da matar tasa wato *matar babanshi* ta kawo masa tsegumin yayi wani laifin ko da kuwa bai yi ba.
Duk da ya so zillewa ya bar musu gidan, amma kasancewar mahaifin nashi wato Mu’az ƙaƙƙarfan matashi ne da bai kai a kira shi da tsoho ba duk da shi ne ɗan sa na farko sannan ya haura shekara arba’in da kaɗan, bugu da ƙari soja ne da ko a cikin sojawan yake amsa sunan Sergent sannan shugaban tawagarsa.
Ƙafar matashin yaron da a ƙalla zai kai shekara 14 ya cabko, hakan ya tilastawa yaron wata irin faɗuwa ya dabsu da ƙasa tare da gwara kan shi da murfin ƙofa, cikin raɗaɗin azaba yayi waa razananniyar ƙara ya dafe kan nashi yana kiran “Wayyo Allah na, Wayyo Baba kaina, kaina ya fashe.”
Bai saurari magiyar da yake masa ba, tamkar yana jan wata dabba haka ya dinga jan ƙafarshi har saida ya ja shi zuwa ɗakin baccinshi ya rufo ƙofa, wannan ɗamarar (belt) tasu ta sojawa mai ƙarfin ikon ladabtar da duk wanda tsagerancinshi bai kai matakin gawurta ba ya cire daga ƙugunshi, kafin ka ce kwabo ya shiga zabgawa *Jabir* da tunda ya ji ya rufo ɗaki ya tashi zaune yana faman haɗewa jikin gado yana bashi haƙuri kan laifin da bai san ya aikata ba, dan shi dai yna shigowa gidan ya ji mahaifin nasa da bai san ma ya dawo daga daji ba ya ce ya wuce uwar ɗaki, shi kuma da ya ji haka yasan ba sirri ko hirar arziƙi zasu yi ba, Shiyasa ma ya nemi tserewa ya bar gidan.
Dukansa yake da wannan ɗamara, ba wai mutum mai rai ba, ko gawar wannan dabbar wato jaki ce ake ma dukan nan, wanda ke nesa ma kaɗai zai iya tsayawa yana zubar mata da hawaye, bare kuma idan kana jin gunji da sautin kukan da kai ka tabbatar yaro ne matashin da ya wuce wannan dukan. Tsabar ɗorawa kai wahala shi kan shi mahaifin nashi a wahalce yake matuƙa, dukan namiji da ya kai shekaru sha huɗu zuwa sha biyar hatsari ne, Shiyasa ma yake ta gumi kuma zaka rantse dambatuwa ne suke idan kana jin su daga waje saboda irin kwaramniyar dake fitowa daga ɗakin, dan Jabir dai ba zaune yake wuri ɗaya yana duka shi ba, ƙoƙarin kare jikin shi yake da riƙe ɗamarar, hakan ya jawo idan ya riƙe ɗamarar da kyau har ya kan kasa ƙwatarta sai ya dinga harbinshi da ƙafa yana kuma marinshi ta ko ina yana faɗin “Saki, saki nace, ba zaka saki ba? Ka rainani ko?”
Cikin azaba za ka ji Jabir yana cewa “A’a Baba, a’a wallahi, zan saki to, amma kayi haƙuri karka dakeni dan Allah, ka yi haƙuri ba zan sake ba koma menene.”
Suna tsaka da wannan tirƙa-tirƙa aka ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin, cikin haki da masifa ya kalli ƙofar yace “Wa ye?”
Daga waje muryar matar tashi ita ma da yanayin masifa tace “Ni ce, ka buɗe ɗakin nan ku fita waje Baban *Uzeifatu*, wallahi tallahi idan kuka min ɓarna a ɗaki sai ka biyani, kaga fa haka kwanakin baya kuke karya min gado, da ƙyar ma ka samo min mai gyara, dan haka ku fito min daga ɗaki, sannan hayaniyarku tana hana min yarinya bacci.”
Tabbas hargagin da take masa ya kai yasa ya haɗa da ita ya jibgeta, to amma ba zai iya hakan ba dan ita ce Hajiar gidan, ɓacin ranta daidai yake da rugujewar tattalin arziƙin gidanshi, hakan yasa tamkar wni ɗan zakin da bashi da haƙora ya amsa mata da” Shikenan, kiyi haƙuri to, ina fata dai Uzei bata tashi ba?”
Duk yayi maganar ne yana buɗe ƙofar ɗakin daya rufe da makulli, hakan yasa Jabir ma tasowa yana shahseƙa da sosar jikin shi suka fito, zaune suka same ta tana jijjigar Uzei da take so tayi bacci, kusanta ya zauna yana ɓalle botiran rigar shi tare da share gumin da yayi.
Jabir take Harare da ya kama hanyar fita daga falon, ganin hareren da take ma yaron duk da ɗan cikin sa ne shi ya haifi abun shi yasa shi daka masa tsawa da cewa “Kai!”
A razane ya dakata yana kallon shi da jiran jin me zai ce, cike da gargaɗi da nuna shi da yatsa yake cewa “Maza ka ɗauki jarkokin nan ka tafi yanzun nan ka debo mana ruwa, tunda ai kasan aikin ka ne amma ka tafi yawon ka baka ɗebo ruwan ba.”
Da mamaki jin haka Jabir ya kalli *Bara’atu*, ruwa kuma? A kansu aka masa wannan dukan? Bayan bai tafi makaranta ba saida ya cika mata kaf abubuwan da take cewa sai ya cika mata da ruwa tsabar son ta sa ya makara har da kansu jarkokin guda biyu saida ya cika su ya aje sannan ya tafi, duk me aka yi da ruwan? Wannan kallon da yake mata yasa ta daka masa tsawar “Lafiya wai? Ni na saka aikin ne da zaka tsaya kana harara ta? Ka ɓace min da gani malam.”
Zabura yayi sannan ya juya ya fita yana jin uban na faɗin “Za ka gane baka da wayo idan baka ɗauko ruwan nan ba.”
Kallonshi tayi cike da kissa da kwarkwasa tace “Baban Uzei, gaskiya ni yaron nan wallahi ya fara bani tsoro, ina gudun wata rana ya rufeni a ɗakin nan ya zaneni, tunda Kaga kai ba zama kake ba, shi kuma yanzu ya idasa lalacewa duk ya zama wani iri, ni fa ina tunani kamar Jabir ya fara shan sigari.”
A razane ya kalle ta ya maimaita kalmar” Sigari?”
Da son tabbartar masa ta ɗaga kai sannan tace” Ƙwarai.”
” Jabir ɗin?” Ya sake nanatawa don abun a bazata ya z mishi, ko shi da yake ubansa kuma soja sigari bata taɓa birge shi ba, ba ma shi ba har da wasu daga cikin milyoyin sojoji, amma a ce ɗansa? Lura da kamar kokonton maganar ta yake yasa ta sake cewa” Kai baka ga idanun shi kullum jajir dasu ba kamar na mai shan wiwi, ga wata rama da yake kamar ana miya dashi, ni dai gaskiya ka raba ni zama da yaron nan.”
Dafa kafaɗarta yayi a tausashe yace” Ki ƙara haƙuri kinji Bebe, idan fa kika duba shekara nawa ta rage ma na kaishi makarantar horon soja shi ma ya zama kamar ni, ai shekarun da kikayi dashi a baya yanzu ko rabin rabinsu ba zaku yi a tare ba.”
Turo baki tayi gaba tana cewa” To ya koma can wajen su Mama da zama mana, dan nidai n’a gaya maka tsoro yake bani yanzu, ga rashin kunya da ya ƙara koya bana saka shi aiki kai tsaye yayi sai na sha wahala.”
Cikin rarrashi yana shafa wuyan ta yace” Bébé ke fa kinsan komai, Mama ba zata taɓa haƙuri ta karɓi Jabir ba, kin fi kowa sanin muhawarar da aka tafka kan Mama ta karɓeshi bayan *rasuwar mahaifiyarshi* tun yana da shekara *huɗu* a duniya, bare yanzu da ya girma ya isa ya ma ka shi komai. Kiyi haƙuri duka Bebe, ina tabbatar miki zan ja masa kunne, ba zaki sake yi masa magana sau biyu ba idan zai miki abu, kin ji?”
Taɓe baki tayi tace” Shi kenan.” A ranta kuma ayyanawa take _” Ina dalili ina ɗan mafari, an haɗani da jaraba tun ina amarya ko amarcina ban ci da kyau ba, to Kakar sa ma ta ƙi shi bare ni da ban haɗa komai dashi ba? Sa’ar sa ɗaya bamu zauna da uwar ta sa ba wallahi, da Ace ta min ba-daɗi da a kanshi zan rama wallahi.”_
*Jabir* kuma na fita jarkokin ruwan guda biyu ya ɗauka hannun shi dafe da kanshi dake masa mugun ciwo mai raɗaɗi, a daddafe yake tunkurarar wurin ɗiban ruwan dake ɗan nesa da gidan amma ba sosai ba, tsoron hanyar yake ji sosai saboda sabuwar unguwa ce mai kama da dajin Allah, wurin nada haɗari sosai musamman yanzu da zafi yayi yawa, haka yasa ganin kunama da maciji a wurin ba wani abu bane, shi kanshi ya kashe wa matar babansa kunama tafi a ƙirga.
Tashin hankalinshi yanzu shi ne jiya tun da rana ba wanda yaje fanfon nan ɗebo ruw saboda macijin da aka gani a wuri kuma an tabbatar mai dafi ne, shi ne yanzu ba tare da tunanin komai ba mahaifinshi ya ce ya zo ya ɗiba, bayan ya san ya cika mata komai da ruwa.
Da wannan tunanin yake tafe yana lumshe idanunshi saboda kanshi har yanzu zugi yake masa, sannan kuma idanunshi da kularshi duk suna kan hanyar ne, babu hasken fitila ko ɗaya a dai nan layin nasu idan ba ka shiga kwanar gidan Alhaji *Kabiru* ba, ba dan babu wuta a gidan su ba sai dan unguwar ce babu mutane sosai, hakan ke haifar da duhun dake samar da rashin amince ga ma’abocin fitar dare a wannan unguwa.
Ga dai ƙofar gidan a zai ɗibi ruwan a rufe alamar sun kwanta, ba zai yarda ya koma babu ruwan nan ba, dan haka gwara ya tashesu dan ya ceci kanshi daga dukan mutuwar da za’a mishi a gidan nan, dan haka a nutse kamar yadda halayenshi da ɗabi’arshi suka zama masu sanyi ya dinga bubbuga ƙofar tare da yin sallama, dan ko da firgici ya sa sun saka tasowa sallamar tashi zai iya saka wani daga cikin mutanen gidan ya ɗauki muryarsa musamman ma dai mai gidan malam *Sule* da yaron gidan *Mujittafa*.
*LOKACIN* da yake buga ƙofar nan daga cikin manyan gidan masu hankali da sanin ta kamata duk idanunsu biyu, sun sa ƴarsu gaba ne suna tattauna wata matsalar tasu da ta kunno musu kai a daren nan, wanda su dai iyayen suke ganin ba dan ƴar ta tsaya kai da fata kan cewa za ta iya ba, to fa da ba zasu lamunce b dub da wasu dalilai.
Maganar son auren *Ummu Kulsum* da Alhaji Kabir wato mai gidan da suke ciki zaune ya zo musu ya zo musu da ita ta girgiza su, mutum kamar shi? Mai tarin dukiya da alfarma da kuma suna, sannan mai shekarun da suka ninka ninkin ba ninkin na Ummu Kulsum, sannan mai mata uku cif sannan wayayyun mata, yana da yara da jikoki bila adadi, a hakane zai ce zai auri ƴar su mai shekara sha bakwai a duniya. Ina! Wannan abu ne da gaskiya da kamar yiwuwar shi.
*Mariƙin* (Ba su ne asalin iyayen ta ba) na Ummu da ya ji ana ci gaba da buga ƙofar ne ya miƙe yana dafa kafaɗar Ummu Kulsum ɗin cikin rarrashi yace “Kinga daina kukan, da safe zamuyi magana kin ji, n ji ana buga ƙofar gida ne zan je na duba.”
Cikin sanyayyar muryar ladabi Ummu Kulsum dake daf da *uwar marayu* kamar za ta fashe da kuka tace “Baba, wallahi na gaya muku da zen aure shi, na yarda ina sonshi Baba, idan ma shi ne ya zo ku ce masa na amince zan aureshi.”
Tsura mata idanu yayi takaci na baibayeshi kamar zai wanke mata fuskar ta da tafi, sai dai kafin ya ce mata wani abu uwar marayu data gane me kallon shi ke nufi gareta ta ja hijabin Ummu har saida tayi kamar za ta kwanta a jikin ta, cike da son ta dawo da ita hayyacinta cikin ɗaga murya tace “Wai ke kanki ɗaya kuwa? Ya daga ji magana kawai za ki wani damemu da kina sonshi za ki aureshi, wannan ɗin tsaranki ne a aure ko shekaru? Kin ma hango abinda muke hango miki ne? To bana ciki da iskanci.”
Sai kuma ta kalli malam Sule dake kallonsu tace “Malam, ka je ka duba Kaga waye a daren nan? Na ji har yanzu bugawa ake, Allah dai yasa lafiya.”
Ajiyar zuciya ya sauke ya nuno Ummu da yatsa yace “Ki ce ta shiga taitayinta.”
Yana fita Ummu da ta bishi da idanu tayi saurin duban Maman nata, duk da ba ita ta haife ta ba, amma ita ta raineta tun tana jaririya, yadda aka bata tarihinta shi ne, an ce a *bola* aka tsince ta an jefar da ita, shi ne *Amina* ta ɗaukota ta kawo ta gidan ta ta raineta har yanzu da take shekaru *sha bakwai*, sun bata tarbiyya iya iyawarsu, basu bambamta ta da yaran da suka haifa ƙwaya biyu ba rak a duniya, hasalima *Lukman* ne kawai gaba da, bayan ta fara tafiya suka haifi *Nabila*.
Hannun uwar marayun ta kamo ta riƙe tana jijjigawa cikin taushin muryar da ya zam halittarta ce take faɗin “Mama, ai kinsan ban taɓa neman abu a wurin ku na rasa ba ko? Mama ina son Alhaji Kabir, ina so na aure shi Mama, dan Allah ki wa Baba magana ya amince.”
Hannu uwar marayu ta ɗaga na damanta, kafin Ummu Kulsum ta ankara ta zabga mata shi a fuskar ta ranta a matuƙar ɓace, da sauri ta dafe kuncin ta tare da kallon maman nata tana zazzare idanu, cikin ɓacin ran da ba kasafai suka fiya gani na uwar marayun ba ta miƙe tana gyara ɗaurin kallabinta, ɓangare ɗaya kuma cikin faɗa take kallon Ummun tana cewa “Ummu dama a tarbiyar da na miki akwai ranar da zaki iya tsare ni da mahaifin ki kina mana magiyar mu miki aure? Dama ban sani ba har kin yi buɗewar idanun da zaki nemi yi mana kuka kina faɗa mana gaba da gaba kina son Alhaji Kabir sannan a aura miki shi? Ba ki ji kunya ba don Allah? Ummu idan ni kin ɗaukeni ƙawarki, shi Babanki abokin wasan ki ne?”
Girgiza kai ta yi cikin shasheƙar kuka duk da bata fara hawayen ba tace “A’a wallahi Mama, ba raina ku nayi ba, kiyi haƙuri.”
Cike da bayar da umarni uwar marayu tace “Da kyau to, idan Babanki ya shigo ki gaggauta bashi haƙuri, sannan maganar auren ki da Alhaji Kabir babu ita, dan baku dace da juna ba ko kaɗan, kin gane.”
Ƙurawa uwar marayu ido tayi tana kallon ta zuciyar ta fal da tunanin _”Me yasa ba zata fahimce ta ba? Me yasa ma dukansu ba zasu fahimta ba?”_
Ita ma *ba son shi take ba*, yadda taji suna tattauna matsalar a tsakanin su da butulcin da suke shirin yi masa matsayinshi na wanda ya dubesu ya basu masauki, gidan nan da suke ciki hada wutar lantarki ga kuma ruwa, ko ɗaya ba sa biyan ko sisi na wannan abubuwan, dan ruwa ma gabaɗaya unguwar anan ake ɗiba, sannan ga jarin da ya ba wa Baban nasu yake juyawa har suna samun abinda suke ci. Ita kanta ko da suka tsince ta suka kawo ta anan gidan ta gansu, a ƙalla shekarar su goma sha tara a gidan nan, bai taɓa cewa ku tashi ina buƙatar wurin ba, shi dai kawai ana kawo masa wasu kayayyakin da suka shafi kasuwancinsa ana aje masa a mangazar (store) dake cikin gidan.
Hakan yasa take ganin bai kamata a ce yau ya zo musu da butun son aurenta ba à ce sun ƙi amince masa, ita dai a yadda ta san ba su suka haife ta ba, ba za ta yarda Hakan ya zamar musu matsala ba, dan tana ji a ranta idan har basu amince ba, to zai iya tashinsu daga nan ɗin, kuma ko da m halayen da suka sanshi da su na karamci basu barshi ya tashe su ba, to ai da kunya suma su ci gaba da zama, to idan sun tashi in zasu koma? Baban su bai d halin da zai iya biyan kuɗin hanya da wuta da ruwa, Hakan kuma zai sa rayuwa ta sake tsananta a gare su ta musu zafi fiye da yanzu.
Uwar marayu na shinfiɗa a fargajiyar gidan malam ya dawo, da kulawa take tambayar shi “Malam waye yanzu a daren nan?”
Saida ya sauke numfashi ya bata amsa da “Wallahi yaron nan ne Jabir, ruwa ne ya zo ɗauka.”
Da mamaki a fuskar ta sosai tace “Ruwa kuma? Yanzu a daren nan?”
A kasalance yace “Wallahi kuwa, ya ɗauka ya tafi, na bar mishi fanfon a kunne, dan ya ce Babanshi ya ce sai ya cika musu komai da ake zubawa ruwa gidan.”
Ita ma ajiyar zuciya ya sauke tana girgiza kai sanda take ƙoƙarin ɗaura gidan sauro tace “Bawan Allah, to ko da safe fa anan ya ɗibi ruwa.”
Girgiza kai yayi cike da jimami yace “Ke dai Allah ya kyauta, amma wannan mahaifi nashi kam sai du’a’i, dan yanzu haka in da kin ganshi wallahi da alama dukanshi ma yayi, dan har fuskar shi ta kumbura, ya ce min kanshi ke ciwo idan ina da magani na bashi, ni kuma na san ba lallai a samu ba a cikin gida, sai dala ashirin na bashi na ce ya si ya sha.”
Cike da tausayawa uwar marayu tace” Bawan Allah, Allah ya jiƙan mahaifiyarshi, shi kuma Allah ya wa rayuwarsa albarka.”
“Ameen.” Ya faɗa yana cire takalmin shi ya bi ta kan shinfiɗar ya shiga cikin ɗakin, kusa da Ummu ya sake yin zaune yana kallon ta cike da kulawa yace “Kuka kike yi Ummu Kulsum?”
Da sauri ta girgiza kai tace “A’a Baba, dan Allah ka yi haƙuri ka yafe min, na san na ɓata maka rai ɗazu.”
Girgiza mata kai yayi yace “A’a Ummu, ni baki min komai ba wallahi, sai dai ina so ki sani cewa, ke da Alhaji Kabir baku dace ba, Ummu Kulsum ni kaina Alhaji Kabir ya haife ni, saboda babban ƴar sa ma ta girmeni nesa ba kusa ba, kenan kinga akwai tawaya sosai idan aka ce a haɗaki aure da shi, ba zaki mori ƙuruciyarki ba Ummu Kulsum, ni kuma abinda bana fata kenan, ina so yadda na reneki cikin kulawa da kyautatawa, na haɗaki da wanda zai san mutumcinki sannan ya dace dake, ta yadda ko bayan raina ruhina zai samu salamar cewa na barki a hannun da ya dace.”
Ta gamsu ƙwarai da abinda ya faɗa mata, dan haka ta jinjina kai tace” Nagode Baba, nima dama ban hango abubuwan da kuka hango min bane, kawai dai Naji ina so na aure shi ne saboda kirkinshi da nagartattun halayenshi, amma tunda baku amince b na haƙura.”
Zuba mata idanu yayi yace” Ummu, da gaske abinda yasa kike so ki aure shi kenan?”
Jinjina kai tayi tare da kallon shi tace” E Baba, daga gare ku nake jin kuna yabon halayensa da kirkinshi, ni kuma sai naga dama ana son mutum ne don kyawawan halayenshi, sannan ko mutum ya girmeka zaka iya zaman aure da shi indai kana da tabbacin zai girmamaka sannan ya mutumtata iyayen ka.”
Shiru yayi na wasu daƙiƙu, sai kuma ya jinjina mata kai yace” Ummu, kin tabbata tsakani da Allah kike son Alhaji Kabir?”
Sadda kanta tayi ƙasa tace” E Baba.”
Sai kuma ya sake jinjina kai ya miƙe yace” Shikenan, idan sun sake waiwayarmu da maganar zan faɗa musu ra’ayinki, amma idan sun yi duba da abinda na faɗa musu tun farko na nuna ƙin amincewa ta, to nasan ba zasu sake dawowa ba sai dai ya aiko mana ɗan aike cewa mu bar masa gida.”
Da kallo ta bi shi har ya fice sannan ta sauke ajiyar zuciya, tana jin muryar mahaifin nata na tambayar uwar marayu wai har yanzu Mujittafa bai shigo ba? Da e kawai ta bashi amsa ta ji sun ɗauki wata hira. Mujittafa ɗa ne ga ƴar uwar uwar marayu, bayan rasuwarta ta ce a bata tunda mahaifi shi ba zama yake ba.
Daddaɓa Nabila tayi dake bacci duk tayi gumi saboda zafin dake akwai, tashin da za ta yi cikin magagi tana kama zanenta, Hakan yasa abu faɗowa daga cikin zanen nata, Ummu da ta kula da hakane ta sunkuya ta ɗauka tana dubawa.
Ganin kuɗi ne har jaka biyu yasa ta kalli Nabila da tuni ta fice a ɗakin ta faɗa kan shinfiɗar da uwar marayun ta gama, kuɗin ta sake kalla ta kalli Nabila, sai kawai ta nufi wurin kayan islamiyarta ta buɗa littafin ta na hisnul muslim ta saka kuɗin ciki da tunanin Allah ya kaisu safe lafiya ta tambaye ta ta ji ina ta same su? Duk da ta san Nabilar na wasu halaye da kullum kake jin hayaniyarta da uwar marayu, amma bata so a ce gaske ne abinda ta ji zuciyar ta na raya mata, bata fatan à ce ƙin jin Nabila har ya kai wannan matakin.
File Name | Rubutacciya Hausa Novel |
Title | Rubutacciya |
Author | Samira Harun |
Group | Ai Hausa Novels |
Genre | Fiction Story |
Published Date | 29/10/2024 |
File Size | 3.33 Mb |
Format Size | Doc |
Book Price | |
Phone No |
Download Yaroma Namijine Complete Novel Document By Aisha Aliyu Garkuwa
Click the below green button to read the novel online
Proceed with your download by clicking the below button
Some Of Related Hausa Novels
Be With Us
-
- Follow our Facebook Page : Ai Hausa Novels
- Follow our Twitter Page : @ Ai Hausa Novels
- Follow our Youtube Channel: Ai Hausa Novels
DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.